Skip to content
Part 3 of 31 in the Series Auren Wata Bakwai by Xayyeesharthul-Humaerath

Duk kokarin da ya yi wajen ganin ya ja kafar kin motsawa tai sam sam.

Jakadiya na fitowa daga kitchen ta hangosa tsaye kafa a kame, rike baki tayi a zahiri tana fadin,

“Subhanallahi Yareema lafiya?”

Ko kallon inta take bai ba bare ya bata amsa ya ci gaba da kokarin daga kafa amman ina tamkar ana kara danna kafar.

Bangaren Uwar Soro tayi tana kurma ihu, “Na Shiga ukuna,Yareema ya kame,kafar Yareema ta kame ya kasa takawa.”

Uwar Soro na jin hakan ta fito cikin sauri tana fadin, “Subhanallahi ya aka yi hakan? Ina Yareeman.”

Jakadiya ta ce, “Gashi can a kofar shiga bangaren Fulani Babba.”

Aiko Yareema na tsaye ban da zufa ba abun da yake tun yana kokarin motsawa har ya hakura.

Uwar Soro na zuwa tayi kokarin jan kafar tasa amman ina sam hakan ya gagara.

Addu’a ta shiga tofa masa,cikin kankanin lokacin gabadaya matan cikin Masarautar sun cika gun.

Fulani Kilishi ce ta fara karasowa garesa tana, “Subhanallahi Yareema meke faruwa haka?in kafar nan taki motsawa ta karshenta sai dai a yanketa.”

Tana fada suka hada ido da Magajiya tare da sakin wani ƙayataccen murmushi.

Uwar Soro ta umarce su da duka kowa ya bar gurin abarta daga ita sai Yareema,ba yadda suka iya ba don sun so ba haka suka tafi, Fulani Babba kuwa daman bata fito ba.

Hajiya Maimuna ta ce, “Uwar soro ko zan iya tsayawa ni in taimaka?”

Girgiza mata kai tayi alamar aa haka ita ma ta bar wajen.

Addua ta ci gaba da tofa masa Kasancewar hakan ba sabon abu bane gareta tun yana karami lokuta zuwa lokuta kafarsa ta kan rike sai ta sha faman yi masa addu’o’i kafin ta sake.

Yau yafi na kullum domin kuwa da kyar kafar ta sake, tana sakewa tare suka shiga bangaren Fulani Babba.

Bayan sun shiga saida aka ɗauki kusan Second biyar kafin Fulani Babba ta fara magana.

“Yareema!.”

Ta yi shiru kafin ta ci gaba da fadin, “ka san dai a yanzu ban da damuwa da burin da ya zarce ace yau ka yi aure.”

Tana fada tsigar jikinsa ta fara tashi kansa na yi masa wani irin tsiro.

“Ban san mene ne dalilinka na rashin son aure ba kasancewar ka haka a yanzu baka da abun da ya kamaceka fiye da aure, na san cewa kana da nauyi akanka na juya dukkanin abubuwan da ke tafiya a masarautar nan, zuwan mata kila tana tallafa maka ta wani bangaren ka samu sauki ban sani ba ko akwai wacce kake so,indai akwaita zan so ace kayi gaggawar bayyanar da ita domin ayi komai kan lokacin da ya dace.”

Shiru ya yi bai ce komai ba kansa na kasa.

Fulani babba ta kalli Uwar soro ta ce, “ko ya sanar da ke wata wacce yake muradin Aure?”

Uwar soro ta ce, “Aa Ranki Ya Dade.”

“Hmm to ina jinka Adeel yanzu kai ba yaro bane kasan abun da ya ce da kai fiye da kowa.” Cewar Fulani Babba.

Yareema ya ce, “Babu Ranki Ya Dade amun hakuri tukun zuwa gaba.”

Fulani ta girgiza kai tana, “Shikenan Allah yasa mu dace.”

Tare suka fice da Uwar soro sai ta tabbatar ya shiga bangarensa kafin ita ma ta koma nata.

Tana shiga ta samu Gaaji na surfa uban kuka ita akaita gun Baffanta tana so ta ganshi kar a kashe mata shi.

Dakyar Uwar Soro ta lallabata har ta samu ta yi barci.

Cikin dare ta farka wai tana jin kashi.

Uwar Soro ta kaita toilet ta ce ta hau tayi.

“Wallahi na Rantse da Ubangiji na ba jan hau wannan abun a wawushe mun duwawuna ba,haka kawai in rasa mazaune ni kam ba zan hau ba, kawai mu fita anuna mun kasa inyi yadda muke yi a ruga.”

Duk Yadda Uwar Soro tayi da Gaaji tayi kashi a toilet dinnan ki tayi fur daga karshe sai leda ta dauko mata,ta bata,ta tsuguna tayi, ga shegen yawa da uban wari tsabar da nannagi abinci harda na hauka.

Tana gamawa tasa hannu ta kulle abunta a ledar ta ajiye a gefe tana, “kuma Aradun Allah karki samun kashina cikin abunnan a ajiyemun da safe zan dauke abuna da kaina inje in binne.”

Sai da ta koma barci kafin Uwar Soro ta samu ta je ta yi floshin din kashin.

Prince Adeel Muhammad Rohaan

Tun da ya koma kansa ke sara masa gabadaya wani gitaccen ciwon kai yake ji, zuciyarsa kuma ban da muradin kasancewa da wata ba abun da take.

Wayarsa ta fara ringing, yana dubawa ya ga number Safina, a jiyar zuciya ya yi aransa yana raya tamkar tasan yana da bukatar ta a yanzu.

Kara Wayar ya yi a kunne ya yi shiru.

A bangarenta ta ce”Prince inzo mu kwana? Na kasa barci Please.”

Da “alright.” Kawai ya amsa mata yana ajiye wayar.

Tuni ta tashi ta feshi jiki da turare ta sa wasu irin kananun kaya da zai iya gigita kowanni Ɗa namiju daga kallo ɗaya, Mussaman ma ita da take da diri bayyananne mai daukan hankali.

Tana zuwa ta kira wayarsa tashi ya yi ya bude mata kofar bayan ta shigo sannan ta rufe ta bi bayansa.

Zama ya yi a gefen gadon yana danna wayar dake hannunsa, tana shiga ta wular da Doguwar rigar da ta rufe jikinta da shi tana wata irin tafiya ta karasa garesa tana shafasa, harshenta tasa a wuyansa tana bi tana leshewa, da hannunta tana bin jikinsa a hankali, tuni ta gama sakar masa da jiki, murya a sanyaye ta ce, “Please Prince, yau kada ka ƙi, ka yarda muyi abun da ya dace,ina da bukata kuma kai ma na Tabbatar da cewa zaka ji dadin hakan kaji.”

Ba tare da yace kamai ba ya kara janyota yana sa harshen sa cikin bakinta yana kankameta, ganin hakan ta fara kokawar rabasa da kayan jikinsa, subulewa tayi daga jikinsa tana binsa da wani munafikin kallo mai kara kashe jiki ta ce, “Wait taya hakan zai yiwu da kaya jikinka bara in cire ma ko.”

Shi ko tsayawa kallonta ya yi kawai tamkar hoto ta rabasa da kayan jikinta tana kokarin janye masa gajeran wando da ke ciki kenan ya dakatar da ita da hannu alamar aa.

Wani guntin tsaki tayi azahiri cikin zuciyarta tana fadin, “duk abun ka dai Wallahi yau sai na samu abun da nake so nayi galaba akanka.”

Murmushi ta masa ta dawo jikinsa tana shafa girjinsa.

Shi kuwa sakewa ya kara yi,yana bin dukkan ilahirin jikinta yana kai mata wasu irin saƙonni, ban da kokarin ta hake masa ita kuwa ba abun da take, da ta kai hannunta zai rike.

Ya gama duk wasannin da yake da bukata janye jiki ya yi yana numfasawa ya ce, “Safina Is Ok Please ya isa haka barci nake ji.”

Kukan karya ta fara yi tana yi masa magiya.

“Prince Wallahi baka ji yadda nake ji ba, zan iya rasa rayuwata muddin baka biyamun bukata ta ba, ka tausayamun Please, ko na yaune kadai just once.”

Jiki a mace idanun sa na rufewa ya ce, “Ki bari Gobe.”

Yana fada ya kifa da kansa tuni barci ya yi awon gaba da shi.

Dafa kai Safina tayi tana, “wai wannan wani irin Bala’i ne kullum sai anzo gabar da zan aiwatar da aikina sai kace barci ko kuma wani abu ya faru? Baka da aiki sai romance? This wil be last time da zan bata lokaci na ba zan dawo gidannan ba sai da maganin da dole zai sanyaka aiwatar da abun da ake da bukata ko na huta.”

Tashi ta yi tasa rigarta ta fice,tana fita cikin duhu wani Mutumi ya karaso gareta yana, “Ya na ganki haka? Ina so inji labari mai daɗi kar ki fada mun akasin hakan.”

Tsaki ta yi ta ce, “ni fa na gaji wallahi kullum sai ya kaini makura sai ya juya mun baya, Gobe ko jibi ina da bukatar anemo mun magani mai karfi da zai rikitashi duk yadda za ayi asa masa cikin abun da zai sha inaga wannan shine shawarar karshe da zata iya aiki in ba hakan ba akwai Matsala,har na gaji da binsa Wallahi.”

“Shikenan kada ki damu zamuyi magana a waya.” Mutumin ya fada yana waige-waige ya tafi.

Washegari.

Tun da akayi sallar asuba ma’aikata da dogarai ke kai kawo cikin masautar kowa na aikinsa.

Masarautar Benon babbar masarauta ce wacce ta amsa sunan masarauta a kasar hausa, ta tsaru iya tsaruwa daga wajenta har ciki,inda kudi da kayan masarufi na magana Tabbas na wannan masarautar in suka fara nasu ba sauki, Aljannar duniya ga wanda ya taba shiga cikinta domin babu mai tunanin fita koda kuwa cikin mafarki ne.

Mai Martaba Sarki Muhammad Rohaan ya gaji sarauta tun daga gun Kakansa, kakansa na rasuwa mahaifinsa ya hau karagar mulki shi ma bayan mahaifinsa ya rasu ya hau wanda yake a yanzu shi ke jagorantar BENONI.

Matansa Biyu Fulani Babba (A’isha) da Fulani Kilishi (Hafsat) Yaro Ɗaya garesa Prince Adeel Muhammad Rohaan wanda yake tamkar gado ga ahalinsu Basu cika haihuwa sosai ba, Kakansa shi kadai ne, kamar yadda mahaifinsa yake shi kadai,haka kuma shi ma ya Kasance shi kadai sannan ya haifi Ɗa shi kadai.

Mai Martaba sarki Muhammad Rohaan mutum ne mai karamci da sanin ya kamata cike da jin kan talakawa,sannan baya taba fadin magana biyu, Indai ya ce abu to babu shakka,ba canji a wannan batun, baya da yan uwa na kusa sai wa inda suka zam dangi garesa na nesa, yan uwan mahaifiyarsa ,yayunta da kanenta, dukkaninsu suna rayuwa cikin Fada da matan su da ‘Ya’Yansu Waziri, Sarkin Fada, da Sarkin Yaƙi.

Waziri shine Mijin Hajiya Maimuna Yaranta mata yan biyu Nasmah da Basmah.

Sarki Yaƙi mijin Hajiya Rabi suna da yara uku mace Ɗaya Khalesa da kuma Ameen da Noor,da kuma sarki fada mijin Magajiya Da yarinyarsu Ɗaya Rumaisa.

Prince Adeel Muhammad Rohaan shike tafiya da shigar da fitar dukka wani kudi da ke wakana a Masarautar Benoni kasancewar ya kammala digirinsa a bangaren tattalin arziki.

Khalesa da Nasmah suna masifar sun Prince Adeel sanadiyar yadda kowa ke bayyana soyayyarsa gareshi yasa basa shiru da juna ko kadan, wajen zama ma in daya na gun daya bata taba zuwa.

Hajiya Maimuna da Magijiya suna matuƙar nuna soyayya tare da kauna ga Adeel cike da gujewa dukkan abun da zai iya cutar da shi saɓanin sauran matan da ke bayyanar da kishinsu da tsantsar tsana a zahiri.

Aranar da Yareema yazo duniya aranar sai da aka nemeshi aka rasa a Masarautar daga karshe sai Uwar Soro ce ta tsinto shi cikin kwali a na kokarin fidda shi daga fadan.

Hakan yasa tun Adeel na karami Mai Martaba ya zaɓi kebantar da shi tun yana da shekara Uku ya koma gun Uwar Soro har sai da ya fara girma ya kammala secondary zai shiga Jami’a kafin aka fara bayyanar da shi Wanda tunanin wasu ma da yawa a garin gabadaya ya mutu fitowarsa kuwa ya girgiza tunanin kowa da ke Masarautar da garin.

Wannan kenan.

Karfe Bakwai na safe war Soro ta ga barci Gaaji fa bana karewa bane tadata tayi ta ce mata tayi sallah.

Kallonta tayi ido duk kwantsa ta ce, “Sallah? Tab ni fa ban girma ba ai sai an girma ake sallah ki barni inyi barcina ni.”

Ta kara shigewa bargo.

Sai da taji tace mata ga abinci aiko zumbur ta tashi ta na kokarin kubcewa.

Uwar soro ta ce, “aa fa sai kinzo munje Kinyi wanka Kinyi brush kiyi alwala kiyi sallah kafin kici abincin nan?”

“Boroshe? wannan abun na jiya da kwashe mun jini ko? Na rantse banyi haka kawai aje ata kwashe mun jini saidai in wannan abun zaki sammun abaki inshanye shi kam da gardi aradun Allah kums wanka nayi jiya ai banyi yau sai ranar sallah ehee.”

Uwar Soro ta ce, “to tashi muje kiyi dai koma miye sai kici abincin.”

Fashewa da kuka Gaaji tayi tana, “Ni yunwa nakeji hanjin cikina kuka suke,na shiga ukuna na mutu na lalashe ki bani abunshi inci kar in mutu.”

Ta ƙarasa maganar tana birgima akan gadon harda rike ciki kamar mai nakuda.

Uwar soro ta ce , “Oh ni Jummai na gamu da gamona, ga shi zan baki kici amman kimun alƙawari in kinci zakiyi duk abun da nace kiyi kin yarda?”

Ta girgiza kai.

Mika mata tayi, tuni ta fisge ta fara ci kamar tsohuwar mayunwaciya.

Sai da ta cinye tas Uwar Soro ta ce, “Yawwa yanzu bara in dauko miki zani ki cire kaya muje bandakin ko.”

Uwar Soro na shigewa dayan dakin ta kalli gefe da gefe taga ba kowa da gudu ta fice ta shige bangaren Prince Adeel.

Tana shiga ya fito daga wanka kenan yana zaune yana shafa mai ya zame towel din jikinsa babu komai a jikinsa.

Tana shiga tana ganinsa da ta kwallara wani ihu…

<< Auren Wata Bakwai 2Auren Wata Bakwai 4 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.