Skip to content
Part 1 of 31 in the Series Auren Wata Bakwai by Xayyeesharthul-Humaerath

Masarautar Benoni

Ihu take da magiya hannunta rike da get din shiga masarautar tana jijjigawa ,”Useni aççe am mi nasta,Hokkam dama je Karshe useni,Don Allah ku barni in shiga Inga Yareema,ku bani dama ta karshe,Miyida misandiri denyo ‘am,Ballite yonki am, Baffana zai mutu, ku taimakawa rayuwata.”

Kuka take na fita a hayyaci, tana fada cikin muryar fulatanci wacce daga ji zaka tabbatar da cewa hausar bata isheta ba.

Daya daga cikin dogaran ya ce, “Karya kike, Mayya anaci, turo ki akayi ki cutar mana da yareema.” 

Yana fada suna janyeta daga jikin get din tana kara kankamewa.

Ta ce, “Aradun Allah,na rantse ba abun da zan wa Yareema, taimakonsa nake nema, don Allah ku barni.”

Bulala suka shauɗa mata wacce ta kara hargitsa mata tunaninta wani irin tsalle tayi ta dire da gudu tana neman hanyar gudu.

Wata farar mota ce kirar MERCEDES-BENZ ML350 ta tawo a hankali.

Adnan dake gefen glass yana hangota cikin sauri ya ce wa Driver ya dakata.

Ya na tsayawa Adnan ya fita yana, “Kee! Kee.”

Idonta a rufe ta daura hannu akai. jikinta na rawa.

Yarinyace da bata zarce shekara Goma Sha hudu ba, sanye da kayan fulani, duk ya fita a hayyacinsa kamar yadda ita ma ta fice a hayyacinta,kallo ɗaya za ka yi mata ka tabbatar da cewa tana cikin wani mawuyacin yanayi,ko dankwali babu akanta, gashi duk a cucure ga yawo da santsi, Dogowa ce siririya mai dirin Fulani,ba a sata sahun farare can can ba kuma baza asata sahun bakake ba,duk da yanayi na tashin hankalin da take ciki hakan bai hana bayyanar da kyawunta ba.

Karasawa ya yi gabanta ganin kamar bata san yanayi ba ya cire hannunta da ta rufe fuska da shi. cike da mamaki ya ce, “You ,?

Cikin isa da kasaita gami da Izza ta jinin sarautar da ke yawo ajinin jikinsa duk wata ilhama da kamala ta bayyana a tare da shi, Prince Adeel Muhammad Rohaan ya fito a motar ya yin da aka bude masa.

Cikin second guda ga dukkan kwayar idon da ya kallesa zai fahimci tsantsar jinin sarauta ne anan wanda Ubangiji ya tsara masa hallita mai cike da kwarjini da Izza, Fatar jikinsa bakine ba irin sosai dinnan ba,baƙi mai kyau da sheƙi,ga idanunsa da suka kasance Sexy Eyes da ke birkita yan mata, yana da fadin kirji da duk wani abu da ‘Ya mace ke bukatar kasancewa ga Namiji ko ince fiye da haka ma.

Kananun kayane a jikinsa kamar yadda ra’ayinsa da tsarinsa yake baya taba sa kayan sarauta har sai in da wani dalili wanda ya zama dole.

Saukarsa kenan daga America wanda ba kowa ke sanin shigarsa da fitarsa ba domin tsaro.

Driver bai ajiyesa a ko ina ba sai daidai kofar part dinsa dake ta bayan masarautar kebantacce wanda ba kowa yasan da nan din ba, yana Parking ya fito ya bude masa kofa cikin hanzari.Tafiya yake tamkar ba zai taka kasa ba.

Shigewa Adeel ya yi kaitsaye ba tare da ko kalli inda Adnan yake ba,bare har ya yi tunanin yi masa magana ko jiransa. Adnan ya gyara tsayuwar sa ya na kare mata kallo ya ce, “What is your Name?”

Zaro masa manyan idanunta da taci kuka ta koshi ta yi.

Ya ce, “Oh Sorry Ya Sunan ki?”

Cikin Muryar fulancinta da gurbatacciyar hausarta ta ce, “Zainab a rugar Jauro ana she mun Gaaji.”

Adnan ya ce, “Alright biyo ni mu je.” Ya karasa maganar yana mata nuni da hannu.

Bayansa ta bi tana kalle kalle har suka shiga cikin bangaren Adeel.

Kai tsaye bangaren Prince Adeel suka nufa cike da mamaki take kallon wajen tamkar wata duniyar a zuciyarta take rayawa, “Oh ba don na san ban mutu ba nace nan shine Aljannata yadda Baffa yake fadamun anya ma aljannar takai nan ko?”

ADEEL na zaune a parlour ya dan kishingida zama irin na sarauta, ganin Adnan da Gaaji kawai sai ya tsaya yana kallon su ba tare da ya ce komai ba cike da mamaki.

Adnan ya kalli Gaaji laɓe a bakin kofa duk alamar tsoro ya gama tattara game da ita.

Ya ce, “ke ya kika tsaya abakin kofa bakya tunanin za a dake ki ne?”

Fashewa ta yi da kuka.

Ta ce, “Don Allah ni taimaka mun Baffana zai mutu.”

Adnan ya juyo yana kallon Prince Adeel ya ce, “Exactly da Mamaki, meyake faruwa ne? Ni dai san zuciyarka irin haka ba.”

Prince ADEEL ya bi sa da ido kawai ba tare da ya ce komai aransa yana so ya yi magana,amman saboda isa da Izza irin ta jinin sarautar da ke yawo a jinin jikinsa ya kasa furta komai illa yanayinsa da ya canja na bayyanar da ɓacin rai.

Adnan kuwa sanin halin abokin nasa sarai yasa bai damu da shirun nasa ba ya ci gaba da magana.

“Atlest koda zaka daina taimakon al’umma, wannan ya zama taimako na karshe da zaka yi, sai ka ga Ubangiji ya kara buda maka hanyar samunka,idan ka taimaki wannan fulani girl din,ba ka san wani hali take ciki ba,da condition din da mahaifin nata ya shiga ba,tunda ka ga har ta nace zuwa wajen biyar, tana zuwa neman taimako baka saurarenta kana wulakanta ta,Don Allah ka taimaka ba don halinta ba, kuma ba don ta isa ba,sai Don Allah,da kuma darajarata na abokinka da nake rokonka.”

A fusace Adeel ya juyo yana, “kai Mahaukaci ne,ko mahaifiyata bata taba shigo mun parlour ba,amman kai ka dauko wata kazamiyar fulanin yarinya ta shigo mun parlour.” 

Yana gama fadan hakan ya yi shiru. Adnan ya ce, “Ai awajen Ubangiji da kai da ita duk dayane babu bambanci, kawai dai anan kai mai kudi ita talaka,kai mai mulki ita baiwarka,so shine bambancin kuma ya zame maka dole ka taimaketa.”

Rai bace Adeel ya furta abun da bai taba furtawa ga duk wanda ya nemi taimako gunsa, “BA ZAN TAIMAKA BA, may be ma uban nata mutuwa zaiyi,ka fitar mun da wannan kazamiyar yarinyar daga part.”

Nan Shi ma Adnan rai ya baci cikin fushi ya ce, “ba zan fitar da ita ba,in kanaso ka tashi ka fitar da ita da kanka ta karfi in zaka iya ko kuma ni ka dakeni ka sa in fidda ta.”

Girgiza kai Prince Adeel ya yi ya sunkuya yana wuce tare da kokarin danne fushinsa a zahiri.

Sai da suka haura sama sosai, ita kuwa Gaaji mamaki take tana kallonsa cikin ranta take sakawa daman akwai mutumin da zai iya yiwa dan uwansa mutum fatan mutuwa? Kenan zuwa zaiyi har rugar su ya kashesa? Ban da haka don kawai Baffanta na kwance bai da lafiya sai yana yi masa fatan mutuwa? Wani abu take ji na yawo a cikin ranta na rashin son ganin Prince Adeel bata san miye tsana ba Amman ji take ta washe sa kamar yadda ta washi mutuwarta.

Shiru suka yi dukan su na yan mintuna, sai da ya ja numfashi kafin ya ce zan iya taimakonta in ta yarda Amman da sharadi zan…

Ya yi shiru nan zufa ta fara keto masa tamkar mai nakuda.

Ya yi shiru.

Adnan ya ce, “Kai muke sauraro fa kuma yi shiru.”

Goge zufar da ke kokarin jika masa jiki ya yi ya ce, “Zan… Zan….zan Aureta na tsawon Wata Bakwai kawai in ta yarda, Ana daura auren zan biya ko million nawa ne a fidda mahaifinta waje a masa magani, sannan duk inda wata bakwai ya yi zanyi signing a takadda in saketa.”

Cike da mamaki Adnan ya ce, “Aure? Kuma wannan? Prince,Why?”

Da hannu ya masa alamar dakatarwa kawai ba tare da ya ce komai ba.

Gaaji ta kallesa ta yi tsalle ta diri tana, “ni? Aure ka? In ma kai mai yankan kai ne ka yanka ni? Cab Allah Saa’anam mi yiɗa ma. Allah ma ya sutura ni bana shonka.”

Murmushi Adeel ya yi yana mamaki wai wannan yarinyar ce ke cewa bata sonsa, shi da yan mata ke bi amman wannan kwailar kazamiyar ce ke cewa bata sonsa.

Tashi ya yi ya shige ciki yana, “In ta yi tunani to,in kuma so take Mahaifin nata ya mutu fine wannan ba damuwata ce ba,ban da hadi da shi.”

Adnan zai mata magana kenan ko tsayawa batai ba ta fice a zuciyarta tana sakawa,me ma zata yi da wannan wanda yake yiwa Baffanta fatan mutuwa da take ji hanjin cikinta ban da kadawa ba abun da suke.

Waige-waige take ko zata samu abun taɓawa ban da ruwan wani kogi ba abun da ta samu.

Haka ta tsaya bakin kogin tasa hannunta ta dibo ta sha sannan ta ci gaba da tafiya.

Tsakanin Rugar Jauro da cikin gari sai anyi tafiya ta kusan minti arba’in ko fi ma wani zubin akanyi awa guda indai tafiyar kafa ne, domin mota bata shiga Rugar har sai ranar kasuwa kadai sau daya a sati.

Tun tana tafiya da kwarinta har sai da ta koma jan kafa a haka ta isa rugarsu, shigewa bukkar su tayi jiki a mace.

Numfashin da taji na tashi sauri sauri a cikin bukkar yasata saurin karasawa ciki. Aiko baffanta ne ranga-ranga jiki ya kara tsanani tuni ta birkice ta ma rasa abun yi tamkar za a zare ransa.

Ta kasa yi masa komai ban hawaye da ke ambaliya daga idanunta.

Ficewa tayi da wani mugun gudu.

Tuni har ta manta gajiyar da ta kwaso a hanya.

Gudu take ba kakkautawa ta fadi ta kurje ,ta kara tashi bata fasa ba,har saida ta isa cikin gari tsabar sauri a minti talatin ta isa. Tana zuwa kuwa bangaren Prince Adeel ta nufa kai tsaye da mugun gudu kasancewar babu kowa agun.

Tana shiga ta na numfarfashi daga kan da zata yi ta ga abun da kara firgitata tuni jikinta ya dau kyarma.

Price Adeel ne kwance da wata matashiyar budurwa suna wasanni, babu komai jikin budurwar shi kuwa daga shi sai gajeran wando.

Jikinta ne ya fara karkarwa ta kasa motsawa tsabar tsorata bata san lokacin da ta sake fitsari ba.

Sautin Numfashinta na kara fita da sauri-sauri, dogowan da zaiyi suka hada ido da ita nan fa ta kara firgita ta ja kafa zata gudu.

Wata irin tsawa ya mata yana janyota, “mene ne ke kuma?” Ita ma budurwar sai a lokacin ta juyo tana kallonta.”

Cikin yanayin firgici ta ce, “Naaa,naaa,naaa ga fada kuna yi ne na zo na fada ma na amince ne,na yarda.”

Auren Wata Bakwai 2 >>

2 thoughts on “Auren Wata Bakwai 1”

  1. Kayyasa….gamu ga prince Adeel nan, toh knn Yana ‘dan ta6a harka shima tnda gashi ga mace shame shame ana azumi 😂😂
    Ga gaaji Kuma taxo danufin ta yadda, toh knn Yana nufin itama zekawo tane Yana diban albrka da ita kome??
    Let’s meet on next page pls, thank you
    More wins nd success

  2. Bilkisu Haruna Abdullahi

    Alhamdulillah hmmm akowani yanayi akwai nashi salon labarin wannan kam yazo da irin nashi na daban Allah ya Kara basira

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×