Skip to content
Part 14 of 80 in the Series Azurfa Da Zinari by Hadiza Gidan Iko

Da wani irin matsiyacin tashin hankali nadiya ta isa dakin su tana tunanin me tayiwa daddy da zaiyi mata wannan wulakancin? A duk duniya babu wanda take so irin show shi kadai ta shiryawa aure da rayuwar aure don duk Rashin mutuncin ta har show din take yarda suna soyayyar rungume juna bata Jin zata iya bashi kanta sai ta hanyar aure don haka bata jin zata yarda da abinda daddy yake nufi wallahi dole a saurara mata

Duk da hakan kam ta kwana cike da zullumi da rudani don ta san da gaske daddy yake ba zata wuce wannan takin ba zaiyi maganar auren ta abinda ta tabbatar sai in show zata aura ne zata yarda amma koma waye wallahi bata Jin zata yarda

Washe gari kuwa da safe  sai ga daddy ya fada mata ta shirya tana da bak’o an jima kuma ta sani dukkan rashin kirkin da ta iya tayi auren ta babu fashi ta soma kuka tana fadin

“Haba Daddy don Allah Ina adalci a cikin abinda kake mini ? wane irin bak’o kake magana ? In aure kake so nayi ina laifin kace na fito da miji amma kace wai zakayi shela ka samo min miji sai kace nayi bandaro nayi kwantai? Ina da wanda nake so sai na kawo maka shi ka daura mana auren.

“Ba na bukatar ki kawo mini wanda kike so nine da kaina na zabi mijin da na san zai rike auren ki na bashi ke kyauta ko sadaki nace ni zan biya mishi don haka kar ki zo min da wata manufar ba zan surare ki ba.

Ya haura saman shi ya barta nan tana mishi rakiya da idanu bakin ciki na shirin kasheta.

A safiyar ko abinci bata iya ci ba babu abinda take dakon zuwan sa sai bakon da daddy ya ambata mata zai zo.

Tana kwance a daki abin duniya ya ishe ta fati ta shigo tana fada mata ana kiran ta a waje.

Ta tashi zaune tana kallon fatin tana fadin “Waye yake nema na?

“Ban bani ba yaya kaisar ne yazo yace daddy yace yayi Miki magana.

Ta mike a fusace ta figi wayar ta inda ta fice amma bata ga kaisar ba sai ma maccid’o da ta gani zaune a karkashin inuwar umbrella ta soma dube-duben inda zata hango bak’on ko kuma Kaisar Wanda ta soma tunanin ko shi daddy yake nufi bata? Ashe kuwa da garin Bauchi ya kama da wuta.

Ta juyo tana kallon Maccid’o wanda ya zamo daya ne daga cikin masu gadin kofar get mutumin Niger ne wani narkeken kato ne mai zafin zuciyar tsiya gashi da shehen karfi tamkar gidan shari a kuma fuskar shi a kullum tamkr an aiko mishi da mutuwar iyayen shi biyu.

“Kai Maccid’o waye kaga ya shigo gidan nan yanzu? Ya kara gyara karin hular shi yana fadin, “Babu wanda ya shigo sai nina nan nika biddar ki mai gida bai hwada miki zanzo ba?.

Da wani irin sauri ta ke duban maccid’o tana mishi kallon k’aska’nta .

“Kai da Allah tsaya kake wani zanzana  kazo min ka ce min ?.

“A dazu mai gidda yayi shela a masallacin sallar jijjihi yace duk wanda ka son sadakar armen ki shi hwada mai ni ko nace Ina biya ya kuma ce ya bar min amma na zaka muyi batu .

“Kai da Allah sauraran min kidahumi da Kai da wani wagegen bakin ka kana magana kana feshin yawu kake cewa an baka sadakar aure na? shi daddyn bashi da hankali ne?  to ka koma ka fadawa daddy idan ka yarda aka aura min Kai wallahi sai na kashe ka mus har kiyama sakarai dabba da kai da Allah tashi a gaba na tun ban falla maka bari ba katon banza katon kauye ka dube ni kace an baka kyautar aure na kai ko a mafarki kaga haka ai zaka karyata bare ka wani tunkaro ni da wani katon kan ka kamar bilo enchi tara .

Zuciyar maccid’o ta hauro don Allah yayi mishi bakar zuciya baya daukar raini don haka tuni fuskar nan ta kirne tamkar kunu ya soma bude manyan hancin shi yana hararen Nadiya wacce ya tabbatar da ba itace tayi mishi wannan wulakancin ba babu abinda zai hana yayi kwallo da ita amma sai ya gyada kai ya wuce Yana jan takanman shi kwarab kwarab  ta bi shi da wani shegen kallo tana fadin

“Da Allah dube shi sai kace wani shuri ya kwaso wani katon jikin shi mai kama da shirgi yen yen yen ko aka ce mishi nima sakarai ce irin shi?.

Kaisar yana tsaye yana kallon Nadiya da maccid’o duk da baya jin abinda suke fada Amma dai abinda daddy ya fada mishi na yayiwa Nadiya magana ga bak’on ta nan yaxo shi yafi komai firgici a gare shi .

yana ta sakawa da warwarewa wane irin bak’o daddy yake nufi ? me zuwan maccid’on yake nufi wurin nadiya?.

Yayi ta jerawa kansa tarin tambayoyin Amma ya rasa amsar su dole ya shigo zuzzurfan tunanin Wanda yayi nisa matuka gaya a son gano manufar daddy in dai aure zaiyiwa Nadiya Anya kuwa Daddy yana nifin yi mishi adalci?.

Fati ta katse mishi zuzzurfan tunanin da ya afka ta hanyar yi mishi sallama da zazzak’ar muryar ta fuskar ta dauke da murmushi Wanda ita kanta ba zata ce ga na menene ba amma dai ba zai wuce maganar daddy ta bawa maccid’o auren Nadiya ba .

Ya juyo yana sauke ajiyar zuciya yana duban ta.

“Kai Yaya kaisar me kake tunani ne haka har kana firgita kamar wanda ya tashi dogon bacci?.

ta fada tana kafe shi da idanun ta masu dauke da sirrin soyayyar sa da take kwance a cikin su.

Ya soma shafa kyakkyawwr sumar kanshi wacce take kwance a Kansa ta kuma Kara fito mishi da sirrin kyawun shi .

“Fati me kika sani akan maccid’o? me Daddy yake nufi ? naga Ni da kaina Daddy yace na kirawa maccid’o nadiya don Allah meye ?

Ya fada da son ta bashi cikakkiyar amsar da zata fidda shi daga zargi.

Fati ta kuma yin murmushi tana duban shi.

“Nifa ban san abunda kenan ba yaya kaisar kawai dai naji daddy yana fadin zaiyiwa Nadiya aure to ban san ba ko da maccid’on yake son hadata.

“Daina fada min haka fati !

ya katse ta da sauri.

Ya mike ya wuce daki fati ta bashi da kallon mamaki tana jin wani Abu mai kama da kishin Nadiya a ranta Don ita kam bataji haushin hadin da Daddy yayi ba nadiya tana son tafi karfin su .

Da dare daddy ya dawo ya kuma kira maccid’o har falo don yaji yadda sukayi da nadiya

Maccid’o ya zayyanewa Daddy irin wulakanci da cin mutuncin da nadiya tayi mishi bai rage komai ba har da sharrin da tayi mishi duka ya fadawa Daddy.

“Kar wannan ya dame ka kaji maccid’o. Ita mace wuyar ta a mallake ta ne amma kafin hakan duk irin wulakancin da ta iya tayi babu abinda za a fasa don haka ungo kudi ka soma hidimar ka tunda na baka auren Nadiya na baka shi har abada babu mai tayar da hakan ka daina damuwa da duk abinda take fada maka daga inda ta bar gidan nan ta koma karkashin ikon ka dole tabi abinda kake so don haka in ka samu lokaci kaje gida can Niger din ka sanar da magabatan ka suzo muyi magana don ba zan ja lokaci mai tsayi ba nan da kwana talatin ma zan iya daura auren ku kaga gara ka kimtsa inda zaka ajiye ta nasan can zaka ajiye ta Niger din ko?.

Maccid’o ya amsa yana fadin

“Eh cann na mai gida don bani da wurin ajiye ta nan amma can a yankin mu tasawa muna gidan mu na gado na gandu kuma akwai shigihwar da zan saka ta.

“To alhamdulillahi maccid’o dukkan abinda kake so ka fada min zanyi maka shi sadaki ma Ni zan biya maka shi .

Maccid’o ya amsa yana godiya cike da murna ya mike ya wuce yana yiwa daddy da mama sai da safe.

Nadiya da taji abinda ya wakana tsakanin daddy da maccid’o ta fashe da kuka tana fitowa don ta san daddy ya gama kashe mata rayuwa idan har ta bari aka daura auren ta da maccid’o wanda yake nufin kaita Niger.

“Wallahi daddy ba zan auri maccid’o ba  ko ka aura min shi Allah zan kashe shi ne tunda ka daina sona.

“Ki kashe shi din kema ba sai a kashe ki ba ? Auren ki da maccid’o ko shine aikin da zanyi na karshe sai nayi shi . In ma ajali na ya riske ni a haka zanyi wasiyyar a cika shi ko na mutu maccid’o kuma na tabbatar da duk taurin ranki ya zarce ki shine kadai namiji mai iyawa da ke a dai yadda kike din nan don haka ba kisa daya ba kiyi mishi kisa dubu ko ma fin dubun

Daddy ya dubi mama yana fadin

“Aliya na tura miki kudi a account din ki dazu gobe ku shiga kasuwa duk abinda ya danganci kayan aure ki siyo su in ma kudin da na tura miki basu Isa ba kiyi min magana na sake tura miki wasu .

“To shikenan in sha Allah zuwa gobe zamu tafi da su su duka ta zabi abinda take so.

Ya haye saman benen shi ya bar Nadiya da kuka tana fadin

“Wallahi tallahi mama ba zan auri wancan matsiyacin ba Niger fa ake shirin kaini? wallahi duk abinda ya biyo baya laifin daddy ne tunda nace mishi bana so baiji ba wallahi ba zan zauna auren nan ba koma me zai faru sai dai ya faru wallahi.

ta mike ta shige daki tana faman kulla mugun Abu

Kan kace me? hidimar auren Nadiya ta kankama  mama sai siye siye take ta fannin amarya komai Yana tafiya bisa tsari yayin da ango maccid’o kuma yaje Niger ya dauko iyayen shi akazo don tsayar da magana

Daddy ya kira dan uwan shi Yaya halilu wanda suke uwa daya uba daya kuma tagwayen da suka fito ciki daya kuma a rana daya kuma sunan su ma iri daya ne sai dai lakabi da ya banbanta su . shi daddy da ya zamo Hussaini ana ce mishi iro . dhi kuwa yaya halilu da yake shine Hassan sai ake ce mishi khalil amma sunan kauye da dole sai an bata shi sai aka mayar da shi halilu . Ibrahim ibrahim Khalil

Dole aka sauki iyayen maccid’o saboda sai gobe su yaya halilu zasu iso kuma shi yaya halilun shine alwalin nadiya

Kaisar kam cike yake da tashin hankali domin kuwa ya gama tabbatar wa daddy ya bayar da Nadiya ga maccid’o kuma har yanzu bai samu damar magana da mama ko daddy ba don ya nuna musu hadin bai hadu ba sam domin an kashe rayuwar nadiya idan aka kaita rayuwar da take k’asa da tata matukar ba a sama mata Rayuwar da ta zarce tata ba.

Haka yake kwana salla yana rokon Allah mafi alheri a cikin soyayyar Nadiya da aka jarrabe shi

Washe gari kuww tun da sassafen sai ga motar yaya halilu ta shigo gidan dan uwan shi daga misau inda alabo ya tuko shi tunda misau din suka iso tare.

fati da taga zuwan su baffan ta sheko da gudu ta rungume baffa yaya halilu wanda shima yake rungume da ita yana murmushi cike da farin ciki.

Shi kuwa alabo kallon fati yake cike da wani dadadden abu da ya jima a zuciyar shi wanda ya kasa furta shi ga fati daga shi sai Ubangiji kadai suka san yadda yake wahala da azabtuwa akan fati amma meye abun yi?

.”Baffa yayi murmushi yana farin cikin ganin fati yake fadin

“Shikenan Aliya ta rike mana ke bintu kin baro innar ki da kewa kullum wakar zuwa take ta tafi dake anya kuwa anwa  innar ki kirki da Kara bintu?

Daddy ya soma saukowa daga saman sa yayin da mama ta fito tana fadin

“Allah ya huci zuciyar babban yaya wallahi cikin satin nan nake shirin aiko ta misau Allah ya huci zuciyar ku .

“Haba dai aliya ke dai dadin baki kawai kike min amma ai ke da  uwar ta ni babu ruwa na.

“Baffa wallahi kuna raina babu ruwan mama nice dai ban taho ba na bari sai nan gaba kad’an.

“To ai shikenan tunda fa kinzo maraya bintu yaushe zaki koma misau? .

“Wallahi zan dawo baffa .

“Ai gashi nan zasuyiwa yar su aure ke kina nan ga yaron nan usi likita Yana ta zuwa ba kya nan ni da na san da wuri ne auren Nadiya ai da iro ya hada har da ke tunda kina da likitan nan usi.

Daddy ya sauko yana musu sannu da zuwa alabo ya duka yana gaishe da Daddy Wanda yake bubbuga kafadar alabo Yana fadin

“Uba na ya gida ya Aiki?

“Duka lafiya lau alhamdulillahi Daddy.

“Masha Allah dama ina jiran zuwan ka akwai mota na nan a parking space ta Nadiya da gilasan ta suka mutu tashi ka Kira sarkin gida kuje a sauya mata gilasan sai ka wuce da ita.

Da murna alabo ya mike inda fati ke fadin

“Yaya alabo tsaya na kawo maka break don Allah tunda sammako kukayi.

Suka fice alabo yana kallon fati da jin abin nan da yake ji game da ita wanda ya hana shi yayi mata musu

Dole ta sauke shi a dakin su tana kawo mishi kayan break

Kallo daya Nadiya tayiwa alabo ta kawar da kanta tana jan tsaki.shima da yake gwanin zafin Kai ne sai yayi kamar bai san tana wurin ba.

Yana duban fati Yana Jin idan har ya rasa ta shi kam ba lallai ya kara rayuwa ba .

“Don Allah kaci abincin Yaya alabo dama zan kira ka sai kuma gaka kazo.

“Me kika aje min ne,? ai inna na can kullum sai tayi maganar ki .

“Ai zan dawo in sha Allah nan mama ce bata son nayi nisa nima dama zaman ya ishe ni wallahi.

yana cin abincin yana fadin

“Kince zaki kira ni me zaki fada min ?.

“Daddy ne ya siya min mota ni kuma ba hawa nake ba shine nace zan baka ita tunda kullum baffa sai yayi maka gori kaima ka huta gorin baffa.

<< Azurfa Da Zinari 13Azurfa Da Zinari 15 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×