Skip to content
Part 28 of 31 in the Series Auren Wata Bakwai by Xayyeesharthul-Humaerath

Sarkin Fada na fita ya tarar da jingum jingum duk sun gama galabaita.

Murmushi ya yi kafin ya ce, “Daman ai duk wanda ya gina ramin mugunta kan shi ya ginawa karshenta shi zai kasance ciki.”

A tare Fulani Kilishi da Jakadiya suka dago suna kallon shi.

Ya ce, “ku fa kwantar da hankalin ku Domin Mai Martaba na raye bai mutu ba kuma shine ya fito kuka gani andai yi niyar kashe shi kuma Allah bai ba, ya nuna ikonsa don haka duk wanda ya yi imani da Ubangiji ba abun mamaki ko tsoro don an sanar da ku cewa Mai Martaba da ransa, wanda hakan abun farin ciki ne gun wasu,haka kuma abun bakin cikine gun wasu.”

Magajiya ce ta fara tashi tana, “Alhmdu Lillah Ma Sha Allah karshen zalunci ya zo cikin masauratar Benoni, zamu sheƙi iskar ‘Yanci fiye da baya tunda akai ruwa kowa ya bayyana kudirin da ke cikin ransa.”

Hajiya Rabi ta ce, “ai kuwa kam ma ga ta fada kan mulkin mallaka.”

Sarkin Fada ya ce, “Duk sauran kuje ku samu Mai Martaba a fada,ku kuwa.” Ya nuna su Jakadiya.

“Koda yake kuma muje can fadar tukunna.”

Dukkansu Fada suka nufa masu murna da Farinciki nayi, masu kuka da jin tsoro na yi.

Suna zuwa Sarkin Fada ya ce, “To In Sha Allah komai dai yazo karshe domin ga Sarki ga Fulani, sannan ga kuma Matar Yareema da Yaransa guda biyu.” Ya fada yana nuna Gaaji da Twins. Cikin mamaki duka suka zura masu Idanu.

Sarkin Fada ya ce, “Abun mamaki ko? Ai haka Allah yake hukuncinsa kai kana naka shi yana na shi,wanda na shin ne kuwa daidai, wannan dai da kuke gani ita ce Fulani mai jiran gado,Matar Yareema Masarautar Benoni,duk masu kai hari da duk wani abu da ke afkuwa kan Yareema ya warware ,ba zan bayyanar da wasu sunaye ba, amman tabbas a yanzu babban hatsari ne ga duk wata da ke kokarin aikatawa Yareema wani abu da ba daidai ba, zai fi kyau a kiyaye domin a zaune cikin zaman lafiya da lumana, Fulani Kilishi , Jakadiya da Waziri dakin duhu shine farkon hukunci a gareku wanda aciki zaku ci gaba da rayuwa har karshen numfashi.”

Kuka Fulani Kilishi ta fara tana durkusawa gaban Mai Martaba, “Ranka Yadaɗe tuba nake, Don Allah a yafe mini, tuba nake, tuba nake, babu shakka na yi kuskure, na yi kuskure da dama, amman yawanci abubuwan sharrin sheɗenne dana jakadiya,domin ni kawai ni kawai nayi Yareema ya haifi Ɗan shege ne kuma sai ya ƙi,kawai nasa masa son ‘Yan mata ne kuma sai ya ƙi Duk sauran makircinta ,makircinta ne wallahi, amun rai Don girman Allah amun rai.”

Jakadiya ma na sharɓan kuka ta ce, “Wallahi karyane bazata saɓu ba, naga kece ma kikai kokarin kashe Mai Martaba har Allah baisa ya tafi ba,ai Bokana ya sanar dani komai kece kika tura aljanni ya kashesa yanzu don kin gansa kuma sai kice wai nice? Tun kafin in sheda cewa safina yarinyata ce ke da Waziri ku kuka fara amfani da ita tana zuwa gun Yareema, kuma indai hakane yau sai asirin kowa ya tonu cikin wannan masarautar , ai ga su Hajiya Rabi da Maimuna nan gabadayansu suma munafukai ne da abun da suke shiryawa a ƙasa namu ne kawai ya fito fili.”

Hajiya Maimuna da Rabi tuni suka fara kuka jiki na karkarwa, “Na rantse da Ubangijin da ke busa mun numfashi ban taba aikata wani abu don cutar da Yareema ba,na san dai ina zuwa gun Boka don kawai ya so ‘Yata Nasmah ya aura.”

Hajiya Maimuna ta fada cikin tsoro. Hajiya Rabi ma ta ce, “Nima nima wallahi na rantse abun da na taba yi kenan saboda Khalesa ta zama gimbiya mu zama masu karfi amman ban da hakan ban taba aikata komai ba.”

Girgiza kai Fulani Babba ta fara tana mamakin yadda Hajiya Maimuna ta iya yi mata makircin kokarin asirce Yareema yadda take Aminiya gareta.

Fulani Kilishi ta ce, “ai gata nan,gata nan babbar Munafukar da ke son ruguza komai cikin Masarautar nan ita ce ta sace Yareema tun yana yaro da ta ga Uwar Soro ta ajiyesa ta gudu.”

Jakadiya ta ce, “Kece kika sani in sace san ai ko an gaya miki na manta ne ko zanji tsoron fada? Muguwa kuma ai duk kece kike sawa Yareema ciwuka a jikinsa .”

“Karyane tsinanniya kawai tanaso ne ta rabani da mijina tun farko ma duk abun da nake ita take sani, kuma tazo ta kashe Mai Martaba zata kwace masarauta Shiyasa nida waziri muka shirya yin aure domin mu kubatar da wannan masarautar a hannunta.” Ta fada tana kallon waziri.

Waziri kuwa da jikinsa ya gama jikewa da gumi ya ma kasa magana girgiza kai ya fara yana, “E….e….e….hakane.”

Duk tone tonen nan da suke ba wanda ya kullasu an zura masu ido kawai ana kallon ikon Allah cike da mamaki.

Fulani Kilishi ta ce, “Ni dai Don Allah koda za a hukuntani kada akaini dakin duhu a mun ko bulala darice in koma dakina.”

Sai a lokacin Mai Martaba ya yi magana, “Wani dakin? Ai kisa aranki cewa yau shine ma ranarki ta karshe a wannan fadar bare kuma ciki, daga nan kikai dakin Duhu ba dawowa daga lokacin da kika kudiri Auren waziri daga lokacin na kudiri cewa na sake ki kije can kwa ci gaba da auren da shi acen sai yanzu ma na fahimci cewa da shi kika fi dacewa ba dani ba ai.”

“Innalillahi wa inna ilahir raji’un Allah na tuba,Mai Martaba kamun rai, ba zan kara ba, ba zan kara aikata ba daidai ba kada akaini dakin Duhu duk hukuncin da za amun gwanda amun.”

Sarkin Fada ya kalli Jakadiya, “Ina ‘Yar ki da cikin Yareema ke jikinta a cewarku?”

Nuna Safina tayi durkushe a gefe kallo ɗaya za ka mata ka tabbatar da cewa tana cikin wani mawuyacin hali.

Ya ce, “Yanzu zaku iya sanar mana da gaskiyar lamari shin da gaske cikin jikinta na shi ne ko akasin hakan.”

Karaf kafin Jakadiya ta yi magana Adeel ya ce , “Ni ban taɓa kusantar wata ‘Ya Mace da ba muharramata ba,ko da ya kasance na so yin kuskure amman ban taba kusantarta ba ita ma sheda ce.”

Jakadiya ta ce, “Maganar ciki kam ba karya ciki,in ba wai so ake adanne mu a zalunce mu ba, cikin jikin Safina bana kowa bane sai na Yareema.” Ta fada tana kure Safina da ido.

Sarkin fada ya ce, “ke Kinji abun da Ta ce, ya tabbata hakan ne gaskiya?”

Ido cikin Ido Jakadiya ke kallonta ta yadda bata isa aikata wani abun da ba daidai ba.

Ganin bata da zaɓi kawai ta fashe da kuka ba tare da ta ce komai ba.

Mamaki abun ya ba Yareema, kenan dai har yanzu Jakadiya ba za ta daina makircin da ta saba ba.

Uwar Soro ta ce, “Ita ma bata da amsar tambayar da aka mata ne domin tasan ba gaskiya bane, wannan a bayyane yake Yareema bazai taba iya aikata hakan ba, tun farkon lamarin ma ni ban yarda ba, ko a baya su sukan san mai suka aikata da yasa ya kasa karyatawa.”

Mai Martaba ya yi gyaran murya ya ce, “Koma mene ne dai a yanzu baza mu yanke hukunci ba,yanayinta tana bukatar kulawa sosai a kula da ita in Allah ya sauketa lafiya komai zai warware komai yana hujja don haka sai mun ga hujja domin gasgata gaskiya.”

Sarkin Fada ya ce, “Maddallah da Sarki mai adalci mai jin kan al’umma.”

Mai Martaba ya kara da fadin, “Kada ka barsu a dakin duhu in an sanyasu na kwana uku ya wadatar da su sai amaida su gidan gyaran hali, acen sai su ci gaba da rayuwa kuma har Allah ya tabbatar da abun da ya dace.”

Birgima Fulani Kilishi ta fara,ta je ta kankame Fulani Babba tana, “Don Allah ki bashi hakuri Yaya,ki bashi Hakuri sharrin sheɗan ne,ni kawai akai ni cen gidan gyaran halin kada a kai ni dakin duhu inna shiga can mutuwa zanyi na shiga ukuna na mutu na lalace.”

Suna haɗa ido da Gaaji tuni ta sake Fulani Babba jiki na rawa.

Jakadiya ma zata yi magana kenan suka haɗa ido da Gaaji, da sauri ta kautar idonta ganin yadda jikinta ya fara ɓari ba shiri.

Sarkin Fada ne yasa dogarai suka kadasu har Dakin Duhu ana hankaɗasu aka rufe kofa wata irin kara dukkanin su suka sake na razana ganin ba wanda ke iya hango wani.

Sunata kokawa da juna duk sun firgice.

Wannan macijin da Gaaji ta tsage suna shiga ya haɗe jikinsa ya tashi.

Fulani Kilishi ya fara sara a ƙafa, ta saki wani fitsariin wahala tama kasa ihu ko magana tsabar azaba.

Sannan ya koma ga Jakadiya ma dalla mata sara a kateriyarta.

Cikin muryar wahala hawaye na ambaliya ta ce, “Ɗuwa…..wuuuuuuu.”

Sai ko ta sume a gun. Shi kuwa Waziri Kaciyarsa ta sare, ji yayi tamkar ana zare masa rai , “naaaaaaaaaaaa mu…mu…tuuuuu.” abun da ya iya furtawa kenan.

Can Jakadiya na farkawa ta gagara zama kan duwawunta cikin Galabaitacciyar murya ta ce, “ku duba mun, duwawuna ya fice ko? Shikenan ya fice ko? Baya jikina ,baya jikina.”

Waziri ya ce, “Nima,nima,ku duba mun kaciyata inaga ta fita ta fita, birne mu akai a kabari ko? Wannan azabar kabarine shikenan.”

Ita kam Fulani Kilishi ta shiga wata duniyar domin ko motsa bakinta bata iya yi, cinnaku sun cije sun kumbura mata shi.

Ko a zuciya ta kasa yin sambatu tsabar radadi ita dai kawai gata nan kamar fanko.

*****

Nan take Mai Martaba yasa kowa ya koma Bangarensa a ci gaba da tafiyar da komai kan tsari.

Sarkin Fada yasa aka shelawa yan Gari cewa Sarki na raye da ransa bai mutu, hakan kuwa ba karamin Farinciki da jin dadi sukai ba wanda har saida talakawa suka shirya kwarya-kwaryan bikin murna.

Aranar aka fidda komai dake dakin Fulani Babba domin sauyawa, Kuma aka maida Magajiya matsayin Sabuwar Jakadiyar Masarautar.

Safina ta koma bangaren Uwar Soro da zama domin ta ci gaba da lura da ita.

****

Adnan ne ya dauki Princess hannunsa suka shiga Part din Adeel.

Suna shiga Adnan ya ce, “Wannan kam da kanwata take kama.”

Adeel ya yi dariya, “Wannan kuma ai saidai don son zuciya amman kowa na ganin yaran nan yasan Ni suka yo,baka ji maganar da Mai Martaba ya yi ba ne, Kodayake ma ba dole suyi kama dani ba, na sha aiki ai kamun samuwarsu cizo da zagi babu wanda ban sha ba.” Ya fada yana kallon Gaaji.

Zata yi magana kenan sai ta tuna da Adnan ta sunkuyar da kai, Adnan ya ce, “Iye? Wai ya naga kanaso ka zama karamin Dan iska ne agabana fa kake wannan maganar anya kuwa?”

Adeel ya ce, “Eheen Yaro Aure Dadi gareshi kai ma dai ka gwada yi kaji zaka ban labari barin ma ka samo ‘Yar Shilar Fulani sunfi gardi.”

Kunya Gaaji taji kamar zata nutse agun hakan yasa ta tashi sumi-sumi ta shige cikin bedroom.

Adnan ya ce, “Ka ga ka koran mun kanwa ko hira ba mu yi ba ko?”

Adeel ya ce, “Na ur own problem nidai ina fada ma yaro ka yi aure Allah, ni yanzu ma a matse nake, da za….”

Adnan ya rufe masa baki da hannu, “Ka ga ni kam kana shirin fin karfina kuma daman ance irinku kinfi naci ai bara in kwantar da Princess Zaraa in tafi gobe zamu zo da Baffa In Sha Allah.”

Har kofa Get Adeel ya rakasa suna wasa da dariya.

Yana komawa dakin ya bi Gaaji Bed room jin mutum tayi kawai ya kwanta ta bayan ta, “Ke yaushe wai kika koyo kunya ne? Anya ba kunyata kika kwashe ba,nasan da dai na fiki kunya.”

Zamewa tayi ya dawo kasanta ta haura ta samansa sai da ta kai masa hot kiss har yana rufe ido kafin ta ce, “Duk wani take-takenka da Sambatunka sai ka jira fa,eheen kwalelenka.” Ta tashi ta fice daga dakin da gudu.

Ya biyo bayanta kenan sai ga Uwar Soro ta ce, “To Uwata mai miji zuwa zaki yi ai ki dawo Part dina kuma kam har sai kin warke keda dawowa nan.”

Nan take Dariyar Adeel ta dauke yanayinsa ya canja.

Ya ce, “To meyasa bazata zauna anan ba?”

Uwar Soro ta ce, “Saboda al’adarmu bata ce haka ba,sannan domin nema mata lafiya ma dole ne ta zauna a inda za ana kula da ita, Don haka ki wuce ki tawo yanzu ma ga ruwa can muje zan miki wanka twins daman nasa an daukesu.”

Ita kanta Gaaji har cikin ranta bata so Hakan ba amman ba yadda ta iya haka ta bi Uwar Soro.

Tana yi masa gwalo.

Kawar da kai ya yi.

Da dare yana son ganinta amman ba yadda ya iya haka ya kwanta.

Washegari

Shirye-shiryen bikin suna aka fara yi ba kama hannun yaro.

Cikin masarauta da gari ya kama ana shirin bikin Sunan Jikokin Mai Martaba Sarki Mohammed Rohaan.

Nakuda Safina ta fara yi, Uwar Soro da Gaaji suke riketa za a kaita Asibitin Fada.

Safina ta ce, “Aa Tukunna Don Allah ku kaini gun Mai Martaba da Yareema inaso inyi magana dasu Don Allah ku taimaka mun, wannan shine abun da nafi bukata Don Allah,Don Allah nace maku kunji.” Ta karasa tana kuka.

Haka suka kaita Fada.

Aka kira Adeel.

Suna zuwa.

<< Auren Wata Bakwai 27Auren Wata Bakwai 29 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.