Skip to content
Part 2 of 31 in the Series Auren Wata Bakwai by Xayyeesharthul-Humaerath

Tashi ya yi daga Kan Safina Yana kokarin janyo rigarsa ya sa.

Ita kuwa wani irin takaici ne ya turnuketa da jin tsana cike da haushin wannan ƙazamiyar yarinyar da ta katse mata jin dadi, domin har cikin ranta ta gama kudurta cewa lallai yau sai tayi nasarar kasancewa da Prince Adeel amman sai dai kash, wannan yarinyar ta hana hakarta kaiwa ga ruwa.

Cikin kasalalliyae muryarta ta ce, “Prince ina za ka kuma? Me wannan yarinyar take anan kasan fa ba mu gama ba kuma?”

Ko kallon inda take bai yi ba take ya shige toilet, ganin hakan tasan sarai ba zata taba samun kansa ba yasa ta tashi ta maida kayanta jikinta tana bin Gaaje da wani irin mummunan kallo.

Ita kuwa kanta a kasa ba ta ma san tanayi ba domin har yanzu jikinta rawa yake, karo na farko da ta fara ganin mace da namiji cikin yanayi irin haka.

Yana fitowa ya sanya riga sannan ya dauki wayarsa ya kira Shamaki ya sanar da shi ya je bangaren Uwar Soro.

Sanan ya kira Adnan ma a waya ya fada masa.

Tashi ya yi sai da yaje har kofa zai fita kafin ya juyo ya ga tana tsaye ya mata alama da hannu kan ta biyo sa, sannan ta bi bayansa.

Ɓangaren Uwar Soro dake daf da bangarensa suka nufa wanda yake shima keɓantacce ne ban da Yarima ba mai zuwa in ba da wani babban dalili ba, kasancewarta wacce ta raine shi tun yana karami har kuma ya girma a yanzu babu mai sanin sirrinsa fiye da ita.

Yana shiga ciki Gaaji ta bi bayansa da mamaki Uwar Soro take binsu da kallo daga shi har gajin cikin sauri ta gyara zama tare da amsa masa sallamar da ya yi.

Yana zama sai ga Shamaki da Adnan sun shigo.

Bayan sun zo duka ban da kallonsu babu abun da Prince Adeel ke yi.

Har cikin ransa yana jin nauyin furta masu abun da ke zuciyarsa ta wani fannin yana jin cewa hakan ba karamin kaskanci ba ne garesa,amman ya zai yi? A tunanin sa hakan dai shine kawai mafitar da zai dakile duk wata kofa da ke kokarin bude masa.

Zufa ce ta ci gaba da keto masa tamkar ba yanzu ya fito daga wanka ba.

Adnan ya ce, “Prince, ka kiramu kuma ka yi shiru Go On Please.”

A gajarce ya ce, “Daura mun Aure da wannan Yarinyar za ayi.”

Cikin yanayi na Mamaki Uwar Soro ta ce, “Ran Yareema ya dade, Aure kuma wannan? Ina tunanin in ma itan kake so akwai bukatar a gyarata kuma a ‘yantata daga baiwa tukunna kafin a gabatar da ita ga Mai Martaba da Fulani.”

Dakin ya dauki shiru na kusan Second Arba’in kafin Prince Adeel ya kara da, “A haka za ayi, ba tare da sanin kowa cikinsu ba, kuma a yanzu nake so a gabatar da komai.”

Dukkannin su suka koma kallon kallo.

A ƙarshe Adnan ne ya katse shirun da fadin, “Shi kenan Shamaki ki kira liman yazo.”

“An gama ranka ya dade.”

Shamaki ya amsa da haka ya fita domin kiran liman kamar yadda aka umarta.

Ba jimawa sai gashi da liman, Adnan ne da kansa ya sanarwa da Liman dalilin kiransa domin ya san in Prince ne zai kara magana sa gaji da zaman jira.

Ba tare da bata lokaci ba Liman ya aiwatar da abun da aka umarce shi da yi, Adnan ya zam Waliyin Amarya, Shamaki ya zama Waliyin Ango bisa sadaki Million Uku wanda Adnan ke hasashen ya wadatar a fidda mahaifin Gaaji kasar waje har a kammala masa komai na bukata.

An daura auren amman har yanzu mamaki ya gagara barin zuciyar Adnan domin ya gagara sanin dalilin da zai sa Prince ya ce zai auri yarinyar nan wanda ya tabbatar da cewa koda kyauta aka basa ba zai taɓa karɓa ba, mutum da a kullum ma bijirewa batun aure yake,tare da nuna cewa bai da lokacin tsayawa kula wata mata da niyar aure, dole akwai dalili, to amman ma ye dalilin?.

Ana kammala daurin Adnan ya ce da Uwar soro , “Baba zamu tafi yanzu, ki ajiyeta agunki ana yi mata dukkanin abun da ya dace kawai.”

Sun tashi zasu fita itama ta tashi tana kokarin bin su.

Rike mata hannu Uwar Soro ta yi da alamar su tafi Gaaji ta ce, “Aa Baffa, Baffana Yana shen.”

Adnan ya juyo yana, “ki zauna anan kinji zamu je akai Baffanki gun mai magani ne yanzu In Sha Allah.”

Haka ta bita ba don ta so ba zuciyarta fal tsoro kar suje su kashe mata Baffa tunda daman Yareema ya fara yi masa fatan mutuwa, ita kuma su cinyeta.

A cikin Part din ta shigar da ita wani dake, dake babban wajene tamkar gida guda wanda ciki da wajensa ya tsaru cikin ƙawa tamkar wata duniya ta daban.

Ko da suka shiga dakin kara binsa da kallo kawai Gaaji keyi tana mamakin kasancewarta a gun shin da gaske nan kuwa duniya ? Cai wannan duniyar inaga dai wacce ake zuwa lokacin da mutum zai bar duniya ne.

Abun da take ta radawa aranta kenan.

Uwar Soro ce ta katse mata tunani tare da fadin, “Ranki ya dade mu shiga banɗaki na haɗa miki ruwa zan miki wanka.”

Binta da wani mugun kallo tayi tana zare ido, wanka kuma? Ita ai ta jima da manta cewa ana wani abu wai shi wanka, ko da Baffanta ke lafiya ma ita sai ranar sallah kadai suke wanka a rafi da sauran matan karkararsu, wannan shekarar kuwa da yazo bai da lafiya ko yi bata yi ba,bare kuma yanzu da ba sallah ba mai zai kaita yin wanka?

Katse tunanin tayi da furtawa a zahiri, “Cab Wanka? Aradun Allah banyi haka kawai ba sallah she tazo ba zaki ce nai wanka? She ka ce Agwagwi?”

Uwar Soro ta ce “Ranki Ya Dade ai ba sai agwagi ne masu wanka ba, hakan tsaftane da tsaftace jiki, kuma kin ga Yareema ba ya son kazanta ba za kuna shiri ba in ba kya wanka zai ce ma baya sonki.”

Gaaji ta cuno baki ta ce, “Ni ba na shon shi daman ai tunda yake yiwa Baffana fatan mutuwa kuma sai dai shi ya mutu ya bar mun Baffana raye.”

Da kyar ta samu ta shawo kanta tare da tabbatar mata cewa in bata yarda an mata wanka ba Yareema ba zai kai Baffanta a masa magani ba.

Suna shiga Toilet din ta fara ihu tana, ” nan ai ba gun wanka ne ba ni ki barni kawai ai dauɗa karin karfine kar ki ragemun karfina a dakeni in kasa ramawa.”

Uwar Soro ta ce, “nan ne ban dakin wanka anan duk haka suke, kuma in kika yi wankan ma kara karfi zakiyi saboda muna da sabulu mai kyau.”

Haka ta tuɓeta da kyar tana sa mata ruwan zafi a jiki ta kara sulle mata tana ihu, “Zaki karni ne Baba, na shiga ukuna ni Gaaji zata ƙona ni.”

Haka sukai ta fama tana gudu tana binta har aka rage daudar dan ba ace ta fita duka ba, kanta kuwa kin yarda ma tayi a taɓasa sam bare a wanke.

Suna gamawa ta dauko sabon brush tasa mata toothpaste ta ce, “Yawwa ungo wanke bakinki.”

Tana karba ta suɗe toothpaste din tas ta shanye ta fara tauna brush din.

Uwar Soro ta bude baki, “Subhanallahi wanke baki ake ba sha ba fa.” Karba tayi ta kara zuba mata wani sannan ta wanke mata bakin da kanta.

Ai kuwa datti kamar ruwan kasa jini ma bakin ya fara yi, tuni Gaaji ta rikice ta fara kuka tana ganin jiki ta ce, “Dok Allah karki shanye mun jinina kadan ne dani ba yawa kuma bai da zaƙi ma Don Allah.”

Sai da dariya ta kusan subucewa Uwar soro ta danne tana, “shikenan yanzu ga ruwa kuskure bakin, kar ki shafa, ki kuskurewa kawai.”

Nan fa tana sa ruwa a baki ta shanye tana, “ita ba zata zubar da jininta a banza ba ta mutu.”

CIKIN GIDA

Fulani ce kishingiɗe a parlour hannunta dauke da tuffa tana ci a hankali, gabadaya yanayin fuskarta sam babu walwala kallo ɗaya zaka mata ka tabbatar da cewa tana da damuwa cikin ranta.

Jakadiyar ta dake gefe tana lure da hakan ta ce, “Ranki Ya Dade Fulani lafiya kuwa?”

Ta ce, “Jakadiya kira mun Hajiya Maimuna.”

Tashi tayi ta je ta kirata cikin sauri.

Hajiya Maimuna wacce take Aminiyar Fulani kuma mata agun kawun Mai martaba ce ta shigo bangaren Fulani kamar yadda ta samu kira daga gun Jakadiya.

Zama tayi tana fadin, “Ranki Ya Dade na amsa kira, amman ya na tarar da fuskarki ba walwala fatan dai muji Alkairi.”

Jakadiya na fita ta laɓe a bakin kofa tana sauraren abun da Fulani zata ce.

Numfasawa tayi tana gyara zama, “Maganar Yareema ne, kina ganin kullum mai martaba kara girma yake, kwanaki na kara ja, lokacin murabus dinsa na ta kara tawowa, tsufa ya kamasa, amman Yareema sam yaki mai da hankali kan batun aure kuma kin san ba makawa shi za a daura, ba ma wannan ba ni kaina ina bukatar ganin wata wacce za ace sirika ce gareni ta haifa mun jikoki, yanzu haka fa ya kusa cika Shekara talatin a duniya.”

Murmushi Hajiya Maimuna tayi ta ce, “indai Don Wannan ne ki daina damuwa Uwar gijiyata, ina tunanin kawai za a shirya yi masa auren ba zata ne kawai ba tare da saninsa ba kuma ba tare sanin kowa cikin Masarautar nan ba, Mai martaba kawai zaki sanar a shirya bikin na tabbatar da cewa Yareema ba zai taɓa bijirewa zaɓinku ba amman kafin hakan a gwada tuntubarsa na ƙarshe ko yana da wacce take zaɓinsa, in ya tabbatar da cewa babu kawai sai mu shiga shirye-shiryen abubuwan da ya dace kuma a zaɓo matar data dace.”

Gyara zama fulani tayi tana sakin Murmushi ita ma ta ce, “Maddallah da ke Hajiya Maimuna babu shakka hakan za ayi domin kuwa shine mafita kawai, amman Babbar Matsalar ma ban san ko yana gari ba, zan binciki Uwar Soro muji.”

Jakadiya na jin motsin Hajiya Maimuna ta wuce da gudu ta nufi dakin Fulani Kilishi.

Amarya ga Fulani Babba wacce take ita ma mata ce ga Mai Martaba ta biyu.

Tana ganinta ta daka mata tsawa, “Ke Lafiya zaki shigo mun daki haka? Kina da hankali kuwa?”

Ta ce, “Ranki Ya Dade labari na samo miki ina so Hajiya Maimuna ta wuce ne kada ta ganni.”

Tsaki ta daka mata tana fadin, “Oya ni fadamun to.”

A hankali murya irin ta munafukai ta ce, “Za ayiwa Yareema auren bazata ance ba wanda zai sani sai Mai Martaba da Fulani Babba.”

Wani irin Murmushin takaice ta yi, “Aure? Wannan zance ne, hakan ba zai taɓa yiwuwa ba ma kada ki damu ni na san matakin da zan dauka, bama wannan ba , shin wa za a aura masa?”

Jakadiya ta ce, “ba su kai ga fada ba, sun dai ce za a duba.”

Dariya ta fara wacce azahirine kadai take dariya a zuciyar ta kuwa ban da tsantsar mugunta babu abun da ke ciki.

“In an fada yarinyar ki zo ki sanar mun, ba wanda ya isa aiwatar da komai cikin Masarautar nan ba tare da sani ba, don ban haihu ba hakan baya nufin in zam saniyar ware ahir.”

Jakadiya na fita ta kara nufan bangaren Hajiya Rabi wacce take kishiya agun Hajiya Maimuna ta sanar da ita.

Tsaki Hajiya Rabi tayi tana fadin, “Lallai kuwa za a sha mamaki cikin Masarautar nan, Mussaman in ya kasance ba ɗaya daga cikin ‘Ya’yana za a baiwa Yarima ba sai dai kowa ya rasa ko ya mutu ko ya yi rai ba aure, ke ban ma ga ta zama ba, amman ina fatan dai baki sanarwa da kowa hakan ba?”

Girgiza kai kawai Jakadiya ta yi alamar eh.

Hajiya Rabi bata kara bi ta kanta ba tuni kawai ta dauki mayafi ta fice.

Tana fita Jakadiya ta tuntsire da wata irin dariya ta yi wasu surutan da ita kadai ta san fassaran su.

Kiran Uwar soro Fulani Babba tayi kan tana neman Yareema.

Uwar Soro ta sanar da shi kai tsaye ya nufi cikin Masarautar.

Yana zuwa zuwa daga kafar shi da zai yi ya shiga ciki ƙafar ta ƙame ƙam…

<< Auren Wata Bakwai 1Auren Wata Bakwai 3 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×