Skip to content
Part 15 of 80 in the Series Azurfa Da Zinari by Hadiza Gidan Iko

“Na kuwa gode my blood amma ai kinga yanzu Daddy ya bani wata yace muje da sarkin gida a sauya mata gilasan.

Da sauri Nadiya ta juyo jin daddy ya kyautar mata da mota .

“Motar tawa aka baka? to kar ka sake ka dauke ta wallahi banda wacce Daddy ya siyawa baban ku kuma shine za a dauki mota ta a baka? wai ku wace irin tsiya ce da ku  da komai sai Daddy ne zaiyi muku? motar da baffan yake hawa ba Daddy ne ya siya mishi ita ba? .

Alabo ya juyo yana kallon Nadiya da wani shegen kallo mai cike da fusata yana fadin

“To tsinanniya shi baffan da kike cewa Daddy yayi mishi abu yayi mishi abu yaya suke ? ke ni kike fadawa haka don uwar ki? To don uban ki bari naga uban da ys isa ya hana na dauki motar in kin kai marar kunya ina son ganin kokarin ki da kalar iskancin ki nafiki daba Yasin .

Ya fada yana zaro mata idanu yana nuna ta da hannu.

Nadiya tayi shiru don ta san da gaske yafi ta dabar tunda baya jin wuyar make ta.

“Don Allah yi hakuri yaya alabo kaci abincin ka.

“Barni da tsinanniyar yarinyar nan marar albarka don uban ta Ni zatayiwa gori? Ita kadai Daddy ya haifa mu ba uban mu bane? har tana wani buda shegen bakin ta tana ambato baffan mu tana mana gori don uban ta.

“Anyi maku gorin kuyi zuciya mana matsiyata kawai .

Nadiya ta fada tana ficewa don ta san in ta tsaya kam alabo make ta zaiyi.

ya gama cin abincin ya fice shi da sarkin gida wurin gyaran gilasan motar nadiya

yaya halilu ya dubi daddy yana fadin

“to kai iro haka akeyi saboda Allah aure haka gatsal tamkar dirar zawayi? kuma sai ka hada yarinyar nan da kaskantacce irin maccid’o? Ina laifin ka samu wani ko daga cikin yaran ka ne ma aikata? Kuma kamar anyi gaggawa fa.

“Wato yaya halilu yarinyar nan ce babu abinda ya sauya daga cikin halayen ta da dabi un ta. tamkar kara zuga ta ake komai tana son tayiwa mutane izgili da gadara. tana takama da arzikin gidan su ni kuma na gane auren kawai zanyi mata na zauna lafiya. yarinyar nan in mota ta hau yaya halilu bata dauki ran dan a bakin komai ba. sau biyu ina ganin yadda take take mutane a titi banda wadan da mutane ke sanar min abubuwan da tayi. ba ayi sati ba baka ga tsohon da ta mara ba mari kuma irin na rashin mutunci abu kad’an zata cewa mutum matsiyaci gori kuwa ko wanda take yi wa fati ya isa ayi mata hukunci to amma sai na gane ko auren za ayi mata dole dai jajirtaccen namiji wanda zata rika shakka kuma wanda zai sa tayi nesa da gida idan har Allah ya zaunar da ita za a san abinda akayiwa shi maccid’on kuma a dawo dashi nan Nigeria tunda a yanzu kam Niger zai kaita in komai ya saitu ne sai ya dawo da ita nan kuma shi din ba zai yarda ta raina shi ba shine dalilin wannan taso maganar auren.

Yaya halilu ya sauke ajiyar zuciya yana fadin

“Kayi hikima kuwa iro Allah ya sa ya zama silar shiriyar ta amma naso ace ka hade su da bintu tunda itama tana da yaron nan usi likita dan gidan malam sanu yana son ta sosai kuma duk yankin nan shine yakke likita Yana da kyamis din sa .

” To yaya shima in ya shirya ai babu matsala sai ya fito kawai ayi da shi tunda sun isa auren .

“Wane irin sun isa ma ita bintu ba ga kawar ta nan naja ta gidan mai jakkai nan ba har da yarta a bayan ta? Ai su don ka daure musu kunkurun karatun bokon nan ne amma yanzu ai kamata yayi su fuka ka kawar da su in yaso tunda muna mayatar son Ya’yan in suka haihu sai mu rido jikokin .

sukayi dariya su duka kafin mama ta shigo ta kawo musu kayan break ta fice

tuni suma iyayen maccid’o da suka kwana a gidan a ka mika musu kayan break suka karya kafin daddy ya fada musu dan uwan shi ya iso daga misau

tuni kuwa sukayi magana ta dattawa aka aje magana duk da basu zo hannu na dukan cinya ba sai da suka ruko wani abu irin na Al adar aure suke taho da shi

daddy yace kar su wahalar da kansu ba zai karbi komai na su ba Sai ma shine yayi musu hidima yayin komawa wacce ta basu mamaki don ya cika su da sha tara ta alheri

sukayi sallama suka wuce Niger

Kaisar ya fito ne yaga yaya halilu ya taho da sauri yana gaishe shi.

“Kaisar kana lafiya? Ya karatu an gama ko? To Allah yayiwa rayuwar ka albarka Allah ya jikan magabatan ka da rahama.

Ya amsa da ameen ameen baffa na gode

Alabo yana tsaye shi da fati Yana nuna mata yadda aka gyara motar nadiya wacce tayi kyau matuka gaya.

Kaisar ya fito suna gsisawa da alabo Fati na Fadin

“Yaya kaisar ga yaya na  ku gaisa

duka sake gaisawa Yana mishi sannu da zuwa

Nan da nan kaisar da alabo sukayi sabo suna ta fira tamkar sun dade da sanin juna har Yaya halilu ya fito da shirin komawa misau fati ta cuko leda da kaysyyaki ta bawa baffa tace a kaiwa innar ta tana nan tafe in sha Allah.

Da haka sukayi bankwana har alabo da kaisar suna misayar lambar waya

suna tsaye har motar alabo ta fice shima baffa ya shiga tashi ya bi bayan alabo suka dauki hanyar misau

Kaisar ya juyo yana kallon Fati yana fadin

“Gaskiya na yaba da kaunar alabo a kan ki fati anya kuwa babu soyayyar ki  a zuciyar yayan naki? na hango wani abu a idanun shi fa.

A firgice fati ta juyo tana fadin

“Astagfurullah yaya kaisar Allah ya yafe maka. yaya na ne fa? .

“To fati yaya nawa ya zama miji? .

“Haba dai sai kace garin da babu masu duban gabas? Uwa daya muke dashi uba daya. Ni fa ba nan ne gidan mu ba ga baffan mu can wanda kuka gaisa garin mu yana kauyen misau. da Daddy da shi baffan mu tagwaye ne wanda aka haifa ciki daya kuma duka sunan su iri daya ne duk Ibrahim ibrahim sai dai lakabi Khalil da iro .

“To banda haka kam da nace alabo yana son ki soyayya kuma irin mai zafin nan wacce take wahalar da mai yinta.

“Shiyasa ai nace Allah ya yafe maka cikin mu daya kuma sunzo ne maganar auren Nadiya.

wani irin tsini ya soki zuciyar kaisar ya dube ta yana fadin

“Aure kika ce fati?

ta dube shi tana murmushi

“Eh ai naji daddy yana cewa maccid’o ne zai aure ta iyayen shi ne ma suka zo jiya wanda aka sauke a wancan sashin.

A take idanun kaisar suka kada tamkar wanda ya watsa wani abu

fati taga irin tashin hankalin da ya shiga sai taji bata ji dadi ba kuma don son kanta ba zata so abinda zai cutar da shi ba don haka ta dube shi.

“Yaya kaisar na san kana son nadiya kuma dukkan ayyukan ka sun nuna hakan har gabban ka ma sun nuna to a yanzu ne nake da taimakon baka tunda ina da wannan damar .

“Fati me yasa kin san hakan kuma kika barni a duhu ? yanzu sai mutane sun taru an daura auren Nadiya sai kice min auren ta ne aka shafa? don Allah idan har kina da yadda zakiyi ki taimaka min to kiyi nima ai dole na samu daddy ba xan iya bari ya raba Ni da ita ba ko da kuwa wanda zai bata ya wuce maccid’o.

“To haka ya kamata nima bari na shiga ciki yanzu na samu daddy muyi magana zan nuna mishi kana son nadiya Kai yafi cancantar ya bawa ba maccid’o ba.

“Nagode miki fati Allah ya gode miki ya cika miki burin ki na alheri.

A zuciyar ta ce buri na Kaisar kaine amma dole na mayar da hakan MAFARKI domin kuwa na rufe babin karatun da zuciya ta take biya min domin kuwa ba zan iya bita da tarjamar sa ba.

ta amsa da ameen ta wuce don jin wani irin tausayin kanta da ya kamata . amma sai ta bawa kanta tabbacci da hakikar ba kowane sone samu ba .

Daddy ya dubi Fati yana fadin

“Yaya ne Fati ?

ta zauna tana fadin

“Daddy don Allah na roke ka wata alfarma mana?.

“Nayi miki alkawarin yi miki ita matukar ina da ita.

“Daddy kana shirin yiwa yaya nadiya aure amma daddy mijin da kake shirin bata sam babu dacewa . Ina ganin da ka sauya mata da wani duniya ma ba zata zarge ka ba amma in aka ga ka bata mai tsaron kofar gidan su daddy kowa zai ta neman dalili .

“Ba zaki gane ba a nan dai fati abu daya zan fada miki shine bana tsoron tuhumar Al umma ko kunji kunjin su har ma da zagin su abinda kawai na sani shine maccid’o shine daidai nadiya kuma Niger din da zai kaita naso ma ace ta Kara nisan gari arlik ko kamaru ko chadi ta yadda zata gane bata da kowa a kusa bare wulakancin ta yayi mata tssiri.

“To Daddy amma ka san yaya kaisar da soyayyar nadiya ya shigo gidan nan? ya fada min yana son ta fiye da a kirga ya kuma tabbatar min da haka . a yanzu ma da ya samu labarin auren ta wallahi daddy baka ga halin da ya shiga ba shine naga bari na zo na same ka wata kil ka fahimce ni don Allah ka sauya maccid’o da Kaisar .

“Fati auren nadiya ba na mijin da ya mutu a soyayyar ta bane ina so ki fahimci wannan sai mijin da yake jajirtacce kuma wanda take shakka. amma kaisar da tuni na gane yana son ta in na bashi auren ta cutar shi nayi ba zai iya control din ta ba don haka ba wai naki yi miki alfarmar da kika nema ba fati sai don ki sani a yanzu nafi son nayi nesa da nadiya inda bata da kowa ta haka ne zata gane rayuwa ta kuma gane babu wanda take takama da su a kusa sai kiga idan Allah yaso ta nutsu kaisar kuma yaje ya nemo mace ko yar gidan waye zan nema mishi auren ta ki tabbatar mishi da hakan fati ni banda ma ance kina da likitan nan usi ai da da ke na hada kaisar don nafi ganin dacewar ku fiye da nadiya shi nutsattse kema nutsattsiya .

tayi wani murmushi mai shirin saka ta kuka ina ma hakan daddy ya zartas ? Ina ma ace fatan daddy ta tabbata?.

tayi  saurin cewa

“Daddy nifa ba wani son usin nan nake ba baffa ne yake ta son abun don dai ba zanyi mishi gardama bane amma ni bana son usin nan yana da jiji da kai wai shi likita.

“to ai dole ne Kuma kiyiwa yaya halilu biyayya duk da na san ba zai baki mijin da ba kya so ba sai muyi ADDU A Allah ya kawo nagari

ta amsa da ameen tana shirin ficewa daddy ya Kira ta ta dawo

“Ina kaisar din yake?

ya tambaye ta tace Yana kofar shi

“To bari na same shi da kaina sai muyi magana jeki abinki .

Daddy ya mike ya fice zuwa kofar kaisar.

Zarya kawai Kaisar yake tsakanin falon shi da uwar dakan. babu abunda kunnuwan sa suke zuk’o masa sai amon sautin muryar fati da take sanar dashi tsayar da ranar auren Nadiya.

zufa sai tsiyaya take a fuskar sa zuwa wuyan sa hankalin sa ya tafi wurin dawo da abinda yake shirin kubucewa  har bai iya jin shigowar daddy ba

Jin hannun mutum a kafadar sa yasa ya dago kanshi da sauri sukayi ido hudu da daddy.

“Sannu da kokari kaisar. lallai zuciyar ka ta tafi da yawa Ina tausayawa Kai kanka da zuciyar ka don sau tari abinda kake so shi yake baka wahala.

“Kayi hakuri Daddy laifin ba nawa bane na zuciya ta ne . Al amarin ba a hannu na yake ba naso na kautar da shi amma na kasa.

“Kayi kokari ka kautar dashi kaisar don shine zaman ka lafiya.

“to daddy duk yadda kace haka zanyi.

Daddy ya kama hannun kaisar suka zauna yana duban shi da tausaya mishi don ya san ya ake ji akan so .

“Kaisar idan har Nadiya tana da daraja dubu a gareni to kai wallahi milyon ke gare ka. nafi son ka sau dubu akan Nadiya . Ina da manufa ta hada auren ta da maccid’o na kuma dade da fahimtar kana son ta kaisar wmma ni na san ba kowane mijin yarinyar nan ba musamman wanda ta raina wanda ya furta mata kalmar so to tafiyar su ba zata zama daya shiyasa kaga na yanke wannan hukuncin Ina fatan ka fahimce ni kaisar? nayi maka alkawarin kowace yarinya kake so ka nemo ta zan nema maka auren ta .

“An gama daddy wallahi na fahimce ka kuma idan nace ka hana maccid’o auren nadiya ni ka bani ai na zama azzalumi don haka Ina musu fatan alheri daddy.

“Alhamdulillahi kaisar Allah yayi maka zabin mata ta gari ni da ka yarda ma ai da na nema maka wacce zata dace dakai amma kuma na san zuciyar kauna tana da wahalar manta abinda take so bari na barka ka bawa zuciyar ka hutu in yaso mu barwa Allah komai

A ranar kam kaisar da zazzanbi ya kwana wanda shock ya haddasa mishi

Washe gari kuma fati da nadiya zasu shiga kasuwa inda a dole daddy ya hana nadiya tuki sai dai sarkin gida ya kaita duk inda zataje. fitar ma ba kowace take yi ba sai wacce ta zama dole

Fati ta soma kwalawa sarkin gida kira amma shiru bai amsa ba ta nufi dakin nashi sai ta Tara’s da dakin a rufe dole ta juyo ta koma tana fadawa mama sarkin gida baya nan ko na bawa anty Nadiya key din ta jamu ?.

“Ban aike ki ba daddy ya kafa doka ni na karya? Sai dai ku hakura da tafiyar har sarkin gidan ya dawo koma ki fada mata ku dawo sai ya dawo .

“Jiki a sanyaye fati ta fita tana cewa nadiya mama tace su koma sai sarkin gida ya dawo.

<< Azurfa Da Zinari 14Azurfa Da Zinari 16 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×