Skip to content
Part 29 of 31 in the Series Auren Wata Bakwai by Xayyeesharthul-Humaerath

Adeel ya fito Parlour ya samu Fulani Babba da Mai Martaba tare ya ce, “Anya lafiya kuwa masarautar nan? Kamar hayaniya nake ji mutane ta ko ina.”

Mai Martaba ya ce, “Eh nima na ji hakan amman bari Sarkin Fada da Liman suzo in muka fita ma ga ke shirin faruwa ko ince meke faruwan ma.”

Uwar Soro ta fito, “Anya kuwa ji nake kamar Yaune ranar daurin Auren Fulani Kilishi da Waziri.”

Mai Martaba ya ce, “Au to abun ma yazo a daidai ai hakan ya yi, Allah sanya alkairi domin kuwa saki ya tabbata akan Kilishi a yau dinnan.”

Gaaji ce ke son fitowa tana laɓe-laɓe.

Uwar Soro na daga kai ta ganta tsaye jikin labule.

Ta ce, “Ah Uwata ba za ki fito bane? Ki zo ki gaisa da Mai Martaba da Fulani.”

Sai a lokacin duka hankalin su ya yi gun.

Kin fitowa tayi ta ci gaba da tsayuwa.

Fulani Babba ta tashi tana, “Ni kam ai sai in dauko sirikar tawa da ban sani ba da kaina ko ince ‘Yata don bana surkuntan.”

Dukansu suka yi dariya.

Karasawa tayi ta riko hannun Gaaji tana, “Kin ga ki daina jin tsoro ko kunya ni kam dai Momynki ce Mai Martaba kuma Dadynki, ga kakarki Kuma Uwar Goyonki Uwar Goyon Yareema, Wannan lamari naku kam ma da ban Al’ajabi wacce ta raini Yareema ita ta raini matarsa.” ta kalli Uwar Soro kafin ta ci gaba da magana, “Anya kuwa babu wani sirri a tattare dake Ranki Ya Dade? Nima inaga zanzo a raineni ko na wata guda ne inji yadda ake ji.”

Ta karasa maganar suna zama.

Dariya suka yi dukansu.

Gaaji dai ta kasa sakewa Murya kasa-kasa ta gaida Mai Martaba.

Ya amsa yana sakin Murmushi , “Barka dai ‘Yata sannu da fama ya jikin?”

Murmushi kawai tayi tana wasa da yan yatsunta.

Uwar Soro ta ce, “Ina Little Prince da Princess suke ko su basu tashi ba ne?”

Karafa Adeel ya ce, “Ai suna gun masu kula da su.”

Sai da ya gama maganar ya tuna a inda yake sai kuma ya yi tsit.

Fulani ta ce, “Ko ‘Yar Kunyar nan ma wato babu?”

Murmushi ya yi, ya dago yana kallon gaaji,suna hada ido ya mata sigina.

Murguda masa baki tayi tana jefa masa harara.

Uwar Soro ta ce, “aiko dai a daukosu Mai Martaba ya sa masu albarka kuma ya raɗa masu suna.”

Ta fada tana shigewa ciki.

Cikin Baby Cribs dinsu na zinare ta janyosu wanda shi kadai ma abun kallone bare kuma kayan dake jikinsu.

Kallo ɗaya ya wadatar wajen bayyanar da cewa lallai ‘Ya’yan Jinjin Sarauta ne, Sarautar ma mai dauke da ɗimbin arziki na alfarma.

Uwar Soro na jan Prince Daya daga cikin Dadynsu kuma na jan Princess.

Har suka shiga da su parlourn.

Fito da su akayi duka aka sanya su cikin Mai Martaba.

Kallo Ɗaya ya masu yaji wani irin nishadi da farincikin da bai taɓa riskar sa ba ya ziyarcesa a yau a zahiri ya furta , “Ma Sha Allah, Barakallahu Fikhu,” ya Kalli Prince ya ce, “Lallai wannan kam sak Yareema har rashin fara’ar ga fuska nan a turbune kamar dusa,ita kuwa baiwar Allah duk da kasancewar ta jinjira tunda ta fito Murmushi take ta sake mun,inaga ya tabbata za ayi auren nan da ita ko ba sadaki.”

Fulani Babba tayi dariya tana, “Daman tunda tazo mun kwacen miji ai dole tayi dariya, shi ma nasan dani na daukesa sai ya yi mun ambaliyar dariya ma ba murmushi kadai ba.”

Dukanninsu suka yi dariya.

Shigowar Liman da Sarkin Fada ne ya katse su.

Bayan sunyi sallama an amsa Mai Martaba ya ce, “Yawwa Liman Maddallah Ga Jikoki nan ayi masu Radin Suna.”

Karbansu Liman ya yi, aka dauko Dabino ya Raɗawa Twins suna.

Prince (Zaayn) da Princess (Zaraa).

Ya kara fadin, “Allah ya yi wa rayuwa albarka,Ubangiji ya sa ku zam silar haske, masu haskaka rayuwar al’umma aduk inda zaku kasance, Ina Rokan Ubangiji ya tabbatar da zuwanku wannan duniyar asa’a.”

Dukanninsu suka amsa da Amin.

Sannan aka maida su Gadonsu, Uwar Soro ta kira Nanies din biyu domin su turasu a cikin Cribs din a fita.

*****

Hayaniya ta ko ina gabadaya maza da mata an hadu a farfajiyar Masarautar.

Jakadiya da Fulani Kilishi ban da wutar maganganu babu abun da suke yiwa junansu.

“Ni ce gaba da kowa cikin masauratar nan,kuma nice shugaba, don haka ba a isa a aiwatar da wani lamari ba tare da yarjewata, in kinga anyi wannan auren to numfashine ya bar jikina ki rubuta ki ajiye wannan.”

Fulani Kilishi tayi wata irin dariya mai dauke da kallon raini ta ce, “In kin fasa, aure kam kamar anyi an daura a yanzu ma kuwa.”

Waziri ma ya kalli Jakadiya ya ce, “Ke wai har yanzu baki daddara cewa cikin shedanu ke jinjira ce ba? To mu zuba mu gani Dan halak ka fasa.”

Ya juyo ya kalli Fulani Kilishi ya ce, “Ranki Ya Dade Amarya ki shige ciki kawai ku ci gaba da hidimarku yanzu zan shiga Masallacin a daura auren In Sha Allah, wannan mahaukaciyar kuma sai dai yau ta hadiye zuciya.”

Jakadiya ta kalli Waziri ta ce, “Adaura? To a daura amman ina Tabbatar maka da cewa daura wannan auren tamkar budewa kanka kofar shiga lahira ne.”

Har waziri ya juya zai tafi ya tsaya , “Ba matsala indai lahira ce harda bargona zan tafi Kodayake tunda makullin kofar na gunki ma ai nasan ba a rasa bargo acen ba.”

Fulani Kilishi ta ce, “Jeka kawai ni fa babban burina naji ance an daura wannan auren komai zaizo karshe ne,kuma ina nan daram zan jira har a daura kafin kofata ta bar kofar masallacin nan.”

Zai shiga Masallacin kenan ya ga Magijiya da Rumaiysa tsaye cikin yanayin damuwa, karasawa ya yi garesu yana, “Wai Miye haka ne duk kunyi kamar wa inda akayi wa mutuwa? Ku da ya kamata ace kunfi kowa murna? Zamtowana Sarki a wannan masauratar Canjin rayuwa sai wanda kuka zaɓa fa ban ce zan rabu daku ko in wofantar da ku ba,muna tare kar kuji komai tare zamu ci arziki, Don haka inma kishi ne kusa shi agefe don ba a kishi da arziki ai kowa ya samu burinsa kawai ya ci.”

Daga Magajiya har Rumaiysa basu ce masa komai ba ya juya abinsa yana Murmushi ya shige.

Daga Fulani Kilishi har Jakadiya da sauran al’ummar masauratar suna tsaye kofar masallacin ana kallon kallo.

Za adaura auren kenan sai ga fitowar Mai Martaba, Gaaji, Adeel, Fulani Babba,Uwar Soro, Liman, Sarkin Fada har ma da Adnan da yazo a karshe, Ga Twins Nanies dinsu sun rikosu.

Kamar daga sama suka diro.

Jakadiya ce ta fara ido hudu da Mai Martaba, da sauri ta sa hannu tana murza idanunta,gani tayi maimakon ɓacewa sai ma karin su Adeel da Gaaji ta gani.

Batasan lokacin da tayi wani tsalle ta dire ta kanta ba tana zabga ihu.

“NA SHIGA UKU,MATTATU SUN FITO,SUN FITO, SUN FITO ZASU JANI, NA SHIGA UKU NA MUTU NA LALACE.”

fada take tana birgima.

Hakan ya ankarar da Fulani Kilishi da sauran mutanen wajen, Suna hada ido Mai Martaba ya sake mata murmushi batasan lokacin ta sake wani irin fitsari ba tsabar firgita jikinta ya dau ɓari ta ce , “Na shiga Uku Gawaaaa, Aljanu, sunzo zasu cinye mu, shikenan mun mutu,Wayyo Allah na,na tuba, Allah na tuba, Allah ka yafemun, Allah kasa ba mutuwa na yi ba Wayyo Allah ka maidani duniya ,mutuwa ba yanzu ba Don Allah, ba yanzu ba, shikenan.” Ita ma ta karasa tana birgima.

Jin hayaniyar ta fara yawa yasa masu daurin aure fitowa dukanin suna cin karo da Mai Martaba da tawagarsa idanu sukai tsilla-tsilla jiki ya dau rawa.

Waziri bai san lokacin da ya dauki Takalmin ƙafarsa ya fara ci ba yana , “Allah Amin, Allah Amin, Allah amin, Allah ka rabamu da ganin matattu a duniya, Wayyo lahira, Wayyo Allah na ko dai har anyi tashin alkiyamar ne ? Shikenan ashe muma mun mutu, Wayyo,wayyooo Shikenan mun mutuuuu.”

Mai Martaba ya ce, “Mu karasa mana kun tsaya anan.”

Mutane na ganin sun fara dumfarosu.

Gudu mai naci ban baka ba.

Hajiya Maimuna da Hajiya Rabi harda Gware da kai, Khaleesa kuwa wuntsila kai ta fara yi, Jakadiya da rarrafe take tafiya don tama rasa ya zatayi.

Fulani Kilishi kayan bakin adon biki duk sun zube a ƙasa hatta zaninta daga ita wani karamin wando.

Waziri na zuwa ya bude Wani durom din ruwa ya shige ciki.

Masaurata ta hargitsa kowa kawai ta kansa yake yana neman hanyar fita, Mai Martaba ya ce da Sarkin Fada, “Kada a bari kowa ya fita cikin masarautar nan a tabbatar da an kulle kowanni Get.”

Duk Abun nan da ake Safina ce kadai zaune ta kasa taɓuka komai banda hawaye babu abun da ke zuba daga idanunta.

Duk sun taru abakin Get ga Mai martaba da iyalansa na kara dumfarosu ga Get a garƙame.

Jakadiya ta ce, “Ashe haka ranar tashin alkiyamar take? Matattu zasu fito har ma da Aljanu? Ya Ubangiji na Ya Allah ni dama na mutu kar inyi gamo da kowa,na shiga ukuna, Wayyo ku bude mu,ku budemu mu fita ko zamu tsira Shikenan.”

Hawaye da majina shaɓa-shaɓa Fulani Kilishi ta wage kafa wai zata haura ta get ta fita.

Tana daga ƙafa kuwa jinta tayi tim ta bugu da kasa, ta kara sakin wata ƙara, “Mutuwa….lahira…. shikenan, Wayyo Allah ka kwace mu hannun wa innan shikenan kuma mu kam.”

Waziri ma yaɗane Get din, Fulani Kilishi ta cafko shi, “Baka isa ba mugu tare zamu fice, kafarka kafata,,ai alhakina ya kusa hawa kanka,” Hajiya Rabi ma ta cafko kamar Fulani Kilishi,” Yawwa Don Allah ka jamu ka ceci musulma Uwar Musulmai.”

Hajiya Maimuna ma na ganin haka ita da Khaleesa da Su Rumaiysa,Basma, Nasmah da sauran duk suka cafkosu.

Wata irin tusar wahala Waziri ya sake, duk sun gama janye masa karfi daga su har shi jinsu sukai tarwatse a kasa kawai.

Sai a lokacin Sarkin Fada ya yi magana, “Ku dakata fa,ku nutsu gabadaya nan ba mattune, Mai Martaba Bai Rasu ba yana raye kuma cikin gidannan wani dalili yasa aka ki bayyanar da hakan.”

Zare idanu suka fara yi Jakadiya na kankame bango tana, “Wallahi karyane kai kanka ban yarda da kai bama,kwananmu bai kare ba kunzo kunaso ku kai mu lahira Don Mugunta kawai.”

Murmushi Mai Martaba ya yi,ya kalli Sarkin Fada ya ce, “Ba komai ka barsu kawai, muje cikin Fada yanzu muga ya take kasancewa.”

Gabadayansu sukai Fada.

Suko suna ganin sun tafi kowa sai Ajiyar zuciya Hajiya Maimuna ta ce, “Allah yasa sun tafi dai kenan.”

Magajiya da tsoro ya gama birkitata ta ce, “Lallai inaga akwai hisabin cikin duniya kafin akai ga lahira.”

Dukkansu sunyi barje barje ban da haki da Numfashin wahala babu abun da suke sunma kasa magana koda wasa.

Mussaman Fulani Kilishi,Jakadiya da Waziri duk sun fi zaburewa har saida suka yi wata karamar rama ta lokaci guda ba shiri, idanu sun shige ciki har a lokacin jikinsu bai daina karkarwa ba.

Mai Martaba kuwa shiga cikin Fada ya yi,yana shiga ya ce abasa Prince Zaayn.

Ya ajiyesa ya kwanta daram kuwa akai ba tare da ko motsawa ba, ana sa shi akai ya saki wani irin Murmushi ta gefe har yana lumshe ido tamkar ba sabon jariri ba.

Shi ma Murmushi Mai Martaba ya yi,ya ce, “Tabbas wannan shine Magajin Yareema, Domin Yareema bai taɓa dariya ba tunda aka haifasa har sai ranar da aka daurasa akan wannan kujerar ya yi Murmushi kuma sak yadda Zaayn ya yi, Maddallah da zuwan sabon Magajin masauratar Benoni, Allah ya kara ingata rayuwa.” Ya kara yi masa wasu addu’o’in cikin kunnensa kafin ya mikasa aka maidasa cikin Cribs dinsa.

Uwar Soro ta ce, “Tabbas ai da anga Little Prince an ga Dadynsa Amman ina tunanin fa wannan sai yafi Dadynsa Miskilanci da izzar sarauta.”

Adnan ya ce, “Dadynsa kam ai yanzu ya tashi daga Miskili kanwata ta gyara shi.”

Dariya suka yi Adeel na kallon Gaaji yana sake mata murmushi.

Mai Martaba ya ce, “To yanzu ya za ayi da wa incen mutanen naka ne?”

Ya fada yana kallon Sarkin Fada.

Sarkin Fada ya ce, “Ban da matsala da sauran amman su Hamshakan cikinsu yanzu zansa ne a fara damkesu tukunna.”

<< Auren Wata Bakwai 28Auren Wata Bakwai 30 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×