Su uku suka nufo ta da sauri ta juya tana fadin
“Don Allah ku duba min nan kamar naga jijiyar wuyan tana motsawa.
Ta fada a rikice tana tab’a wurin a wuyan Abdulhameed.
Daya daga cikin masu tsaron kofar ya fada a ranshi cewa matar nan fa tana dab da ta haukace sai kace akan danta aka soma mutuwa kullum tana kwakwufe da gawa kenan tana son nuna mana danta bai mutu ba kenan? duk mutanen da suka rasa ahalin su uwa ko uba ko dangi duk basu san kaddara ba kenan sai ita?
Yana tsaye yana mita a zuciyar sa don ta fili dai ta fi karfin sa don ya san ko wacece ita da ganin ta kuma ya san ba zata yi kara ko alkunya ba.
Wani daga cikin wanda suke tab’a wuyan Abdulhameed da take nunawa ya ji harbawar jijiyar ya kuma dube ta yana fadin
“Hakika ranki ya dade naji kamar akwai motsin jijiyar wuyan nan .
ta zabura tana fadin
“Don Allah duba min da kyau yana numfashi? bai mutu ba? taimaka min don Allah shi kadai gareni
ta fada cike da doki da son ganin abdulhameed ya motsa
Su duka suka rufu a kan gawar abdulhameed suna tattaba jikin shi wuyan shi da gurbin zuciyar shi da kuma sangalalin hannun sa wanda nan ma sunji jijiyar wurin tana harbawar.
Kan kace me? sai ga likitoci sun karaso suna duba gawar abdulhameed wanda alamu suka tabbatar da sauran ruhi a jikin shi .
Haj laila da ta gama rudewa ta soma aunawa mijin ta kira babu kakkautawa yayin da shi kuma yana can yana fafutukar ganin an bi mishi kadin jinin dan shi Abdulhameed an kuma sauke haddi akan yar gidan alh iro GIDAN KUDI kafin Al amarin ya juye ya koma ga dan gidan iron wanda ya amsa shine da alhakin kisan
Kan kace me? aka gano Abdulhameed da ruhi a jikin sa ai kuwa babu jimawa haj laila ta dauki passport ta nemi visa urgently ta kuma samu nan da nan tayi nufin ficewa ingila a duba mata yaron ta wanda take ganin ingilar ne kawai suke da likitocin da zasu tayar da Abdulhameed din
tuni kuwa jirgin ya nutsa a samaniya tare da haj laila da Mustafa Tero wanda ta kira ta sanarwa sai wani hadimin gidan nasu mai suna bashir saboda su taimaka mata wurin hidimar abdulhameed din
*****
Nadiya ta shigo falon tana fadin
“Daddy kana kira ?
ya amsa da
“Eh Ina so ki hada kayan ki zaki wuce can jama are wurin halima .
“Ni fa daddy ka san ba son kauyen nan nake ba wallahi komai na gidan su yakumbo hali irin na talauci da tsiya ne ga matar nan Allah ya zuba mata masifa tamkar ba musulma ba ni kuma bana son zagi ita kuma ta iya wulakanci kamar bamagujiya gaskiya daddy ba zanje ba gidan matar nan in ma wani sako ne gara ka bawa malam Ango ya kai mata don in kam idan ka matsa akan naje danyen aiki za ayi don zan biye mata mu fasa tangararen bala I ne.
“Kin kuwa san wacece Halima Nadiya? kanwar Aliya ce kike neman zagin ta saboda baki da mutunci?.
“To Daddy don tana kanwar mama sai tayi ta mana wulakanci? .
“Ke shiga hankalin ki wallahi to albishir din ki ma ? can jama aren zaki koma d zama don ni wallahi ba zan iya zama da ke ba Nadiya tunda kikayiwa Kaisar silar rayuwar sa naji kin fita a raina dama ai na fada miki ban baki a rufe ba cewaar nafi son Kaisar da ke don haka ki tafi jama are can ki zauna da misau ma zan kai ki Amma na gane idan na kai ki misau fitina na kaiwa dan uwa na gara ki zauna wurin Halima in naso ganin ki zamu zo mu ganki.
A rikice Nadiya take kallon Daddy tana fadin
“Daddy? akan Kaisar din kayi min haka? daddy har ka fi son Kaisar da ni ? daddy waye wannan Kaisar din da kuma irin bajintar da yayi maka har kake fifita shi a tsakanin mu? Daddy ko kana neman maza ne kake neman wannan tsinannen Kaisar din ? ni dai ban san shi a cikin ahalin mu ba ko mai kama da shi ban sani ba amma daddy har kake cewa kafi son shi da ni yar cikin ka?.
Wani murmushi mai ciwo daddy jin maganar da yarinyar nan take furta mishi na danganta shi da neman maza har tana zargin ko neman Kaisar din yake.
Kafin yace wani abu yaji Haj Aliya ta gaurawa Nadiya mari ta sake maka mata wani marin tana fadin
“Wannan yarinyar daddy babu .
Da sauri daddy ya dakatar da ita ta hanyar daga mata hannu.
“Kar kice komai Aliya Barta na bata amsa yi hakuri kar ki furta ki zubar da ladar ki.
Ya dubi Nadiya yana fadin
“Da ace kinyi min wannan tambayar kafin yau Nadiya da na baki amsar ki amma a yanzu lokaci ya kure kin kuma makara amma zan baki amsa daya shine bana neman maza bare n nemi Kaisar kike kyautatawa mutane zaton alheri. abu daya nake so ki gane shine nafi son Kaisar da ke ki rike wannan hakan da nayi miki na maida rayuwar ki gaba daya a kauye shine zai tabbatar miki da lallai nafi son Kaisar da ke duk da kuwa baya doron duniya. Nadiya ban tab’a ganin butulu a duniya ba irin ki naso ace akwai sauran aminci a duniya ko da kuwa baki san shi ba baki tab’a yin sa ba na zaci zaki yiwa Kaisar. ban zaci mugun halin ki ya kai haka ba zuciyar ki babu Allah da manzon Allah a cikin ta Nadiya. shiyasa nake fada Miki Kaisar ya fi min ke sau fin a kirga duk da baya duniya kasar kabarin shi ta fiye min ke zaki gane hakan ta yadda na nemi nayi nesa da ke na mayar da ke jama are ta haka zaki gane fin da Kaisar yayi miki ba na kusa bane ba don ba don ba Nadiya da nace miki wani abu amma kije ki tuhumi kanki akan abinda nake fada miki. naji zafi mtuka da kika yi gum da bakin ki a lokacin da yaron nan ya nemi fansar da rayuwar sa akn taki . na zaci ko baki san aminci da alheri ba zaki gane Kaisar ya yi miki su ko da kuwa sun kare a duniya amma nasha mamaki da kika budi baki kika ce ba ke kika saka shi ba shi ya ji ya gani Nadiya tun daga wannan ranar kika fice min a rai har naji da ma ke na rasa ba Kaisar ba don haka na gaji da zama da ke a gida daya gidan da babu Kaisar a ciki Ina son ki tafi jama are yadda mutuwa ta shata shata tazara mai tsayi tsakani na da Kaisar haka nake son rayuwa ta shata tazara mai tsayi tsakani na da ke Kaisar yana a hannun dama ta ke kuma kina a hannun hagu. ki rike wannan a ranki ba don ba don ba da nace miki wani abu amma Allah yana a tsakanin mu don haka kar ki wahalar da kanki wurin laluben dalilin da yasa na maida ki jama are don son nayi nesa da ke don haka idan kin shirya malam Ango yana zai kai ki kar kuma ki sake kizo min gida sai da rubutaccen izini ko ki kira ni kafin kizo bana son kizo ba tare da na san zaki zo ba. a can na mayar da zaman ki da rayuwar ki ko ki gyara rayuwar ki ko kara tuburewa duka ruwan ki amma ni da ke kam sai a jama are ba dai a nan ba tunda duk duniya Nadiya idan akwai wani mutumin da yayi min sanadin bak’in cikin da ba zan yafe shi ba to kece dole kuma nayi hannun riga da ke. da tun farko kin tambaye ni waye Kaisar da na baki labari kuma da abinda kikayi da bakiyi shi ba amma s yanzun da kika yi min sanadin rayuwar sa to na yanke alaka da ke Ina fatan nima zaki yankee ta tsakani na da ke !.
Hawaye ya gama wanke fuskar Nadiya ta zubawa daddy ido kafin ta dubi haj Aliya tana fadin
“Mama kinji abinda Daddy yake fada min ? .
“Nima irin shi zan fada miki koma wanda yafi shi d’aci da ciwo. bana son azzalumi a rayuwa ta Nadiya sai na gane ke azzaluma ce . haka Kuma bana son mutum butulu mai butulci sai na gane ke uwar masu butulci ce ! naji a raina zan iya shanye kowane irin halin ki In kuma yafe miki amma banda abinda kikayi wa Kaisar wannan kam Ina Taya shi neman kadin rayuwar sa don wallahi nafi ganin bak’in ki akan wanda sukayi hanging din sa don haka ni kam maukar muna gida daya da ke to zuciya babu k’ashi wata rana za ayi mugun aiki nace jinin Kaisar nabi kadi gara kawai ki tafi jama aren ki zauna s can ki kuma rungumi rayuwar da kika gani .
Jiki a sanyaye fuska shar kaf da hawaye Nadiya ta mike ta shiga daki tana jawo akwatun kayan ta ta loda har bata san abinda take sakawa ba yayin da fati ke kuka tana alhinin rabuwa da Nadiya duk da ba wani dadin zama da ita take ji ba
Babu abinda ke ran Nadiya sai haushin su daddy da mama da take ji akan fifikon da suka nuna mata akan Kaisar tana jin koma kawai tayi tafiyar ta ?
Fauuui ta fice bata kuma bi ta kan su daddy ba bare tayi musu sallama babu abinda take ji nasu sai haushi da takaici
Malam Ango ya taso da sauri ya karbi trolley din ta ya saka mota ta shiga motar tana cije lebe tana ta faman sakawa da warwarewa har malam Ango ya bude motar ya shiga ya kuma ja suka bar gidan inda take cewa malam Ango
“Kaini studion show ka aje ni a can kayi tafiyar ka.
“Mai gida yace kar mu tsaya ko ina sai gidan Halima a jama are don haka kiyi hakuri.
“Kai malam Ango uwar wa kake fadawa hakan ? baka san ko da wa kake magana bane ? da Allah sauke bi a nan nace banza da kai dabba.
ta soma zagin malam Ango amma yayi kamar Bai ji abinda take fada ba sai auna Uban gudu yake a saman hanya
tayi ta zagin shi amma Bai ko juyo ba yaci gaba da tafiya har ta gaji da zage zagen ta tayi shiru tana hararen shi ta mirror
tafiya mai nisa har suka iso kauyen suka kuma dauki wata hanyar wacce itama sunyi tafiya mai tsayi kafin suka iso kofar gidan yakumbo hali wacce mijin ta ya jima da rasuwa take zaune a gidan ta ita daya tana Sana ar kuli kuli da Koko da kosai da safe don haka gidan yakumbo ali dawan dawan yake da maiko saboda kayan maikon da take mu amulan ta shiyasa duk lokacin da Nadiya zata zo gidan cike take da kyankyamin gidan tun ya kumbo hali bata gane yarinyar ba har ta gane ko abinci aka Bata bats ci sai tayi ta tsirtar da yawu. Ai kuwa Yakumbo na gane abinda Nadiya take nufi ta Kama ta ta Zane ta tas da zabori . Tun daga nan kuwa aka shiga wata irin tsama tsakanin Nadiya da yakumbo hali wacce take cewa tafi son Fati akan Nadiya tsakaninta da Nadiya sai zare ido sai gashi a yau zama ya kawo Nadiya gidan da take tsirtar da yawu zama kuma na dindindin
Malam Ango ne ya fito yana daukar akwatin kayan Nadiya ya shiga da shi cikin gidan yakumbo hali wacce take amsa sallamar malam Ango tana fadin
“Kai malam Ango amma kunyi sauri gaskiya sannun ku da hanya alamar ta san da zuwan kenan.
Ya amsa yana aje akwatin Nadiya suna gaisawa da yakumbo hali Nadiya kuma ta coge a bakin kofa. yakumbo ta mike tana zubowa malam Ango zazafe na tuwon dawa miyar kuka wanda ta hade shi da miyar ta dafe ya kuwa gyara zama yana warba loma
Sai da ya gama ne ya ke bawa yakumbo sakon daddy na kudi wanda yace a kawowa Halima yana fadin
“Gashi mai gida yace a kawo miki kuma ki karbe wayar da take hannun Nadiya kar ki bari take fita ko kofar gida haka ma aiki kowane ki saka ta kuma kar taxo gida shi zai zo ya duba ta duk kuma laifin da tayi ki hukunta ta ya baki wannan damar.
Yakumbo ta karbi kudin tana fadin
“Ai kuwa ko bai ce ba malam Ango yaushe ake barin yaro ya sangarta? duk da dai laifin su ne da suka bar yarinyar nan ta k’ek’ashe to ni dama ai wasa ma wuri gare shi dama yaushe ake sakin yaro sasakai ? ai yaro ko ba nawa bane ina mishi tarbiya kuma tarbiyar yanzu sai suna ji a jikin su ko za a zauna lafiya ni fa wuri na ai rashin jini ne rashin tsagawa cin uban mutum nake lada waje suma ai su suka sangarta yarinyar nan tuni kuma nake fada musu sune zasu ji a jikin su gashi kuma yanzu mai gari ya wayar musu? yarinya ko kamar wanna ace ta iya kisan kai?
Malam Ango dai sai cewa Yake
“Allah ya kyauta .
Ya kumbo ta waro dubu biyu a cikin kudin ta bashi sukayi sallama ya fice yana yiwa Nadiya sallama amma tana cike da tsoro akan abinda taji malam Ango na fadi wanda daddy yace a karbe mata waya a hana ta fita a kuma sakata aiki kowane iri inda ta gane anyi nufin wulakanta ta. bata tsinke da hakan ba sai da yakumbo ta karbe mata waya ta kuma bata aikin surfe da wankin waken kosan ta.
Jirgin saman mallakin k’asar US da yayi dakon haj laila da su mustafa Tero ya sauke su a babban birnin k’asar amurka wato washing tone a babbar Asibitin mafi daraja da tsada wacce ta karbi mutum mutumin Abdulhameed ta shiga check up din sa ciki da bai har ta gano matsalar ta shi ta yankewar jijiyar sadar da sako mai karfi wacce ta ratso ta gefen cikin shi
Abu ga k’asar da ta Jima da samun ci gaba mai yawa tuni kuwa aka shiga kanikancin rayuwar abdulhameed da son ganin an dawo da lafiyar Abdulhameed Mukhtar Biro bisa doka da oder
Tuni suka gane matsalar Abdulhameed wacce aka soma da yi mishi allurai da kuma jona mishi jini don yana daga cikin abinda yaja shi doguwar sumar wato jinin da ya zubar fiye da kima
Akayi ta jona mishi Robobin jini da an cire wata za a jona wata tare da allurai masu kyau da tsada tare da karfi
A cikin kwana daya da wuni sai ga numfashin Abdulhameed ya soma hawa da sauka duk da dai bai san abinda ke faruwa ba amma dai alamun nasara suna ta bayyana.