Cikin Fushi zai fita har sai da yaje bakin kofa ya tuna da gajeran wando ne a jikinsa, tsaki ya yi ya koma, yana zura jallabiya ya fita zuwa bangaren Uwar Soro.
Gaaji na ganin shigarsa da gudu ta koma bayan Uwar Soro tana kankameta, “Baba Wallahi shin zalina zai kara yi don kawai na rama marin da ya mun.”
Bude baki Uwar Soro tayi da mamaki tana kallon Gaaji ,don ita a iya saninta babu wani mahalukin da ya taba dagawa Yareema hannu, bare kuma batun mari, ah lallai yar nan kin taro ruwa.
Ta fada aranta.
Yanayin yadda yake huci ita kanta Uwar Soro ta razana ta yadda ta kasa ce masa uffan.
Gaaji kuwa kara kankameta take tana, “Aradu mugune karki bari ya taɓani zai kashe ni.”
Ji tayi kawai ya dauketa cak.
Ya fice da ita, bai direta a ko ina ba sai kofar wani kurkukun daki, karami, mai bala’in duhu mutum baya iya ganin ko hannunsa a ciki, jefata ciki ya yi ya rufe kofar sannan ya koma dakinsa.
Nan take Gaaji ta birkice, Wani irin kuka take tamkar ba mutum ba, ta gama ficewa a hayyacinta, kayanta duk ta yayyaga su da fisga, gashin kanta ma sunyi carko-carko, tana ta fisga cikin lokaci kalilan ta dawo mahaukaciya.
Uwar Soro kuwa tana ganin Prince Adeel ya shigar da Gaaji dakin nan hankalinta ya matukar tashi, tasan manya ma aka shigar da su ya suka kare bare kuma yarinya? Dakin da babu ko windo bare wani sakon da haske zai shiga, nunfashi ma mutum na ciki in ya dau lokaci dakyar yake iya yi, wasu ma kan a cirosu sun mutu.
Ganin bata da wata mafita yasata saurin kiran Adnan ta sanar da shi halin da ake ciki, wayar Adnan sam bata shiga domin ya tafi India gun aikin Baban Gaaji ya duba yadda lamuran ke gudana, kuma daga nan zai koma America domin yin wani bincike da yake.
Tun tana gwada kiran har ta gaji ta hakura, domin babu alamar shiga.
Adnan ya sanar da shamaki cewa bai yarda wani yaje Gaaji take ba sai shi, kuma shi ma din ruwa kadai zaina bata kada a kuskura a bata abinci.
Gaaji tun tana ihu har ta gaji ta daina ban da ajiyar zuciya babu abun da take, kamar wasa har dare ya yi, ya tabbata dai sai da ta kwana adakin, duk da cewa ita bata san dare ko rana ba sai dai wani lokacin kawai ta ji barci ya dauketa, inko ta farka ma duk daya tunda duk abu ɗaya idonta ke gani wato duhu, barcin ma tana farawa wasu irin samudawan sauro zasu isheta da kuka a kunne, a jiki suna cizo, ya zamana bata da aikin yin da ya zarce kuka.
Uwar Soro ce ta roki shamaki da ya taimaka yana bata abinci ko da kadan ne ba tare da sanin Yareema ba, tunda ita ma ya ce ba ruwanta kada ta bari a hannunta ya shiga ciki, hakan kuwa ya kasance a boye kullum yake bata abinci da ruwa.
Gaaji na cin abinci tana kuka, laluba take domin ko bakinta ma takan iya rasawa wani abincin ma kan ya shiga bakinta ta zubar a lalube lalube, kusan rabin abincin a kasa yake, kafin rabi ya shiga cikinta.
Ranar da ta kwana uku a dakin Adnan ya dawo, yana zuwa masarautar bangaren Uwar Soro ya fara nufa domin ya yiwa Gaaji tsaraba sosai kasancewar yasan zai sha daru zata ce yaki zuwa gunta inko yace yayi tafiyane ma zata ce me yasa bai tafi da ita ba.
Da fara’arsa ya shiga yana fadin, “Wai ina Gaaji Beautyn ne? Tana ina? Bata ji Yayanta ya zo bane? Ko dai fushi tayi ne? In fara tsallen kwado daga nesa ko? To na fara.”
Ya ƙarasa maganar yana shiga cikin Parlourn Uwar soro, tsayawa ya yi turus ganin Uwar Soro ce ita kadai babu Gaaji bare alamar ta.
Ya ce, “kar dai fushin yasa ta buya bata son ganina?”
Cikin yanayi na rashin jin dadi Uwar Soro ta ce, “Ina fa, Gaaji na dakin Duhu.”
Zaro ido Adnan ya yi cikin fargaba ya ce, “Subhanallahi! Me ya faru? Waya kaita?”
Nan da nan Uwar Soro ta kwashe dukkanin abun da ya faru ta sanar da Adnan.
Ko magana bai kara ba cikin fushi ya nufi gun Adeel.
Yana shiga Yaga Adeel hankali kwance yana zaune a daining yana cin abinci.
Ko sallama gagararsa ta yi yana shiga kawai a harzuke ya ce, “akan me zaka rufe Gaaji a wancen dakin duhun? Ni kam wai ina imaninka ne Prince? Me yasa zaka kulleta kullewan ma bana lokaci kadan ba yau har kwana uku? Wannan Yarinyar Amana ce fa agunka Wallahi in har ka cutar da ita wani abu ya sameta Ubangiji ba zai taba barinka, me yasa zaka aikata haka?”
A gajarce Adeel ya ce, “saboda na isa na yi mata hukunci a matsayina na mijinta.”
Kallonsa Adnan ya tsaya yi da mamaki, wai har Adeel ne ke dangata kansa da Gaaji matsayin miji, abun da bai taba furtawa ba koda da wasa?
Ya ce, “To naji ni kuma a matsayina wanda nake yaya awajenta ka fitomun da kanwata.”
Adeel ya tashi ya nufi 2sita ya zauna kafin ya ce, “ba ka isa ba, in kuma kace zaka shiga sabgar da ba taka ba zan nuna maka asalin wane ne Prince Adeel Muhammad Rohaan.”
Ran Adnan ya matukar kara ɓaci zuciyarsa na bugawa cikin zafin rai ya ce, “Au haka za ayi? Ya karasa maganar ya bugawa Adeel hannu a kirji.
Adeel ma a fusace ya buga masa kirji yana fadin , “Kwarai.”
Kokarin fara kokuwa suka yi kowannensu na wuce zuciyar maza na bugu rai ya baci.
Uwar Soro ce ta katse su da fadin, “Subhanallahi! Me zan gani? Me yake shirin faruwa anan kuma, da girmanku?”
Adnan na wuce ya ce, “na rantse da girman Allah indai yau bai fito da Yarinyar nan ba babu shakka sai na je fada na sanar da Mai Martaba da kowa ma’ in tabbatar da cewa gata nan matarsa ce.”
Cikin fushi Adeel ya wurga masa keyn dakin yana huci ya shige cikin bedroom.
Adnan ya fice Uwar Soro ma ta bi bayansa suna zuwa cikin sauri jikinsa na rawa ya bude Gaaji.
Hasken da tagani ya kashe mata ido rufe idon tayi a tsorace, haske har ya fara zame mata sabon abu.
Uwar Soro ce ta shige ta riko hannunta da sauri ta fito da ita.
Gabadaya yanayinta ya canja mata da maraba da mahaukaciya har ta fi fasali lokacin da ta fara zuwa fadan akan yanzu.
Jikinta duk wasu irin cuhuka da kuraje.
Idonta arufe ban da hawaye babu abun da take.
Adnan ya tsaya yana kallonta bai san lokacin da hawaye suka fara zuba daga idanunsa ba jikinsa kuwa ya kasa daina rawa.
Cikin Muryar kuka ta ce, “Ina za akai ni? Don Allah kar a maidani irin wancen dakin zan mutu.”
Uwar Soro ta ce, “ba za a mai da ki ba, Gimbiyata nice nan kinji daga yau ma baza ki kara shiga cikin dakin ba In Sha Allah, ki bude idon ki a hankali kinji mu tafi.”
Tana bude ido tana ganin haske sai ta kara rufewa a karshe sai haka suka tafi kawai.
Adnan kums tsabar tausayinta ya kasa furta komai ma sai binsu da kallo kawai.
Suna shigewa cikin daki shima ya fice a Masarautar rai bace ba tare da ya koma bangaren Prince ba.
Da kyar ta iya bude ido, uwar Soro ta mata wanka,vana wankanma tana kuka domin ko ina aka taba ciwo yake mata, da kyar aka wanke mata jikin sama-sama ta sha magani, duk son abincin Gaaji kasa ci tayi da kyar tasha tea dan kadan ta kwanta barci.
Tana barcinma ban da razana, ihu da surutai babu abun da take tana birgima, sai da Uwar Soro ta mata addu’a to tofa mata sannan ta samu barcin nata ya dan yi nisa.
Gabadaya duk ta kumbura,har yanayin kamanninta ya canja.
Tun daga Ranar Adnan ko ya shiga fada baya neman Adeel sai dai ya duba Gaaji suyi hira ya tafi, ko da sun hadu da Yareema sai dai kowa ya yi harkar gabansa ba mai kula wani.
Ita kuwa Gaaji na zaune sai dai aji tayi kwafa, in Adeel ko Uwar Soro suka ce mene ne? Saidai kawai ta washe baki ta ce ba komai.
Daukan Gaaji Adnan ya yi zasu fita kenan sai ga Adeel ma ya fito suka ci karo da juna Gaaji ta…