Skip to content
Part 20 of 80 in the Series Azurfa Da Zinari by Hadiza Gidan Iko

Yayi maza yaja blanket yana Rufe mishi tsiraic yana kuka yana duban Mustafa yana fadin

“Waye ya aikata min wannan ta addancin Mustafa? waye su waye? Ya mike da sauri  yana kiran motar asibiti wacce tazo daidai da zuwan haj Laila wacce treo ya kira itama yana kuka yake fada Mata Hameed Hameed.

Jikin ta yana kyarma take duban motar asibitin da ta iso suka shiga tare inda idon ta ya hango mata dan nata kwance cikin jini ga wuka soke a cikin shi.

Da wani irin amo take kururuwa tana kuka duk da ta cika dakin da ihun kukan ta tana fadin waye ya yiwa abdulhameed din haka?

babu wanda ya iya bata amsa daga distinguish mukhtar biro har zuwa Mustafa Tero bare kuma su keso

Jami an lafiyar da suka soma aikin su na auna Hameed wanda tuni rai ya yi halin sa suka soma aunawa duk da sun fahimci babu ruhi a tare da shi.

“Ya zaku tsaya wani aune aune mutum yana cikin wannan halin ba don ku tafi da shi asibiti na kira ku ba in ya mutu fa sai nayi shari a da ku.

cewar distinguish mukhtar Biro

Likita ya dago yana bashi hakuri yana fadin

“Ayi hakuri ranka ya dade aai anyi jinkirin kawo shi asubiti tun kafin Al amarin yayi tsanani amma yanzu kam sai dai kuyi hakuri amma abdulhameed ya cika babu numfashi a tare da shi.

Wani uban ihu da haj Laila ta kwantsama shi ya gigita likitan Mam sanar da mutuwar ta kuma yi RAM da wuyan rigar shi ta rike tana jijjigawa tana fadin.

“Ku kuka kashe shi wallahi kuma wallahi ba zan yarda ba kuna aikin me ya mutu ? ku kashe min yaro? nima kuwa zan kashe ku wallahi wallahi ba zan barku ba ba zan yarda.

likitan ya so ya kwace kanshi amma ya kasa yayin da haj Laila kuma take ta sambatu har dai suka gane ba ta cikin hankalin ta kidima ce akan jin mutuwar Hameed din.

Da kyar likita ya samu ya kwaci kanshi dole kuma suka fice daga gidan suna wa juna barka.

Kan kace me?

Sai ga jami an bunciken sirri sun iso gidan suna ta daukar hotuna tun daga farfajiyar gidan da sawayen kafafun masu dauke da jinin har kan gawar Hameed da yake kwance reras .

kukan da haj Laila ke garza ne tare da Tero tana fadin

“Don Allah ka tashi abdulhameed kar ka mutu ka barni ka tashi abdulhameed please and please.

“Mustafa fada min me ya faru da abdulhameed? waye ya kashe mini shi ?.

cewar distinguish mukhtar Biro wanda ya ritsa Tero da  jajayen idanun shi da suke cike da tashin hankali

Tero ya soma share hawayen shi yana fadin

“Daddy wata yarinya ce .

Da sauri distinguish ya mike yana tuna yarinyar da ya gani ta fice daga gidan a guje kuma jikin ta faca face da jini idan ya fahimta ma tun lokacin da yaga fitar yarinyar abdulhameed yake a cikin wannan halin?.

“Wacece wannan yarinyar Mustafa? meye alakarta da shi ? wallahi tallahi na rantse da Wanda raina yake a hannun sa sai ta mutu fiye da irin mutuwar da abdulhameed yayi fada min ko yar gidan waye.

“Daddy uban ta ba kowa bane Yar gidan iro GIDAN KUDI ce Kuma dama ta sha alwashin kashe shi .

“Iro GIDAN KUDI? Kasan gidan su ne? ba ita ba har uwar ta da uban ta ta jawo musu mutuwa

Jami an bunciken sirri suka gama dauke dauken hotunan su suka bukaci da akai abdulhameed mutuware har zuwa lokacin da zasu gama bunciken su do gano ta yadda akayi kisan da kuma wanda yayi kisan .

Sai dai haj Laila ta ce bata yarda a fita da abdulhameed ba a kai shi cikin gawarwaki bai mutu ba suje zai farko.

Duk juyin duniya tace ba za a raba ta da danta ba bai mutu ba dole jami an suka fice suna mamakin wannan soyayya da iyayen mamacin suke mishi hat da ya mutu ma amma suna dakon dawowar shi duniya . anya kuww tunda fiyayyen halitta ANNABI MUHD sallalahu alaihi wassalam ya tafi bai kuma dawo ba akwai wanda zai tafi ya dawo? to bari mu gani ko haj laila zata tako wannan sa ar.

A guje Nadiya ta fice daga gidan shakatawar da Tero ya kawo ta ta gamu da boss wanda ya soma keta mata haddi

Da wani irin matsiyacin tashin hankali take tafe musamman jinin da ya wanke fuskar ta na Boss. babu abinda ke amsa kuwwa a kunnuwan ta sai karar da abdulhameed ya saki lokacin da take burma mishi wukar

Duk da yadda take jin tamkar ana yankan ta da reza a gaban ta saboda shigar ta da Boss yayi amma bata ji zata tsaya langwai ba akan hakan illa matsera da take nema don ta tabbatar da idan aka biyo bayan ta Akan ta adin da tayi ko da ba a rama abinda tayi ba to zata ji jiki don haka take son ficewa daga layin ta nemo hanyar gidan su suka da Bata san ko a wane yankin take ba

Kanta babu dan kwali bare takalmi bare ayi maganar mayafi duk da dama ba wani na kirki take sakawa ba duk ta yaso su a gidan da aka sato ta har aka keta mata haddi wanda duka ba su take ji ba sai abinda zai biyo bayan ta adin da tayi don ita da kanta ta soma laluben waye boss waye uban sa?

tamkar mai gudun wuce sa a haka take auna uban gudu sai dai abinda bata sani ba shine gara tsayawa akan gudun neman tsirar da take domin kuwa unguwar dinke take ta jami an tsaro na mopal da sibil difens saboda manyan mutanen da suke cikin ta da kuma kiyaye mai shiga da mai fita da kiyaye lafiyar ya’yan su shiyasa ma har get ke ga layin na gidan distinguish mukhtar Biro domin kuwa ire iren shi ne masu rike da madafun iko suke da muhallai a yankin na makera G R A dan da office din gwamna a unguwa mafi daraja shiyasa aka saka tsaro matuka gaya kuma babu ta inda za a fita sai ta wannan layin koma ta Ina aka so fita kasancewar get get din sun kai sha biyu ko ta Ina akwai masu tsaro . get din ba kofa bace sai wani dogon karfe da aka ratsa tsakiyar titin da shi yayi crossing ta yadda babu damar wucewa sai an daga maka musamman ga mai abin hawa mota ko babur haka ma mai tafiya a k’asa sai yabi ta gefen inda ma su tsaron ke zaman dako don haka tun a nesa nadiya ta hango kakin mopal wanda yasa ta ja ta tsaya don ta san sai ya tsaya tambayar ta ba asin jinin da yake jikin ta wanda bata bukatar dogon bayani a yanzu so kawai take ta ganta a gida su .

ta juya da sauri ya yanki wani titin duk da bata san inda zai kaita ba don kowane da inda ya dosa.

bata san Ina zai kaita ba amma taji gara tabi shi ko don ta tsira da rai.

tana cikin gudun taji tsuwwar motar ta biyo bayan ta abinda da ya kara firgita ta.

Kafin ta san abinyi motar ta Sha gaban ta inda taga jami an suna sauke gilashi suna mata kallon baki da gaskiya ne ?

taja tayi turus tana makyarkyata domin kuwa ta gama nuna kanta a marar gaskiya.

Suka fito daga motar su biyar suna zuba mata idanu kowane dauke da bindinga tsoro mai tsanani ya kuma rufe ta .

“Wacece ke? me ye a jikin ki? daga ina kike? Me Kuma kika aikata da har kike tsoron fita kina sauya hanya? Ina kallon ki tun lokacin da kika taho a guje kina zuwa get kika ga mai tsaron kofar kuma kika juya hakan ne ya nuna min baki da gaskiya.

“Dubi jikin ta jini ne fa?

duk sai suka mayar da hankalin su akan jinin da ya soma bushewa a fuskar ta da jikin kayan ta.

“Jinin meye a jikin ki?

wani ya jefa mata tambayar.

Cikin rawar murya da in ina take magana.

“Biyo ni sukayi.

“Su waye suka biyo ki? suka tambaye ta da hasashen gaskiyar ta biyo ta din akayi.

“Ban san su ba .

“Wannan jinin na jikin ki na meye?

“ban san ko na meye ba.

Suka kalli juna kafin daya daga cikin su yace

“Shigo mota muje ki nuna mana inda aka kaiki don akwai alamun tambayoyi da yawa akan ki da wanda suka kawo ki

Jikin ta yana ciri ta shiga motar suka dauki hanyar shiga cikin makera G R A din suna tambayar ta zata gane inda aka kawo ta da wanda suka kawo ta?

tace ba zata iya gane inda aka kaita ba Amma zata iya gane mutanen biyu.

Haka sukayi ta zagaye da ita suna tambayar ta amma tana cewa ba ta gane ba.

Suna ta zaga makera da ita inda kuma jami an lafiyar da suka iso ne suka sanar da masu tsaron get din can sashin cewa anyi kisa a cikin makera G R A an kashe dan gidan gidan distinguish mukhtar Biro a yanzu Kuma ba a san wanda yayi kisan ba don haka akwai yuwuwar rufe makera G R A don gudanar da bincike.

Kan kace me? aka bada umurnin rufe get get din babu fita ga na ciki sai dai mai shigowa zai iya shigowa

Lokacin da aka bada wannan sanarwar wanda suke tare da Nadiya basu da labari shiyasa nadiya bata fada tarkon ba.

Sun gaji da zaga get get har dai suka gane Nadiya wasu bata garin ne suka so cutar da ita don haka suka so sallamar ta inda suka fito a kofar get din da suke tsaron suka sauke ta suna fadin ta yi maza ta koma gida

ta fice a motar da sauri tana godiya

daya daga cikin su yana kallon ta ya kuma kallo wanda ya bata umurnin tafiya yana fadin

“Ban fa yarda da amsoshin yarinyar nan ba ya’u don ni dai gaskiya ban yarda da ita ba dubi jinin jikin ta fa.

Musa da yake bakin kofar ya juyo yana fadin

“Kai ? wai wata ce kuke tuhuma ? ance fa anyi kisa a G R A din nan yanzu har an hana fita daga ciki me ya sa kuka barta baku tuhume ta ba?.

Da sauri ya u ya dubi musa yan fadin

“kai da gaske kake Musa?.

Jiniyar masu bunciken sirri da ta tunkaro kofar get din inda suka bude motar ta shiga a guje ta yanki kwana zuwa gidan distinguish mukhtar Biro ita ce ta sa musa fadin

“To ga amsar ka nan amma lallai wacce kuka saki ko bata da hannu a cikin kisan to ta san wanda yayi shi.

A guje ya’u ya koma mota yana fadin

“Muje sani mu bi bayan yarinyar nan na tabbatar da batayi nisa ba sai yanzu nima naji a raina ta san komai munafuka tace bata san komai ba.

A guje suka shiga motar suka fice tamkar masu shirin zuwa sama ta bakwai.

Nadiya da ta samu ta kunto daga mopal din can sai ta soma auna uban gudu tana son ganin tayi nisa da yankin amma yanayin unguwar tsit ko mashin bata gani ba bare napep da take fatan samu.

tana cikin gudun ne wanda ta kusa shanye dogon titin taji karar motar ta juyo inda taga wata katuwar mota ce ta danno sai ta soma tsayar da motar don ta nemi taimakon fidda ita daga yankin nan.

Motar ta tsaya tana sauke gilashin ta wata mata ta leko tana fadin

“lafiya?.

“Don Allah haj ko zaki taimaka mini ki fidda ni daga an .n

“Ayya yarinya ai ni nazo gida ne Amma karbi dari biyar ki samu napep ya fidda ke.

Bata tsaya karbar kudin ba ta juya da sauri ta wuce inda kuma motar su ya’u mopal ta soma hango nadiya wacce ta tare mota tana neman lift.

“Sani kamar yarinyar nan ko?.

“Itace in ka cire kamar.

ya kara taka motar yana son isko nadiya wacce ta tsayar da napep wanda ya fito daga yamma inda ta waigo kuma taga kamar motar nan da ta rike ta tana tahowa don haka da sauri ta shige napep tana fada mishi inda zai kai ta ya kwasa a guje.

ta cikin gilashin napep din take hango motar tana biye da su a baya.

Wani irin matsiyacin tashin hankali ya mamaye ta asirin ta kam ya gama tonuwa  tunda har aka gano ta ana biyo ta

“Yi sauri don Allah ka bacewa motar nan dake biyo mu yi maza ka shige cikin go slow.

Ai kuwa tuni dan napep din ya kutsa cikin tarin babura da motoci har da napep ya bace bat kafin ya dauki hanyar gidan su nadiya ya kuma kawo ta har kofar gidan su inda kuma murnar ta ta koma ciki domin kuwa tana zuwa kofar gidan su motar su ya ‘u na karyo kwana ta tunkaro kofar gidan tamkar in tazo zatayi cikin gidan.

Aguje nadiya ta kwasa da gudu ta danna a cikin gidan har ta na banke su maccid’o ta wuce  a rude  da son ta bacewa motar su ya’u .

ta wuce a guje inda maccid’o ya bita da kallo ta fada kofar sai kawai ta danna sashin kaisar ta kuma nufi can cikin toilet ta maido kyauren ta datse

Kaisar yana zaune yana karatu yaga giccin mutum sai da yaga fuskar nadiya lokacin da take maido kyauren kafin ya ankara itace amma abinda ya bashi mamaki ina taurin zuciyar ta da har ake biyo ta a guje haka har tana yin masauki a bandaki?

<< Azurfa Da Zinari 19Azurfa Da Zinari 21 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×