Skip to content
Part 23 of 31 in the Series Auren Wata Bakwai by Xayyeesharthul-Humaerath

Yana juyowa ya ganta don baiyi zaton faruwar hakan ba,ya ce, “Zizi ke ce? Lafiya ? Me ya faru?”

Turo baki tayi, “Ni ba komai.”

Ya tashi ya zauna yana, “Ko su ice cream din naki sun kare ne? Na tawo miki da wasu ganin dare yayi yasa ban je part dinku ba bara in dauko miki.”

Ya ƙarasa maganar yana sauka daga kan gadon ita ko tana kwance abinta.

Ya dawo hannunsa dauke da ice cream ya ce, “Yawwa ga shi nan ki sha to sai in rakaki ki koma.” Ya mika mata.

Tashi tayi ta karba a hannunsa ta ajiye kan bedside sannan ta janyosa ta shi kwanciya cikin muryar

shagawabar ta ce, “Ni ba wannan ina so ba kai ina so.”

Ya matukar jin mamakin me ta furta hakan yasa shi saurin fadin, “What? Maimaita me kika ce ban ji ba.”

Gaaji ta ce, “Umm ba komai ni barci ina ji.”

Adeel ya tashi, “ba fa za kiyi barci ba sai kin maimaita me kika ce.”

Ta kara tashi ta jasa ya kwanta daf da ita, “Ni bance komai ba,mu yi barci.”

Ya tallafo fuskarta yana kallonta, kwarjinsa yasa tai saurin sunkuyar da kai, “Da gaske ni kina so yau ba Ice Cream ba?”

“Umm umm aa ni.” Ta fada.

“To indai baki ce ni kina so ba, maidaki part dinku zan yi ba ruwana da ke.”

Gaaji ta ce, “Barci ni.” Ta ƙarasa maganar tana rufe ido.

Juyar da ita kasan shi ya yi,ya hau kanta,Wata irin damƙa Adeel ya mata daga kasan har sama wanda sai da gabadaya ilahirin jikinta ya amsa tun da ga kanta har tafin kafafu, rikon da ya mata ya sa mata kasala nan take.

Ya ce, “Wa kike so?”

A sanyaye ta ce, “Kai kaine.”

Adeel ya yi Murmushi” ni wa? Ni ban da suna ne?” “Ya… Yareema.”

“Eheen shi Yareeman wane ne agunki?” Ya fada.

Cikin kasalalliyar murya Gaaji ta ce, “Don Allah ka bari na tukura barci nake son yi.” Ta karasa kamar zata yi kuka.

Adeel ya ce, “Aa fa sai kin fada mun matsayina agunki ai.”
“Mijina ne kai.”

Rage matsin da ya mata ya yi yana rike da ita ya ce, “Good My Fulani Gurl.” ya katse maganar da haɗa bakinta da na shi.

Hot Kiss Ya bata yana, Gyara mata kwanciya akan kirjinsa. A hankali yana wasa da gashin kanta.
Tuni barci ya yi awun gaba Gaaji.

Shima barcin ya yi, can tana farkawa ta kara ƙanƙamesa abunta.

Da Asuba zai tafi masallaci kokarin janyeta a jikinsa ya fara yi a hankali.
Tayi wata ajiyar zuciya tana kankamesa.

Yasa bakinsa daidai setin kunnenta ya ce, “Zizi Time For Prayer, kar in rasa jam’i ki sake ni kinji.”

Ta Shagwabe cikin muryar barci ta ce, “Umm ni barcin bai isheni ba.”

Adeel ya ce, “Sorry Inje in dawo to sai inzo mu ci gaba da barcin ke ma kiyi.”

“Uhumm.

Ta ce kawai ta kara rungume shi.

A Karshe dai da kyar Adeel ya lallaɓa Gaaji suka yi sallar tare A dakin Don an riga an idar a masallaci lokaci ya kure. Suna idarwa kuwa suka koma barci.

Jakadiya tun kan a kira sallar asuban take ta wajen part din tana jiran ta ga fitowarsa ta shige,amman abun mamakin kuma ko alamar fitowarsa babu, Har Shamaki yaje ya dawo,ta san dai duk rintsi babu abun da ke hana Yareema zuwa Masallaci amman yau kam ba alamar shi.

Kwafa tayi ta wuce,ta koma cikin Fada ganin cewa har rana ta fara fitowa ba ta ci karo da abun da take bida ba.

Sai karfe tara Yunwa ta ishe Gaaji ta tashi, tana tashi ta fara dukan Adeel a kirji.
“Umm yunwa ina ji.”

Adeel ya tashi yana, “Oh Sorry Zizi muje muyi wanka ayi brush sai muyi breakfast din.”

Riketa ya yi tare suka tafi toilet din, duka suka yi wanka tare suna wasa Adeel ya fara watsa mata ruwa yana dariya.

“Umm ni ko, sai na rama.” Ta fada shi ma tana watsa masa.

Abun mamaki ranar ta sake jiki da shi sosai babu kunya ko wani abu, haka suka kammala wankan ya sunguma abarsa ya dire kan gado, janye mata towel din da ke jikinta ya yi,ya durkusa gabanta yana sa kan shi jikin Dan karamin ƙoƙon cikinta gwanin sha’awa ya ce, “Hee Baby , mun jima bamuyi hira ba, ka bani labari ya kake a cikin Mominka? kana jin dadi? In baka ji ka dawo nawa cikin ka ji, na san ma kama dani kake ko?”

Abun mamaki cikinta bai taɓa motsi ba sai ranar,haka taji wani irin nushi , ta Shagwabe hawaye na fitowa ta ce, “Naushina yake kana masa Magana.”

Adeel ya ce, “Eyyy ka na naushin Momynka zamu yi fada fa bana so ka ji ko ka zama good Boy, Oya give me five.” Ya fada yanasa hannunsa a cikin nata.

Gaaji ta ce, “ni dai Wallahi yunwa nake ji.”

Adeel ya ce, “Sorry Uwargida Momynmu yanzu an daina cewa Aradun Allah ne?”

Murmishi tayi tana kai masa duka a hankali a kirji.

Tashi ya yi,yana dariya ya dauko mata kaya tasa shi ma yasa sannan suka yi Daining area.
Gaaji na zuwa gun Bata ko bude kalolin abincin ba, ta kallesa.

Cikin yanayi na nutsuwa , “Ba za ka ci wannan abincin ba.”

“Why?”

“Kawai ba za ka ci ba akwai abu a ciki ban yarda da su ba.” Gaaji ta fada tana daukan tire din abincin, shiga tayi toilet ta zubda su duka tayi floshin Shi dai Adeel na kallon ikon Allah.

Sai da ta dawo ya ce, “Ehen To Madam Zizi yanzu me zamu ci tunda kin hana cin wancen.”

“Ni daman ba abinci ina so ba, cake zan ci in sha Ice Cream dina kai ma kazo kawai ka ci.”

Adeel ya bude baki, “breakfast da ice cream? Wannan kam ai sai ke din don ni ba ciki gareni ba amma ban sani ba ko daren jiya kinmin da aka naniƙe ni.”

Gaaji ta ce, “Ni kuma inma ciki? Ai bana da jelar yi.”

Adeel ya yi dariya,”sai in ara miki tawa,yanzu dai ki gama shaye-shayen ki da ciye ciyekin ki zo mu je ki rakani in yo take Awaya tunda ke kika hanani cin nawa.”

Bayan ta kammala Gaaji ta ce, “Tom ai Hijabi da gyalena suna part dinmu kuma ni kunyar shiga ina ji.”

Adeel ya ce, “ehen baki ji kunyar fitowa ba yanzu na komawa kike? Aiko sai kinje.”

Gaaji ta ce, “Umm nidai kaje ka dauko mun sai kace mata kaine ka zo ka daukeni jiya da daren kuma.”

Dariya maganar ya ba Adeel ya ce, “Ah lallai yarinya ni zaki yiwa wayo kenan? To muje ai yanzu nasan bata dawo daga Fada ba.”

Tare suka shiga Part din suna shiga Gaaji ta canja kaya ta dauki gyale ta yafa.
Adeel ya kalleta. “Ina zaki haka wai?”

Gaaji ta ce, “Kaine kace in rakaka mana.”

Adeel ya taɓe baki , “Ba dai haka ba in zaki bini sai dai ki dauko Hijabinki har kasa kisa,ni inaga ma nikaf zan siyo miki ki dunga sawa.

Ta dauko Hijabin tana, “To saboda me wai?”

Ya rike mata hannu yana, “Saboda ina kishin matata.”

Suka fita tare, dake motar me bakin tintek ce tana gaba amman babu me ganinta sai ita dake iya hango mutanen da ke waje.

Suka je restaurant bai bari ta fito ba, shi kadai ya fita ya yo take awaya ya dawo.

Yana shiga motar kamshin abincin ya daki hancinta, ta ce , “Tab zan ci wannan abincin ya mun.”
Adeel ya kalleta, “Ni fa iya nawa na karbo ai kince ke ba za ki ci Food ba.”

Tuni Gaaji ta murtuke fuska.

Adeel ya ce, “Ni awa? Rufa mun asiri na isa in batawa Momyn Little Prince Rai Sorry bara in koma in karbo wani karba wannan.”

Kafin ya koma har ta bude ta fara cin nashin..

Cin abunta take ba kakkautawa tunda cikin nan ya fara girma rabonta da abinci har ta manta amman yau kam jinta take a wata duniyar dadi har cikin kunnenta yake gilmawa.

Har ya dawo ko kulasa batai ba bare kallonsa.

Adeel ya ce, “Oh su Zizi an samu duniya kila kuma yanzu na shiga uku kullum sai anta faman zuwa restaurant.”

Sai a lokacin ta dago ta kallesa tana marairaicewa, “Nikam ma Don Allah a karo mun wani zan ajiye na anjima abincin ya mun dadi sosai.

Haka ya fita ba yadda ya iya yaje ya karo mata takeaway sannan suka koma.

Suna shiga Adeel ya ce, “Yawwa yanzu dai ki koma cen ta ganki tukunna ko.”
Gaaji ta cuno baki, “Umm ni saidai mu je tare.”

Adeel ya ce, “To muje in ci abincina nima tukunna sai mu je taren.”

Haka ta bisa suka koma part din nasa sai da ya gama cin abinci sannan ya ce, “Oya to muje, tunda nine shugaban marasa kunya, rasa kunya ɓeran masallaci.”

Dariya Gaaji ta yi, “Umm nidai mu je tare ,amman in munje dawowa nan zamu yi fa ni bazan zauna ba kums ka ce mata zan dawo nan zama.”

Adeel ya bude baki, “Lallai wannan bayanin kuma kya yi mata da bakinki.”

Suna shiga suka sami Uwar Soro zaune a parlour tana kallo. Gaaji sai laɓe-laɓe take tana tafiya a hankali.

Suka gaisheta ta amsa da fara’arta alamun farinciki ya bayyana Sosai a fuskarta.

Ta ce, “Ko ku fa, ai na tambayi Shamaki ya sanarmun Gaaji na part dinka na ji dadi Sosai ina so ina ganinku tare wannan shine babban burina, daman jira nake ma Anjima in bada kayanta a je a jiye acen watakila a yanzu tafi bukatar ka ma.”

Adeel kasan a kasa shi dai ya kasa cewa komai.

Sai kuma ta ce, “Daman ina nemanka kam ya kamata Adnan ya zo , mu zauna da Liman ayi gaggawar neman mafita,domin halin da ake ciki yanzu Jakadiya ta shedawa Mai Martaba cewa ‘Yarta Khaleesa matarka ce ba wai ciki kayi mata ba,kuma ya amince da hakan tare da kudirin inta haihu zata tare.”

Wani irin faduwar gaba Adeel ya ji nan take kansa ya fara juya masa.

Dafe kan ya yi,bai san lokacin da ya fice cikin Part din ba ransa ɓace cikin wani yanayi.

Uwar Soro ta kalli Gaaji ta ce, “Ki bisa ki lura da shi in kuma da kwai wani abu ki sanar da shi alamu sun nuna an kusa zuwa gabar da nake so.

Gaaji bata ce komai ba,tana zuwa part din ta tarar ya fadi kawai.

Da taimakon Aljanunta ta janyesa suka daurashi kan gado, ta dunga shafa kan shi da wani irin mai, daga karshe kawai ta kwanta kan kirjinsa.

Tana kwantawa ya bude ido ,ta dago tana kallonsa ya sake mata murmushi, “sai da kika biyoni ko?”
Ta kai masa kiss a kumatu tana , “Eh din.”

Ya kara yin murmushi , “Mai nacin Mijinta kawai.”

Jakadiya ta ce, “Ban yarda da lamarin Yareema ba fa sam Domin yau ko da asuba bai hallarci Masallacin Fada ba, sannan kuma ga dukkan alamu bai ci abincin sa na safe ba domin kuwa da ya ci dole ne yazo ya nemeki aduk inda kike kuma ya bayyanar da soyayyarsa a gareki, hakan ya kara tabbatar mun da cewa lallai akwai wannan makirar cikin Masarautar nan,tana nan shirina ba zai taɓa tasiri ba.”

Safina ta ce, “To wai wannan wacce irin mayyar yarinya ce?”

Jakadiya ta yi tsaki, “Mayya ma ta karshe, amman in tasan wata ai bata san wata ba.”

*****

Adeel da Gaaji sun kara shakuwa Sosai tare da nunawa juna tsantsar kauna, Mussaman Adeel duk motsin Gaaji na idonsa motsi kadan zai ce me takeso.Kwana kuwa ta koma part dinsa gaba-daya sai dai in baya nan ko ya yi tafiya ta koma Part din Uwar Soro.

Jakadiya da Safina kuwa sunata fafutukar Neman mafitar yadda zasu gano Gaaji.

Tun asuba Jakadiya ke tsaye ta baya a part din Adeel tana lura da duk wani motsinsa.
Karfe Sha biyu kuwa sai ga da Gaaji sun fito ya kai ta Part din Uwar Soro shi ya fita.

Da sauri ta koma bangarensu tana murna tare da sanar da Safina ta ga wannan yarinyar yau.
“Ashe ma wata ‘Yar Shila ce Yar Fulani ai kuwa koda ace aljanace ni zan iya da ita wallahi ko ni ko ita a masarautar nan ,ba shakka ita ce na taɓa zuwa bangaren Uwar Soro ta ta mareni amman yanzu kam komai yazo ƙarshe ba zata kara kwana cikin Masarautar nan ba.”

Komawa tayi Part din Adeel din ta sanar da shamaki kan cewa Fulani Babba ce ta aikota ta duba abubuwan da suke buƙatar gyara a bangaren, tayi abun da zata yi sannan ta fice cikin sauri.

Cikin dare aka kafa shela kan cewa anyiwa Fulani Kilishi satan sarkokinta na zinare gabadaya an kwashe su, hakan yasa sarkin Fada da dogarai suka shiga bincike lungu da saƙo da ke cikin Masarautar.

Uwar Soro ta samu sarkin ta fada masa lallai ita kam ta ga wata yarinya ta shiga bangaren Fulani Kilishi kuma ta dawo ta shiga bangaren Prince Adeel wanda bata yarda da ita ba sam kuma ita bata ma santa ba,ya kamata a bincika.

Haka kuwa aka yi suna shiga Adeel na zaune Gaaji ta kwanta akasan da mamaki ya tashi yana “lafiya?”

Sarkin Fada ya ce, “Mai Martaba ne ya umarcemu da yin bincike bisa gagarumar satan da aka yiwa Fulani Kilishi wanda muke da zargi akan wannan yarinyar ya fada yana jan Gaaji.”

Cike da tsoro ta kallesa ido ya ciccciko yajata ya fitar da ita Adeel ya bi bayansu.

Gaba-daya mutanen masauratar sun yi cirko cirko a fili, ganin sarkin Fada da wata yarinya abun ya matuƙar bawa kowa mamaki kuma daga part din Adeel.

Gaban uwar Soro ban da bugun tara-tara ba abun da yake.

Sarkin fada ya cewa Jakadiya ta duba jikinta yayinda aka tura sauran dakarai bangaren Adeel su kara dubawa.

Aiko tana taɓa kasan hijabinta ta dago wani kulli.

Budewan da zata yi ta ciro sarkan zinare da yankunaye.

Daidai lokacin da sauran dogaran suka dawo suma da sauran a hannayensu.
Wata irin tsawa sarkin Fada ya yiwa Gaaji.

Take ta fara kuka jikinta na rawa ya ce, “Tabbas wannan yarinyar ta shigo Masarautar nan ne da shirin yin sata tunda har ta koma bangaren Yareema don haka ku mikata dakin duhu.”

Ya karasa maganar ana shauɗa mata wata irin dorina wacce ta sata fita daga hayyacinta nan take ta fada kasan gwiwoyinta.

Wata irin kara Adeel ya yi, “NO…..NEVER…. Matata ce,na ce muku matata ce ba ɓarauniya ba ce, wannan matata ta ce,ba ɓarauniya bace.”

Ya karasa maganar yana rungumeta. Dukanin mutanen wajen sukai wani irin suman tsaye mai dauke da lamarin mamaki.

Sai a lokacin Mai Martaba ya yi magana, “bana son shirme anan wajen,akaita dakin duhu kafin ayi binciken tabbatar mata da hukuncin in kuma yaki saketa ku sa su cikin dakin tare.”

Yana fada ya tafi. Adeel kuwa fir ƙin sake Gaaji ya yi gam a jikinsa Fulani Babba ban da kuka babu abun da take ita da Uwar Soro, domin Uwar Soro ta san a yanzu kam duk bayanin da zatawa Mai Martaba bazai saurareta ba, kamar yadda yake dokace ta Masarautar hukuncin kisa ne ga dukkan wanda aka kama da sata ko aikata wani babban laifin da ba daidai ba.

Haka Sarkin fada ya hada Adeel da Gaaji Ya turasu cikin dakin duhu ba tare da yaso hadawa da Adeel din ba illa don bai da wata mafitar da ta zarce hakan.

Gaaji na kuka Adeel na kuka ya ce, “Kar kiji tsoro kinji ina tare da ke.” Ya kara ƙanƙameta

<< Auren Wata Bakwai 23Auren Wata Bakwai 25 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×