Skip to content
Part 19 of 31 in the Series Auren Wata Bakwai by Xayyeesharthul-Humaerath

“Ummm ummm.”

Daga Hannunsa ya yi zai kara taɓata sai kuma ya janye.

“Dodo ne ni kike guduna? Ba kya so in tabaki?”

Kuka ta fara tana fadin, “Umm dukana zaka yi kuma ni bana so.”

Jin kukanta yake har cikin ransa yana ji dama ace zai iya dakile zubar hawaye daga idanunta daga yanzu har abada.

Karfin hali ya yi ya kara fadin, “Ba bu abun da zan miki ki daina tsorona kinji.”

Gaaji ta ce, “cewa kayi zaka kashe mun Baffana Yaaayah kuma shi kulawa yake da Baffa.”

Dafe kai ya yi, yama rasa ta ina zai bullowa wannan yarinyar.

Daga karshe tashi yayi kawai ya nufi wajen Liman.

Bayan sun gaisa ya ce, “Liman wata tambaya ce na zo da ita.”

Liman ya ce, “Ina saurarenka Yareema.”

Prince Adeel ya yi shiru kafin can ya ce, “Shin har yanzu Zainab ba matsayin mata take gareni ba? Na ji kace sai ta haihu tukunna a kara aure, kuma kamar a karantarwar da kayi mun ka sheda mun cewa ko da miji ya saki matarsa muddin da ciki a jikinta bata saku ba har sai ta haife abin da ke cikinta.”

Liman ya ce, “Wannan gaskiya ne, har yanzu Zainab a matsayin mata take gareka har sai ta haihu. Sakin da ka mata zai hau kanta domin kuwa wancen auren da tayi babu shi, inko ka maidata shikenan, wannan batun da na fada na kara aure bayan ta haihuwa kuwa kan shi Mijin da yake bidarta ne da sukai aure bisa kuskure, in shi zata koma dole sai ta haihu kafin a kara sabon aure.”

Ajiyar zuciya Adeel ya yi wanda sai da ya bayyana azahiri cikin zuciyarsa kuwa ya ce, “In sunsan wata ai basu san wata ba, babu mai rabani da matata kuma na maidata da ita zan yi rayuwa har karshen numfashi.” A fili kuma ya ce, “Ma Sha Allah Na Gode Allah kara girma.” Ya fada yana tashi.

Binsa da kallo Liman ya yi, domin tunda yake bai taba ganin Yareema ya nuna damuwarsa ga abu ƙarara har haka ba.

Komawa ya yi ya sami Gaaji harta koma barcin, babu abun da zuciyarsa ke raɗa masa illa ya rugumeta ya ji dimun jikinta ko zai ji sanyi da raguwar soyayyarta dake yi masa radadi a azuciya.

Kallonta ya tsaya yi kawai tunda yake bai taɓa jin cewa fuskar wata ‘Ya mace na da kyan kallo da sha’awa ba kamar yau,ya kasa Kau da ido da ganinta, Zuciyarsa na kara ayyanar masa sex dinsa na farko da ya kasance da ita da kuma numfashinta da ya shaƙa lokacin da bata da lafiya, kasa jurewa ya yi a hankali ya karasa inda take, tabbacin tana matuƙar buƙatar barci fitansa bai fi minti biyar ba da dawowarsa amman har ta kara yin nisa a wani barcin.

Ta gefe ya bi ya daga hannunsa zai rikota sai kuma ya sake yana kokarin hada fuskarsa da tata.

Bakinta ya cafko da bakinsa yana tsotsa jin sabon al’amarin da bata taɓa ji ba yasa ta sake ita ma tana maida masa da martani suna tsotse bakin juna.

Fara ficewa ya yi daga hayyacinsa yana bi mata jiki tare da tallafowa.

Wata irin razana Gaaji tayi tana buɗe ido.

Duk a tunaninta mafarki take ashe zahirine.

Adeel kuwa bai ma san ta farka ba kara tura jikinsa cikin nata yake yana kokarin wuce gona da iri.

Ita kuwa fara kokarin kwatar kanta tayi ta karfi , ta gantsara masa cizo a kirji amman ina kara kankameta yake.

Tana mutsu mutsu Hannunta ne ya kai kasan wandonsa ba tare da ankare ba ta rike masa gaba.

Tamkar za a zare masa rai ,Wata irin ƙara da ya yi yana saketa sai da ita kanta razana.

Ganin ya rike kasan wando yasa ta fahimci inda ta rike masa ma ashe.

Duk ya sururuce Idanun sa sun juya Ga zufar radadi da ta fara keto masa.

Ya kalleta tayi saurin kawar da kai, wani irin numfashin wahala ya yi hannu rike da wando ya yi hanyar fita, yana zuwa daidai kofar fita a part din ya ci karo da Uwar Soro.

Kallonsa tayi sama da kasa cike da mamaki ta ce,

“Yareema lafiya kuwa? Ya na ganka haka?”

Kansa a kasa ya ce,

“Ba komai.” Sannan ya ci gaba da tafiyarsa.

Binsa da kallo tayi yanayin yadda yake tafiya tamkar sabon dan kaciya ga wando rike a hannu yana wawwage kafafu.

“Oh Allah ko me ya faru kuma? Umm.” Ta fada sannan ta shige Part dinsa.

Shi kuwa Yana shiga cikin Part dinsa ya zame wando, sai a lokacin ya ji zafi a kirjinsa ya tuna cewa ta cijesa, cire rigar ya yi ita ma ya ga sai da ta datsa masa fata da hokaransa.

Haka ya zauna zigidir akan gado ba riga ba wando ya babbaje kafafu iskar fanka na hurasa yana sakin numfashi kamar wanda ya dauki tulin kaya akai.

Uwar Soro tana shiga ta ga Gaaji Zugu a zaune kan gado tana gwalalo idanu.

“Mene ne ya faru ne? Yareema ya shigo nan?”

Gaaji ta girgiza kai alamar “eh.”

Uwar Soro ta kara fadin, “Ya miki wani abu ne?”

Girgiza kai ta kara yi alamar aa.

“To me ya faru?”

Gaaji ta girgiza kai akaro na uku.

Uwar Soro ta ce, “Wai kurma kika zama ne ko shi Yareeman ne ya kara ce miki kar ki fada abun da ya miki?”

Gaaji ta ce, “Aa kawai yazo ne ban sani ba ina barci na rike masa wannan dinsa.”

Uwar Soro ta ce, “wannan dinsa mene?”

“Wannan dinsa, wannan.” Ta fada murya na hardewa

“Mene ne wannan kuma? ” Uwar Soro ta fada cikin rashin Fahimtar inda Gaaji ta dosa.

Gaaji ta sunkuyar da kanta kasa ta ce, “Wannan jelar… ta wandon shi.”

Sai a lokacin Uwar Soro ta fahimta tana tuna yadda ta ga Adeel dazu, dariya ce ta kusan suɓuce mata sai kuma ta daure ta fita daga dakin.

Gaaji kam daman barcin bai isheta ba, tunda aka fada cikin nan kamar an tawo mata da ciwon barci, don yanzu a rayuwarta babu abun da take ba gajiya kamar barci.

Daman tsoron kar ya dawo ya ce zai daketa yasa ta kasa komawa tunda uwar Soro ta dawo kuwa gyara kwanciyarta tayi ta ci gaba da barcinta hankali kwance.

Sai da azahar tayi kafin Uwar Soro ta tada Gaaji a Barcin ta yi sallah, ta sha fura kasancewar Bata son cin abinci sannan ta kara komawa ta kwanta.

Adeel kam ya kasa maida wando jikinsa koda zai je masallaci haka ya zumbula jallabiya ya tafi, yana dawowa daga masallaci sai ga Adnan.

Ganinsa sanye da jallabiya ya matukar basa mamaki domin yasan Adeel dai ba gwanin sa jallabiya bane kuma koda yasa ma saidai iyaka Part dinsa baya taba fita da ita.

Adnan ya ce, “Yau kuma Jallabiya kayi ra ayin sawa? Ko duk na shirin angoncin ne?”

Wani irin Murmushin dole Adeel ya kakalo ta gefe kawai yana kauda kai.

Tare suka shiga Part din, Adnan na lura da shi, wani irin bajewa Adeel ya yi yana kokarin zama tamkar yaron da ke gudun fama kaciyarsa.

Adnan ya ce, “Anya lafiya kuwa? Ka na zama kamar wani dan kaciya? Me ya faru ne wai?”

“Nothing oh.” Adeel ya

fada.

Adnan ya yi Murmushi, “To nidai ina ganin abun mamakin da ban taba gani ba yau.”

Tashi Adeel ya yi ya nufi Daining area Yana, “in ka gama mamakin zaka iya zuwa kaci abinci.”

Dariya Adnan ya yi yana tashi “wannan mamakin ai ba me karewa bane don naga lamuran kara karfafa suke don haka dole in rufawa kaina asiri inci abinci.”

Ranar sai dare Adnan ya bar Masarautar ko da yaje part din Uwar Soro Gaaji na barci, duk da cewa daman baya ma so ta ganshi ta tada rigima.

Prince Adeel kamar jira yake Adnan ya fita duk ya takure, aiko yana ficewa tuni ya zame jallabiyar don ita dinma damunsa take ganin ba yadda zaiyi ne ya barta a jikinsa.

*****

“Ni kam na fada ma na hakura da duk wani rudin duniya, kudi, har ma Da Yareeman so nake kawai na fita na bar cikin gidannan ko zan samu in tsiratar da rayuwata, kowa da kudirinsa kowa da manufarsa sam Babu imani da tausayi a zukatan mutanen masarautar nan duk ji da kaina da nake na sara masu wallahi abun ya fi karfina ka barni in tseratar da rayuwata.” Ta fada tana kuka.

“Na ce miki ki kwantar da hankalinki, shirinsu ba zai taba tasiri akanki ba domin duk abun da zasu aiwatar a tafin hannunmu yake, kuma wallahi kika yi gigin fita a masarautar nan zaki tarar da abun da bakiyi tsammani ba ma,sanya kafarki a kasa da niyar fita tamkar insa kafa ne zaki kai kanki makabarta, makabartar ma wacce tafi kowacce haɗari, ni dai na fada miki.”

Jefar da wayar tayi gefe tana daura hannu aka, “ni kam na shiga uku, wannan wacce irin masifa ba bala’i ne? Wannan wani irin tashin hankali ne na shigo da rayuwata ciki garin son duniya?”

Tsabar gurnani buga kanta tayi da bango bata an kare ba, ga tarin kayan abinci da duk wani nau’in jin dadi amman bata iya bi ta kansu sam, yunwar ma bata ji bare tai tunanin ci.

*****

Fulani Kilishi Zaune da Jakadiya agefe tana jawabi, “Hmm Ranki Ya Dade abu fa ya baza gari ana cen ana cecekuce kan cewa Yareema ya yi wa wata cikin shege ina fada miki batun nan kaf birni da kauyuka da ke wannan jahar labari yaje garesu ko ina kaje batun kawai ake.”

Rai ɓace Fulani Kilishi ta ce, “Hmm Allah dai ya kyauta Amman ko ta halin ƙa-kane wannan yarinyar bata isa ta ɓata mun shiri,duk yadda za ayi sai ta bar cikin Masarautar nan duk rintsi duk wuya,ai ni ba haka nake fata ba,kuma ba haka nakeso ba,zuwanta tamkar dakilemun kofar nasara ne,inma cikin gaske gareta tabbas sai nasa an zubar da shi daga nan kinga in aka je gwadata aka ga ba ciki ai zance kuma ya kare.”

Jakadiya ta bude baki, “Lallai Uwar Dakina shirin ki daban ne cikin sauki kin samawa kanki mafita zanso ace hakan ya kasance don abun Babu dadi sam, duk da cewa na tsani Yareema amman bazan so yi masa fatan cewa silar sa asamu dan shege cikin Masarautar nan ba.”

Fulani Kilishi ta ce, “ita wannan yarinyar bata san cewa tamkar ta kawo kanta lahira bane.”

Jakadiya ta leƙa window tana, “Hmm bara in tafi na ga Magajiya na zuwa kinsan ba karamar munafuka bace yanzu sai tayi mana laɓe.”

*****

Cikin dare Gaaji ta farka da wata azababbiyar yunwa.

Dakin Uwar Soro tayi tana tashinta.

“Subhanallahi Uwata lafiya?” Uwar Soro ta furta .

Gaaji ta Shagwabe kamar zata yi kuka, “Yunwa nake ji.” Tana karasa maganar sai hawaye.

Tashi tayi ta riketa ta zaunar da ita gefen gadon kafin ta ce, “To yanzu abincin za ki ci ko kuwa fura da Nonon?”

“Fura zan sha bana son abincin.” Ta fada.

Tashi Uwar Soro tayi ta dauko mata a fridge ta dama mata sannan ta mika mata.

Gaaji ji take kamar ta kwace aiko tana karba da ta kafa kai sai da ta shanye tas ta mikawa Uwar Soro Bowl din tana sakin Numfashi.

Can kuma sai ta ce, “nikam wai sai inta barci kuma inta shan fura, yaushe zan daina?” Ta karasa maganar a raunane.

Cike da tausayi Uwar Soro ta ce, “Ranar da kika haifi Babyn dake cikinki In Sha Allah zama ki daina jin ciwon komai.”

“Baby? Mutum kenan fa? Kuma a cikina.” Gaaji ta fada tana kallon cikinta.

Uwar Soro ta ce, “Eh mana.”

Gyara zama tayi don ita duk jawabin nan da ake bata fahimci cewa wai ita ke dauke da ciki ba.

“To Babyn waye?”

Uwar Soro ta yi Murmushi, “Babynki mana ke da Yareema.”

Nan take ta zumburo baki, “ni da Yareema? Cab ni bana son shi Yaayah nake son na haifawa Baby ba shi ba Nikam.”

Ta fada tana juyawa Uwar Soro baya.

“To koma miye dai yanzu kije ki kwanta adakinki ko in rakaki?”

Kwanciya tayi tana, “Nikam yau anan ina son kwana.”

Ta karasa maganar tana shigewa blanket.

*****

Misalin karfe takwas na dare an idar da sallar magrib

Uwar Soro na cikin Masarauta suna tattauna yadda za a tsara bikin Adnan da Nasmah kamar yadda Hajiya Maimuna ta bawa Fulani shawara.

Prince Adeel na dawowa da ga masallaci ya shiga Part din hankalinsa kwance domin ya tabbatar da cewar Uwar Soro na ciki.

Gaaji na barci kamar yadda ta saba cikin nutsuwa, zuciyarsa ce ta raya masa kawai ya dauketa ya kaita Part dinsa.

Haka ya sungumeta a hankali cikin dabara ya dauketa suka

Cikin Part din zai kwantar da ita kenan ta bude ido,suna kallon juna, da sauri ta matsa daga jikinsa gefe jikinta na rawa ta ce, “ka yi hakuri ban san zai yi ma zafi ba, ba da sani na na rike ba, ba zan kara ba, ka yi hakuri, wallahi ban sani bane, da nasan da zaka ji zafi bazan rike gun ba.” Ta karasa maganar tana hawaye, jijiyon wuyanta har motsi suke tsabar tsoro.

Shi kuwa binta da kallo ya tsaya yi kawai a zuciyarsa yana jin cewa dama ta ci gaba da maganar, domin sautin muryarta dadi yake yi masa a kunne, ya ma rasa dalilin da yasa a yanzu komai nata yake birgesa, shin dama haka so yake? Ni kuwa na ce BABU RUWAN SO littafina na farko.

Ganin yadda ya kura mata ido zuciyarta ta kara firgita da tunanin cewa lallai yana hada muguntar da zaiyi mata don ya rama ne, a hakan yasa tayi wata jarumtar tashi zata gudu.

Tsawar da ya daka mata ne yasa kafafunta fara rawa ta kara firgicewa, “Don Allah kar ka mun komai ka barni in tafi nace na tuba ba da sanina bane.”

Rike mata hannu Adeel ya yi kawai ba tare da yace komai ba, ya ja ta suka koma parlour.

Kan 2sita ya zaunar da ita tana dari dari tare da jin cewa yau kam ta shiga uku ta shigo hannun mugu sai yadda Allah ya yi.

Wata leda ya dauko yasa kan Centre table sannan ya janyosa gabanta shi ma ya zauna a gefe yana ciro kayan ledar, Ice Cream, Chocolate da su Cake ne.

Ice Cream din ya fara budewa, Gaaji na gani da tayi wani irin hadiyar yawo sai da ya nuna daga bakin har wuyanta.

Ji take kamar ta fisga a hannunsa ta kai baki.

Ya kalleta ya ce, “za ki sha?”

Tana so ta ce eh kuma tana jin tsoro, sunkuyar da kanta kasa tayi ba kawai tana kokarin danne son shan.

Adeel ya ce, “ba za kiyi magana ba? In baki ko zaki sha da kanki?”

Dagowa tayi ta kara kallon robar sai kuma ta kara sunkuyar da kanta.

Ya mika mata, tuni ta amshe da sauri kamar abun da zai gudu.

“Oyaa to ki sha, in kika gama shanyewa sai kici sauran abubuwan ko?”

Ina Gaaji bata ma san yana wani batu ba tunda ta karba sha take kawai tamkar mayunwaciyar da ta kwana uku bata kai komai cikinta ba.

Haka ya kara zura mata idanu tamkar wanda ke kallon Tv.

Tsabar shan ice cream duk sai da ta bata saman bakinta.

Tana gama sha ta dauki cake din a hannu tana ci, kafin ta gama barcin fama ya fara kwasheta da cake din a hannu ta fada kirjinsa tana barci.

Shi kuwa harda gyara mata kwanciya a jikinsa, ya sunkuyar da fuskarsa daidai bakinta ya leshe Ice Cream da ta bari da bakinsa.

Hatta barcinta birgesa yake, ya samu babban aiki na kallon Gaaji.

Yana zaune sai da Shamaki ya yi sallamar bashi izinin shiga ya yi,tukun ya shiga ya sanar da shi cewa Mai Martaba na nemansa.

Wata irin ajiyar zuciya ya yi nan take domin yasan kiran mai martaba cikin daren ba kalau ba.

Daukanta ya yi, ya shigar da ita bedroom ya kwantar da ita sai da ya rufe ta da blanket kafin ya janyo kofar ya fita.

Bayan sun gaisa Mai Martaba yake fadin, “Yareema na kira ka ba don komai ba sai ƙara jadadda maka wasu batutuwa, da kuma sanar da kai abun da baka sani ba kuma yake daf da afkuwa, har yanzu Raina bai amince mun da cewa Waccer baiwar Allahn da ta zo da gaske abun da ke gareta naka bane, Zuciyata na raɗaɗi inna tuna wannan lamarin amman kuma sai ina jin cewa ina karyata faruwar hakan, ka da ka manta gidanmu,gidan mutuncine da dattako, ba a taba samun mu da aika wani mummunan aiki ba bare ya kai ga saɓon Ubangiji, ko sau ɗaya ka gagara fitowa ka karyata abun da tazo da shi duk da cewa ko da ka yi shirun ma gwaji zai iya tabbatar mana da gaskiya,

Amman kuma duk da hakan rashin maganar ka tamkar guba ce ga Zuciyata da ta mahaifiyarka.

Kuma ina so ka sa wannan aranka duk ranar da aka ce ya tabbatar kai ka aikata wannan mummunan kuma kazamin aikin, babu ni, babu kai, sunanka ya shafe cikin wannan Masarautar, zan yi rayuwa tamkar ban taba haihuwa a duniya ba, har Ubangiji ya dauki raina, kuma ba zaka taɓa zama magaji gareni ba, bare har girma ya riskeka ace Ɗan da kake da shi ba zai zam magaji ba, kasancewar sa ba Dan halal ba, don haka tun kafin ka rusa tarihin wannan masarautar ni zan fara rusata, sannan a karshe kuma mahaifiyarka ta umarci da ayi maka auren sirri tsakanin ka da Yar Uwarka Nasmah, ban amince ba kuma ba zan taba amincewa da kayi wani aure ba a yanzu kam har sai ranar da ka wanke kanka daga wannan badaƙalar.”

Tunda Mai Martaba yake jawabin nan kan Adeel na kasa, ban da gumi babu abun da ke keto masa.

Mai martaba ya kara da , “Za ka iya tafiya, Amman ina kara jaddada maka cewa tabbatuwar lamarin nan daidai yake da cire ka a cikin wannan ahalin.”

Jikin Prince a sanyaye ya tashi ya bar Parlourn, zuciyarsa na son sanar da mahaifinsa cewa bai taba kusantar wata ‘Ya Mace da ba muharamarsa ba, amman ya gagara, batun Nasmah kuwa daman baya gabansa hakan ya masa daidai domin bai da ra ayin wata mata a yanzu da ta wuce Gaaji.

Yana tafiya hawaye sun cika idanunsa, tunda yake Mai Martaba bai taɓa yi masa magana cikin kakkausan lafazi irin na yau ba, tabbas akwai matsala wanda magance Allah ne kawai zai iya.

Har ya koma Gaaji na barcinta, ya kalleta ya yi ajiyar zuciya sannan ya shiga toilet ya yi alwala ya yi nafila sai da ya yi addu’o’i sosai tukun shi ma ya je ya kwanta a gadon.

Zuciyarsa na raya masa ya kawar da yunwar ta da dasa masa na tsawon watanni, amman kuma yana tsoron tabata ta tashi kuma yasan lallai ta tashi bazata taɓa yarda ta kwana a part dinsa ba.

Ganin bai da wata mafita yasa ya manna jikinshi daf da ita suna jin dimin juna tare da shakar numfashin juna, ya yi addua ya shafa mata sannan shi ma ya shafa a jikinsa.

Can dai ya gagara yin barcin kuma ya lura barcin da take na yanzu ya yi nisa Sosai kasancewar abubuwan da ta ci sun kara sake mata jiki.

A hankali ya cire mata hijabin da ke jikinta, doguwar rigace a jikinta ta barci mara nauyi irin yanayin ta masu ciki yadda zasu sha iska yadda ya dace babu takura.

Cire hijabin kadai bai masa ba, yasa hannu yana balle mata bottle din gaban rigar, nan Dukiyar fulaninta suka ce masa Hi kasancewar ba breziya a jikinta mussaman yanzu da suka canja launi suka kara fitowa hakan yasa bata jure sawan ko tasa ma sai ta cire, wata irin zabura ya yi yama rasa inda zaisa kansa, ganin tabawa da hannun ba zai yi masa ba yasa shi kai bakinsa yana sucking a hankali, can kuma ya dago idanunsa akan karamin bakinta, ya kai mata kiss sannan ya kara sauka kasan, wasanninsa yake son ransa cikin nutsuwa tamkar wani karamin yaro har sai da ya karasa zame mata rigar, idanunsa suka koma kan karamin tulin cikinta da ya fara fitowa, ya na shafawa a hankali can kuma ya kai kansa ya kwanta akan cikin, dumin cikin na kara ratsa sa ,duk da cewa bai san mene ne a cikin cikin ba, amman zuciyarsa tasa masa kaunar babyn da ke ciki fiye da komai a duniya a haka har barci ya kwashe shi.

Ranar kuwa ya yi barcin da rabonsa da ya yi har ya mance hakan kuwa ya samu barci har da munshari.

Da asuba tayi , ya yi sallah yana dawowa ya je kunnenta yana radin, “Zizi WakeUp, time for Prayer.”

Gaaji idonta a rufe ta ce, “Baabata ki barni, ban gaji da Barcin ba.”

Adeel ya dagota yana shafa mata baya a hankali.

“Ki tashi kiyi sallah kiyi wanka sai ki koma barcin kinji?”

Jin Muryar Adeel yasa tayi saurin bude idonta.

Ta gansa yana sake mata murmushi da sauri ta kara rufe idon domin tabbatar da cewa mafarki take.

Tana kara budewa shi dinne dai tsaye gabanta yana sakin Murmushi.

Cikin rashin Fahimta murya na rawa ta ce, “nan…..? Anan…na… na…kwana?” Sai kuma ta kalli jikinta ta ga ta ga daga ita sai Pant, da sauri ta janyo hijabinta tasa tana rufe jikinta

A zuciyarsa ya ce, “daga baya ma kenan,” a zahiri kuma ya ce, “Eheen Oya tashi.”

Zumbur ta mike domin har yanzu ta gagara amincewa da wai Adeel ne ke mata magana murya kasa-kasa kuma yana sakin Murmushi a fuskarsa mutumin da inya turbune fuska shanu ma sun fishi fara’a amman yau shine yana magana har ana ganin hakoransa kuma gata tsirara ba kaya jikinta.

“Zan koma can inyi sallah inyi wankan.” Ta fada tana tattare hijabin da ke jikinta.

Ta tashi zata fice.

Rike mata hannu ya yi, “Wait haka zaki koma ba kaya a jikin?”

Gaji ta kalli hannunta da ya rike, sannan ta dago ta kalli fuskarsa kamar zata yi kuka ta ce, “Umm ,e…eh… Zan sa acen.”

Ya ce, “Ba ni hijabin.” Ya fada yana mika mata dayan hannun.

Ya zaunar da ita gefen gadon, sannan ya durkusa ta gefenta zai dauko rigar ta da ta ma manta da ita.

A daidai gun wuyanta yadan tsaye, take tsigar jikinta ta fara kadawa, tayi saurin rufe ido.

Wucewa ya yi, ya janyo rigar ya kalleta ido rufe.

Ya ce, “daga Hannunki insa miki rigar.”

A hankali ta bude idon tana daga masa hannun, yasa mata rigar, yazo mai da mata bottles din gabar rigar hannun sa na kaiwa kirjinta ya tsaya yana kallon fuskarta tayi saurin saukar da kai kasa tana kautarwa.

Ya na sa bottle din ya ce, “ba kya son kallona ko? Ko nayi muni da yawa ne? Babyn cikin ki dai kama da ni zaiyi.” Ya fada yana sa hannun sa a cikin.

Bata ce komai ba ita dai Alla-Alla take ta ga ta bar masa part din.

Yasa mata hijabin sannan ya ce, “In daukeki in maidaki kamar yadda na dauko ki ko?”

Gaaji ta girgiza kai, “Aa.”

Daukanta ya yi tana motsutsu har sai da ya kaita kofar Part din Uwar Soro kafin ya direta yana, “Bye bye Take Care.”

Ko juyawa ta kallesa batai ba, bare ta basa amsa ta shige.

Tana shiga Uwar Soro na fitowa daga dakinta kenan taje ta tashinta tayi sallah ta ga bata nan.

“Uwata ina kika je? Kar dai ma ba anan kika kwana ba? Ba tun yanzu ba, Na fada miki fa karki bari a ganki cikin Masarautar nan.”

Gaaji na tsaye murya araunane ta ce , ” bani ce na fita da kaina ba, shine yazo ya daukeni ina barci.”

“Shi wa?” Cikin rashin Fahimta Ta tambaya.

“Yareema.” Gaaji ta fada kanta na kasa.

Uwar Soro ta ce, “Okay yanzu kije ki shirya ki canja kiyi wanka ki canja kaya kizo nan ina jiranki.”

Shigewa dakinta tayi ta fara wanka, sai a lokacin ta ga nipples dinta sun jajawur tana wanke kan breast din na mata zafi, haka tayi wankan tana tsaki, “Wannan mugun shi ko mutum na barci ma sai ya mishi mugunta, ni daman ban yarda da Murmushin nan nasa ba, yanzu haka rama abun da namai ya yi, kuma sai Allah ya saka mun, kuma In Sha Allah bazan haifi yaro mai kama da shi mara dariya ba, yana yiwa mutane mugunta kawai.”

Tana ta sambatun nan a zuciya har ta gama wankan tayi alwala sannsn tasa kaya tayi sallah.

Yanzu ta saba koda asuba sai ta sha fura take samun kwanciyar hankali, hakan yasa ta fita ta dauko a fridge.

Ban da binta da kallo ba abun da Uwar Soro ke yi.

*****

Cikin tsakar rana Jakadiya ta je bangaren da ake aje Safina.

Duk da cewa daman cen zaman tsoro take, amman shigar Jakadiya sai da ya kara birkitata jikinta na karkarwa ta zam tamkar public toilet da kowanni lokaci da wanda ke zuwa ya yi mata kashedi ya fita , “Wato ke har yanzu baza ki aiwatar da umarnin da na sanar miki ba? Shin kina wasa da rayuwarki ne? To ahir dinki wallah In ma da wa inda ke zuga ki kan cewa ki zauna kan bakarki kin taka babban kuskure, inaso kiyi gaggawar neman magana da mai martaba tun kafin dare ya miki duhu daga yau zuwa gobe kadai suka rage miki, sabanin kasancewar hakan kuwa daidai yake da kisa aranki daren gobe i yanzu kina lahira.”

Durkusawa gabanta tayi tana rike mata kafafu, “Don Allah kiyi mun rai, ki gafarceni wallahi ni kadai nasan halin da nake ciki a wannan masarautar.”

Bangajeta Jakadiya tayi har sai da ta fasa kanta jikin bango ya fara zubar jini kafin ta kalleta tana nunata da hannu.

“Ban da Tausayi kan kowa, kamar yadda nima ba a tausayamun a rayuwa ba,ni ma,bazan taɓa tausayawa wani ba, don haka kada ki taba tunanin cewa zan tausaya miki koda kuwa na dakika gudane,bana fatan ci gaba ga rayuwar kowa a cikin Masarautar nan kuma indai ina da rai ina numfashi sai na tarwatsa ta.” Tana fada ta fice abinta.

Cikin kuka Safina ta dauki kyallen dankwalinta tana daure wajen da jinin ke zubar mata.

Jakadiya na fita ta sanar da ma’aikata kan cewa a tura daya daga cikin Nurses din Masarautar su duba Safina ta samu rauni.

*****

Gaaji Tunda tasha furar da asuba yau ta gagara ci gaba da sha ji tayi duk ta gundureta wannan ice cream da cake din da Adeel ya bata jiya kawai take son ci da sha.

Tana ta kokarin daurewa amman ta gagara ga wata irin mssufaffiyar yunwa da take ji.

Duba fridge din dakinta tayi ta ga, ga ice cream Amman kamshinsa ba irin wanda take so ba,

Strow-Berry ne ita kuma Vinila take so irin wanda Adeel ya bata jiya.

Ganin bata da wani Option yasa ta tashi ta zumbura hijabi, har zata fita ta kara dawowa ta cire hijabin ta zare doguwar rigar jikinta ta sa riga da sket sannan ta kara sa hijabin ta leka ta ga Uwar Soro na cikin Bed room dinta.

A hannu ta rike takalmanta tana takawa a hankali har ta fice.

Tana zuwa Part din nasa ma ta cire takalmi , Shamaki ya tsaya kallon mamaki ita kuwa ko kallonsa batai ba bare ta tsaya kulasa.

Takawa take a hankali kar yaga motsinta yana cikin bed room shi ma hankalinsa na kan System yana aiki.

Tun shigowarta ya ganta ya sunkuyar da kai kawai ya ci gaba da aikin da ke gabansa.

Ita kuwa tunaninta bai ganta ba, ta bude fridge din a hankali aiko da ice cream din ta fara cin karo da sauran cake .

Kasa hakuri tayi agun ta fara cin cake din, ta cika bakinta da cake ga Ice Cream a hannunta dago wan da zata yi kawai sai ga Adeel gabanta yana murmishi.

Kunya kamar zata nitse tama rasa yadda zatayi tsayawa da tauna cake din tayi tana neman hanyar guduwa.

Ta juya zata tafi Adeel ya rike hannunta.

“Ina zuwa? Ai tunda kika zo sai kin cinye zaki tafi kuma.”

Ya jata ya zaunar da ita, ya karo mata cake da ice cream din.

Ganin kunya ya hanata ci, ya ce, “tunda kin kasa ci bude bakin ni in baki to.”

Girgiza kai tayi. Alamar aa.

Ya ce, “to maza ki ci ko ni in miki dure da kaina.”

Kau da kanta tayi ta Ci gaba da cin abunta tayi tamkar baya wajen don ji take kamar tana ci ana kwashewa.

Tana cikin cin cake din tayi wata irin kwarewa da sauri ya riketa, tallafotan da zaiyi ta sake masa amai ajiki mai tun daga kan kirjinsa har cikin jikinsa.

Zaro Idanu tayi azuciyar tana fadin, “Na shiga uku.”

Shi ko bata kansa yake ba sai ya bige da fadin, “Sannu sannu ki dinga ci a hankali.”

Ya karasa fada yana rike ta, ya kaita toilet ya bata ruwa ta kuskure baki, sannan shi ma ya cire rigar ya wanke jikinsa ya fito.

Jiki a sanyaye ta ce, “ka yi hakuri ban san amai zanyi ba.”

Ya ce, “tunda kinyi aman cake din ki sha ice cream din ko shi zai zauna a cikin naki sorry.”

“Aa na koshi.” Ta fada cike da tsoro.

Adeel ya fahimci tsoro take ji, hakan yasa ya ce, ” Ki dauka to ki tafi dashi Part din ku ki sha.”

Ya fada yana dauka ya mika mata.

Karba tayi ta fice da sauri zuciyarta tana, “ai kuwa ina ga yau da ban sha ice cream din nan ba mutuwa zanyi.”

Haka ta lallaba ta kara komawa nan ma a tunaninta Uwar Soro bata ga fitarta da dawowarta ba, ta cire kayan sannsn ta fito Parlour tana shan ice cream din.

Tana cikin sha, Uwar Soro ta fito ta zauna kusa da ita.

“Uwata kin dawo kenan?”

Cike da kunya Gaaji ta ce, “ni? Sai kuma tayi shiru.

Murmushi ta yi ta ce, ” Na san Adeel na da ilimin addini da na boko kuma bana zaton zai iya kokarin aikata wani abun da bai dace ba, duk cewa mun yi kokarin danne gaskiya domin canja shi, na san ya san abin da yake koda bai bude baki ya furta komai ba, Zainab yanzu fa kin tashi a sahun Yara, ba batun shekaru bane Amman kin kai gabar da ya kamata kinsan wasu abubuwa.”

Gaaji ta ajiye Cup din Furar da ta gama sha gefe tana kallon Uwar Soro.

“Eheen, kin tashi daga sahun yara, yanzu ke matar aure ce, kuma ke uwa ce, ina jinki acikin jikina tamkar ‘Yata ta cikina duk da cewa Allah bai bani haihuwa ba, amman banjin cewa akwai wata hallita da na so a doron duniya fiye da soyayyar da nake miki, ba zan so abun da zai cutar da ke ba, kuma ba zan so abun da zai cutar da Yareema ba domin shi ma ya jima da zama jinin jikina.”

Gaaji ta ce, “amman ai kinfi sona da shi ko?”

Murmushi Uwar Soro ta yi tana, “dukanku ina sonku mana, kin ga yanzu abun da nake so in tunatar da ke masu mahimmanci shine, ki Kasance mai goyon bayan mijinki duk rintsi duk wuya, kina tare da shi, kada ki taba bari hawayensa su zuba mudin hannuwanki zasu iya tarewa.”

Gaaji ta taɓe baki, “To ni fa bana son shi, ni inna haifa masa babynsa ina zan koma gun Yaayah ne?”

Uwar Soro ta mata harara da gefen ido, “ki kiyaye ni fa, kenan ba kya son zama dani? Bare ma kina son shi, kila lokacin fahimtar hakanne bai zo miki ba, kuma ki mun shiru kiji abun da zan fada miki don wannan shine sako mafi daraja da kowacce mace indai zata rike a gidan aure ta gama samun daraja da kima a idanun mijinta.”

Ta yi shiru na seconds kafin ta ci gaba da maganar.

“Batun zamtowa tamkar bango abin jingina ga miji na da matukar muhimmanci, kome zaiyi indai bai saɓawa shari’a koda duniya zata juya masa baya ke ɗaya ki zam gatansa kuma kada ki karaya ko kiji cewa bazai iya ba koda hakanne zai kasance a karshe, Ki kasance mai tsafta kowanni namiji na son tsafta mussaman Yareema da bai shiri da kazanta sam sam, kasancewarsa miskili agunki ba abakin komai yake ba, yadda ya ke Sonki cikin ruwan sanyi zaki canja shi yadda kikeso kila in ya fara surutu har sai kince kin gaji ya yi shiru, dole zaki karanci abubuwan da yafi so ne, kema koda bakya so ki koyawa kanki so ta nan baza ku taba rasa abun hira ba,kuma hira tsakanin mata da miji na kawo mafita sosai a zamantakewar aure,ta yadda ba wanda zai iya rike wani a zuciya,ku zam tamkar aminai.”

Uwar Soro ta gyara zama.

“Ki kara bude kunnuwanki ina fada miki abubuwan da zasu amfaneki ne har ma ki fadawa ‘Ya’yanki nan gaba.”

Gaaji kuwa kara zuba mata ido tai tamkar wacce ke kallon tv.

“Batun kaya, ya kasance a duk lokacin da kike tare da mijinki kayan jikinki su kasance na daban, na Mussaman kuma, wanda koda daga ido ya yi ya kalleki duk bacin ran da yake ciki zai ajiye su gefe zuciyarsa tai sanyi, babban abun kuma kada ki taba gazawa a fannin shimfidar mijinki, ki zam gwana mai neman duk wata hanya da zaki bi don ya samu biyan bukata kuma ya gamsu, Kada kice don sabani ya hadaki da miji zaki horasa ta waje biyu, girki ko shimfida aa ban baki wannan shawarar ba, kuma ban umarceki ba, domin hakan kamar kin kashe kanki da kanki ne, ki masa komai yadda kika saba, in kika dauke duk wata walwala da ke fuskarki hakan ma kadai wani babban hukuncine da zai fahimci kuskurensa kuma ku zauna ku sasanta ba tare da sanin kowa ba, hatta ni ba bukatar na sani, duk wani abu tsakanin ke da mijinki sirrine kada ya fita tsakaninku.

Girki koda cewa anan masu aiki keyi amman akwai dole abun da zai zam kina bukatar yiwa mijinki da kanki kin ga jajircewa ya zama dole kenan a gunki.”

Gaaji ta cuno baki tana, “Tom ni ai ban iya girkin ba, Yaayah ya fara koya mun kuma muka dawo nan.”

Uwar Soro ta ce, “ni zan koya miki ai da kaina, a yanzu kam ba zan taba bari ki koma gun Yareema gabadaya ba duk nacinsa saidai ku hadu ki dawo har sai kin haihu kafin komai ya daidai an sanar da Mai Martaba sai ayi duk wani abun da ya dace, zamu yi hatta tsumin da ya kamata kowacce matar aure tana sha wanda zai kara mata lafiya da ni’ima, don banso inji kin fada neman wasu magungunan mata marasa amfani da seti garin gyara a bata komai.”

Gaaji ta ce, “To wai yanzu duk wacce tayi aure sai an farfada mata abubuwan nan kuma an koya mata abubuwan da kika ce dinnan?”

Uwar Soro ta ce, “Eh mana duk Uwar da ke son ganin ta inganta rayuwar Auren ‘Yarta ai dole ta fada mata gaskiya kuma ta daurata akan hanyar gyara tare da koya mata dukkanin wasu abubuwa da suka dace, har ma da wa inda ban fada miki ba, kin ga a hankali zamuyi amfani da wannan damar kafin ki haihu ki fahimci komai don tunda aka fara zaryan daukan nan kila sai dai abu ya canja ba tare da na ankare ba, gwanda in fara tararki da su tun yanzu.”

Dariya Gaaji ta yi tana, “Nikam ba ruwana da shi ai kuma.”

Sallamar Adeel ce ta katse su duk suka zuba mishi ido.

Uwar Soro ta kalleshi ta ce, “Ah Yareema kaine? Shigo mana ka zauna.”

Hannunsa rike da Leda yaje ya zauna yana satan kallon Gaaji.

Ita kuwa data lura yana kallonta sai ta kawar da kai kamar bata san me yake ba.

Haka ya zauna rike da yar ledarsa ya kasa sakewa.

Duka dakin ya dauki shiru na tsawon seconds Uwar Soro ta katse shirun da fadin, “Ko za muyi magana ne ta bamu waje?”

Adeel ya girgiza.

“To mene ne kuma a ledar?” Ta tambayesa.

Fara sosa kai ya yi alamun jin kunya ya ce, “Na Zainab ne.” Ya karasa fadan Maganar yana kallonta.

Uwar Soro ta yi Murmushi tana tashi daga Parlourn ta ce, “Ka ga ma ka tuna mun yau akwai baki a Fada kuma ina so mu gaisa kila ma har sunzo.”

Ta yafa gyallenta ta fice.

Tana fita Adeel ya tashi ya koma kujerar da Gaaji take, 1sita ce amman don jaraba sai da ya zauna ya matseta jikinsu na shiga na juna.

Shagwaɓe fuska Gaaji tayi tana kokarin tashi, kam ya riketa.

“Ina zaki je? Ai ba inda zaki je ai kuma.”

“Ka matse ni.” Ta fada kamar zata yi kuka.

Dagata Adeel ya yi, ya daurata a cinyarsa yana sakala kansa ta gun wuyanta ya ce, “Yanzu fa? Ai ba ki matsu ba ko?”

Kara turɓune fuska tayi ba tare da ta ce komai ba.

Lumshe idanunsa ya yi, yana wata irin ajiyar zuciya ,yana shakar kamshin dake tashi a cikin jikinta.

Dumin numfashinsa na sauka a jikinta ji take kamar ta hankadesa ta gudu amman ba dama ya riga ya riketa.

“Iyee Zizi? What’s wrong? Ba za ki yi magana ba? ba wannan ba ma wannan wani irin kamshine haka yake tashi a jikinki? Sai kace wacce take wanka da ruwan turare?”

Ji tayi kawai bakinta ya furta, “ai daman da shi nake wanka.”

“Really? Inzo zaki sammin kenan?” Adeel ya fada.

Nan ma bata ce komai ba tayi shiru.

Adeel ya kara da , “Wai duk ina bakin tsiwar nan ne? Ki sake jikinki fa ni ba abun da zan miki, gashi na ga kina son su ice cream dinne na je na karo miki.” Ya fada yana dago mata ledar.

Ta karba ta ajiye tana sunkuyar da kai.

Adeel ya fara kokarin daga mata riga, da sauri ta rike da hannunta hawaye na shirin zuba, “Don Allah kar ka mun komai har yanzu ina jin zafin No…” Sai kuma tayi shiru.

Murmishi ya yi, “Ni ba breast dinki zan taɓa ba so nake na gaisa da babyna za muyi sirri.”

Ya kara sa hannu zai cire, ta danne.

Ya dago ya kalleta ido cikin ido nan take jikinta ya yi sanyi ya yi mata wani irin kwarjini ya ce, “Ko ki bari in yi magana da babyna ko in miki abun da bakyaso duka biyu mussaman dayanma da kika fi tsoro.”

A hankali ta zame hannunta ya daga rigar sama sannan yasa hannunsa yana shafa cikin, “Hi Baby Boy, Little Prince, Am Ur Dady, How Are You? Na san kana lafiya ko? Alhmdu Lillah, na kawo maka karar Momynka ka ce mata ta daina tsoron Dadynka kuma ta zama jarumar mata domin matsoraci baya taɓa iya zama gwani, da dai nasan ko me zan mata bata tsoro amman yanzu inma kaine kake zugata gwanda kace mata ta daina kuma adinga bawa Dady Hakkinsa ka ji ko? Yawwa Good Boy.” Ya kai bakinsa kan cikin ya masa kiss sannan ya ce, “Byebye, Ur Dady Luvs U So Much.”

Ya kara shafa cikin ya kalleta yana, “wai tsakanin nida ke waye baya dariya ne? Kullum fuska a cunkushe a kumbure kamar bread ko fashewa za kiyi ne? Ni fa na gaji da kumburin nan yau sai kinyi mun dariya.”

“Umm umm umm ni.” Gaaji ta fada.

“Sai kinyi fa.” Ya fada yana yi mata cakulkulu.

Bata san lokacin da ta fara dariya tana wangale baki har sauti na fita ba.

Tsayawa ya yi kawai yana kallonta yadda dariyar ta kara mata kyau.

Ta kai tsawon Minti guda tana dariya .

Shi ko harda tagumi yana zura mata idanu, sai da tayi mai isarta sannan ta daina a lokacin ta lura da kallon da yake mata, da sauri ta sunkuyar da kai tana wasa da hannunta.

Ya ce, “Ban gaji da kallon dariyar ba ai ki ci gaba.”

Kiran sallar da ya ji anyi ne yasa shi dagata a cinyarsa ya zaunar da ita akan kujerar ya ce, “Ki shirya zan dawo a part dina zaki kwana yau ma.” Ya karasa maganar yana fita da sauri kar ya rasa jam’i.

Yana tafiya ita ma ta shiga dakinta tana, “Taɓ ba inda zani aradun Allah barcina anan zanyi, kuma zaka ga Baby Boy ai, In Sha Allah Mace me kama dani zan haifa kwalelenka, haka kawai sai naje na gama sake jiki da kai ka mun mugunta ko zaneni, wayasani ma ko kace zaka kaini wannan dakin duhun.”

Ita kadai ta dunga sambatu…

*****

Ni dai kam ban san mafita ba a yanzu kuma, Mai Martaba ya yi fushin da ban taba ganinsa ciki ba, sannan ya tabbatar mun da cewa ba wani auren sirri da za ayiwa Yareema har sai Waccer Yarinyar ta sauka an samu gamshashshiyar amsa, hankalina ya matukar tashi domin hakan barazana ce Babba ga rayuwar Yareema, har ma dani da ma masarautar nan gabadaya.”

Hajiya Maimuna ta ce, “Gaskiya ban ji dadin hakan da mai Martaba ya ce ba, amman nafi alakanta wannan lamarin da sa hannun Fulani Kilishi zata iya komai don tabbatar da tabarbarewa tsakanin Yareema da Mai Martaba,kuma Allah ya fita, duk hakan baza mu karaya ba,ina dai wannan yarinyarce ta kawo dukanin matsalolin nan? Zan samo hanyar katseta cikin gaggawa In Sha Allah.”

Fulani Babba ta ce, “Allah ya bada iko, kuma ya tabbatar, Ni yanzu wallahi duk hankalina ma yafi kwantawa ga yareema ya auri Nasmah fiye da Khaleesa,ban yarda da Hajiya Rabi ba sam sam zuciyata ta kasa aminta da ita, Mussaman yadda naga suke fadi tashi tare da Fulani Kilishi.”

Wani irin Murmushin ƙeta ta gefe Hajiya Maimuna ta yi kafin ta ce, ” kar ki damu daman yanzu duniyar nan sai hakuri mutanen cikinta ba kowa ke da amana da gaskiya ba, Allah dai yasa mu dace, amman Don Allah ki kwantar da hankalinki daga yanzu zuwa gobe zan gwada kokarta kawo sauyi.”

“To Allah ya tabbatar mana da Alkairi, Allah ya bar zuminci na gode sosai da halarcinki gareni.”

Fulani Babba ta fada.

Hajiya Maimuna cikin fara’a ta ce, “Ah haba dai ai mun jima da zama ɗaya yiwa kaine Mussaman ma yanzu da Nasmah zata kara hada karfin zumuncin.”

*****

Jakadiya na gama yi masu labe tana fita ta canja kaya,ta shige cikin Jeji wajen Bokanta.

Jikina rawa rai bace ta durfana gabansa.

Ya sake wata irin gigitacciyar dariyar da ya saba kafin ya ce, “Ke ai bakya jin magana, don haka aikinki bazai taba samuwa yadda kike so ba, muddin baza ki bi umarnina ba.”

“A gafarceni amman nayi iyaka bakin kokari na wajen ganin na samo wannan yarinyar lamarin ya gagara duk nacina da son jin kwakwaf dina ban samu labarin wannan yarinyar ba, kuma ban ganta ba, sannan ban kara gamo da wasu aljanu ba kwanakin baya har ya kai ga ina ganin Uwar Goyon Yareema ta shiga Fada na kan je bangarenta da kaina nayi bincike amman bana taba samun komai, hatta bangaren shi ma Yareeman na sha satan hanya inje amman amsar guda ce babu canji bana cin karo da kowa.”

“Haaaaaahaaaaahaaaaa lallai rayuwar ki tana cikin Tekun maliya, yayin da Aljanu tamanin da tara kadai suka isa su iya tallafoki su ciroki.” ya karasa maganar yana buga kasa wanda gabaɗaya sai da ta gaure wajen ya canja kala na tsawon seconds.

Murya na rawa JAKADIYA ta ce, “Ataimaka mun a cironi bana son farinciki ya tabbata cikin wannan Masarautar daidai da na dakika guda, Gwanda rayuwar kowa ta ruguje ciki kuwa harda ni, yanzu wata ce tazo da ciki wai Yareema ne ya mata na yi mata kashedin cewa ko ta sanar daga yau zuwa gobe ko kuma ta yi asarar rayuwarta, sannan wani bangaren kuma suma suna nasu kokarin da ban san shirinsu kada a ruguzamun nawa.”

“Dole fa a koma batuna na farko ya zam wajibi ki nemo wannan yarinyar domin ba zaki taba iya daukan fansa a masarautar Benoni ba muddin tana ciki, kuma mutane na sun tabbatar mun da cewa a yanzu babu wacce Yareema yake kauna sama da ita , sunyi aure har tana dauke da cikinsa a jikinta, kinga kuwa wannan yarinyar ta haihu bake bama duk wani mai mummunan motsi cikin wannan Masarautar sai ya gagara.”

JAKADIYA ta rike kirji cikin jin mamaki.

“Aure? Aure kuma? Yareema ya yi aure? Taya kenan? Yarinyar da tazo dai cewa tayi ciki ya yi mata ba tare da aure ba, to ko dai ita ce matar tasa dalilin da yasa tayi shiru kenan? Ko dai ita ce yarinyar?”

Dariya ya yi yana juya kansa sama da kasa, “Wannan kuma ya rage naki,ko kije ki nemota ko kuma shirinki na shekara da shekaru ya ci gaba da tarwatsewa in kin nemota ki dawo tukun nan ne aikinmu zai fara.”

Jiki amace JAKADIYA ta tashi kanta na juyawa kwakwalwata na kara birkicewa.

Tafiya take tana maimaitawa , “Yareema? Aure? Aure? Ciki? Haihuwa? Yarinya? Wallahi bazai saɓu ba, ba zai taɓa sabuwa ba, aaaaaa, aaaaa,,sai dai duk mu rasa komai, kowa ya rasa rayuwar kowa ta rushe ba zan taba bari ba wannan alƙawari ne.”

Tana wannan sambatun har ta koma cikin masarauta .

Bangaren Adeel ta fara yi tana, “indai ko waccer yarinyar ce zan gane ko yana zuwa gunta da dare ai don haka part dinsa zan fara dubawa ko yana ciki ko baya nan.”

Ta kalli Part din Uwar Soro tana , “Ina dawowa sai na duba nan dinma ai daga yanzu ba daga kafa wallahi ko a mutu ko ayi rai.”

Tana dosan Part Adeel kuma yana fitowa da Gaaji kenan ya rikota tana…

Ga Jakadiya ga Gaaji, ga Adeel

Ya za ta kaya?

<< Auren Wata Bakwai 19Auren Wata Bakwai 21 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×