Skip to content
Part 24 of 80 in the Series Azurfa Da Zinari by Hadiza Gidan Iko

Ya nuna Kaisar wanda yaji wani matsiyacin firgici da tashin hankali domin kuwa a yanzu ya gama tabbatar da idan Nadiya ta shiga hannun wannan mutum mai izza da takama da madafun iko babu ko shakka cika bakin da yake shine mai kashe Nadiya murus har lahira don haka ko da yaji umurnin da daddy ya bayar sai ya shiga rudani da tashin hankali

Tuni kuwa aka hada mota tare da jami an aka dauki Kaisar zuwa gida don tahowa da Nadiya amma shi kam cike yakke da tashin hankali don yana tsoron abinda zai tadawa Nadiya hankali. kukan ta kadai yana sashi sarewa. babu abinda yake tunani sai ta yadda zai kyautar da Nadiya daga wannan case din . yanzu haka fata yake ace ta fice daga gidan ta yadda za a neme ta ba a ganta ba ko kuma ta yadda zai juyar da tunanin jami an da suke tare har su fito basu leka sashin sa ba

Motar ta karaso kofar gidan alh iro suka fito s duka maccid’o da zubairu suka bude musu kofar inda hikima ta fadowa Kaisar wanda yace

“Maccid’o Nadiya kuwa ta dawo gidan nan ?

Da sauri maccid’o ya amshe  da cewa

“Walla babu wanda ya shigo gidan ga yau kwana biyu  babu kowa a ciki sai iskokan gidan ne dai suka wali a ciki .

Kaisar ya dubi jami an yana fadin

“Kunji bata dawo ba muje s sanar dashi.

“Bata dawo ba,? to ina ta tafi har kwana biyu ,? Ko kuwa dai da gaske an kaita kasar wajen ? cewar wani ma aikaci.

Kaisar dai bai tanka mishi ba dole kuwa suka shigo mota suka dawo office din shugaban suna fada mishi wai Nadiya bata dawo gidan ba cewar masu gadi.

“Ahaf ai nace ya fidda yarshi waje ne boye ta amma da yake ya raina hankalin mutane yana fadin bai san anyi ba.

Hankali a tashe daddy ya mike yana fadin

“Ina yarinyar nan ta tafi Aliya? ba zanji komai ba idan ya kasance guduwa tayi saboda auren da zanyi mata amma zanji matukar zafi da ciwo idan hasashen da ake min na zaton n boye ta ya tabbata. wallahi tallahi Allah shine daya ban boye yarinyar nan ba kuma ban san abinda tayi ba amma idan ta gudu ne don auren da zanyi mata ban ji haushi ba sai don zargin da ta ja min wanda ban san komai a Kai ba.

Fati da ta tuna da firar da taji sunayi da su keena ta cewa ta gudu tazo gidan su idan an daura auren to ta gudu kawai.

Fati ta dubi daddy tana fadin

“Daddy a duba gidan su kawayen ta ko tana can tunda rakiyar su ta tafi s ranar in ma bata can su sun san inda take.

Kan kace me kuwa ga su keena da su lubabatu da safina an kwaso zuwa hukuma amma suka bada bayanin tun ranar da suka zo gidan nasu basu kuma ganin Nadiya suma kuma a studion show suka sauke ta

Aka sake tura jami an zuwa studion show shima aka figo shi amma shi kam yace bata zo ba rabon shi da Nadiya tun ranar da suka dauki vedion wakokin sa.

“Akwai makirci da munafunci a cikin wannan Al amarin akwai manuba. dama nace mutumin nan ya boye yarsa ne kuma yake mana wasa da hankali. to zan nuna mishi nafi shi sanin wasu a Nigeria wallahi tallahi matukar ba fiddo yarinyar nan akayi ba to zai tabbata nee rufe har ya cimma ajalin sa shi da dukkan ahalin sa don haka ishaq kuyi ta ajiyar su  har su cimma ajalin su in kuma sun hutar da kan su doguwar wahala sunyi bayanin inda tsinanniyak yarsu take to a Kira ni.

cewar distinguish Mukhtar Biro Wanda yake bayar da umurnin kanshi tsaye kuma da tabbacci da hakika.

Kaisar da yaji ba zai iya bari a wulankata alh iro akan hakan ba don zai iya hakura da dukkan abinda yake ji a kirjin shi duk girman sa kuwa da dai a wulakanta Daddy ba akan hakkin sa  ba sai  yayi maza yace

“Zan nemo ta a yau in kuma ban kawo ta a yau ba ayi min hukuncin da za ayi mata a madadin ta da  dukkan ahalin ta na dauki wannan alkawarin.

Distinguish Mukhtar Biro ya juyo  ya kalli Kaisar a wulakance cike da izza da fusata yana fadin

“Ai da dai ka bari kunji wutar da nayi nufin dandana muku wata Kil magana daya zakuyi kuce kurunkus Kan dan Bera domin kuwa nk gama yarda ku yaudare ni kuma ayanzu a cikin minti nawa zaka kawo ta? don na gane akwai manuba da munafunci a cikin Al amarin ku sai an biyo muku ta bayan gida .

“Minti talatin ma zan kawo ta .

“Ishaq hada shi da yaran ka kaji munafukin ya tona asirin uban zai kawo ta Allah yasa kuma ya dawo yace min ga zance ga magana yaga yadda zansa a wulakanta uban su don naga su waye Uban gidan sa a Nigeria? wallahi yadda suka zamo sanadin bak’in ciki na har badda su sai anyi don su gane sun tabo abinda yafi karfin su

Kaisar da yaji ba zai iya bari a wulakanta Daddy ba yaji koma me zai faru gara ya faru ya gurfanar da Nadiya da dai a tozarta Daddy shi kam bashi da uba amma Daddy ya zama madadin uban sa yayi mishi gata ya share mishi hawaye ya kuma zama silar sama mishi farin ciki ya kuma hana shi kukan maraici don haka zai iya sadaukar da nashi farin cikin don na daddy don haka ya hakura da dukkan abinda yake ji a zuciyar shi game da Nadiya 

Motar ta kawo su har kofar gidan alh iro inda  ya fito zuwa ciki jami an suka mara mishi baya amma ya dakatar da su suka ce dole ne su kasance tare da shi tunda shima safe ne in ya gudu suce me? don haka duk inda ya saka kafa dole su maye da tasu

Ba don ya so ba suka shiga tare yana fito da wayar shi yana kiran layin Nadiya da dayan layin shi da yake hannun ta wanda ya bar mata tun a ranar

A bakin kofar shiga suka tsaya basu shiga kofsr da zata sadaka da kofofin gidan ba don baya son suga ta inda Nadiya zata bullo

wayar tayi ta kara tana kwararato amma ba a dauka ba sai da ya jera kira kusan takwas kafin ta dauka murya a dusashe.

“Kina Ina? Kin dawo gidan?

Itace kalmar da ya fada bayan yaji ta dauka

“Fito nan bakin kofar fita ina son ganin ki yanzu yanzu akwai matsala ne fito da sauri

Ya fada kamar bai san komai ba kuma bai san tana gidan ba

ya dire wayar ya saka aljihu yayin da jami an kuma suka bishi da kallon manuba suna zare idanu tamkar masu shirin cinye babu.

Kaisar ya dago ya dube su kamar bai san irin kallon da suke mishi ba cikin ko in kula yace

“Tana ciki zata fito yanzu .

yadda ya fadi maganar shima bai fada don yana jiran amsa ba inda ya mayar da fuskar shi ga kallon fulawoyin da suka zagaye gidan alh iro sukayi musu kawanya amma kuma idanun sa ne kawai akan fulawoyin amma zuciyar sa tana can ga lissafin me zai faru da Nadiya idan ta bayyana s gaban distinguish Mukhtar Biro,? zai kashe ta ne kamar yadda yake ikirarin ta kashe mishi dan shi? shi kuma yaya zai kasance shi da zuciyar shi a duniyar da babu Nadiya a cikin ta? hawaye suka soma taruwa a kwayar idanun shi har suka soma gangarowa bai sani ba.

Nadiya da tayi wurjanjan a saman rufin dakin duk ta fige a lokaci daya domin kuwa Al amura sun ganar da ita duniya makaranta. Kuka take tana nadamar abinda tayi na kisan Abdulhameed amma kuma ta bar karin tun ran tubani.

Wuni cur tayi shi a sama kamar wata tsuntsuwa sai fa da dare yayi ta sauko ta shiga sashin su mama wanda ta tabbatar da kama su akayi kaf mutanen gidan

Bata iya kulawa da yunwar ta ba domin kuwa bata ma jin yunwar abinda kawai take so shine ta gudu ta bar garin nan amma tn yaya ?

Motsi kadan ma sai ya firgita ta ta koma sama ta lafe tana leken me zai faru?

ta kasa bacci bare ta iya sauya kayan jikin ta don tana ganin kamar a kowane lokaci za a iya shigowa gidan neman ta

Lokaci zuwa lokaci ta kan sauko kasa ta garji kukan ta da nadamar ta da Kuma hango ta yadda za ayi ta fidda bakin fentin kisan Boss da kuma ta yadda za a sako su mama da fati da dukkan mutanen gidan da aka zo aka yaye

Kwanaki biyu tana kulle a dakin Kaisar bata a toilet Bata a sama duk ta kasa sakewa

A ranar ne kuma taji dawowar Daddy da irin wayoyin da yake amsawa kamar ta fito amma kuma ta san fitowar ta shine gangancin don haka ta koma sama a cikin silin

Tana jin fitar Daddy amma bata sauko ba sai da ta ji wayar da take k’asa tana ringing ana ta kira babu kakkautawa kafin ta sauko ta duba mai kiran taga sunan Kaisar shine ta dauka yake bata umurnin fitowa

Cike da tashin hankali ta ajiye wayar  ta nufi kofar fita

Tana fitowa kuwa tayi arba da jami an wanda suka wuff da ita zasu buga mata handcuffs amma Kaisar ya hana yace

“Ni nayi alkawarin kawo ta to ba sai kun saka mata handcuffs ba tunda gata ai magana ta kare.

Nadiya da kuka ya kwacewa ta soma kuka tana kallon Kaisar da neman agajin sa don ta kasa bude baki tayi begin.

Tuni zuciyar Kaisar ta tsinke ya cije yana kallon titi suka fice daga gidan suka dauki hanyar hukumar yayin da Nadiya ke shatatar hawaye Kaisar kuma yana lissafin dokin rano har suka Isa office din shugaban jami an

Distinguish Mukhtar Biro ya zubawa Nadiya ido yana kallon jinin da ya jima da bushewa a jikin ta ya kuma kalli Tero yana fadin

“Mustafa itace wannan ?.

“Itace Daddy

cewar Tero

Sai kawai distinguish Mukhtar Biro ya kece da kuka yana yi yana dauke hawayen shi da tissue paper kafin ya dago kanshi yana duban alh iro yana hararen shi

“Ga jinin abdulhameed a jikin ta? yanzu wannan har ta Isa tayi kisan Kai? To kayi mata albishir da mutuwa irin wacce Abdulhameed yayi kamar yadda ta soka mishi wuka nima a haka zan kashe ta da kakkaifar wukar wallahi don haka ishaq hada min su iyayen nata da ahalin ta ka kulle ita kuma a kaita dakin duhu a gidan dutse.

Kukan da Nadiya ta fasa shi ya saka Kaisar mikewa zaiyi magana amma distinguish Mukhtar Biro ya nuna shi da yatsa yana fadin

“Kar kace min ko uffan ba zan kuma sauraren wani abu ba sai an gama buncike akan gawar abdulhameed.

Daga haka ya fice bai kuma sauraren kowa ba.

Alh iro ya dubi shugaban Yana

“Ina son belin iyali na su duka banda mai laifin

Ishaq kuwa ya amsa da fadin

“Babu matsala alh kuma kaima zaka iya solved din kanka tunda ga mai laifi

A take daddy ya yi belin din su haj Aliya da su fati da Kaisar yayin da aka sakawa Nadiya sasarin hannun da kafa za a wuce da ita amma Kaisar ya rike sasarin.

“Sake ta mana Kaisar.

cewar Daddy da yaga rukon da yayiwa sarkar.

Fati tana kuka itama ta Rike sarkar yayin da kukan Nadiya ya zarce nasu amma dole aka fice da Nadiya zuwa inda aka bada umurnin kaita

Alh Sule da yazo gidan alh iro ya kira wayar shi yana jiran shi shi kuma ya fada mishi inda yake amma gashi nan isowa.

Daddy yajawo motar tare da ahalin gidsn shi da aka sakaya har kwanaki biyu

Alh Sule yana zaune a motar shi har su daddy suka shigo shima ya biyo bayan su yana ganin yadda Haj Aliya ta fito tana dauke kwallar idon ta mamakin dalilin da ya hada Nadiyar da dan wancan mutumin marar mutunci har ta iya kashe shi shine damuwar haj Aliya

Alh Sule ya dube su su duka babu mai alamun farin ciki sai ma fuskokinsu masu cike da jimami da alhini.

Alh iro ya ruko hannu alh Sule Yana bashi hakuri akan saba alkawarin da yayi mishi .

Haj Aliya ta gaishe da alh sule yana fadin

“Aliya yau dai banga kina murna da zuwa na ba ko an samu matsala ne da aboki na?

“Ko daya alh yau da gobe ce kawai

ta fada tana wucewa inda alh iro yake fada mishi Al amarin da yazo yau ya Tara’s .

Ya kwashe  komai ya sanarwa alh iro a game da kisan dan gidan Mukhtar Biro wanda akace Nadiya tayi da irin wulakanci da alwashin da distinguish Mukhtar Biro yake sha akan daukar fansa.

“Subhallahi iro kuma baka fada min ba?  To shiga mota muje ai ba a barin irin wannan maganar ta jima sai ayi amfani da madafun iko a sauyawa maganar fassara kafin su gama binciken mu kuma mu shigar da kara maganar ta zama kotu ta san da ita ta kaka ne za a bi komai mataki mataki don tabbatar da shari a a muhallin ta

Ai kuwa kafin kace kwabo alh sule ya shigar da maganar a babbar kotun jihar har an saka Ranar shiga kotun  kwanaki biyu kacal

Idan akwai wanda ya shiga tashin hankali a gidan alh iro to Kaisar ne duk da haj Aliya ma tana cike da son sanin ta yaya aka haihu a Ragaya?

Kaisar kam ko a ranar da aka tafi da Nadiya sai da ya dauki mota ya tafi kai mata abinci a gidan dutse

sai ya zama dukkan abincin safe da rana da dare sai ya kai mata ya kuma duba ta

Yaya halilu ma ya iso bauci daga misau yana jajantawa dan uwan shi halin da aka samu kai

Kaisar kuwa har da lauya ya daukarwa Nadiya ba tare da su Daddy sun sani ba ma ya kai lauyan ya gana da Nadiya wacce take bayar da labarin abubuwan da suka hada ta da abdulhameed da irin daukar da Tero yayi mata ya kaita gidan da Boss din ya soma keta mata haddi wanda yasa ta soka mishi wuka a cikin

Dukkan abubuwan da ta fadawa lauyan ya Rubuta su a takardar shi yayi mata tambayoyin ta bashi amsa sukayi sallama ya baro ta tana kukan da ya aure ta daga lokacin da Al amarin ya faru zuwa yanzu.

<< Azurfa Da Zinari 23Azurfa Da Zinari 25 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×