Daddy ya kasa motsawa saboda ya gama Jin komai tunda a hands free ya yi maganar wacce akayi da harshen turanci
A Dole sukayi wa Alkalin godiya sukayi mishi sallama suka fito
Da suka koma can kotun don son ganin Kaisar ma ba a basu dama ba don ance babu shiga babu fita a inda yake sai dai suyi hakuri har zuwa ranar da za a futo da shi zuwa filin rataya.
Babu yadda daddyn ya iya dole alh Sule ya jawo mota suka taho daddy kam banda kuka babu abunda yake sai faman dauke kwallar idon sa yake Nadiya kuma tana mota babu abinda yake ranta irin masoyin ta show wanda duniya ta jirkita mata lissafi har suka dauki lokaci mai tsayi basu ji juna ba don haka babu abinda take son ji da gani sai shi da Kuma son jin ta rungume shi
Karfe takwas saura na dare suka iso bauci aka fara sauke su alh iro shi da yaya halilu da Nadiya slh Sule Kuma ya wuce gida
Haj Aliya da take cike da firgici tana ta fama kiran wayar mijin nata amma ta kasa kama shi haka ta wuni cike da firgici da tashin hankali har dare ta dora kiran wayar alh iro
tana cikin sallar Isha I ne taji shigowar shi don haka tana kare sallar ta fito inda ta soma kicibus da Nadiya abinda yayi matukar bata mamaki amma ganin halin da Daddy yake ciki ya shafe mata murnar dawowar Nadiyar.
ta matsa da sauri tana fadin
“Sannun ku da hanya daddy Ina nan cike da zullumi da tashin hankali sai kiran waya nake network Yana min yawo da hankali.
ta fada bayan ta bude fridge ta dauko ruwan sona mai sanyi da kofi ta nufi shi
ta tsurawa mijin nata ido ganin yanayin shi irin na wanda ya zubar da hawaye babu adadi.
“Me ya faru ne daddy? don Allah me ya faru? Ina Kaisar ne yaya kuma akayi da case din nata ?
Daddy ya kuma dauke kwallar idon sa yana fadin
“Aliya Ina cikin tashin hankali matuka gaya domin kuwa na gane bani da mataimaki sai Allah amma babu mai taimako a cikin mutane .
Hawaye suka kuma kawo mishi abinda Kuma ya Kara tada hankalin Haj Aliya.
“Menene wai daddy? don Allah ka fada min shin Ina Kaisar ne ?.
“Kaisar yana can Aliya ya fanshi Rayuwar Nadiya da tashi Rayuwar. Aliya Kaisar ya yi kirari a kasuwa ya dab’awa cikin sa wuka. Kaisar bai kyauta min ba Aliya da na san haka zata faru wallahi da ni ne nayi abinda Kaisar yay.
“Don girman Ubangiji Alh ka fidda ni duhu ta yaya Kaisar ya fanshi rayuwar Nadiya da tashi rayuwar? na kasa gane abinda kake nufi wallahi.
“To aliya Kaisar ya karyata Nadiya cewa ita tayi kisa ya amsa da shine ya kashe yaron nan dan gida Mukhtar Biro har da bayanin da ni ban san inda ya samo su ba har sukayi daidai da abunda ya fada . shine fa Mukhtar Biro yace hakikatan tunda ya boye yarinyar sai da yaji zan maye gurbin Nadiya ya fito da ita abin haushi shine Kaisar ya gasgata hakan har ma ya kara da cewa shine mai kisan Abdulhameed ba yarinyar nan ba. In takaice miki magana Aliya yanzu haka ranar rataye Kaisar kawai za a saka ganin shi ma a yanzu ba a bari Aliya naci amana idan har na bari akayi hakan amma na jaraba neman taimakon wasu manyan Alkalai tun a can Abuja amma an nuna min bakin Alkalami ya bushe .
Haj Aliya da ta dora duka hannuwan ta akan ta baki bude ta kasa cewa komai sai duban alh iro da take.
Sai kuma ta fashe da kuka tana fadin
“Inna lillahi wa inna ilaihir Raju un don Allah idona biyu ne ko kuwa mafarki nake ? da gaske ne wannan abun ?.
“Babu zancen mafarki Aliya abinda dai ya tsaya min a rai shine ta yaya yarinyar san ta san komai tayi shiru da bakin ta bata karyata yaron nan ba? A irin halaccin da yayi mata ina ganin kamar bai cancanci irin wanna muguwar sakayyar ba amma ta taho babu wanda tacewa Kaisar bai kyatawa kanshi ba ko kuma ta karya ta shi cewa bai san komai akan hakan ba amma kinga ta ma manta da babin shi ta shiga sabgarta.
“Haba daddy kai kuma sai ka kwaso ta ku dawo? Ai tun can ya kamata ka barta matukar dai bata ce babu ruwan Kaisar ba to wallahi sai dai s kashe su tare da Kaisar din amma maganar ta dawo taci gaba da Rayuwa wallahi bai taso ba ko dai ta wanke yaron can tace bai san komai ba ko kuma a hada su tare s Kashe nafi yards da hakan.
Daddy yayi shuru yana tunanin matar tashi a nan kam ya zarce na mazan da ake cewa sunfi mata nazari . Abinda ya kamata kenan sai dai a kashe Kaisar da Nadiya kamar yadda tare suka Yi tarayya a zuwa gidan distinguish Mukhtar Biro.
“Haka ne Aliya kira min ita yanzu naji ra ayin ta don na gane a me take kallon wautar Kaisar.
Da sauri mama ta mike ta wuce dakin nasu inda ta samu Nadiya ta sheko wanka tana gaban mirror tana kwalliyar tafiya wurin show fati kuma tana ta jera mata kayan tarba tare da tarin tambayoyin yadda Al amura suka wanzu tana bawa fatin amsa musamman akan zaman ta gwarunfa da irin ukubar da ta sha na matan bursuna wanda tayiwa bauta kuma bata barranta daga mugun dukan da suke lakada mata ba.
Mama ta shigo tana yiwa Nadiya wani shegen kallo kafin tace
“Zo daddy yana kira
Ta mike tana fadin
“Shi fa daddy ya san inda nake son zuwa ? wallahi hankali na wurin my love my show.
Daddy ya dube ta ta caba kwalliya alamar babu damuwar komai a tare da ita.
“A me kika dauki abinda Kaisar yayi? me yasa kikayi shiru da bakin ki lokacin da ya furta shi ne ya kashe abdulhameed? me yasa baki karyata shi ba? kuma kika yarda k inika taho har gashi kina caba kwalliya alamar wani wuri ma kike shirin fita shin da gaske ne abinda Kaisar ya fada shine ya kashe yaron nan ba ke ba ce? A me kika dauki hakan da yayi? Ko bai fada ba na san dawainiyar da yayi miki tun a zama sarkar nan garin bare kuma shige da ficen da yayi na daukar miki lauya shin ke me kike shirin yi mishi na irin wannan alherin da yayi miki shima gashi a yau yana neman irin wannan taimakon a me kike shirin rama alherin shi da alheri ko kuwa sharrin dan adam din zamani?
Nadiya ta kwabe baki tana fadin
“Daddy nifa ban ce yayi abinda yayi ba kuma ya fadi haka a gaban alkali me zance ? kuma fa ni dama ina ta mamakin yadda akayi nayi kisan nan sai nake ganin kamar ni kamar ba ni ba na san dai na dauki wukar nan amma ban san yadda na soka ta ba kaga Allah ya matsi bakin sa ya fada ni kuma Allah ya fidda ni .
Daddy yayi murmushi yana fadin
“Amma kuwa kyan dan halal ya nuna halacci Nadiya nasan Kaisar yayi miki abinda ni banyi miki shi ba ko a zaryar zuwa duba ki da daukar miki Lauya duk yaron nan shi yayi na Kuma san kin san hakan.
“Ni fa Daddy ban ce yayi ba shi yaji ya gani ni kuma Daddy da me zan biya shi ? Ai sai dai nayi mishi ADDU AR Allah ya bashi mafita irin wacce ya bani kawai.
Ta juya ta koma daki Daddy da mama suka bita da kallo mama rike da baki ta kasa cewa komai Daddy kam wani Abu mai kama da nadama yake a yau domin kuwa ya gane Nadiya babu daya da zata nuna a waje Wanda za a yaba musu sai ma zagi da kushe da take shirin bar musu
Haka Nadiya ta fice daga gidan ta isa studion show wanda ya rungume ta yana kissing din ta yana tambayar abubuwan da suka faru tana bashi amsa suna rungume da juna inda ake ta shan soyayya har goma da rabi kafin ta dawo gida mama da Daddy kam basu iya kai kafada k’asa da sunan bacci ba . daddy dai yana zaune gefen gado yana lissafin Al amarin da ya faru akan Kaisar. mama ce ma ta daura alwala tana nafila da kai mishi kukan ta da nemawa Kaisar mafita a wurin Allah
Fati kam kad’an ya rage ta zauce samun labarin da mama ta fada mata akan siyar da Rayuwar da Kaisar yayi yace shine yayi kisan ba Nadiya ba.
tashin hankalin da fati ta sami kanta ba kadan bane don tana ganin idan Kaisar ya rasa Rayuwar sa to ba shi kadai ya mutu ba itace wacce zata mutu fiye da shi.
A ranar kam fati ta kwana kuka domin ta kasa sirrin ta abinda yake zuciyar ta . don haka su mama da daddy tasu damuwar kawai suka sani amma fati tace musu salamun salamun
Kwanaki biyu Al ummar gidan iro GIDAN KUDI na cikin tashin hankali da tsaka mai wuya amma fa banda Nadia wacce bat san suna yi ba inda mama ta matsa da son zuwa Abuja don ta gano halin da Kaisar Yake ciki Daddy kam ya yankar musu tikitin jirgi suka nufi Abuja tare da fati da tayiwa daddy magiya ya kuma yarda suka bar Nadiya s gida babu ko a gaishe shi bare wani sako.
*****
Ranar da aka kai Kaisar gidan sarkar da yake gwarunfa hankalin sa a kwance babu nadama bare da na sani tamkar yana a gida
Dakin da aka saka shi shi kadai yake ciki babu kowa saboda hukuncin sa ba mai dogon zama bane ya jima da yaws yayi sati daya shiyasa ake ware irin su a daki daya don in aka hada su da wasu to in aka dace da muguye har kisa sunayi saboda sun san tasu ta kare shiyasa ake ware su wuri daban don gudun ta adi
Yana zaune cikin dakin wanda akayiwa dakin kyaure da san dunan rodi ba kamar kyaure shiyasa na ciki yana iya hango na waje amma na waje ba zai iya hango na ciki ba saboda duhun dakin wanda ko tafin hannu ba zai ganu ba matukar ba da fitila aka shigo ba
Dare yayi duhu ya kara mamayar dakin yayin da sauro ya soma cin kasuwa a saman jikin shi da son ya zaki jinin shi ya more
Ba wannan ne abinda yafi damun Kaisar ba irin sallolin da suka wuce shi bai yi su kamar la asar da magaruba ga Isha I tana tahowa. babu abunda yafi bukata a yanzu irin ruwan alwala amma bai ji motsin mutum a kusa ba sai can yake jiyo hayaniyar muryoyin bursu suna shewar su da harkokin su.
Har wurin goman dare baiji motsin kowa ba ya koma ya zauna idan har akwai wani Abu da ya dame shi s yanzu to na Rashin sauke farali ne sai ya koma ya zauna cike da damuwar hada sallolin nan sai kawai ya soma tilawar Al kur Ani yana maraja a yana daga sauti tamkar dai ya bude Al kur anin.
Ya jima yana karatun kafin yaga an doso shi da butar ruwa wanda ke rike da butar kuma yana rike da wata fitila mai hsske wacce bai san ko wace irin ce ba don bai tab’a ganin irin ta ba.
“Allazi wahidun Allah da GIRMA yake.
Muryar ta doki konnen Kaisar wanda a take ya gane dattijon nan ne mai bara Wanda Nadiya ta mara .
Cike da mamaki da zullumi Kaisar ya mike cike da tsoro don ya gane tsohon nan ba mutum bane tunda har ya iya keto inda babu mai shiga.
“Kar kaji tsoro dan samari kaji ? karbi ruwa kayi alwala kayi salla sai dai in da kake babu tsarki ko zan kaika inda ke da tsarki kayi sallar ?
Ya fada yana kallon fuskar Kaisar wacce hasken fitilar da take hannun shi ta haske dakin har ya bashi damar gamin tsohon wanda yake kallon shi ya kuma ga rashin tsarkin da dakin yake da shi don har da tutu kashi kashi ga rashin tsabtar dakin babu shara babu kintsi.
“Kar kaji tsoro Dana nima ana Muslim mun kuma hadu babu mugunta a tsakanin mu sai alheri to yi alwalar ga wurin salla nan
Ya fada yana ajiye mishi butar wacce take ta walkiya tamkar tasa kamar kuma butar karfe
Kaisar ya karba jiki a sanyaye yayi alwala ya mika mishi butar yana fadin ya gode.
“To taho nan kayi sallar
ya fada yana rike hannun Kaisar tamkar zai fito dashi daga daki sai gashi a cikin wani tangamemen masallaci mai dauke da fitulu tarwai da shimfidadden kafet layi layi ga alkibla wacce aka kawata fankoki suna ta wulwulawa yayin da mutane dai daiku suke jefi jefi zaune a masallacin wasu na jan carbi wasu kuma sun bude Al kur ani suna karatu
tsoro ya kara kama Kaisar amma sai ya ji kyakkyawan zato ga Allah wanda ya haramta zalunci akan sa ya kuma sanya shi haram a tsakanin bayi . ya tuna da maganar dattijon nan wanda ya ke fada mishi sun hadu a ciki alheri ba mugunta ba .
Ya tayar da ikima ya tada sallah har yayi ramakon sallar ya gama ya zauna yaja carbi wacce ya gani a dab da shi tare da Al kur Ani wai girma ya kuma soma kalle masallacin wanda ya tabbatar da Allah ne kadai ya san ko wace shiyya ce wata kil ma ba yankin mutane ba
A can ya hango tsohon nan rike da Al kur ani yana tarjama inda hankalin Kaisar ya kara kwanciya.
Ya soma tuna haduwar su da tsohon nan wacce ta zamo sau uku . haduwar farko a gefen titi ya bashi sadaka. haduwa ta biyu kuma shigowar shi gidan lokacin da Nadiya ta mare shi sai haduwar karshe wacce suka hadu wurin mai saida nama sunje shi da king wurin wani fitaccen mai nama a garin bauci saboda ya iya gasa nama inda Kaisar ya hangi tsohon gefe daya yana Fadin
“Allazi wahidun Allah da GIRMA yake . Kaisar ya juyo ya kalle shi ya mika dubu biyu aka nad’o naman ya kai mishi . shikenan haduwar su uku
a rayuwa amma gashi a yau cikin rayuwar sa.
Ya sauke ajiyar zuciya yana rokon Ubangiji da sunan shi Al hayyu Al kayyumu tare da ADDU oi masu yawa ya shafa ya ja Al kur anin da yake dab da shi ya bude yana tarjama har ya kare ya rufe yana shafa ADDU A.
yana gamawa ya ajiye Al kur anin yaga dattijon nan yana nufo Shi ya ce .
“Ka gama ko?
ya amsa da Eh
ya Kama hannun shi kamar yadda yayi mishi a farko sai gasu a cikin inda yaxo ya dauke shi yana fadin
“An dan gyara maka wurin har da shimfida kuma zaka iya yin sallar ka ga abinci nan an ajiye maka zan dawo na sanar maka wani Abu amma dai kar ka gaji da Rokon Allah tare da ADDU A amma kuma zan fada maka kayi wauta akan abinda kayi zan tafi sai Allah ya dawo dani amma dai ina kara jaddada maka kayi ADDU A ka roki Allah don Allah shine allazi wahidun.
Bai bashi damar cewa komai ba ya juya ya soma tafiya har ya bacewa ganin shi.