Skip to content
Part 20 of 23 in the Series Azurfa Da Zinari by Hadiza Gidan Iko

Kan kace me? labari ya karade makera G R A cewa an kama wata yarinya wacce take bakuwar fuska a cikin makera G R A din jikin ta faca face da jini kayan ta ma haka kuma a firgice kanta babu ko dan kwali bare mayafi alamar da take alamta bata da gaskiya.

Haj Laila da distinguish mukhtar biro da suke zaune tashe da gawar abdulhameed suna kuka inda haj Laila ta mika hannu ta zare mishi wukar da take soke a gefen cikin shi tana kara rusa kuka.

tuni makera G R A ta sanar da kisan kan da akayi kan kace me? sai ga motocin jami ai kala kala suna dannowa zuwa cikin makera suna fakawa a kofar gidan distinguish mukhtar Biro wanda tuni duniya ta shaida dan sa ne kwallid kwal aka kashe

tuni jiniya da kugin motocin hikimomin tsaro suka soma jera layin gwano a kofar gidan kasancewar a wannan zamanin mai kudi da madafun iko shine shafaffe da mai  kuma kafin ma yayi kira an amsa mishi shiyasa distinguish mukhtar Biro Bai kira kowa ba amma har ya tara gayya

Sai karar jiniyar motocin hikimomin tsaro kake ji tun daga yan sanda zuwa Soji da mopal da kowane irin kaki sun gayyato kansu kafin a kira su saboda son a san dasu su kuma cika fada

ganin abin na gaske ne sani da yake sanar da su Musa yarinyar da suka sauke ko mai laifi ce shine ya kira su kuma yana fada musu makera fa ta cika ta batse da jami an force abin har ba masaka tsinke  Yaya sun samu gano yarinyar? ya fada mishi sun ganta har sun biyo bayan ta har zuwa gidan da ta shiga yanzu haka ma  suna kofar gidan da ta shiga zasu shiga su fito da ita ko a fito musu da ita.

tuni kuwa sanin ya kaiwa distinguish rahoton gama wacce tayi aika aikar wacce aka fada mishi a yanzu.

Kan kace me? an nemi su musu su bayar da address din inda suke don a karo musu da jami an tsaro

tuni kuwa su musa suka bayar da address din kofar gidan Iro GIDAN KUDI wanda suka ce nan gidan yarinyar ta shiga

Kan kace me? Sai ga motocin hikimomin tsaro sun taso tamkar tashin yaki sun soma jerawa a kofar gidan Iro GIDAN KUDI tamkar tashin yaki suna jiniya da cikawa Al umma kunnuwa .

Alh iro da yake zaune yana waya ya jiyo karar jiniyar motocin hikimomin tsaron kara kuwa kala kala alamar ba kala daya bane mabanbanta ne kuma sunfi a kidaya har suna hana shi jin shi Wanda suke wayar dashi don karar ta cika mishi kunnuwa.

Haj Aliya ta shigo da kofin ruwan bakin shayin da ta hadawa mai gidan tana fadin

“Wai Daddy bakaji karar jiniyar motocin nan bane? ni fa har tsoro ya kama ni wallahi abu haka kamar tashin yaki?

Ya karbi kofin yana fadin

“Shi don dai tsoro bashi da wahala Aliya? ai bari tsoron kira ji tsoron laifi ina ruwan mu da jiniyar su tunda mun san bamu tabo kayan kowa ba?.

“To ai abun ne ko dadin saurare bashi da kuma su irin wadan can motocin da anji su to ba lafiya ba daga na asibiti sai na gidan yari ko kuma hukuma shiyasa abun nasu yske da tsoro.

Musa da ya Ggma faka motar ya fito da nufin zuwa bakin kofar gidan Iro GIDAN KUDI wacce take dankam da masu tsaron kofar shiga saboda tsaro.

Wayar musa ta dauki tsuwwa yana dubawa yaga abokin aikin sa ya dauka da sauri wanda Yake fada mishi makera G R A fa ta cike ta batse da motocin hikimomin tsaro duk dai akan kisan dan gidan distinguish mukhtar Biro har ya kare da tambayar shi sunyi nasarar ganin yarinyar? ya kuma amsa mishi da eh sun biyo ta sun kuma ga gidan da ta shigo har yanzu ma zasu nemi shiga su fito da ita ko kuma a fito musu da ita.

suka gama wayar ya tunkari kofar wacce yayi sallama su maccid’o suka taso da sauri suna amsawa suna tambayar lafiya?

Musa ya fito da I’d card din sa yana nunawa maccid’o yana fadin

“Sunana ibrahim ibrahim ma aikaci ne ni force mopal kuma mun biyo wata yarinya ne mai laifi da ta shigo gidan nan shine muke son a fuddo mana ita wannan shine dalilin zuwan mu nan.

Zubairu ne abokin aikin maccid’o wanda yake da zololon wuya yayi maza yace

“Babu fa wanda ya shigo gidan nan yanzu amma ta ina ka ga ta shigo? Yarinya ce ko kuwa tsohuwa? kai ba ma nan gidan ta shigo ba gaskiya sai dai ko wannan lungun don nan dai muna nan munfi mu goma amma babu wanda ya shigo.

Maccid’o ya karbe yana fadin

“To nima dai tambayar da zanyi kenan don banga ta inda wani mutum ya shigo gidan nan ba .

“Yanzu fa ta shiga wacce napep ya ajiye ta shige a guje?.

“Gaskiya ba dai nan ba kai dai duba inda ta shiga amma nan dai ko sauro bai shiga ba in kuma son shiga kake to ba haka ya kamata kace ba don in kace wani ya shigo kana son ka nuna

mana bamu da amfani a zaman mu nan kenan tunda har wani zai shigo bamu ganshi ba .

Kan kace me ? Rigima ta kaure tsakanin su musa da maccid’o musa yana cewa yarinya ta shigo su maccid’o suna cewa su dai fadi wani abun ba wannan ba inda zubairu ma har ya soma fadin

“Wannan ai leken asiri ne da rana tsaka in ana son duba sirrin ka sai a fake da yaudara a shigo gidan ka to iro dai kafin Allah ne Kuma yanzu da wannan kakin na karya ake cutar mutane sai dubu ta cika zaka gane kakin duk ruba ce ba kakin bane.

Rigima ganga ganga inda sauran  jami an ma suka shiga ciki ana neman rikicewa da balaki har maccid’o ya soma hunce riga zai danko Musa .

Wani daga cikin ma aikatan gidan da ya ga ana shirin yin danyen aiki sai ya nufi ciki gidan inda alh iro ke waya yana rike da kofin ruwan shayin Ango ya shigo yana sallama haj Aliya ta amsa mishi tana bashi izinin shiga ya shigo ya zube Yana gaishe ta.

“Malam Ango yaya ne?

haj Aliya ta tambaye shi ya soma fadin

“Haj rigama ce akeyi a waje da su maccid’o da hukuma shine naga kar ayi danyen aiki nace gara na sanar tunda ita rigama an san farkon ta ba a san karshen ta ba ko za ayi musu magana?.

“Subhallahi malam Ango hukuma kuma? To me ya hada su maccid’on da hukuma kuma?.

“Eh to wallahi haj ban dai san abinda ya hada ba amma  na dai ji suna fadin zasu shigo su kuma suna cewa ba zasu shigo ba to har dai ana shirin dambacewa shine naga gara alh ayi musu magana kar ayi mugun aiki.

Alh iro ya ajiye wayar yana duban Ango yana fadin

“Me yake faruwa ne malam Ango?

ya sake rattaba mishi  yadda akayi .

“Daddy abin nan ba na lafiya bane meye ma dalilin zuwan hukumar?

Da sauri alh iro ya mike yana fadin

“Allah yasa dai lafiya.

ya fice malam Ango ya rufa mishi baya suka fita

mutane dankam a bakin kofar ana ta hayaniya Daddy ya yiwa su maccid’o magana suka nutsu kowa yayi shuru daddy ya dubi jami an yana fadin

“Me yake faruwa ne kuma da hankalin ku zaku biye wadan nan da ba cikakken hankali ne da su ba?.

su musa suka sake rattaba mishi yadda abin yake na wata yarinya da ta shigo gidan wacce suka biyo suke son  Kama ta

Alh iro ya dubi su maccid’o yana fadin

“Yaushe ne yarinyar ta shigo ?

suka hada baki wurin fadin babu wacce ta shigo mai gida suna son dai cewa suna son ganin sirrin gidan ne kawai amma mu kusan goma sha biyu bamu ga Wandw ya shigo ba sai su su biyu kacal?

cewar zubairu.

“To kunji babu wanda ya shigo kuma sune masu gadin kofar kuma dole sai sunga mai shiga da futa ko dai ta shiga wannan sakon ne kuka ga kamar nan ta shiga?.

“Alh nan yarinyar nan ta shigo ni na biyo ta tun daga makare G R A kuma ta shigo nan amma suna min gardama.

“To kaji dai sunce bata shigo ba in kuma kuna bukatar shigowa ciki na baku izinin ku shigo ku bincike ko Ina in kun ganta ku tafi da ita in kuma baku ganta ba shikenan ni ma dai banga shigowar kowa ba amma nayi muku izinin shigowa ko don ku fita a shakku tunda kunce kunga ta shigo nan din Bismillah

ya dubi su maccid’o yana fadin

“Ku bude musu kofar su shigo su binkita.

Mutum biyar suka shiga yayin da sauran kuma suka tsaya a bakin kofar sauran kuma sukayi cikin gidan

Haj aliya taga jami an sun shigo cikin gidan ta soma ambatar sunan Allah inda alh iro yayi mata bayanin abinda ya tara’s a bakin kofa na neman wata mace da ta shigo gidan a cewar wasu daga cikin su don haka ya basu ikon shiowa don su bincike gidan in sun ganta su tafi da ita in basu banga ta ba kuma shikenan

Aka fara da bincike sashin haj Aliya wacce har saman rufin dakin nata da toilet da da sako da lungu na dakin nata sai da aka bincike mutum biyar kowa yana bincike ko ina hatta da kasan gadon haj Aliya sai da aka duba amma babu komai dole aka fita zuwa sashin alh iro shims kaf aka bincike shi babu komai  inda fati ta shigo taga abinda yake faruwa daya daga cikin su ya dubi musa yana fadin.

“Ko itace wannan ?

musa ya dubi fati wacce take cike da tsoro yana fadin

“Ba ita bace wacce tafi wannan tsayi kuma tana sanye da kaya masu ruwan hoda ne .

“Kai su dakin ku fati su duba ko kin ga wata mace ta shigo nan ?

cewar haj aliya.

“Babu wanda ya shigo haj banga kowa ba.

“Kaisu dai su duba nima nafi zaton ba nan gidan ta shigo ba koma wacece Ina nadiya take ?

fati tace ta bi kawayen ta su keena kuma ba ta dawo ba.

“Kaisu dakin ku su duba har toilet da kasan gadon duk ki nuna musu Allah kadai yasan inda ta shiga koma wacece amma bana zaton tana gidan nan

fati ta juya suka rufa mata baya zuwa dakin nasu.

Kaisar ya juyo yana kallon kofar toilet din  da nadiya ta shige ta kuma mayar da kofar ta datse

Ya rufe Al kur anin ya mike yana nufar kofar toilet din don yana cike da shakku da mamaki na abunda ya koro bera daga rami ya fada wuta. Nadiya bata tab’a yin muradin shigowa sashin sa ba bare irin wanna da yafi ganin tamkar an firgita ta kuma ta shiga toilet har da mayar da kofar ta rufe bayan gangami da labari.

Ya tura kofar yaji ta gam a datse .

ya soma bugaww ta bude ya shiga ciki yana sauke kallon shi gareta itama da take a firgice shi take duba.

Jinin da yake jikin ta wanda ya wanke mata fuska da wanda yake jikin kayan ta shi yake kallo da mamakin na meye?

suka zubawa juna ido suna kallon kallo yayin da yake hango tsoro da firgici a kwayar idanun Nadiya abinda bai tab’a gani a tare da ita ba sai fa tsabar izza da izgili da wulakanci

Hawaye ya wanke ta shar ta yi k’asa da kanta tana fadin

“Don Allah ka taimake ni mana? wallahi ina cikin tashin hankali na san sun biyo ni kuma idan su daddy suka ji abinda nayi zasu bayar dani ne ga wanda suka biyo Ni .

“Me kikayi ne? su waye suka biyo ki?

Kaisar ya tambaye ta idon shi a kanta.

tayi shiru ta kasa fada mishi abinda tayiwa abdulhameed na kisan kai wanda kuma ta tabbatar da an biyo sawun ta har motar tana zuwa kofar gidan su dole Kuma a miko ta.

“Ka taimaka min ka fidda ni daga gidan nan wallahi Ina cikin tashin hankali da rudani ban san zai mutu ba wallahi da ban yi.

sai kuma tayi shiru ta kasa karasawa don tana ganin akwai nauyi akan fadar abinda tayi.

K’ofar da aka buga ne ya kuma jiyo muryar daddy yana kiran shi shine abinda yasa firgicin nadiya ya linku.

“Kaisar akwai wanda ya shigo sashin nan naka yanzu?

Daddy ya kuma fada.

Da sauri nadiya ta toshe bakin ta tana takawa kukan da ke shirin kwace mata burki tana kadawa kaisar kai alamar yace babu kowa.

“Don Allah kace babu kowa don Allah nema na suke nayi.

“Fada min abinda kikayi nayi alkawarin rufa miki asiri.

“Na kash.

sai kuma tayi shiru tana zubar hawaye tana toshe bakin ta don hakikatan maganar tayi mata nauyin fada.

“Kaisar ko bacci kake ?

Daddy ya sake fada.

Da sauri Kaisar ya  taka saman toilet din ya soma kokarin zaro robar silin din da take saman rufin dakin har ya yi nasarar zaro robar silin din yayi mata kofa kafin ya sauko ya nunawa nadiya yana fadin

“Shiga saman can na rufe ki ciki.

Ai kuwa da azama nadiya ta mike ta taka inda taga kaisar ya taka ta haye saman ta kuma shige ya mayar da robar silin din ya rufe tamkar ba a huda ba.

ya bude kofar yana fadin

“Yi hakuri daddy bacci ne ya dauke ni.

Idon shi ya sauka akan jami an bunciken har su biyar sai daddy na shida da fati ta bakwai mama kuma ta takwas

Gaban shi ya sara yana fadin

“Daddy lafiya?

“Eh to lafiyar kenan sun ce sun biyo wata yarinya ne wacce tayi kisa kuma sunce wai nan gidan ta shigo su kuma masu gadin kofar sunce babu wanda ya shigo shine nace su shiga ko Ina na gidan su duba tunda ance bata shigo ba sunce sunga shigowar ta . to duk dai sun bincike ko ina tun daga sashi na zuwa sashin Aliya da na su fati amma basu ganta ba shine suka ce suna son shiga nan sashin to kuje ka bude musu ko Ina har duk wata kofa da take sashin har k’asan gadon ka ka bude musu in kuma kai ka ga zuwan wani ko wata sai ka fada musu.

gaban shi yayi amsa kuwwar maganar daddy ta cewa wai wata tayi kisa ta shigo gidan.

Jinin da yake jikin Nadiya kadai ya gama hada mishi biyar a tara da uku takwas kenan .

Suka shigo tun daga falon yake daga musu komai suna gani hatta kujerun falon sai da ya daga musu suna dubawa yayin da hankalin sa da tunanin sa yake ga Nadiya. waye ta kashe? meye dalilin kisan ? ashe tana da karfin halin kisa ta kowace irin siga? kisa Duka kisa ne ta makamd ko ta hanyar bada abin kisan ko da kuwa guba ce sai mai karfin hali da dakakkiyar zuciya.

Cike da sanyin jiki da kasala yake jagorantar jami an bunciken suna shiga ko ina yana daga musu komai suna dubawa tare da leke ko ina suna bincikaawa

Dakin shi kuwa kamar yadda daddyn yace ya daga katifar gadon shi ya kuma bude wadrob tare da akwatin kayan shi duk suka gani kafin suka nufi toilet shima tun daga na wanka zuwa na bukata babu kowa hatta da sinks sai da suka duba kafin suka yarda babu kowa a sashin suka juya suka fice

Sukayi wa daddy sallama suka wuce inda su maccid’o ke fadin

“Kwa gano su ko? 

shi kuwa zubairu cewa yake

“Dama sirrin gidan suka zo gani sun kuma gani ni kam har lambar motar su na dauka yasin nan da shekara ashirin duk abinda ya samu gidan nan sune yau da sun gano yarinyar da suke magana shikenan mu sun kashe mana kasuwa don ka san dai mai gidan nan zai canja mu ne yace bamu da amfani amma yanzu da suka shiga suka duba ai sun gano ta ko?

<< Azurfa Da Zinari 20Azurfa Da Zinari 22 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×