Adeel na hangota ya yi saurin komawa Part din Uwar Soro, motsin da yake yasa Gaaji farkawa, zata yi ihu kenan ya rufe mata baki da hannu.
Ya shige Bayan kofa da ita.
JAKADIYA ta murza idanunta domin ita dai tana tunanin ta ga kamar Yareema ne dauke da wata amman kuma cikin seconds guda sun ɓace mata.
“Ah ah kamar Yareema ne dauke da wata fa, ina jin ma yarinyar nan ne kuma sun ɓace mun, bara dai in leka part dinnan mu ga.”
Ta fada tana tura kofar Part din Uwar Soro.
A karfi ta tura kofar tana bankadawa har sai ta ta bige kan Gaaji, Adeel ya kara danne mata baki ganin zata yi kara.
Ta shige tana duddubawa.
Ta duba ko ina ba kowa ta dawo ta rike kofar zata ja.
“Oh Allah, kar abun nan ya zam na haukace fa basa nan ba alamar mutum ma.”
Har ta fara ja sai kuma ta sake zata duba bayan kofar kenan ta ga gilmarwar mutum zai wuce bangaren Adeel.
Da sauri ta sake kofar ta fice.
Adeel na rike da Gaaji tana ta wutsil-wutsil tana son sauka yaki saketa.
Lekata ya ke da idonsa ta gefen kofar.
Da sauri ta yi wajen Part din ta ga Shamakine ya dawo daga fada ya zauna awajen zamansa.
Tsaki ta yi sai kuma ta ce, “Kai Shamaki Yareema fa yana ciki kuwa?”
Shamaki ya ce, “ehto bara in duba miki dai.”
Ya shiga ya je ya duba, sannan ya fito ya ke sanar mata, “Yareema baya ciki fa ina ga daga Masallaci bai dawo ba ko ya fita.”
JAKADIYA ta ce, “anya? Kai kam dai kaji tsoron Allah Shamaki, Fulani ce ta ce in dubo ko yana nan fa.”
“Allah kuwa da gaske nake.”
Shamaki ya fada.
JAKADIYA ta ce, “Bara dai in duba da kaina don ban yarda da kai ba.”
Ta karasa maganar tana kutsawa cikin Part din.
Duk lalubenta bata ga alamar Yareema bare wata ‘Ya Mace.
Hakan yasa ta fito aranta tana fadin, “yanzu haka ma waccer matsiyaciyar yarinyar ce yana tare da ita, aikuwa yanzu zan je indai ya tabbata ita ce komai yazo karshe ai kuma nikam Alhmdu Lillah.” Ta fada tana wucewa cikin Masarauta.
Adeel na ganin wucewarta da sauri ya fito ya shige Part dinsa da Gaaji Shamaki ya bisa kawai da kallon mamaki.
Yana shiga bed room ya wuce da ita ya sauketa kan bed yana cire hannun sa abakinta.
Kakakin Aman wahala ta fara yi , duk tayi zufa, da sauri ya rikota yana , “Amai kike ji ko? “
Rufe bakinta da hannu tayi tana girgiza masa kai alamar eh.
Sungumarta ya yi, ya kaitsla toilet aiko suna shiga ta fara kurma amai sai da ta zubar da duk abun da ke cikinta.
Tana yi yana shafa mata baya, “Sorry, Sorry Dear kin gama?”
Gaaji ta girgiza masa kai.
Ruwa ya sa mata abaki ta kuskura ya wanke mata fuska sannan ya dauketa ya maidaita kan gado duk jikinta ya mace ba karfi ko kadan.
Ta ce, “Zan tafi in kwanta don Allah.”
“Ki kwanta anan, ai na ce miki anan zaki kwana yau , yanzu ki huta anjima sai ki sha ice cream ga cen da su Cake din duk nasa an siyo miki.”
Ita dai bata kulashi ba domin ta riga ta gama jigata har wani jiri-jiri ne ke dibanta.
Sai da ya bari ta huta ku san minti biyar kafin yaje ya dauko Ice Cream ya hau kan gadon yana, “yanzu nasan zaki iya sha tunda duk kin amayar da abun da ke cikinki.”
Ta girgiza kai da sauri domin kamar yasan yunwa take ji.
Ya kara matsawa daf da ita, “Yawwa ni zan baki da kaina bude bakin.”
Bude baki tayi yana bata ice cream har ta sai da ta ji ta koshi ta ce, “Na Koshi.”
Adeel ya ce, “Yawaa to bara in ajiye ko, da fitarsa zuwa aje Cup din Ice Cream din da dawowarsa baiyi cikakken minti biyu ba amman wai har barci ya kwasheta, kuma ta kankame jikinta da hijabi ta yadda bazai iya cirewa ba.
Da mamaki ya kalleta yana dariya, “Oh Allah Allâhumma yahdikhi Zizi.”
Ya cire kayansa yasa na barci shi ma ya kwanta daf da ita suna shakar numfashin juna.
Har barci ya dauke sa shima.
*****
Jakadiya kuwa tana zuwa ta tarar da Safina ita kadai hankali tashi.
Ta karasa gabanta tana fadin, “Yareema yazo nan ko? Ki fadamun gaskiya, kuma Yareema ya aureki ko?”
Ta fada tana rike ma Safina gashi.
Cikin mawuyacin hali Safina ta ce, “Aa na rantse da Allah aa bai aureni ba, kuma baizo nan ba.”
Ta kara fisgar mata gashin, “wato dai ba zaki fadamun gaskiya ba? Kin fiso ki ci gaba da wasa da rayuwar ki kina ganin bazan iya illata ki da gaske ba ko? To kinyi babban kuskure kuma na ji a jikinsa cewa ke ce wannan yarinyar da nake nema, don haka zuwa gobe kiyi saurin gaggawar aikata abin da na umarce ki.”
Ta fada tana saketa ta fice aranta tana sakawa, “Tabbas daga ta aiwatar da kudirina na farko na biyun kuma da kaina zan aiwatar akanta ita ce, babu shakka ita ce.”
*****
Can cikin dare kamar a mafarki Adeel ya fara jiyo Gaaji na shesshekan kuka.
Yana tashi ya ganta gefen gado ta takure tana ambaliyar hawaye.
A tsorace ya riketa yana, “Lafiya zizi? Me ya faru? Me aka miki? Ko wani abu kike so? Fadamun.”
Cike da shagwaba cikin Muryar kuka ta ce, “Duk Jikina ciwo yake mun.”
Wata ajiyar zuciya ya yi kafin ya ce, “har kinsa na tsorata, yanzu in danna miki kike so?”
Ta ce, “Eh.” A sanyaye.
Oya to kwanta.
Ya riketa ya gyara mata kwanciya sannan ya fara bin jikinta a hankali yana danna mata..
Shiru tayi tana jin dadin dannar da yake yi mata, Prince Adeel ya ce, “haka ko? Yanzu jikin ya daina miki ciwo.”
Ta ce, “Eh.” Cikin yanayin samun Nutsuwa.
Ci gaba da bin jikinta ya yi ya dawo harta kafarda yana danna mata.
Ya ce, ” Zainab.”
Ta amsa tana mamakin jin cewa tunda take bau taba fadan sunanta sai yau ko Gaajinma baya cewa da sai ke, yanzu kuma da yake iya kiranta Zizi yake cewa.
sai kuma can ya yi shiru.
Tukun ya numfasa ya ci gaba da fadin, “Ban san ya zan furta har ki fahimta ba, amman kin shigo cikin rayuwata kuma kin chanja komai na cikinta ko ince kina cikin canjawan ma, I have Lost Total Control of my Self, I am a changed Person, ba Prince Adeel din da ba, My Heart Does not Belong Anymore To me. It’s Given away to you, da ina yiwa duk wani namiji da idonsa ke kan mata ko yake batun aure kallon mara tunanine wanda bai san abun da ya kamace shi ba, ashe nine mara tunanin kuma na gagara sanin abun da ya kamace ni? Ashe zuwanki cikin rayuwata haske ne da ban taba mafarkinsa ba?”
Ya yi ajiyar Numfashi yana ci gaba da yi mata dannar kafin ya ce,
“Ban san me zanyi ba babu ke, kuma ban san ya zan rayuwa ba, in babu ke, watakila ba zan kara samun damar fada miki abubuwan da ke kunshe cikin zuciyata ba, but i just want u to know that u mean the World to me, kuma ina so in fada miki, Ina so in sanar da ke, kalmar da banjin cewa ko cikin mafarki na taba kokarin fadawa wata ‘Ya Mace, umm amman ban sani ba ko hakan zai miki dadi ko akasin sa, nidai burina kullum ki Kasance cikin Farinciki da ingantacciyar lafiya ko hakanma kadai ganin cikin walwala zai faranta mun nima, ummm.”
Sai kuma ya tsaya dannar ya yi shiru .
Can ya ce, “ina so ince kawai umm , I just want to say… I…. ya kara yin shiru sai da ya yi ajiyar zuciya kafin ya ce, “I love you, ina sonki, ina sonki Zainab ina so inyi rayuwa da ke har karshen numfashina, don Allah kar kice zaki barni, in kika ce zaki barni tamkar barazana ce babba ga rayuwata.”
Gaaji ko bata ma san yana yi ba tun farkon jawaban da ya fara ma a sama sama tajisu tunda ta samu abun da take muradi tuni barci ya kwamusheta.
“Kin yi shiru baza ki ce komai ba? Ba kya sona ko? In dai haka zaki furta ma Gwanda kiyi shirun Please, but kice wani abu mana kinji.” Adeel ya fada yana leka fuskarta.
Ganinta ya yi tana barcinta hankali kwance wanda kallo daya wadatar a fahimci cewa mutum ya dade da yin barcin.
Ajiyar zuciya ya kara yi karo na uku yana goge zufar da ke keto masa ya gyara mata kwanciya sannan shi ma ya kwanta.
Kallon saman dakin ya dunga yi har barci ya kwashe sa.
*****
Cikin dare kawai safina taji filo a fuskarta ana danneta, kokarin rabata da numfashinta ake tayi karfi da ya ji.
Tana ta kokarin kaucewa amman ga dukkan alamu mutane biyune zuwa uku akanta kuma kowa baya da burin da ya zarce ace ya tsaida numfashinta.
Kyakkyawar kara ta gagara, sai motsin da taketa kokarin yi, gashi an kashe wutar bangaren gabadaya duhu ne ta ko ina ba a iya gano komai bare batun bambamcewa.
Jefa hannayenta gefe kawai take, aikuwa tayi nasarar cafko wani cup din tangaran, bugawa daya a cikinsu tayi sai da kansa ya fashe, ta samu da kyar ta kara bige sauran ta mike tana neman hanyar fakewa.
Dukansu ukun suka hadu kanta suna duka ta ko ina, ta samu da kyar ta riko kawunan su biyun ta hada da juna ta gwara.
Dayan ya ja mata kafa sai jinta tayi kawai akasa dim.
Suka kara bajar da ita suna rike mata hannaye.
Dayan ya dauko pilon zan kara maida mata tayi wani irin tashi tana cizon hannun na gefenta.
Shi ko wancen nasa mata filon ta saki wata irin gigitacciyar kara da saida duka masarautar ta dauka.
Dakarai, dogarai, da sauran mutanen ciki duka suka nufi Part.
Ana kunna Wuta aka ga Safina ita kadai hannu rike a wuya tana wani irin mawuyacin numfashi, ga jikinta duk jini da wasu irin manyan ciwuka, ciwon goshinta ya kara fashewa ban da jini babu abun da ke bulbula.
Da sauri aka dauketa aka shigar da ita asibitin masarautar aka fara bata taimakon gaggawa.
Sarkin Fada yasa wasu dakarai su tsaya suyi tsaronta har zuwa safiya kafin Azauna da Mai Martaba a Fada.
Haka kuwa aka yi suka zauna tsaronta har safiya.
Adeel na tafiya masallaci Gaaaji ta lallaba ta koma Part din Uwar Soro tana yin Sallah ta koma barcinta.
*****
Karfe Goma na siya, Fadar Masarautar Benoni duk wani mai rayuwa cikin Masarautar ya hallara ga wannan zaman kasancewar sa zama na gaggawa da Mai Martaba ya bi ayi.
Dukanninsu suna durkufe gabansa, ya yinda bangaren Fulani Babba da Fulani Kilishi daban haka ma na Adeel.
Safina na tsakiya jiki duk ciwuka da bandeji an rurrufe, idannunta gabadaya sun yi cicciki fatar wajen sun kumbura, yanayin kamanninta har sun fara sauyawa.
Sarkin Fada ne ya fara Magana, “Baiwar Allah me ya faru dake cikin daren jiya? Mai Martaba na bukatar jin ba’asi daga bakin mai ita.”
Safina da har yanzu a tsorace take ta kasa magana jikinta rawa kawai yake.
Sarkin Fada ya kara fadin, “Ke yarinya kina fadar Mai Martaba Sarkin Masarautar Benoni kuma saurarenki yake, ba a wajen wasa kike ba.”
Cikin muryar dimuwa ta ce, “cikin daren jiya ne wasu mutane suka zo zasu kasheni sunata danna mun filo a suna kokarin datsemun numfashi.” Sai kuma ta fashe da kuka.
Sarkin Fada ya ce, “Atakaice dai wannan yarinyar jiya an samu wa inda sukai kokarin kai mata hari cikin dare wanda ba don anyi sa’a dakarai sun ankare kan lokaci ba tabbas sai dai a riski gawarta da safiya.”
JAKADIYA suna haɗa ido da safina tana ta mata alamun magana da ido tana kaucewa.
Sarkin Fada ya kara da fadin,”Lallai koma su waye da wannan aika aikar suna cikin masauratar nan kuma bana fidda ran cewa suna zaune anan wajen ma.”
Yana fadan hakan dukkanin su suka yi wani turus gaba na bugun tara tara.
Gyaran murya Mai Martaba ya yi ya ce, “A shiga bincike lallai a binciko mun wa inda suka kai wannan harin kuma in akai nasarar samosu lallai akwai hukunci mai tsauri kansu kuma lallai a kara tsaro akanta da duk wani motsinta.”
“An gama Ranka Yadaɗe Uba ga Yareema miji ga Fulani Babba da Fulani Kilishi.”
Safina tai saurin katse shi da fadin, “Ina da magana Mai Martaba.”
Duka Fada tai shiru gabadaya ana saurarenta.
Safina ta ce, “zan fada gaskiya, nikam zan fada gaskiya ko zan huta da wannan ukubar rayuwar barazana ake mun da raina.” Ta fada hawaye na kwarara daga idanunta…
Jakadiya tai saurin katse ta da fadin, “Daman ai makaryaciyar ce ni fa sam ban yarda da ita ba Mai Martaba tazo ne kawai domin ta ruguza masarautar nan kuma babu shakka turota aka yi, jiyan ma yanzu haka hadin bakine ba wani hari da aka kai mata ban yarda da ita ba sam sam kawai ta fita ta bar Masarautar nan nasan yareeema bazai taba iya aikata abun da take nufin shi da shi ba wallahi sharrine.”
Safina na kuka ta ce, “Don Allah kuyi mun rai bansan wanni furuci zanyi a gasgata ni ba, Mai martaba kayi mun rai wallahi na san duk tsaron da za a samun sai sun ci gaba da bibbiyar rayuwata.” Ta karasa maganar tana tsugunawa gaban Mai Martaba.
JAKADIYA ce ta karasa inda take tana, “Munafuka, algunguma wacce bata fatan ganin zaman lafiya sai kin bar gidan nan a yau ko kinki ko kinso.” Ta karasa maganar tana jan Safina daga gaban Mai Martaba ta hankadata gefe.
Zata juyo kenan idanunta ya sauka kan kafar Safina, cikin wani yanayi sauri JAKADIYA ta tsuguna gabanta tana rike kafarta murya na rawa ta ce, “Keee…keee… ke…ce.