“Mama don Allah kiyiwa anty Nadiya magana ta daina wulakanta mutane . haka fa ta da muka fita dazu ta tofawa wani saurayi yawun bakin ta a fuskar sa daga kawai yace yana son ta Wai ita bata ma tsoron duniya da rayuwa ne? Komai nata sai ta saka gadara da izza?
“Subhallahi yaushe tayi hakan Fati?
“Ai Mama haka take wallahi duk saurayin da zai ce Yana son ta sai ta karta mishi rashin mutunci ga wulakanci ga gadarar ita yar gidan Mai kudi ce tafi karfin talaka . ni kuma idan na fada mata gaskiya sai ta rufe ni da masifa har ranar nan sai da tayi min gori wai Nima na baro gidan mu nazo gidan su cin arziki tunda gidan mu babu jar miya shine zan zo gidan su na tare kuma nace zan fada mata maganar banza ta yarda?
Mama ta kame baki cike da mamakin Nadiya na son nuna Uban ta mai kudi ne.
Nadiya da tazo shigowa taji Fati tana fadawa mama abinda tayi sai ta tsaya bakin kofar tana Jin abinda Fati take fadawa mama abinda tayiwa Boss har ta kare kafin ta shigo tana fadin.
“Sannu anty munafuka sai akayi Yaya kuma bayan na tofa mishi yawun? Wai ke Nan haka da ke kema kin iya munafunci Fati? To naji karya nayi miki ne ? ba gidan ku kika baro kika zo nan don ki rike cin arziki ba? Ai in gori na yayi miki ciwo sai ki koma naku gidan. Kuma da kike cewa na wulankata wannan dan iskan Ni zai kalla da wannan motar tashi irin ta yan kwana kwana yace yana sona? sai karyar banza bashi da ko sisi aka fada mishi nayi kama da matar talaka irin shi? ai wallahi nafi karfin talaka irin shi.
Mama tana rike da baki tana kallon Nadiya da take ta tijara.
“Ke ! saurara mini kinji ko? wai ke a me kike daukar kanki ne? kudin da Uban ki yake da su ne yasa kike wulakanci? baki da tarihin dan karuna halan? to kibi duniya a sannu jirgin sama ma da yayi gudu bai kure sararin samaniya ba ya gaji ne ya dawo gefen duniyar ya dakata bare ke kayan banza . duk yadda nake fada miki ki bi komai a sannu tamkar kira ne a kunnen kurma to na gaji da fada miki ki gyara halin ki . bana fatan duniya ta fada miki Nadiya amma taurin Kai da taurin zuciya sun haka ki don haka Allah ya baki sa a. Nadiya ta dubi Fati tana fadin, “Zaki San kinyi min wannan munafuncin zaki shigo ki same ni shegiya kwadayayya in ba gudun gidan ku kike ba ki koma can Mana ku yi ta sharbar miyar kuka da tuwon dawa shegu matsiyata Allah ma kadai yasan mugun halin ku shiyasa ya barku da talaucin ku.
Tatsss!!! Mama ta wanke ta da mari tana fadin
“Ba zaki daina wannan muguwar dabi ar taki ba ko ? to Allah yasa naji kin tab’a ta wallahi zan sa a koya Miki hankali tunda kullum rashin mutuncin ki kara gaba yake. Ta wuce fauu tana dafe da kumatu yayin da Fati take jin Mama ta jawo mata wani balakin musamman akan marin nan ai shiga uku ta same ta.
“Mama da baki mare ta b wallahi sai ta rama marin Nan wuri na.
“Da ta tab’aki ki fada min ni zan sa a rama Miki.
“Zan koma gida Mama don Allah kiyi hakuri.
“Saboda abinda ta fada miki ne zaki tafi? Cewar Mama wacce take duban Fati.
“A a Mama na san dai Inna na can tana kewa ta shine zan koma amma in an kwana biyu zan dawo.
“To sai ki bari sai satin gaba amma ba zaki koma ba in kuma tace miki wani abu ki fada min. Jikin Fati a mace ta amsa Amma ta San TANA KASA TANA DABO tsakanin ta da Nadiya musamman akan Marin Nan sai ta sauke mata kwandon tijara tare da gore gore. Kiran sallar magariba ne yasa Fati mikewa zuwa daki don tayi sallar magaruba inda ta iske Nadiya gaban mirror ta tsuke da kayan da suka bayyanar da surar jikin ta musamman ma kirjin ta da kugun ta ta zuba kwalliya ta neman fitina.
“Yauwa bakar munafuka ga kayan ki maza ki debe su ki bar gidan nan in dai ba gidan Uban ki bane . kar ki yarda wallahi na dawo gidan nan na iske ki kuma Allah yasa Mama ta neme ni ki fada mata inda na tafi ba kinji abinda mukayi da su lubabatu ba ? to ki fada din kiga abinda zai faru. shegiya makwadaiciya Nan gidan Uba na ne dole a barni nayi yadda nake so. Ta zurma Uban hijabin ta har kasa kafin ta suri wayar ta da ake ta kiran ta ta fice da sauri ta bar Fati da binta da kallo tana tuna inda taji suna fadin zasu je ita da kawayen ta wato together party. Da sauri ta shige motar ta mai kololuwar daraja ta fizgeta da karfi ta fice daga gidan ta nufi gold and silver Park.
*****
Tero ya tako motar da karfi ya na tuki yana cizon leben sa Yana son ganin yarinyar nan tazo hannu
Ya dauki wayar shi dake gaban dash board din motar Yana kiran wayar Killin Yana fadin
“Killin kana ina ? don Allah ina son ganin ka ina zan same ka? Ok na manta wallahi da together nan shaf kuma na san za a samu new baby masu zafi a wurin nan wallahi na manta shaff . dama wani aiki ne ya taso na gaggawa amma tunda baka Nan bari mu barwa gobe kawai nima gara nayi attending together nan sai zuwa goben zan neme ka Killin. Ya katse kiran yana kiran wayar Boss.
Yana kwance akan sofa yayin da Tsagera yake zane Yana chatting.
Yaja wayar da sauri Yana ganin kiran Tero ya dauka Yana fadin “Yaya aka yi ne friend an kama?
“Ba a Kama ba Boss na Kira Killin ne don ya Kama min aikin shine ya fada min yana gold and silver wirin together Nan sai na tuna zamuyi attending shine na ce ya bari zuwa gobe zan Kira shi amma yanzu ku shirya ina tsagera yana nan? sai na dawo muyi attending don na san dole a Tara baby girl masu zafi Wanda zasu yi fire.
“Kai na manta wallahi dawo kawai mu tafi Tero ai mami tayi min albishir da ko yar uban waye a garin nan in dai ina son ta zata sama min ita ko da kuwa zasuyiwa yar su kudin tsiya ne.
A guje Tero ya juyo motar ya tako ta a dubu ya iso tuni kuwa suka dauko hanya zuwa gold and silver park cikin shigar su ta manyan yara da kuma babbar motar su ta manyan yara.
*****
Motar Nadiya ta paka kusan lokaci daya da motar lubabatu kafin safina da keena suka karaso suma cikin motocin su na manyan yara amma duk motar Nadiya ta zarce tasu nesa ba kusa ba.
Ta fito da zurmemen hijabin ta inda keena ta kyalkyale da dariya tana fadin
“Meye haka matar malam? together da sallaya sai kace dai masu zuwa gidan makoki?
da sauri Nadiya ta cire hijabin ta wulla cikin motar ta soma taku bisa takalmin ta high hill na kamfanin channel inda komai na surar ta ya fito masha Allah su keena ma sai suka bita da kallo suna Jin wani Abu a kasan zukatan su.
carab idon shi ya hasko mishi ita ta kumayi maukar tafiya da imanin shi
King ya dube shi don ya nuna mishi halittar da ya hango sai kawai yaga idon kaisar din akan ta ya shagala da kallon ta tana taku cike da izza da son nuna matancin ta inda duk mazan wurin idon su ya koma kan Nadiya don sai ta zamo zara cikin taurari.
“Masha Allah tabarakallahu ahasanul khalikeen king Allah ya sani ba zan cuci kaina ba ina son yarinyar nan ban tab’a Jin so at first sight ba sai a yau .
King ya sheke da dariya yana fadin
“Bauci fa kazo malm ai kasan kawawan bauci ba wasa ba.
“Na yarda King daga zuwa na ka jawo Ni rakiya kuma nayi tsuntuwar soyayya?
“Muje ka tashi abar ka mutumi na ai da zafi zafi akan daki karfe.
da sauri suka fito a motar inda wayar kaisar ta dauki tsuwwa ya jawo ta da sauri yana ganin mai kiran ya dauka Yana rusunaww kamar yana gaban shi Yana gaishi.
“Kaisar ka sauka bauci kuwa?
aka tambaye shi daga can barin.
“Na sauka Daddy Amma kuma aboki na ya ja Ni rakiya Amma in sha Allah ba zamu jima ba zan karaso.
“To alhamdulillahi tunda ka sauka lafiya in kun kammala sai kace abokin naka ya kawo ka gidan don in dai dan nan cikin garin bauci ne to ya san gida na ga mamar ka ta shirya maka kayan tarba tana ta cewa ko baka sauka ba.
“In sha sha Allah Daddy muna Nan isowa a bawa Mama hakuri gani Nan dab.
“To sai ka iso kaisar ga alama babu gajiya a tare da Kai.
“Wallahi akwai ta Daddy sai dai karfin Hali kawai.
suka gama wayar king yana fadin
“Gaskiya nayi mamakin da kace min gidan kudi kazo dama kuna da relations da su ne?
“Kai muje naga yarinyar nan my guy duk hankali na ya koma gareta wallahi duk da ina cike da dokin zuwa na bauci amma ganin wannan furen yasa na manta da komai.
King ya yi dariya suka nufi inda su Nadiya suke zaune su hudu ita da safina da keena da lubabatu.
hankalin Nadiya Yana can tana kallon wasu yan mata da suka shigo cikin motocin su na manyan yara wanda suka dame nata haka ma kayan su da kwalliyar su suka zarce nata duk sai taji ta raina kanta.
su king sukayi musu sallama keena da take kallon kaisar ta amsa yayin da safina da lubabatu suke musu kallon su waye ku?
“Sannun ku da hutawa zamu iya zama bamu takura muku ba?
Keena ta amsa da fadin
“Babu komai bismillah ta fada tana kallon kaisar duk da a ranta fadi take gaye har gaye sai dai gajerta tayi mishi cikas . don kaisar kam babu tsayi kuma bai cika girma ba amma kuma da kadan ya fi yaro dan shekara sha biyar shi kan shi ya tsani rashin tsayin nan nashi. amma bayan hakan bashi da makusa kyakkyawa ne na karshe .
Suka zauna keena na kallon kaisar inda shi kuma king yake kallon safina.
“Sannun ku fa ya kuke ya gari ya Jin dadi?
cewar kaisar cikin muryar shi wacce tasa nadiya juyowa daga kallon yan matan da take sai taga wani mutum marar tsayi da kuma wani mai suma .
Tayi maza ta tsuke fuska inda Kaiser ya daga mata gira ta kalle shi sosai sai kuma ta kyalkyale da dariya amma bata ce komai don haka bai San abinda take wa dariya ba ita kuma gajertar shi takewa dariya.
“Don Allah ina son ganin kawar ku minti biyu in babu damuwa?
Keena da tayi fatan ace ita yake son gani sai taga Yana nuna nadiya. Ta mike tana fadin
“Babu damuwa bismillah
Nadiya ta bi keena da harara kan kace me? sun mike sun wuce sun barta a gun kaisar kuma ya zauna kusa da ita Yana gaishe ta.
“Sunana kaisar Al Mustafa tunda na shigo nan nagan ki naji ina son ki duk da ni ban tab’a soyayya ba amma naji ina son ki fatan ban takura Miki ba?.
ta auna mishi wani shegen kallo tun daga saman shi har kasan shi kafin tace.
“Kai kasan kowacece ni da kake kallo na kace min kana sona? nayi maka kama da matar talaka irin ka? wai Kai a tsaye kake ma ko a zaune don na ganka dab da kasa ? Waye Uban ka a garin nan kuma waye shi me ya mallaka? .
Kaisar yayi murmushi yana fadin
“Ubana Allah ya yi mishi rasuwa da jimaww.
“Kuma a haka kake cewa kana sona? To kar ka kuma duba na ka kawo min maganar banza don ni In ba baban ka zaka nemawa aure na ba kar ka kuma kallo na don zan saka a daure min Kai a gidan yari . sakarai da Kai guntun banza ko a wace tsiya kake Kai da duka dukan ka baka wuce kafada ta ba kace kana sona ? In aure ka nace na auri namiji ko na auri mace yar uwa ta mace? Ni bana zaton ma an yaye ka daga nonon uwar ka in ko kuma bakwaini.
wata irin kunya ta kama kinga ya kasa cewa komai ya kuma kasa motsa.
Kaisar yayi murmushi yana fadin
“Kar ki dubi hakan masoyiya ta ina mai tabbatar miki da ba kowane namiji ne yafi ni ba wallahi zan zamo miki duk kalar mijin da kike so .
Ta juyo a fussce Jin abinda yake cewa sai kawai tacire hannu ta tsinke kaisar da mari saboda takaicin da maganar tashi ta bata.
motar su Boss tana shigowa Park din daidai lokacin da Nadiya ta gauraww kaisar mari.