Ta karasa maganar tana daga kafar Safina.
Cike da rashin Fahimta Safina ta ke binta da kallo kawai ta ma rasa abun cewa.
Jakadiya ta rungumeta tana hawaye ta ce, “Ita ce, Wallahi ita ce.”
Dukanninsu suka shiga cikin wani yanayin rudu da zaƙuwa wajen son jin wace ce itan.
Safina ta ce, “ni ? Ni kuma wace ce?”
Tana kokarin matsawa daga jikin Jakadiya.
Kara rikota tayi tana, “Ke ce ‘Yata ta cikina da na haifa, na taka shekara da shekaru ina nemanki amman ban samu ba, Alhmdu Lillah Allah na gode maka da ya dawo mun da ke wannan farcen naki na babban dan yatsan Kafa shine ya tabbatar mun cewa kece Ɗiyata, Domin kalar kafatane sak da ke kuma a lokacin da na haife ki da shi kika zo duniya kamar yadda mahaifiyata ta sanar mun da cewa wannan shine gadonmu duk wani ahali namu na dauke da shi a kafa.”
Sai a lokacin safina ta daga ido ta kalli Jakadiya , Tabbas suna matuƙar kama sosai illa bambanci daya da zai iya ɓoye kamannin, Jakadiya baƙace, Safina kuma fara ce sol.
Rugumeta tayi tana kuka, “Me yasa to zaki barni? Me yasa kika banzantar da rayuwata tun ina da karancin shekaru? Kin san kalubalen da na fuskanta kuwa? Kinsan wahalar dana sha? Ba ki kyauta mun ba, baki kyauta mun ba sam.”
Jakadiya tasa hannu tana share mata hawaye, “Labarin na da tsayi kuma nima nayi nadamar komai, ki yafe mun ni…”
Sarkin Fada ne ya katse Jakadiya da fadin, “Ma Sha Allah, Alhmdu Lillah hakan ya yi sosai muna tayaki farinciki da samuwar ‘Yarki Jakadiya, amman duk da haka mudai muna bidar jin ba’asin gaskiyar zance kan batun Yareema.”
Jakadiya ta ce, “Mai Martaba ina neman afwan da a barni in gana da Ɗiyata domin tabbatar da asalin zance , babu shakka ba zan taɓa barin duk wani abu da zai cutar da Masarautar nan ba, kuma zanyi iyaka yina domin bayyanar da gaskiya.”
Sarkin Fada ya ce, “Maddalah da Jakadiyar Masarautar Benoni mai son ci gaban Sarki da ahalinsa, Sarki ya baki wannan damar kije ki bincika daga bisani sai asanar da Fada matsaya.”
Rike Safina tayi tana tafiya da kyar ta tallafa mata suka fice daga Fadar zuwa dakinta.
Sauran yan Fadar ma gabaɗaya fita akai jiki a sanyaye ana alhinin tare da jin mamakin kasancewar sabon al’amari.
Ƙofa Hajiya Rabi tayi tana takaicin cewa Jakadiya ta ɓata mata shiri.
Waziri ido ya yi kulu-kulu ciki ya kada.
Ita kuwa Fulani Kilishi gabadaya birkicewa tayi kan jin cewa Safina ‘Yar Jakadiya ce, ba shiri ta fice daga fadar cikin yanayin damuwa.
Suna shiga da sauri Jakadiya ta dauko first aid box ta gogge mata ciwon tasata tayi wanka ta bata wani kaya tasa sannan ta bata abinci ta ci, tasha magani.
Safina ta kalleta ta ce, “Ke ce mahaifiyata kuma da yanzu kin zama silar zuwana lahira, domin duk da bana ganin fuskarki da nake wancen dakin na rike muryarki kuma ban gagara fahimta ba.”
Jakadiya ta zauna tana dafata ta ce, “Tabbas dana tafka babban kuskure fiye dana baya kuwa a rayuwata, amman ina godiya da Ubangiji ya yi saurin nusar dani domin kuwa hakan ma ba karamar nasarar canja akala bace.”
Safina ta ce, “Kamar ya fa?”
Jakadiya ta yi Murmushi ta ce, “Ba wannan ba tukunna, yanzu bani labarin asalin dalilin zuwanki da gaskiyar lamarin, kar ki je komai yanzu ba wanda ya isa ya cutar dake.”
Safina ta ce, “Batun Gaskiya Yareema baiyi mun ciki ba, hasali ma duk harin da nake kai masa sai dai kawai ya yi Romance dani amman baya taba iya yin sex dani, wannan shirine a cikin Masarautar nan da aka shirya kuma mace da namiji ne masu gudanarwa, da farko munyi kokarin jan shi yaki bada hadin kai, shine aka masa asirin yadda zaina yawan jin sha’awa har ya mun ciki, asirin ya fara tasiri amman kuma sai dai ya tsaya a Romance koda ya yunkura wajen kusantata sai ya ƙi saboda taurin kansa ya yi yawa, shiyasa kawai shi wanda ake haɗa abun da shi ya mun ciki kan cewa in zo in nuna cikin yareema ne, kuma daman shirin namu akan lallai kada Ɗan Yareema ya mulki masarautar nan tunda tamkar gado yake garesu yara ɗaya suke haifa, in ya haifi Dan da ba da aure ba komai zai lalace kuma in munyi dace ma shi kansa bazai mulki Masarautar Benoni ba muna so Mai Martaba ya koreshi a cikin Masarautar nan gabadaya, ni ko kudine kawai damuwata.”
Jakadiya ta gyara zama, “Lallai ikon Allah kowa da damuwarsa ma wato, Amman wa innan su waye ne?”
“Waziri ne da Fulani Kilishi, cikin jikina na yanzu ma mallakin waziri ne.”
Jakadiya ta kyalyale da wata irin dariya kafin ta ce, “Sunyi mun aiki ba tare da saninsu ba, kuma zancen nan a haka zai zauna cikin jikinki na Yareema ne kuma ke zaki aure shi, sauran aikin ya rage nawa, burina na daf da cika, tabbas Mai Martaba da ahalinsa duk sai sun dawo karkashina a matsayin matsiyata kuma makaskanta, wa incen batun Fulani Kilishi da Waziri ki barsu ki shashantar da su bazan tona masu asiri ba muddin nima baza su tona mun ba, bare ma babu hanyar tonawan.” Dariya ta fara tamkar mahaukaciya.
Safina ta ce, “amman me yasa kike da burin tarwatsa Masarautar nan? Kuma me yasa kika jefar dani tunda yarintata?”
JAKADIYA ta zauna tana fadin, “Ina rayuwa cikin Masarautar nan ne kawai da zuciyar daukan fansa ban da hakan babu komai araina, Shekaru talatin baya lokaciin ina ‘Yar shekara Bakwai Aduniya Mai Martaba yasa aka yiwa mahaifina da mahaifiyata kisan gilla saboda kawai an kamasu da rashin bawa al’umma kayan hatsin da yake umarta abada duk karshen wata, su kan ba wasu, wasu kuma su hana, sannan in za su bada sukan raba kashi uku su bada ɗaya, kasancewar sune ke kula bangaren rayuwar al’umma hatta kai ga kowanni magidanci suna karban haraji agunsa ba tare da sanin Mai Martaba ba, ba sai ya zamto rayuwar al’umma ta fara shiga kunci, maimakon ya yi masu afwaa sai ya bi tsarin dokar masarautar nan duk wanda ya ya yi abun da ya karya doka har ya ja matsala ga al’umma hukuncin kisa ne kawai, a gaban idanuna aka kashe mun mahaifina, ko dan kasancewata karamar yarinya basu tausayamun ba, a karshe ma cikin bayi na ci gaba da rayuwa maimakon ajani jiki a rikeni tamkar ‘Ya, ni kuwa na dauki alwashi kamar yadda aka tarwatsa mun farinciki babu shakka shi da ahalinsa sai na tarwatsa masu, sannan kuma wazirin da ya miki ciki shi ne mahaifinki.”
“Mahaifina? Cikin mahaifina a jikina?” Safina ta fada hawaye na zuba mata daga idanu.
Jakadiya ta ce, “Kwarai kuwa, shi ne mahaifinki duk da cewa ya yi asara da ya kasa daina halinsa wanda ya kaisa da yiwa ‘Yarsa ta cikinsa ciki, amman kar ki damu shi ma baza mu barsa, a lokacin da nake matsanancin neman taimako kan lallai sai na maye gurbin Jakadiya a fadar nan shi kuma ya bullo da bukatarsa, wanda cikinki da haihuwarki a boye nayita, sai bayan ya umarci da in jefar da ke ne na dawo na ina dana sani na sanar da Mai Martaba an yi nemanki sosai amman ba a samu ba har mun fidda rai, amman gashi dawowarki ta zo mun adaidai domin da shirina in yiwa yareema Ƙurciya ya bi duniya ne, Mai Martaba kuwa guba zan sa masa, kinga yanzu kuwa saidai fada ta kasance mallakinmu, zaki zauna kan bakarki cewa cikin jikinki Yareema ne ya miki amman kunyi aure a boye kin ga shikenan baza a kore sa ba kuma Ɗan cikinki ya fita a sahun shege, kina zama matar Yareema komai ya dawo hannunmu sai yadda mukai da kowa cikin wannan masarautar, amman kafin nan fa akwai gaggarumar matsala Bokana ya tabbatar mun da cewa akwai wata yarinya da suke tare da Yareema sunma yi aure tana dauke da cikinsa da gaske kuma indai tana tare da shi duk abun da zamu yi baza mu taba cin nasara ba,
Aikin da ke gabanmu kan komai shine nemota kuma musam yadda zamuyi ko mu kasheta ko mu koreta daga wannan masarautar.”
“Wata kuma? Taya ma kuma har ya aureta?”
Safina ta fada.
Jakadiya ta ce, “Umm Allah kadai masani kuma yarda lallai akwaita domin yawanci yanzu duk abunda nake masa tsallakewa yake baya taɓa samunsa, Dadina ɗaya Mai Martaba na jin Maganata kuma ya yarda dani don haka zamu cimma nasara muddin muka samo wannan yarinyar,kawai dai mu haɗa kai da fata mu kai muyi kokari.”
Safina ta yi dariya, “ada nai mara dalili ma bare yanzu me dalili kuma? Anyi an gama kuma muna samun cikar burinmu Nikam zubar da cikin nan zanyi don ban san me zan haifa ba Ɗa na ne ko kanina? Gwanda dai daga baya yareeman ya mun asalin ciki wanda zai amsa sunan Ɗa na kuma jinin sarauta.”
Jakadiya ta ce, “Wannan duk ba matsala bace indai zamu samu nasara ai shikenan domin bani da babban tashin hankalin da ya zarce ace ana zaune lafiya cikin wannan Masarautar, shiyasa kullum nake cikin kutsa masu gaskiya da karya saboda kada zuciyar kowa ta samu salama, tun lokacin da aka haifi yareema nayi attempting sace shi amman aka samu akasi karshe ma aka fitar da shi kasar waje .”
Jiki na rawa Fulani Kilishi suke tsaye da Waziri ta baya.
Ta ce, “Yanzu Shikenan duk shirinmu ya ɓaci, ni gabadaya hankalina a tashe yake, kasan Jakadiya wallahi karamin aikinta ta tona mana asiri kuma tana tonawa Shikenan komai ya taɓe.”
Shi ma jikinsa a mace ya ce, “Ke kike cikin tashin hankali ko ni? Ai gwanda ke, ni tunda nake a duniya ban taba shiga tashin hankalin da ya kai wannan ba Ina cikin ɗimuwa ya zama lallai asamo mafitar da zamuyi gaggawan dakile faruwar hakan.”
Fulani Kilishi ta ce, “Hmm Burinmu na daf da cika wannan matsiyaciyar ta ɓata, ina ga bamu da wata mafita a yanzu da ya zarce a koma gun Boka shine kawai zai iya yi magana maganin wannan matsalar kuma ya kawo mana mafita cikin sauki.”
Waziri na goge gumin da ke keto masa ya ce, “Hakane, hakanne kawai mafita kuma ina ga yanzu daga nan ma zan wuce cen kawai.”
Fulani Kilishi ta ce, “Yawwa shikenan nima da daddare zamu haɗu Sai mu tattauna.”
Adeel zaune da Uwar Soro a parlourn ta.
Ta ce, “Wai ba zaka fito kayi magana akan lamarin nan bane? Ya kamata kayi magana domin anzo gabar da zaka magantu.”
Adeel ya ce, “Ban taba yiwa Mai Martaba karya ba kuma bana fatan inyi masa, shirun nawa shine mafita kawai a yanzu domin nace zanyi magana ban ma san me zance ba, kuma ban san ya zan yi ba.”
“Har yanzu ban amince cewa ka aikata ba kuma ina kan bakana,dole sai ka furta koma mene ne ko dan nemawa Zuciyarmu sanyi da kuma gujewa afkawa kogin wannan muguwar.”
Uwar Soro ta fada.
Adeel Ya ce, “ko da nayi yunkurin kwatanta wata magana Indai ina gaban mai martaba bana iya.
Fitowar Gaaji da bata ma san yana nan bane ya sa shi sakin baki yana kallonta.
Wata yar karamar riga ce pink a jikinta da dangale ana hango cikin da ke jikinta, ga gajeran wando wanda ya kama mata jiki surar jikinta ya kara fitowa sosai.
Kanta kuwa ko dankwali babu kitson kalaban da aka mata sun sassauka akan fuskarta da kafadarta.
Da ɗan gudunta ta fito wanda ko ina na jikinta ke motsawa ana jiyo sautin jigidar dake ƙugunta.
Ta fito tana fadin, “Baabata Bottle Water dina ya kare.”
Sai a lokacin ta lura da Adeel da ya zura mata ido.
Inda-inda ta fara…
Ta ma rasa me zata ce sai , “Umm umm.”
Tana sa hannu ajikinta tana kokarin rufewa.
Uwar Soro ta ce, “Alright ki dauka a fridge din Parlourn nan zan zo insa miki ana kinma.”
Da sauri Gaaji ta je Fridge din ta dauka tana kokarin komawa dakinta.
Uwar Soro ta kalli Adeel tana murmushi har yanzu hankalinsa na kan Gaaji .
Ta ce, “Wai me kake tunanine game da yarinyar nan?”
Bai ji ta ba sam.
“Yareema, me kake tunanine game da yarinyar nan?”
Ta fada daidai lokacin da Gaaji ke shigewa dakinta
A rude ya juyo yana, “Umm humm Nothing.”
Uwar Soro ta ce, “Kan batun karatunta Gaskiya akwai bukatar a samu matsaya tana da kokari sosai lessons din da Adnan ya yi mata tayi catching yanzu abubuwa da dama ta sani kuma tana fahimtar English ba laifi nima ina dan kara mata kuma tana dauka, inaga kuma an kaita makaranta na tabbatar da cewa zata fi haka kokari.”
Adeel ya ce, “Ba matsala sai a dauko wacce zatana yi mata special lessons in anga komai na tafiya daidai tukun sai ta fara daga secondary…..
Sai kuma ya yi shiru ya kara tafiya duniyar wani tunanin domin fitowar Gaaji a yau ya kara tada masa da sha’awarsa fiye da ko yaushe, wanda ya ke kokarin gaza rike kansa.
Hade kafafunsa ya yi,yana sunkuyar da kai yadda zufa ke keto masa .
Uwar Soro ta kallesa tana, “lafiya kuwa?”
Wani irin Murmushin Dole ya kakalo mata kawai ya ce, “Eh.”
Ta ce, “Ok to bara inje in duba yadda abubuwan gidan nan ke tafiya don na san Jakadiya bata da nutsuwar dubawa yau.”
Bai ce mata komai ba.
Tana fita cikin wani irin hanzari ya shige dakin Gaaji karar rufe kofar da ya yi yasata saurin dagowa.
Jikinsa na karkarwa ya ce, “Zizi Please! In har ya kasance yau baki aminta dani ba zan iya rasa raina, Don Allah Kinji.”
Ya fada yana haurawa kan gadon.
Jan jikinta ta fara yi tana yin da baya-da baya yana binta.
Yana cafkota ta…….