Skip to content
Part 22 of 80 in the Series Azurfa Da Zinari by Hadiza Gidan Iko

Su dai jami ai basu takawa su maccid’o ba suka shiga motocin su suka  wuce

Kaisar ya dawo ciki ya shigo toilet ya na bude inda ya saka nadiya  ta sauko tana sharben hawaye.

Ya zuba mata ido ita kuma tana jin nauyin shi matuka gaya musamman da ta tuna tozarci da wulakancin da ta sha Tata mishi.

“Yanzu nadiya har kina da karfin halin yin kisan kai? waye kika kashe ? me yayi miki kika kashe shi ? ta yaya kike tunanin kin tsira alhalin sunga fuskar ki wacce zasu iya shaida ta a ko yaushe?

ta fashe da kuka tana fadin

“Na fara haduwa da Boss ne a malina shopping wanda ya ce min Yana sona amma na tofa mishi yawun baki na kuma ce mishi yafi kama da monkey man. muka sake haduwa da shi a silver and gold inda na mare shi na kuma sake tofa mishi yawu . yayin da abokin sa yaso mari na amma na saka aka Kama shi amma ban san yadda akayi aka sake shi ba shine kawai a yau ina bakin update plaza naji an kama ni da karfi an ja ni cikin mota shine fa har aka dora min wuka a makoshi har xuwa wani gida da ban san a makera G R A yake ba .

Tayi shiru tana kuka Kaisar bai ce mata komai ba yana sauraren ta kafin taci gaba da fadin

“A cikin gidan ne na iske wanna gayen da na tofawa yawu tare da wanda na saka aka kama . k’atti uku ne Wanda yasa ka suka fince min kayan jiki na shi kuma yayi min.

Nan ma ta kasa karasawa tana kuka  kafin ta ci gaba da fadin

“Yadda ya keta min haddi ne yasa na soka mishi wuka har ya mutu jinin shi ne a jikina.

wata irin majaujawa ta soma katan tanwa da Kaisar wanda ya gane wulakancin da nadiya take ne aka dauke ta don  a rama.

Ya dafe kanshi da hannu biyu babu abinda yakke hange sai mafitar da zai samowa nadiya ya fidda ta wannan kangin da take ciki. ta yaya zai sama Mata mafita?.

sukayi shiru a cikin toilet din Yana laluben mafita.

Haj Laila da take ta kuka tana kankame da gawar abdulhameed tana Jin gara mutuwar ta da mutuwar abdulhameed.

Shi kuwa distinguish mukhtar Biro yana tsaye ya goye hannayen shi a baya yayin da Tero ma yake taya haj laila kukan ta  suka cika dakin da koke koke .

Hawaye ne kawai suke gudu a fuskar distinguish mukhtar Biro wanda ya dafa kafadar Tero yana fadin

“Wacece wannan yarinyar Mustafa da ta iya kashe mini Abdulhameed? laifin me yayi Mata har ta  zab’i ta kashe shi min shi? wace irin alaka ce a tsakanin su?

Tero ya share hawayen shi yana fadin

“Daddy yarinyar sa ce  bayan tayi mishi wulakancin kala kala sai dai ba zan iya sanin ta Yaya akayi kisan ba? Bana gida sai da nazo na samu bata nan shi kuma da wuka a cikin sa don haka ina ganin uban ta za ka saka a kama in aka Kama shi zai fiddo ta   idan ta bayyana zatayi bayani kuma in dai CCTV camera din falo a kunne take zaka iya ganin yadda Al amarin ya fara.

A guje distinguish mukhtar biro ya nufi falon ana hada wayoyin CCTV ya kuma tashi TV ya soma gano abubuwan da suka faru a tsayin satin har zuwa shigowar Tero da nadiya wacce ya kafawa wuka a makoshi da irin yadda boss ya saka su keso sukayi mata fit haihuwar uwar da irin romantic din da ya faru da daukar da yayi mata zuwa dakin wanda shi ya hana ganin karshen Al amarin sai fa suntirin jami an da CCTV ta nuna  kafin TV ta dakata

“Wacece wannan yarinyar? waye uban ta? ka san ta ne Mustafa?.

“Na san ta daddy Yar gidan iro GIDAN KUDI ce shine uban ta.

Da sauri daddy ya figo wayar shi yana dauke kwallar ido shi ya kira yana bada umurnin a kamo mishi iro GIDAN KUDI da ahalin sa gaba daya yanzu kafin cikar awa biyu yadda abdulhameed ya bar duniya ta sanadin yarsa to yarsa ta ja mishi mutuwa shi da ita da zuriar sa gaba daya  ko hankalin sa zai kwanta sai ya ga babu ko burbushin ahalin iro GIDAN KUDI don in har yana duniya abdulhameed kuma baya duniya to bakin ciki ne ajalin distinguish mukhtar Biro. Kan kace me? motocin hikimomin tsaro sun dauki  hanyar gidan alh iro GIDAN KUDI bisa umurnin distinguish mukhtar Biro wanda ya sha mugun alwashin yadda yarsa iro tayi mishi sanadin gudan jinin shi abdulhameed th Haka ahalin iro da duka zuriar su zasu bar duniya don su gane ran abdulhameed yafi Rayukan kaf mutanen da suke rayuwa a garin bauci kima da tsada shiyasa dyk wanda ya danganci iron yasha alwashin salwanta da sunan daukar fansa

Bayan Jami an bunciken sun gama buncike GIDAN na iro GIDAN KUDI suka yi mishi sallama suka fice shi kuma dama yana kan shirin fita waje zuwa Senegal akan wani kasuwanci don haka jirgin karfe biyu yake da shi shiyasa ya koma kan shirin sa

Haj aliya da take ta maida batu akan yadda aka hargitsa mata muhalli da sunan bincike gashi an tayar mata da zaune tsaye na mayar da komai inda yake

sai tsaki take ja tana fadin

“Duniya dai babu gaskiya babu amana shiyasa babu Mai yin magana a yarda in ba haka ba ta yaya za ayi maka wannan wulakancin ace wai an shigo gidan ka in dai ba wata manubar ba?

tana ta tsegumi yayin da alh iro yake shirya akwatin tafiyar sa yana jin ta bai dai tanka mata ba ita kuma bata fasa maganganun ba har dai ya tanka ta da fadin

“To aliya ai wannan ihu ne bayan hari tuni ya kamata kiyi maganar nan amma yanzu ai tamkar a kunnen kurma kikeyi da zaki hakura da maganar ma da kin huta tunda sun duba babu abinda suke nema ba sun tafi ba? amma ke kina ta nanata magana.

“Abin ne da takaici daddy dubi yadda suka watsa maka daki don Allah? Jeka nawa dakin ka gani shima haka yau zan wuni akan su babu gaira babu dalili .

“To ni banga amfanin da cancana maganar zaiyi miki ba ai amma wata kil kina jin dadin yin ta ne amma gyaran daki ba ga fati da nadiya ba ko su sun Isa gyara miki naki ke kuma ki gyara nan .

“Ina naga Nadiya bayan ta fice rakiyar kawaye ban ma san ta fita ba? zata dawo ta same ni .

“Ni dai karasa hada kin kayan nan nayi wanka har daya da rabi ni da naso kamar yanzu ace ina filin jirgi na san alh sule bai karasa ba da yanzu ya ishe ni da waya.

Ya fada yana shiga bandaki haj Aliya kuma ta karasa hada mishi kayan ta kammala

Ya fito ya shirya haj Aliya da fati suka rako shi har bakin mota yana cewa haj Aliya ta saka ido akan Nadiya kafin ya dawo duk da tafiyar ta kwana hudu ce wacce zatayi daidai da saura kwana biyu daurin auren nadiya da maccid’o

Direban shi yaja suka fice yanayi wa ma aikatan gidan kyauta tare da yi musu bankwana suna mishi godiya tare da ADDU A har suka fice

Fati na taya haj Aliya gyaran daki suna ta magana akan zuwan mutanen da bincike su tas da sukayi

Motocin hukimomin suka soma jerin gwano suna haniniya da jiniya .

Suka soma fitowa suna nufo kofar get suna fadin a kira musu mai gidan .

Zubairu ne yace mai gidan baya nan ya tafi Senegal.

Aka kira distinguish mukhtar Biro aka fada mishi alh iro baya nan wai ya tafi Senegal.

“In shi baya nan iyalan sa fa? dukkan ahalin sa a kamo su shima matukar ba lahira ya tafi ba zan sa daga nan a bishi har Senegal din a kamo shi don haka ko kyanwar gidan iro ce ku nad’o min ita ku kai ku kulle shegu.

Daya daga cikin masu gadin ne ya shiga yana fadawa haj Aliya ana neman alh iro

ta kuma ce baya gari don yanzu direban shi ya dawo daga kai shi air port.

Ai mai kawo sakon ma bai koma bada ba asi ba suka ga jami an sun tararo tamkar tashin duniya suna shigowa suna wara idanu.

“Inna lillahi wa inna ilaihir Raju un malam lafiya haka kuke shigowa gidan mutane babu neman izini? .

“Kuyi hakuri haj dole ce ta sa kuma mun nemi mai gidan aka ce baya nan to muma umurni ne dole kuma mu cika don abin yafi karfin mu .

“Ba kune kuka zo ba kuma kun duba gidan nan kaf babu abinda kuke nema meye kuma naku na dawowa saboda Allah in dai ba wani abu ba?.

“Kuyi hakuri dai haj a yanzu kam sawun giwa ne da ya take na rakumi abunda ya kawo mu yanzu ya wuce wanda muka zo dazu don a yanzu dai dukkan ahalin gidan nan ne aka ce mu zo mu tafi da su haj har da mai gidan wanda shine jigon tafiyar kuma ance baya nan.

“Inna lillahi wa inna ilaihir Raju un akwai magana kenan dama dai ba binciken ya kawo ku ba dama zubairu ya ce akwai wani Abu gashi kuma ya bayyana to Allah yana bayan Mai gaskiya ku kama mu mu tafi Allah yayi mana mafita.

K’arar haya hayar da ake ne da jiniyar motocin ne yasa nadiya ta mike tana leko kofar kaisar inda ta leka ta ga jerin gwanon motocin suna ta jiniya da haniniya yasa ta juyo a guje ta dawo toilet din tana kuka tana fadin.

“Don Allah kar kace Ina nan ka rufa min asiri wallahi ni aka zo nema.

Wani irin firgici da tashin hankali ya shigi kaisar yana neman mafitar da zai samawa nadiya don shigar ta tashin hankali shigar sa ne koma ace fiye da nata.

Ya fito ya jawo kofar toilet din ya rufe ta ya taho jiki a sanyaye ya nufi kofar waje da yake jin hayaniya inda kuma ya ga mutanen suna shigewa babban falon gidan sai ya bi su inda ya jiyo ana cewa umurnin tafiya da Yan gidan aka zo.

Ya kutsa ya isa ga haj Aliya wacce ke cewa a tafi da su.

“Mama lafiya?

ya fada yana kallon jami an suka kuma yi mishi bayani don haka haj Aliya tace a tafi da su din kawai.

Aka soma taso keyar su har da masu aikin gidan mma Haj Aliya tace .a

“Su kuma masu aiki meye nasu ? ba kunce zuriar iro kuka zo kamawa ba? to su yan aiki ba zuriar iro bane hakkin su suke nema babu abinda ya shafe su da koma me kuke son yiwa iro da ahalin sa .

<< Azurfa Da Zinari 21Azurfa Da Zinari 23 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×