Ta kalli Adeel cike da mamaki.
“Kai kuma fa? Daga ina ka diro?”
Ta karasa maganar tana bin dakin da kallo.
Fara sosa ƙeya ya yi,yama rasa abun cewa.
“Wato shine adakin dazu da na shigo kika kasa sakewa ko? Allah abun Godiya yanzu dukanku kuyi hakurin na dan lokaci ne ya gagara? To ba dani ba, baza ana lalubowa ana sato hanya ba, ana gama bikin suna zan tattara ma matarka ku karata can,wato kai yanzu har kasan dadin mata ? Kasan ka bita? zan yi maganinku duka kuna nan da idanuwa kamar na agwagwa.”
Adeel dai ya sunkuyar da kai don kunya,Gaaji kuwa ta kasa jurewa ban da dariya ba abun da take sharba.
Uwar Soro ta kalli Adeel ta ce, “To baza ka fitan bane? Ko kana jira tazo ku tafi tare ne?”
Haka yaje ƙafarsa da guntuwar kunya ya fice.
“Ke ko? Zaki sani ne.” Uwar Soro ta kalli Gaaji tana fada.
Gaaji ta ce, “Na yi shiru nikam.”
Ta galla mata harara ta gefe kafin ta ce, “duk kunsa na manta ma yin abunda ya kawoni,yawwa kizo muje ki zaɓawa Twins kayan da zasu sa ranar suna inji Fulani.”
Gaaji ta Shagwabe, “ni kam kawai ku zaɓa masu don Allah duk wanda aka zaɓa ya yi daidai ba sai na zo.”
Uwar Soro ta ce, “Ok to Shikenan,saura inna fita ke ki bishi ko kuma shi din ya kara biyoki.”
Dariya kawai Gaaji tayi bata ce komai.
*****
Yau aka fito da Fulani Kilishi, Jakadiya da Waziri, gabadaya yanayin hallitarsu ta sauya, sun dawo kamar wasu dodunaye.
Jakadiya ta gefe take tafiya dake take jan kafafunta,Waziri kuwa a gwale yake tafiya duk kafafuwansa a wangale.
Fulani Kilishi idannunta gabadaya sun rufe bata ganin komai sai dubi dubi da bin bango take.
Ana Dukansu aka hankadaso cikin gidan yarin masarautar.
Fulani Kilishi na kuka ta ce , “Don Allah ku yi mun alfarma guda, Mai Martaba ya yafe mun wallahi na tuba, azabar duniya ma kadai babbar isharace kafin akai ga ta lahira, na yi nadama son zuciyata ne ya ja mun, ku taimaka ku hadani da shi ya yafe mun,Fulani da Yareeema ma su yafe mun, na san shikenan nikam na gama domin jikina kamar laka nake jinsa a yanzu.”
Sarkin Fada ya ce, “Ke da ganin Mai Martaba kuma ai sai a lahira, alfarma guda zan yi miki, in nema miki yafiya a wajensa kuma nasan zai yafe miki da ikon Allah.”
“Na gode ,Na gode sosai, Allah saka ma da Alkairi, Allah ya rabaka da duniya lafiya,na gode sosai.” Ta fada hawaye na kwarara.
Waziri ma ya ce, “Nima Don Allah ka nema mun yafiyarsa dama duk wani wanda na cutar a wannan fadar, da Yareema da kowa,na yi nadama na Tabbatar da cewa rayuwa ba abakin komai take ba, duk wanda zai aikata sharri haka karshen rayuwarsa zata maido masa da sharrinsa kansa.”
Sarkin Fada ya ce, “Kai ma In Sha Allah zan isar da sakonka.”
Jakadiya kuwa kamar bata san suna yi ba.
Sarkin Fada na tafiya ta kallesu ta ce, “Ku wai har kun sare ne? Lallai anyi motsoratan banza Kodayake ku ba fansa kuke dauka ba, ni yanzu fafutukar fitana anan nake, kuma da ikon Allah zan fita Safina ta haihu dole ne Yareema ya Aureta su ci gaba da rayuwa kuma in mulki.
Bata karasa maganar ba kawai taji wani abu na tsiro a bayanta.
Yanayin jikinta ya fara sauyawa, kuraje manya sai billowa suke kamar ana turosu.
Ga wani ƙaiƙayi da ya addabeta.
Tuni ta fara susa tana ihu.
“Innalillahi wa inna ilahir raji’un, Allah na tuba, wallahi wasa nake na taba ba zan kara komai ba, Allah ka yafe mun,ku kira mun sarkin Fada ya ce Mai Martaba da sauran mutanen masarauta su yafeni, shikenan, Wayyo Allah,na shiga uku,na mutu na lalalace, shikenan,ni kam Wayyo Allah na,na cuci kaina,na cuci rayuwata, munafurci da son zuciya bai yi min rana ba.”
Haka ta dunga hargaginta ita kadai, har bakinta ya rufe ta gagara tai shiru, dukan su sun gama jigata kowa ya koma yin ta kansa.
(Niko na ce tunma a duniya kenan abun da ka shuka babu shakka shi zaka girma khairan Ko Sharran)
*****
Shagalin Suna ya kankama, an kawata masarauta da ado na kece raini,ko ina daukan ido yake.
Tsabar farinciki tare da nuna godiya ga Allah Mai Martaba yasa an rabawa Talakawa kayan abinci kyauta.
Raguna biyu, da Manyan Shanu Hudu aka yanka na murnsr sunan jikokin Mai Martaba Sarkin BENONI.
Gaaji ta fito cikin shigar Farar Shadda mai Adon Gold da aka jera stons din zinare.
Mayafinta fari, takalmin fari, Karamar Jakar hannun ta Golden, mai dauke da duwatsun gold a jiki.
Sarka da dan kunnen zinare masu daukan idanu.
Daga hoda,kwalli sai lipsglow a bakinta amman ba karamin kyau ta yi ba.
Tsaye take gaban Mirrow tana mamakin ganinta haka,ita kanta aranta tambaya take, shin itan ce da gaske ko kuwa gizo hakan ke mata.
Ji tayi an rikota da baya.
Adeel tsaye yana sake mata wani irin Murmushi.
Dauke yake da farar alkyabbar ta yi masa kyau sosai Mussaman yadda ta tsaya jikinsa tamkar Don shi aka yi ta.
Ya ce, “Zizi Fulani.”
Hannu tasa ta dan bigesa ta gefe, “Umm ka yi kyau Zauji.”
Adeel ya ce, “Kema kinyi kyau sosai tamkar ‘Yar tsana, but tsaya ma, waya koya miki cewa Zauji ?”
Gaaji ta yi dariya, “Babata ta ce ba a kiran sunan miji,da kanta ta bani sunaye nikam na zaɓama wannan saboda duk sanda zan furta asan cewa kai din mijina ne, kuma nawa ni kadai.”
Adeel ya dago kanta suna kallon juna, ” Umm kina nufin ba wata kenan mijinki ne ke kadai?”
Gaaji ta ce, “Eheen nawa ni kadai duk masu tunanin shigowa ma su daina Kodayake tuni ma sun daina.”
Dariya suka yi duka sun.
Sai ga Magajiya na Nocking Kofa.
Ranka Ya Dade ga Twins din an fito da su ku ake jira.
Rike mata hannu ya yi suka fita.
Suna fita ta mikawa Yareema Prince Zaayn, Gaaaji kuma Princess Zaraa.
Su kansu shigar fararen kayan aka yi masu Zaayn sak irin shigar Adeel, Zaraa kuma irin na Gaaji hatta sarkokin zinaren sai da aka mata nata na yara.
Sunyi kyau dukkaninsu tamkar a sace su a gudu.
Tafiya suke ta kasaita har suka isa wajen taron.
Wajen taro ya ƙawata sosai, Fulani Babba da Mai Martaba,Uwar Soro tare da Sauran Mutanen MASARAUTAR.
Zama sukai, aka yi saukar Al-Qur’ani, aka yi addu’o’i, sannan aka ci aka sha, aka bada kyautttuka tare da yin hotuna taro na girma da alfarma cikin mutuntawa tare da girmama juna aka yi wanda aka ba kowa damar shiga ya ci abun da yake so son ransa, kowa ya yi Farinciki.
Adeel ya lura da Adnan ba wacce ya kurawa ido irin Rumaiysa yana binta da kallon duk wani motsinta.
Ana kammala taro,Gaaji, Adeel,da Adnan suna dakin Uwar Soro, suna hira da dare.
Uwar Soro ta shigo tana, “To to yau dai kam ni na yafe ka dauki matarka ku tafi can bangaren ka don na lura karfi da yaji kana son zama mara kunya.”
Adnan ya yi dariya, “aiko dai kin kyauta Don wallahi ni yanzu har tsoron Prince nake lamarin nasa kara girmama yake a kullum.”
Adeel ya galla masa harara, “Shiyasa ai dazu na ganka kanata bin wata da kallo.”
Dukansu dariya suka yi.
Uwar Soro ta ce, “Nidai kuje Allah raka taki gona na gama wankan,nasa an maida miki da komai naku can daman.”
Adeel farinciki ya kasa boyewa,sai washe baki kawai yake.
Haka suka tashi suka koma Part din.
Suna shiga Adeel yasa a kira Rumaiysa.
Ya ce, “Ka ganta nan, ita ce kanwata da nafi ji da ita cikin masarautar nan kuma duk tafi sauran hankali ,Don haka na baka amanarta.”
Sunkuyar da kai Rumaiysa tayi kasancewar tsantsan kunyar da taji.
Adnan ya yi Murmushi kafin ya ce, ‘Yau dai rana ta farko da ka mun abun arziki.”
Bar musu Parlourn Gaaji da Adeel sukai suka koma Bedroom.
Adnan kuwa ya zauna ya dunga sharbowa Rumaiysa kalaman kauna har saida tai sanyi murus ta amince da shi, bayan sunyi exchanging Number ya rakata har part dinsu kafin ya dawo ya yiwa Adedl da Gaaji Sallama.
2 Years Letter
Mai Martaba ya yi murabus Adeel ya dau karagar mulki, Gaaji ta zam Cikakkiyar Fulani dauke da lukeken cikinta domin Prince da Princess sun Girma har an yaye su, sun koma gun Uwar Soro da zama.
Adnan ya Auri Rumaiysa sun dawo rayuwa cikin Masarauta Adeel ya basu bangare guda, har Rumaiysa ta haifi Yarinya Mace.
Baffan Gaaji kuwa an daura masa Aure da sabuwar Jakadiya (Magajiya Maman Rumaiysa) bayan Waziri ya rasu ta gama idda.
Zaune take jiki ya yi nauyi ko tafiya ba wani iyawa take ba,Zaayn ya shiga cikin dakin da gudu yana hayewa kanta.
Gaaji ta ce, “Wash Subhanallahi Zaayn ba ka ga yadda nake bane?”
Zaraa ce ta karasa tana shafa mata fuska ta ce, “Sorry Momma Ya Zaayn dinnan baya ji haka ma Kaka take cewa ba ruwanta da shi ai.”
Adeel ne ya shigo shi ma ya tashi daga fada kenan yana zuwa ya kwanta akan cikinta.
Gaaji ta ce, “Oh Allah ni kam na ga takaina ‘Ɗa da Uba duk hali Ɗaya.
Adeel ya kara kwantar da kanshi yana, “In bamu raɓeki munji dumin jikinki ba to nawa za mu ji?”
Gaaji tasa hannu tana wasa da gashin kan shi ta ce, “Amman dai in an girma asan an girma Mai Martaba Sarkin BENONI.”
Adeel ya ja hannunta ya mata kiss kafin ya ce, “A waje nake Mai Martaba amman a cikin daki nima mulkata ake ai.”
Zaayn ne ya katse su da kutsa kansa shi ma yana, “Dady ka matsa mun nima, Momma zan kwanta.”
Haka suka hadu duka suka kwanta mata a jiki, Zaraa ce kawai ta rungumeta tana, “Sorry Momma Kinji, Daddy da Yah Zaayn basa jin magana.”
Adeel ya ture Zaayn gefe yana, “Wai kai kishi kake dani ne? Ka je gun matarka mana,wannan tawa ce ni kadai.”
Gaaji na ganin yadda Adeel yake shisshige mata ta fahimci cewa lallai akwai bayani.
Ta ce, “Zaayn, Zaraa Oya Ku je gun Granma tana jiranku kuyi karatu ayi barci,amman ku fara zuwa gun Little Amrish (Yarinyar Adnan) ku gaida mun ita kunji gudnyt.”
Zaayn Ya ce, “Gudnyt Momma, take care, kiyi Addua kafin ki kwanta Kinji kuma ki shafawa Dady Addu’an shi ma.”
Zaraa ma ta ce, “Yes And Our Unborn Sister, We Loves U so much byebye.”
Har sunje zasu fita suka dawo da gudu..
Suka yiwa Adeel Kiss, sannan sukawa Gaaji ,suka yiwa cikinta ma kafin suka rike hannu suka fice da gudu.
“Gudnyt byeebyee miss u so much.”
Suna tafiya Adeel ya rungume Gaaji.
Cikin Shagwaba ta kallesa tana, “Baka tausaya mun wai?”
Adeel ya ce, “ba abun da zan miki nayi alƙawari kawai ina so yau mu kwana muna hira ne in sanar da ke abubuwan da ya kamata ki sani.”
Ya fada maganar yana kwantar da ita kan jikinsa.
Kafin ya ci gaba, ” Ban sani ba ko lokaci ya Ƙure duk da cewa ina nuna miki a aikace amman ban samu lokacin bayyanarwa ba kamar yau, Zainab, ina sonki, ina kaunarki, furucin hakan ba wai daga baki bane daga zuci, gangar jiki da ruhina,
They say when love is real, it never fades away. It just keeps getting more and more stronger with time. That is the way I feel with you. Married life would never have been half the fun it is, without you as my wife. I could never give you away for anything in this world. You are so special to me, my dear wife.
Na so nayi gangancin rabuwa da ke wanda da ace nayi bansan ya rayuwata zata kasance ba.
Ke ce bangaren rayuwata, kuma farincikin Rayuwata, haka kuma Uwar ‘Yayana,
With you by my side, I feel like I am the luckiest man alive to have the most pretty, understanding and loving wife. I look forward to the wonderful years ahead in our lives.
Na gode Zainab,na gode sosai banma san yadda zan yi miki godiyar ba, Ina kaunarki har bayan raina.”
Karasa maganar ya yi,yana kuka ya rungumeta.
Gaaji ta fara share masa hawaye tana fadin, “Nice da Godiya domin kuwa kaine Namiji na farko da ya iya jure shiriritata da duk wani shirmena, kaine ka taimaka mun a lokacin da nake bukata don haka kaine hasken rayuwata domin tare da kai nasan mene ne so kuma ya ake so, ina kaunarka har cikin rai.”
End