Fuskar Mukhtar Biro ta kirne yana karanta dogon sharhin wanda yake nuna babu laifi guda daya tak da aka ambata na yarinyar nan da tayi kisan Abdulhameed duk da kisan ta addancin da tayi Sufi yana nufin bata yi laifi ba?.
ya wurgar da takardar yana kallon barrister.
“Shi Sufin ne ya yankee wannan hukuncin barrister? har ikirarin biya tara yake don na nunawa mutumin nan bindiga? nine za a kashewa yaro kuma na biya tara? ni Sufi zaiyiwa tozarci da wulakanci irin haka? .
“Nima nayi mamaki ranka ya dade ban zaci hakan ba duk da dai Mustafa ne ya dagula Al amarin da ya kai CCTV camera wadda ta fallasa komai don mai shari a ya tabbatar da gaskiyar yarinyar ne akan abinda ta fada wanda yayi daidai da abinda yake cikin CCTV din .
“Ko Mustafa Bai kai camera ba dama Sufi yayi nufin tozarta ni tunda ya hade mu da mutanen nan yana son nuna min sai ya fayyace gaskiya a tsakanin mu bayan an kashe min yaro to amma zan nuna mishi irin abinda ya nuna min sai na saka shi yayi nadamar abinda yayi wallahi.
Ya fada a fussce yana figo wayar shi ya kira justice inda femi a ma aikatar shari a ya nemi permission a ranar kuwa aka turo mishi takardar wacce ya aikwa alh iro GIDAN KUDI aka kuma turawa Sufi a kotun su cewar shari ar da yayi batayi ba ya tattaro case din gaba daya ya tura shi Abuja takardar mai dauke da saka hannun justice inda femi
Mai shari a Sufi yana ganin zuwan takardar ya san daga dan uwan sa Mukhtar take don haka ya tattare baya nai da shaidu da hujjoji da record na komai ya aike da su Abuja kamar yadda aka bukata yana mamakin halin dan uwan sa na son kan sa da zuciyar sa
Alh iro Yana gida ma Aikin takardar sammacin daga babbar kotun Alkalai dake da mazaunin ta a Abuja ta iso mishi da son ganin shi don tuni aka aike da Nadiya dake gidan sarka zuwa babban gidan kason da yake a gwarumfa a birnin tarayya Abuja
Mamaki ya kama shi yana cikin yadda za ayi da son fito da Nadiya daga sarka sai ga wani tashin hankalin
Ya dubi haj Aliya wacce take duban takardar cike da tsoro da zullumi yana fadin
“Aliya sammaci ne fa daga babbar kotun Alkalai dake Abuja? Ita kuma wannan takardar ta mecece? me kuma ake nufi ?.
“Daddy bana ko shakka wannan takardar daga uban yaron nan ta fito dama Raina ya bani ba lallai su yarda cewa dan su ne mai laifi ba to shine suka daukaka kara ko shakka kar kayi akan hakan.
Daddy yayi shiru ana kallon takardar tamkar mai shirin gano wani Abu ta cikin takardar.
Sunyi jugum jugum an Rasa mai cewa uffan sai ga Kaisar ya shigo a hargitse tamkar Wanda yayi gamo.
Daddy ya dube shi ya zube a gaban su idanu jajir tamkar garwashi ya kasa cewa komai.
“Yaya ne Kaisar? me yake faruwa da kai ne nagan ka haka hankali a tashe,?.
ya dubi Daddy da jajayen idanun shi yana fadin
“Daddy daga gidan sarka nake naje kaiwa Nadiya abinci ban same ta a gidan ba da na tambaye wani gandireba a gidan shine yake fada min wai case din ta ya koma Abuja har kuma an tafi da ita Abuja a yau din.
Haj Aliya da daddy suka dubi juna cike da tashin hankali amma suka kssa cewa Kaisar komai.
“Daddy ina tausayin Nadiya ina tausayawa halin da take ciki. ta yaya za a fahimce ni Daddy? Nadiya Ruhi na ce jinin jiki na ce daddy ba zan tab’a zama lafiya ba matukar Nadiya tana cikin wani hali daddy nayi alkawarin fidda Nadiya daga cikin wannan halin don Allah kar kace min A a Rayuwa ta fansa ce ga Rayuwar Nadiya zan kuma fansar da ita nayi shahadar soyayya.
Hawaye ya biyo idon Haj Aliya wacce a yanzu ba tausayin Nadiya take ba sai tausayin Kaisar . hakika ya cancanci a tausaya mishi matuka gaya.
“Kayi hakuri Kaisar kowane bawa da kaddarar sa a duniya haka kaddarar Nadiya take ni kam ba zan bari wani Abu ya same ka ba Kaisar kayi ADDU A Allah zai kimsa maka hakuri da k’ana A rai da zuciyar ka .
Hawaye ya tararo wa Kaisar ya yi k’asa da kanshi yana sauraren daddy.
Maccid’o yayi sallama a falon aka bashi umurnin shigowa ya shigo ya zube a gaban daddy da Haj Aliya yana fadin
“Mai gidda dama nazo akan maganar armen da ka bani to yanzu nissamu sako gada mahaihwa na cewa a bar batun armen ga tunda ga abinda yarinyar tayyi na kashe sarmayin ta ayi hakuri a bar maganar an gode.
Daddy ya dubi maccid’o yana fadin
“to maccid’o babu komai ka burge ni da kayi wa iyayen ka biyayya Allah yasa hakan shine alheri nagode da mutuntaww.
“Ka wuce nan mai gidda ai mutumin kwarai na Kai albasa ce batayi harlin Ruwa ba .
Maccid’o ya mike yafi Kaisar ya bishi da kallon mamaki zuciyar shi na tambayar shi har an fara gudun auren Nadiya saboda wannan abun da ya faru?
Ya share hawayen shi ya mike zai wuce Daddy ya tsayar da shi yana fada mishi gobe tare zasu tafi Abuja ya shirya sammako zasuyi su bi jirgin karfe bakwai da Rabi ya amsa da to ya wuce
Motar distinguish Mukhtar Biro ta faka a farfajiyar gidan dan uwan shi Sufi mai shari a ya fito ya wuce ciki don ya san yana nan don bays zuwa ko ina da dare sai fa makaranta daukar karatu shima tsakanin magaruba da isha I ne amma bayan nan karfe tara zuwa sama yana gida
Mukhtar yaso ya hadiye abinda dan uwan sa yayi mass amma yaji ba zai iya hakan ba shiyasa ya taho ya iske shi.
Sufi ya tarbi dan uwan shi yana mishi maraba mai kyau da ruwa da lemu har da kayan lambu dangin fruit.
Distinguish Mukhtar ya zauna yana watsawa Sufi da kayan tarbar wani matsiyacin kallo cike da fusata.
“Brothe barka da zuwa Bismillah.
“Kar ka kuma ce min brothe nemi brothe din ka a cikin Usman da abubakar amma ni tuni na cire ka daga wannan alfarmar kira ni Mukhtar kawai .
“Ba zan iya hakan ba brothe sai dai kayi hakuri.
“To ni zan iya maka sufi amma ni da zuciya ta wallahi tuni na cire ka daga hakan. ba komai ya kawo ni wurin ka ba sai albishir da nazo nayi maka kuma in jaddadda maka nafi ka sanin mutane a duniya tunda ka zabi ka tona min asiri Sufi to ni ba zan tona naka ba amma zan nuna maka wannan Nigeriar wa ka sani wa ya san ka ne ? To ai ka riski sakon daukaka kara ko? To kaima din ba tsira zakayi ba ko babu danganta ka sufi Kayi min haka ai sai na nuna maka fin da nayi maka bare ace uwar mu daya uban mu daya Kuma ina a matsayin yayan ka a kashe min abdulhameed amma kayi min wannan wulakancin har kana fadar ni zan biya Tara ba ni za a biya ba wallahi karya kake kayi wani motsi na saka maka ido na barka. kuma wallahi wannan yarinyar sai an kashe ta don na gama shirya komai daga abuja lahira zata zarce wallahi kaima don duk abinda ka gani ka zargi kanka don kar ka ga Abu daga sama ka wahalar da kanka tambayar yays akayi hakan?.
“Brothe banyi mamaki ba ko da na ga hakan na dan daga kaine. amma me ya sa kake amfani da karfin ikon da yake hannun ka wurin murde gaskiya alhalin ka san karya batayi kama da gaskiya ba ko da kuwa an canja mata suna? hakan fa ya kara fahimtar dani duniya kawai kake tunani ba ka tunanin goben ka shin in ka nuna karfin iko ka yi yadda kake so Ranar goben kuma me kake hange? Ina Abdulhameed a yau? na tabbatar da baka bashi mutuwa a yanzu ba sai gashi ya tafi bakayi tunanin Yana can yana girbar alherin shi ko muguntar sa ba? Shin kai wane garantin Rayuwa gare ka da har kake baje hajar ks duniya kana takama da madafun ikon ka,? shin bai ishe ka wa zi ba shekara takwas kana mulkar jihar nan da wa adin ka yayi aka ssuke ka? shin ka manta da Inna wa adallahi hakkan? to ni duk abinda ka ga damar yi min kayi ba daga kai nake kallon komai ba sai daga Allah don na san baka taya Allah komai a halitta ta ba brothe haka zanen kaddara ta ma baka san shi ba wallahi don da ka san shi tsakanin jiya zuwa yau da ka shafe babi na kuma bari na fads maka abinda kake kallo a matsayin wulakancin da kake fadar nayi maka ba dan ka ba ko kai ne brothe kayi abinda abdulhameed yayi haka zanyi maka wallahi kaje ka saka Mustafa ya kunna maka camera CCTV kaga irin atakin din da Abdulhameed yayiwa yarinyar nan . laifuka biyar Abdulhameed ya aikatawa yarinyar nan wanda kowane laifi daya mai zaman kanshi shi ne . ya sato ta ya kuma yi mata barazana da kafa mata wuka a makoshi ya kuma saka yan iska sun fincike mata kaya sun mayar da ita naked sannan ya keta haddin ta da karfin tsiya in kai akayiwa hakan meye ba zai faru ba? In yarka akayi wa hakan yaya zakaji? kwatsnta hakan akanka kaji yaya ake ji? Idan yarinyar nan bata soka mishi wuka ba ta Yaya zata kwaci kanta? don ina dan uwan ka sai na dannewa Mai hakki hakkin sa don kaji dadi? me zaka iya yi min a ranar da Ubangiji zai tambaye ni zaluncin da nayi ? A me kake a ranar da na tabbatar kaima ta kanka kake? to kar ka wahalar da kanka brothe dukkan abinda kaga ya same ni daga Allah ne ba daga kai ba zaka yarda dani idan kaga ina tsaye da kafafu na ba tare da na jingina da komai ba. ka kalle ni ka kuma kalli abdulhameed da ikon a hannun ka yake na tabbata da bai amsa sunan gawa ba in kuma zaka iya to naga kokarin ka a hurumin da zan yarda ka Kai a Nigeria.
Tatss ! Distinguish Mukhtar ya kifawa mai shari a sufi mari cike da wata irin fusata yana nuna shi da yatsar hannun shi manuniya.
“Ka manta da hannu na a bisa kai ka inda kake Sufi? ka manta banda ni baka Isa tako wannan matsayin ba ? nine a yau har lalacewa ta ta kai ka Karanta min wannan wulakancin? To nayi maka alkawarin barin wannan kujerar wallahi sai na sa an sauke ka don na nuna maka gaba nake da Kai.
Mai shari a Sufi yayi murmushi tamkar ba mari aka tartsa mishi ba ya dubi Yayan nashi distinguish Mukhtar.
“Babu hannun ka a cikin dukkan wani tagomashi da Ubangiji yayi min brother saboda na san ba ka Kai matsayin Wanda Allah zaiyi shawara da Kai ba ko bin ra ayin ka sai dai ban musu zaka iya zama sila ba. Ka fa gane brothe matukar babu numfashi na a hannun ka to ka yarda Allah ne mai tasrifin komai idan kuma kana yi to taso min Abdulhameed wanda na tabbatar da yafi kowa da komai soyuwa a gareka don haka matukar Kuma Babu wannan ikon a hannun ka to barwa Allah koman shi don haka ko ka zamo sanadin da na sauka daga judge to in sha Allah zaka ganni a wani wurin don haka komai yazo daga Allah a wuri na abin marabta ne brothe kuma Ina son kara tabbatar maka akida ta akan Aikin Shari a wallahi ko akan ka hukunci ya sauka sai na yanke shi matukar na gane manufa a kanka . haka kuma duk lalacewar mai gaskiya sai na tabbatar mishi da gaskiyar sa haka na zaba kuma haka zanyi don nafi tsoron Allah da son haduwa dashi babu datti . don haka bana tsoron wanda basu tsoron Allah a hukunci gaskiya daya ce a wuri na kuma bata neman ado ko gareni ko ga wani na zan so a tabbatar da ita a gurbin ta.
“Ni kake fadawa haka Sufi? Ni kake ciwa fuska don nazo gidan ka? Ni kake fadawa ko a kaina ne zaka tabbatar da shari a ? To ka tabbatar da ita akan wacce ka yanke yanzu kuma da na san hakan zakayi da ka gane Borno ba gabas take ba arewacin Nigeria take zaka san kayi dani Sufi.
Ya juya ya fice yana sababi da ganin rainin da aka yi mishi ya wuce misali.