Da sauri masu lura da shi suka rikesa ganin zai tashi.
Cikin wani yanayi ya ce, “Ina Yareema? Ina Yareema yake? Ku kiramun Yareema, ku kira mun Adeel na yi mafarki An haifa mun jikoki,Jikokina suna cikin gidannan a kira mun Yareema, zan ganshi,zan ga jikokina, kada a bari wani abu ya samesu,cikin huta na gansu,na gansu cikin wuta na cinsu macizai na kokarin kai masu hari,cinnaku ya cizon su, Don Allah ku nemo mun su ku cire su,a cire mun su.”
Da kyar suka samu suka kwantar da shi ya na wata ajiyar zuciya ya ci gaba da fadin, “Na fada maku Rayuwar Yareema na cikin haɗari ni na gani.”
Da sauri Wata Nurse ta dauki waya ta kira Adnan da Dr Habib ta sanar da su.
*****
Jinjirayen ban da tsalla ihu babu abun da suke yi,wani irin gigitaccen kuka na wahala sun jigata domin jini har cikin idanuwansu, gashi ba a goge masu jiki ba.
Ƙara zuwa Fulani Kilishi tayi ta janye Shamaki daga kofar.
Yareema duk ya duburbuce ya ma rasa tawa zaiyi, ta Gaaji ce da take cikin matsanaicin ciwon mara da zubda jini ko kuwa jaririya biyu da suma suke buƙatar taimako.
Dauko su ya yi cikin tsimmar wandonsa ya sanya su a kirjinsa, Ita ma Gaaji ya janyota jikinsa.
“Allah na gode ma, Allah na tuba ga dukkan kuskuren da na taba aikawata gareka,na zahiri dana baɗini, Allah ka yafeni, ya Ubangiji na ya Allah ina roƙanka da ka bani ikon cin wannan jarabawar, Ya Rahman ka bani ikon kare wa innan bayin naka koda kuwa hakan zai iya zamtowa silar ƙarshen rayuwata,su su rayu zan fi farinciki Ya Rabbie ka tsere mun su ko da ace nina gagara tsaresu…..
Kafin ya yi wata magana wuta ya hango ta fara ci kamar daga sama,a hankali ta fara ruruwa tana ci, tana kara girma tana nufo inda suke.
Adeel ya kalli hutar arazane take ya kara ƙidimewa ganin ba shi da wata mafita wutar kara kusanto su take ajiye Yaran Yayi Kan Gaaji kawai ya hau samansu ya rufe.
Wutar ta fara cinshi ta baya,yana zuba yana hawayen radadi amman ya ki sake su bare ya tashi, Ita kuwa Gaaji a lokacin ma ta jima da ficewa a hayyacinta bata san meke faruwa ba.
Yaran kara kwarara ihu suke tamkar wa inda za a zarewa rai.
*****
Adnan na zuwa ya yi Part din Mai Martaba .
Yana shiga Mai Martaba ya ce, “Adnan ina Adeel? Ina Yaransa da matarsa? Suna cikin wani hali aduk inda suke ka nemosu Don Allah.”
Adnan ya rikesa ya ce, “Sannu Mai Martaba, Yareema suna dakin duhu kuma bamu san inda ka aje makullin ba.”
Dafe kai Mai Martaba ya yi sannan ya dago da sauri yana nuna karkashin Gadonsa, wata kwaryace yar karama, Adnan ya dauke ya mika masa.
Gabaɗaya a mummule kwaryar take babu kofa, amman yana zura hannunsa kuma ya shige, ya ciro key din ya basa.
“Ka je, ka bude su.”
Adnan na karba yaje ya fara sanar da Liman da Sarkin Fada kan suje bangaren Mai Martaba ya tashi.
Duk abunnan da ake Jakadiya, Fulani Kilishi da sauran mutanen masarautar ba wanda ya sani domin dare ya riga ya tsala kowa ya yi barci.
Sai da ya fada masu kafin yaje ya kira Uwar Soro kan ga Key nan zai bude Yareema.
Da mamaki ta tsaya tuhumarsa, “Key kuma? A ina ka samo kuma,to ai kofar bazata bude ba ko kasa tunda Mai Martaba baya raye.”
Adnan ya ce, “Yanzu ba lokacin bayani bane kawai dai muje.”
Suna zuwa suka ga Hayaƙi da kauri na tashi,da sauri Adnan ya bude kofar yana tun kuɗawa.
Ganin wuta yasa Uwar Soro fita da sauri suka ɗibo Ruwa da suka watsa.
Adeel har ya suma duk bayansa ya ƙone.
Ya tallafe su duka.
Gaaji ma duk da mata cikin hayyacinta amman hannayenta na kan Twins.
Gaba-daya sun rike yaran gam.
Uwar Soro bata san lokacin da ta fara hawaye ba, Adnan na daukan Adeel sai bangaren Mai Martaba,yana dawowa ya dauki Gaaji Uwar Soro kuma ta kwashe Twins a hannunta ita ma ta yi Part din da su.
Mai Martaba ya ce, “na fada maku daman suna cikin matsala suna cikin matsala so ake a kashesu so ake akashe su.” Ya karasa maganar yana dafe kai.
Dr Habib da wasu cikin Nurses dinne sukai kan Adeel suna kokarin ceto rayuwar shi.
Sauran Nurses din kuma suna kan Gaaji.
Uwar Soro ta shiga da Twins Toilet tayi masu wanka tas, Mussaman idanunsu da jini ya cika.
A bargo tasa su sannan ta ta fita da a hankali ta je gun Fulani Babba.
Zaune take kawai tana kallon sama daga ita sai Ubangiji ne suka san me take tunani.
“Ranki Ya Dade zo muje ki ga abun mamaki, abun al’ajabi.”
Ɗagowa tayi kawai ta zura mata idanu domin babu baki.
Rike mata hannu Uwar Soro tayi kawai ta jata suka fice.
Tana shiga
Wani irin kallon kallo suke yi da Mai Martaba ,yana mamakin kasancewar ta cikin wani yanayi da sauyawarta ita ko tana mamakin ganinsa araye.
Ya ce, “Fulani? Ke ce haka? Wai me yake faruwane? Ku fahimtar dani mana.”
Ta kura masa ido, can kuma ta hangp Adeel kwance anata faman treating dinsa ,ga Gaaji ma gefe a kwance ita kam ma jini ake kara mata tsabar zubar da jinin da tayi.
Can kuma twins su biyu cikin tsumma.
Fashewa tayi da kuka,tana kokarin yin magana amman sam ta gagara bata ma san ta inda zata fara ba.
Mai Martaba ya tashi ya rikota yana, “Me ya sameki ne wai? Ni kaina ma me ya sameni? Duk a tunanina jiyane kawai na kwanta barci yau na farka amman na ga wasu abubuwan da bana zato, Fulani ki fadamun meke faruwa? Kin ga Yareema kwance ba lafiya,kin ga matarshi, waccer ita ce asalin matarshi Kakana ya taɓa fadamun tare da siffatamun cewa ita ce zato zo a matsayin matarshi cikin salo na mamaki kuma Zata rusa sihirin haifan yaro ɗaya cikin masauratar nan, na ganta cikin mafarkina gashi ta haifa mana, Haihuwarsu abun al’ajabi ne,zuwansu na daban ne ‘Ya’Ya baiwa ne, sune sirrin MASARAUTAR BENONI duk wani Sirri na tattare da su, Fulani kiyi magana meke faruwa? Ina Fulani Kilishi ina Jakadiya?”
Fulani Babba banda kuka babu abun take ta kankame hannun Mai Martaba.
Liman ya ce, “Ranka Yadaɗe ka yi hakuri ka kwantar da hankalinka , Fulani bata iya magana tun ranar da ka fara rashin kunya wanda yanzu akalla kayi wata guda da kwanaki Goma kwance, tsarin masaurata da sarauta ya canja tsari wanda mata biyu suka shige gaba kan mulkar mu, Jakadita da Fulani Kilishi, suke jogarantar komai kuma suke lura da kowa kuma bamu da damar kin binsu wanda kin hakan daidai yake ga barazana a rayuwarmu, sun gaje ko ina, sun hana kowa sakewa, Masu Sarauta sun zama bayi, bayi kuma sun zam masu sarauta, a kullum cikin addu’a muke da Allah ya bude idanunka cikin aminci ko komai zai samu daidaito,Talakawa da sauran Al’umma na masaurata cikinta da wajenta sun shiga cikin halin tsaka mai wuya,
Talauci ya yi yawa, duk da cewa har yanzu ba wanda yayi nasarar zakulo ainihin arzikin Masarautar,sauran abubuwan da suke bayyane kadan da su aketa wadaƙa ana cin su tamkar baza a bar duniya ba.
Ga shi babu mukullin bude Yareema bare koda munce zamu bude dakin bazai taɓa buduwa ba kasancewar baka numfashi a doron duniya, hakan yasa mu ka mika lamuranmu ga Allah muka ci gaba da kai masa kukanmu babu dare Babu rana.
Wanda azahiri mun bayyanar da cewa baka raye a duniya kwata-kwata muka rufe wannan bangaren tare na tanadar masu lura da kai duk da cewa su Jakadiya da Fulani Kilishin tare da Waziri sunyi kokarin zuwa nan din amman ya gagara ganin cewa mun sheda masu cewa bamu san inda makullin yake ba,wanda har ya kai ga ni da Liman an hukunta mu kan lallai sai mun bada mukkulin amman muka bijere,haka suka Sarkin yaƙi da tawagarsa suka dunga zabga mana wasu irin dorinai wanda har ya kaiga dukanninmu sai da mukai jinyar kanmu, Hatta Fulani Babba da Uwar Soro bamu sanar masu da cewa kana raye ba domin gudun kawo matsala, tunda aka fara kawo ma hari na farko dole inhar akasan kana raye zamu fuskanci kalubalen da ba a zato.”
Mai Martaba ya kalli Fulani kafin ya kalli Sarkin fada, Liman da Adnan ya ce, “Ubangiji ba azzalumin kowa bane shi zai kare bayinSa aduk halin da zasu shiga, a yanzu ma bana so asan da cewa Yareema ya fito kuma bana so asan da cewa Allah ya tashi kafaduna na farka abar su cikin duhu, sannan Fulani kuma Liman ane mata magani Don Allah asan duk yadda za ayi a nema mata magani, Kujerar Sarautar Wannan Masarautar babu wanda zai iya zama muddin bani ba, ko Yareema ko Yaransa, duk abun da zasuyi Allah ya fisu, tsafe tsafensu saidai ya tsaya kanmu,kuma kanmun ma mun dogara da Ubangiji zai kare mu da mummunan nufinsu.”
Liman ya ce, “Ba matsala Mai Martaba in sha Allah za ayi abun da kace, kenan dai wa innan marasa lafiyan zasu zauna anan?”
Mai Martaba ya ce, “Eh amman Fulani ta biku afara mata magani koda a boyene, can kuma zasuyi tunanin Su Yareema na ciki su ci gaba da aikata mummunan kudirinsu.”
“An gama in sha Allah Ranka Yadaɗe.”
Sarkin Fada da Liman suka fada.
Lokacin har asuba tayi ana kiran sallah.
Su Dr Habib kuwa har lokacin suna kokarin ceto rayuwar Adeel da Gaaji.
Adnan na fita sallah yaje ya kara rufe dakin duhun kamar yadda yake aka goge duk jinin da ya zuzzuba tamkar babu abun da ya faru.
Uwar Soro kuwa cikin asubar nan ta fita taje ta samowa twins kayan Sawa.
Da sauri taje ta dawo ba tare da kowa ya sani ba,tana zuwa ta sanya masu.
Dr Habib ya ce, “In Sha Allah Yareema zai farka cikin koshin lafiya,illa jinyar bayan da ya ƙone da za ayi,ita kuma Madam ita ma jinin da ta zubar ne kuma tunda gashi ana sa mata in sha Allah inta farka za aga Alkairi,duk da cewa ita ma dai tana bukatar kulawa na Mussaman bisa ga yanayin yadda haihuwar tazo mata cikin wani hali. bare kuma dukkanin su sun shaƙi hayaki sosai.” Ya karasa maganar yana zuwa gun Uwar Soro ya karbi Twins.
“Kuma kunga abun mamaki su yaran lafiya lau duk da cewa basu cika lokacin haihuwar su ba,Gaskiya dole a jinjinawa Yareema da Madam sunyi kokarin kare yaransu ko ince wa innan yaran yan baiwane Don wannan lamari nasu kwai al’ajabi.”
Uwar Soro tayi murmushi ta ce, “Mai Martaba da Gimbiya zuwansu ai na Mussaman ne daman kamar yadda suke na Mussaman suma.”
“Ah lallai kam, duk da cewa lafiyayyune fiye da zato amman ana kiyayewa wajen daukansu Don Allah kada ana bawa mutane suna dauka a bari su dan dara lokaci ko kadan ne.” Dr Habib ya fada.
Uwar Soro ta ce, “Ba matsala In Sha Allah.”
Kara gaida Mai Martaba ya yi, sannan ya fice Uwar Soro ta bar yaran da Nurses din da zasuna lura da su ita da Fulani suka fita, aka bari daga Yareeema sai Gaaji da Mai Martaba.
Gari ya waye Fulani Kilishi na mamakin rashin jin kwaroroton al’umma kan cewa dakin duhu ya kama da wuta ba,hakan yasa kai tsaye ta nufi Dakin.
Ita ma Jakadiya ta tashi kenan ta nufi bangaren domin tabbatar da cewa aikenta na jiya ya tabbata.
Dukansu suka ci karo da juna,wani irin kallon banza suka yi suna tsaki.
Fulani Kilishi ta tabbatar da cewa babu wutar da ta kama dakin ta saki wani mummunan tsaki ta wuce ta bar jakadiya.
Jakadiya ta karasa tana tambayar shamaki, “Shamaki kai kuwa kaji motsin Yareema yau kuwa?”
Shamaki ya amsa da. “Aa Ranki ya dade gaskiya banji ba,kila suna barci.”
Wani irin ƙayataccen murmushi ta yi a zuciyarta tana fadin, “Umm duk wanda yace zai kara dani kuma ai ya yi kuskure babba tabbas,na sam yanzu sun jima da shekawa lahira Yanzu ne nake da dama mai karfi da jin cewa zan iya mulkar masauratar Benoni tunda kujerar ma taki zaunuwa munne ai don kasancewar Yareema na raye yanzu kuwa komai zai tafi yadda nake so,don haka zan fara ne da bangaren Mai Martaba ko da tsiya tsiya yau sai an budemun na shiga na koma cen da zama, sabuwar rayuwa mai dauke da sabon tsari.” Ta fada tana kara sakin Murmushi.
Zuwa tayi ta tattaro kaf dogaran masarautar, sarkin yaki da tawagarsa da duk wani mai dauke da wani makami suka nufi Part din Mai Martaba kai tsaye.
Sarkin Fada ya ce, “Ranki Ya Dade a tsarin masarautar nan ba a taba bude wani bangare ta karfi wanda yin hakan zai zamto tamkar an rusa Dokokinne.”
Jakadiya ta yi masa wani kallon raini sama da ƙasa ta ce, “In ce kai zaka fadamun abun da zanyi daidai ne ko akasin hakan? shin ma wai kai wane ne a cikin Masarautar nan? Oh sarkin Fada kake ko? To bari kaji na jima da cire ka ai yanzu wani bawan ma ya fi ka daraja, Don haka kasan mene zaina futuwa a bakinka a karshe ma in har ina waje,kuma ban umarceka da zuwa ba,kai da wannan ƙasurgumin tsahon munafukin da gemu kamar na akuya.” Tana fada tana nuna liman.
“Kar in sake ganinku gabana, ku je can kuta aikace-aikacen da aka umarce ku.”
Ta kalli Sarkin Yaƙi ta ce, “Ku kuma bazaku aiwatar da abun da na sanyaku bane ko yaya? A buɗe mun wannan bangaren ta karfi inma za a rusa shi ne ban damu domin ba damuwata bace a rusa domin tunda na bincika bangaren Yareema banga komai ba,lallai na Tabbatar da cewa arzikin wannan masauratar yana cikin wannan dakin, in banda rashin hankali taya za a tafiyar da sarauta ba arziki? Ko kuna nufin da Mai Martaba ya tashi tafiya lahira da arzikinsa ya tafi ne?”
Kokarin fara budewa suka yi,kowa ya daga Makaminsa yana daɓawa a kofar Part din Mai Martaba.
Sai dai abun mamakin shine kofar ko alamar girgizawa bata yi bare ta tsage,haka kuma ko alamar tsagewa bata yi bare ta tsage,ba wani sassa na jikinta da ke kokarin ficewa.
Sun gama sa karfinsu.
Sun kara sawa, Amman babu canji tamkar basu taɓa ba.
Sarkin Yaki ya kalli Jakadiya ya ce, “Ranki Ya Dade abun fa ba mai yiwuwa bane, dakin nan bazai taba buduwa ta karfi ba,duk yadda za ayi ba zai ba.”
Wata tsawa ta daka masu ta ce, “Wasu irin matsiyata ne ku wai? Dan abunnan kun gagara? Ince ko kun zama matane? Matan ma wa inda wahala ta gama cinsu, bana son aikin tsiya fa, inaga yau.” ta fada tana fisgar Makamin hannun Sarkin Yaƙi.
Wani irin kuwa tayi ta daga zata sake a kofar.
Kafin ta karasar da hannun tana dagawa ya kame.
Gabaɗaya jijiyoyin jikinta daga kasa har sama suka daure.
Ihu ta fara, “Na shiga Uku,ni kam na mutu na lalace,ku taimake ni. Wani munafukin ne ya yi hakan wai? Wannan wani irin munafurci ne? So ake a kasheni cikin wannan masauratar ko? To ta Allah ba taku ba, Nace ku banbaremun jiki daga wannan wajen,,,kunji..na ce kunji…wai bakwa jini…”
Duk yadda suka sa karfin su wajen kokarin cireta sun gagara,a karshe sai Sarkin Yaƙi ne yasa Sandarsa ta daidai kafarta ya buga mata.
Wani irin ihu tayi, nan take tajita ta haye sama sannan aka dirar da ita ƙasa.
Ganin kowa na kallonta kuma duk dariya suke shirin ƙunsawa ban da Safina da tayi saurin zuwa tana rike ta.
Tashi tayi, da Burin kunyarta tana, “Ni nasan wannan shirin wace ce, koma Zanyi maganinta, duk rintsi duk wuya sai na bude wannan Part din ku kuma kananun munafukai duk ku kama gabanku ba zaku iya tsinana komai ba sai kallon mutum kamar wa inda suka samu T.V.”
Tuni suka fara watsewa sumi sumi, suna tafiya ita ma tai ɓangaren Fulani Kilishi.
Fulani Kilishi na nan ta baje ana mata Dilka duk na shirin Aurenta da waziri.
JAKADIYA na shiga suka fara kallon-kallon.
, “Eheen ƙasungumar munafuka kanwar shedan, to ni Yayar Sheɗan ce, ina so ki sani cewa akwai bambamci tsakanina dake, ina jadadda miki da cewa ki bini a sannu domin tsairatar da rayuwar ki ma kadai a wannan yanayin yafi miki komai mahimmanci.” Cewar Jakadiya.
Fulani Kilishi ta bita da harara, “Kinsan ni fa da yake ba karya ce ba,bana gane yaren karnuka zaifi kyau ki fito ki yi mun maganar mutanen da suka isa kuma suka san kansu har ma suke ji da kai.”
Jakadiya ta yi dariya, “Oh su dangin tsiya an samu waje fa ya yi yawa, na dai fada miki, domin nasan cewa babu wacce zata hada manakisan da bangaren Mai Martaba zaiƙi buduwa kamar ki,kuma wallahi na rantse miki in baki janye makircinki akaina ba, za ki ga sakamakon da ba kya zato bare tsammani,na lura duk don kina ganin ina raga miki ne.”
Tashi Fulani Kilishi tayi da sauri ita ma tana dariya, “Au ashe kin fara ganin izzar haduwar jini kenan, ban toshe miki kowacce kofa ba,amman ina so ki sani da cewa ni bana da wata matsala da bude bangaren Mai Martaba a yanzu domin wannan bangaren na ajiyesa ne matsayin inda zanci Amarci ni da sabon angona,kuma ba makawa ko yanzu na so zan bude in shiga, wacce jini ya gauraye Sarauta ai da ban da wacce jinin tsiya ke yawo.”
Jakadiya ta yi tsaki, “Ki ji tsoron gamuwarki da ni, Domin daga ke har shi matsayincin wazirin sai nayi maku korar kare cikin Masarautar nan kisa aranki kuma ki rubuta ki ajiye.”
Tana fada ta fice.
Bangaren Fulani Babba ta shiga wanda karfi da yaji ta maida shi mallakinta.
Tana shiga ta kalli Safina zaune da cikin da yaiy mata tozo ta ce, “Ke wai wacce irin gantalliyar yarinya ce? Komai wai saidai inyi ni kadai bazaki taba iya tabuka komai ba arayuwarki? Daidai ana ganinki an ganni domin tabbatar da cewa zaki iya aikata fiye da abubuwan da nake aikatawa amman kwana biyu duk kin wani canja kamar wacce akai wa albishir din mutuwa? Kar ki manta fa duk abunnan da nake ba don wa kaina kadai nake ba har wa ke ne.”
Jiki a sanyaye Safina ta kalli cikin da ke jikinta ta ce, “Ni Wallahi komai ya fice mun arai yanzu a duniyar nan, cikin jikina kullum kara girma yake da tabbacin zuwansa duniya, wanda a kullum zuciyata ke raya mun nina haƙawa kaina rami na shigar da kaina da kaina gashi yanzu a karshe ba riba, Ubana ne fa ya mun ciki,Ubana… Ban san me zan haifa ba,kuma ban san ya zan fahimtar da abun da zan haifa yadda akai yazo duniya ba,ni mahaifiyarsa ce ko kuwa Yayarsa?, Uwa Uba me zan fadawa Ubangiji na? Mai na aikata a duniya? Zunubin da cutarwan ta yi yawa, nikam na hakura da duk wani kyalkyalin duniya, inji da jarabtar da Allah ya fara yi mun a duniya ma kawai. babban burina a yanzu bai zarce ace inga Yareema in nemi gafara a garesa ba,kuma in ci gaba da neman yafiya gun mahallicina.”
Tunda Safina ta fara maganar nan Jakadiya binta take da wani mummunan da kallo da ta ga ta yi shiru ta ce, “Au kin gama ne? Na ce kin gama? Ki saurareni da kyau kiji ai ba kanki farau ba Don Ubanki ya yi miki ciki, ke da kankinma da ba ta aure aka sameki ba,to miye sabo anan? ahir dinki, na ce miki ahir dinki da wasu batutuwan shirmen ki in zaki zaƙe damtse mu nemi duniya mu taka wanda mukeso mu daga wanda muke so zai fi miki,batun Yareema kuma kima cire rai don ba za ki kara ganinsa ba har duniya ta naɗe.
Sannan In ma ziga ki a fara tun wuri ki zubar Don in baki bini ba wallahi babu abun da zai sa bazan daga miki nono in tsine miki ba, Yoo wannan cikin jikin naki ma da nakeso lallai ya zam namiji inma bai fito a namiji ba dole insa Boka ya maida mun shi namiji domin shi nake yiwa sharar fagen zama sarki a wannan Masarautar,ni zan fara rike mai kafin ya fara girma ya haye abun sa.”
Tana gama maganar ta wuce,ta barta agun.
Ban da hawaye babu abun da ke kwarara daga idanun Safina.
Hannunta rike da cikin ta ta daga kanta sama a zuciyarta tana raya wa, “Ya Ubangiji na ya Allah na tuba ka yafeni,ka rabani da kara aikata sabonka komin kankantarsa, Ya Rabbie na rokeka ka kareni da Ɗan da zan haifa ga kasancewa azzalumai marasa tausayi jinƙai da imani, Ya Allah indai rayuwarmu zata ci gaba da cutar da al’ummarka ne , Allah na tuba gwanda dukanninmu mu rasa ranmu a duniya mu koma gareka, Allah ka ganar da mahaifiyata kamar yadda ka ganar dani, Allah ka cire mata son zuciya,da burin cutar da wasu ta hanyar daukan fansar da bata da amfani.”
Mai Martaba na shingide akan gado yana Taking Breakfast dinsa duk Wannan kurereton da Jakadiya tayi bai ma san tana yi ba kasancewar kafin a shiga can cikin part din yana da nisa daga kofar.
Prince Adeel ya fara atishawa yana fadin, “Zizi.. kina ina? Kina lafiya? Ba ki dai mutu ba ko? Kar ki tafi ki barni,in kika tafi kika barni mutuwa zan yi Don Allah kar ki tafi kece rayuwata, Ni ba komai bane in har dai babu kai , Don Allah karkisa in bude idanuna inga bakya gareni,na gwammace na dauwama idanuwana rufe in har zan ji numfashinki da muryarki.”
Rikesa suka yi ganin yana kokarin fama kunar dake jikinsa.
Ya yi saurin Bude ido yana, “Ina take? Ina zizi? Waya kawo mun? Ina kuka kaimun ita?”
Suna rikesa yana daga kai ya hangota wani irin fisga ya masu ya tashi ya je kan gadon da take.
Ya rike hannunta yana, “Zizi… Zizi …na ce ki tashi wallahi in kika tafi banki zan yi,ba zan rayu babu ke ba,ni ba zan iya rayuwa ba,ke ce rayuwata Don Allah ki tashi,” ya fada yana jijjigata.
Nurses biyu din suka zo suna rikesa kara turasu gefe ya na, “Ku barni, na ce ku barni,kuna gani tana so ta tafi ta barni,so take fa ta tafi ta barni ta manta cewa na fada mata bazan iya rayuwa babu ita ba.”
Ganin bata da alamar motsi ya kwanta a kirjinta yana sakin hawaye.
Ji ya yi kawai ta rungumesa.
Ya yi sauri dagowa yana kallonta.
Ta sake masa wani irin ƙayataccen murmushi ta sa hannunta tana goge masa hawaye.
“To ka yi Murmushi mana.”
Adeel ya…