Skip to content
Part 32 of 33 in the Series Azurfa Da Zinari by Hadiza Gidan Iko

“Allazee wahidun Allah da girma yake ! Kalmar ta shiga kunnen Kaisar da yake kwance  a saman shimfidar wacce ya dawo ya iske bayan tsohon ya maido shi daga masallacin da ya kaishi wanda bai san ko a wacce shiyyar bane

Ya tashi zaune inda ya hango tsohon rike da fitilar sa mai shegen haske.

“yi hakuri dan samari na tayar da kai daga bacci ko?.

“A a baba ba bacci nake ba.

cewar Kaisar

“Har nayi nisa naji suna maganar kashe ka a gobe shine na dawo don alheri ne ya hada mu da Kai ba mugunta ba kuma yaron da ake son kisan saboda shi bai mutu ba yana can a raye zai bayyana koda ya mutu ma nayi nufin rama maka alherin ka da alheri don haka sammako zasu yi suzo su tafi da kai filin kisa shiyasa nazo na taimaka maka ungo buta yi alwala kayi salla koda raka A biyu ce ga Al kur ani shima ka karanta ko Aya biyu ce .

Mamakin bai wani kama Kaisar ba tunda ya gama gane dattijon ba mutum bane don haka babu mamaki idan ya san abinda wasu suke ciki a yanzu

Hasken fitilar dattijon ta haskake dakin gaba daya inda Kaisar ya yi alwala ya tayar da salla yayi raka a biyu ya roki Allah alherin da yake hannun sa a cikin sujudar sa ya gama  ya sallame ya bude Al kur ani yana  karatu har dab da asubahi ya sake jin muryar tsohon yana fadin

“Kwanta kayi barcin ka in kuma baka jin baccin zauna ka yi tasbihi da salati ga  shugaba mai cikakkiyar daraja ka saka ni a cikin ADDU AR ka .

Kaisar ya amsa da

“Na am baba in sha Allah

yana zaune yana jan carbi har garin yayi shaa inda yaji an shigo ana tashin motar gingimari irin mai kofar nan daga sama mai kalar kayan gidan yarin wacce ake dauko mai laifi ko mika shi inda za a mika shi da ita

yana zaune ya sake jin Amon sautin dattijon yana fadin

“Yi zaman ka kar ka matsa ko sun shigo ba zasu ganka ba amma zasu dauki mutum mutumin inuwar ka suje su Rataye suna fadar sun Rataye ka .

Ai kuwa ba a rufe minti sha biyar ba Kaisar yaji ana abude kofar rodikan wacce take zarge da sarkar karfe wacce aka Ratayo kwado aka datse

yana kallo mutum uku suka shigo suna haska fitila amma abin mamaki sai yaga sun haska wani wuri a cikin dakin yayin da mutane biyu suka kama wani abu mai kamar mutum mutumi suka wuce dashi suna rike da shi su biyu sunyi kama kama shi kywa wanda ya bude kofar ya tsaya maida sarkar kwadon ya datse ya juya da sauri ya bi bayan su

Kaisar ya juyo inda yaji sautin dattijon yana fadin

“Zaka so ganin inda zasu da mutum mutumin inuwar ka d’ana? In kana son ganin kudirin da suke nufi yi maka sai muje ka gani in kuma baka son gani shikenan.

“Zanso na gani baba amma baba wace irin godiya zanyi maka da ka yi min wannan alherin? .

“Kar ka damu dana sakamakon alheri alheri ne duk da ni bana saka sharri da sharri da Ina saka sharri da sharri da yarinyar nan ta gidan iro bata kawo kamar yanzu ba duk da gata can ma iron ya bada ita zuwa kauyen jama are inda zata zauna a can ya kuma ce baya son ta saboda abinda tayi maka .

“Kauye baba ?

“Kwarai kuwa gata can za a kaita gidan kanwar uwar ta a jama are amma abinda nake son fada maka kabi a hankali kar ka bari so ya rufe maka Ido  duk da akwai al amari mai girma tsakanin kai da yarinyar can amma kayi a hankali shaidaniya ce .

“to baba nagode Allah ya kara girma.

“Babu komai yaro muje gashi can zasu Rataye inuwar ka da muka bar musu muje ka gani

ya kama hannun Kaisar tamkar zai fito da shi daga dakin sai kawai Kaisar ya gansu a kan wata bishiya inda ya hango daddy da fati sai mama wanda mota ta ajiye ya kuma ga yadda akayi ratayar har zuwa lokacin da su daddy suka bar wurin

ya jima a saman bishiyar har dare inda dattijon ya zo ya ke fada mishi a nan mutum mutumin zai kwana a Rataye har sai ya kwana a rataye ne ake dauke shi ko a kai mutuware jiran yan uwa ko kuma su binne in babu wanda ya biyo sawu

Kwana biyu Kaisar a cikin wata alkarya wacce ya tabbatar da ba ta bil adama bace amma fa shi bai ga abu daya na tsoro da tsoratarwa ba illa yana ganin mutane masu irin suffar sa amma a idon sa ne hakan amma babu bil Adama a ciki sai don tsohon da ya kawo shi ya kawo shi ne ba don ya zauna ba kuma ana ganin kimar sa

A ranar da ya cika kwana biyu ne dattijon yake fada mishi zai koma gida amma ya barwa cikin sa al amarin da ya faru in kuma ya so zai iya fadawa yardaddun sa irin uban rikon sa da matar sa koma wanda ya aminta da su  a nan ne tsohon ke fada mishi alh iro yana gadon asibiti babu lafiya duk don saboda damuwar da ya saka a ranshi

Damuwa ta bayyana a fuskar Kaisar jin daddy yana gadon asibiti.

“Nogode baba yanzu sai yaushe kuma zamu sake haduwa?

“kar ka damu dana zamu kasance  in sha Allah kamar yadda yayi ta hada mu ungo maganin nan ka baiwa uban rikon ka in sha Allah zai samu saukin ciwon zuciya Allah ya sada mu da alheri sai wata rana !

ya rike hannun Kaisar sai ga Kaisar a kofar sashin sa a cikin gidan Alh iro

ya jima bai iya motsawa ba inda yaji gidan tsit duk suna asibiti yayin da Nadiya take can jama are

ya jima a bakin kofar kafin ya tura ya shiga komai yana nan inda ya barshi hatta da wayar shi tana nan sai dai cajin da ya sauka

ya zauna yana tunanin wane asibiti ne aka kai daddy? bai sani ba dole ya mike don ya je ya tambaye su maccid’o

Ya fito ya tunkaro su inda maccid’o ya zuba mishi ido yana mamakin yaushe ya shigo bai sani ba ? don ba kowa ne ya san fansar da rayuwar da Kaisar yayi ba shi kuma daddy bai yayata zancen ba saboda baya ma cikin kwanciyar hankali bare  har  su san yaci haddi shiyasa basu wani ji mamaki ba

ya mika musu hannu sukayi musabaha da maccid’o yana tambayar wane asibiti daddy yake? zubairu ne yayi maza yana fadin

“Yallabai baka je bane halan? Ai yana can asibitin kwararru ne yallabai ni kwana biyu ma Ina ka shige ko kana kasar waje?

Kaisar yayi murmushi yana fadin

“Bana nan ne zubairu bari naje sai na dawo.

Ranar da daddy ya cika sati biyu ne a asibiti jiki yayi kyau sai dai jini ya sauka amma yana fama da kasawar zuciya wanda a yanzu shine matsalar duk da shima ana tayi dai

A ranar ne kuma Daddy ya samu sallama sai dai sati sati zai rika zuwa check up

A ranar ne kuma yakumbo hali ta shirya musu  zuwa bauci dubiyar alh iro inda ta ce Nadiya ta shirya su taho tare ta duba alh iro abinda kuma ba haka Nadiya ta so ba taso ace yakumbo ta taho ita kadai itama ta samu ta  samfe sai gashi yakumbo ta roshe mata bajet babu kuma damar tayi gardama don ba ayiwa yakumbo gardama in kuma mutum yana son wulakanci mai kalar ruwan hoda to yayi mata gardama don haka babu ja Nadiya ta biyo bayan yakumbo suka iso bauci kai tsaye aka sauke su a asibitin kwararru

Yakumbo tana gaban alh iro tana ta mishi sannu da ADDU AR samun sauki inda ta taho mishi da wainar kosai mai kyau ta kuma zubo ta a kula mai rike zafi don ta san yana son wainar kosai sosai ai kuwa ya yaba da wainar nan .

Nadiya tunda ta shigo ta gaida daddy da mama bata sake cewa ko ya mai jiki ba

fati ce ma take tambayar ta jama are da mutanen can amma tayiwa fatin wani shegen kallo tana jan tsaki tana fadin

“Da Allah ni rufa min baki munafukai kawai ai ni wallahi na rufe ku ku duka mutanen gidan nan na jefar da dan makullin a kogin maliya tunda babu mai sona a gidan nan nima bana son kowa wallahi banki ma uban kowa ya mace ba.

“Ke me kike fada ?

cewar yakumbo wacce taji abinda Nadiya ke fada.

Da sauri Nadiya ta kame bakin ta don ta san yanzu ne yakumbo zata wulakanta ta

Daddy da yake cin wainar kosai yana murmushi yake duban Nadiya mama ma bata tanka mata ba sai fa yakumbo wacce ta balbale Nadiya da masifa tamkar zata make ta.

“Ai an ma sallame mu Halima yanzu ne zamu wuce gida kuma ga kudin mota ku wuce da ke kadai ce  sai nace mu wuce gidan amma tunda tare da yarinyar nan kuke tafe kawai ku koma gida na gode Allah ya kara zumunci.

Nadiya ta soma share hawaye tana fadin

“Daddy akwai kayan da zan dauka a gida fa?.

“Kije malam Ango zai kawo miki koman ki can .

cewar Daddy inda yakumbo ta mike tana fadin

“Wannan yarinyar kun b’ata ta da yawa yaya Aliya ni har ta Isa tayi min wannan wulakancin? kin tashi mun tafi ko kuwa?

Da sauri Nadiya ta mike tana share hawaye yakumbo tace

“Me kike nufi da muka zo banga kin duba marar lafiya ba bare kiyi mishi ADDU A? haka kawai zan sako ki gaba sundum sundum sai kace rakuma?.

Nadiya ta koma ga Daddy tana fadin

“Allah ya kara sauki .

daga haka bata kuma cewa komai bare tayiwa mama sallama ta fice yakumbo ta bi bayan ta suka fice

Suna tafiya daddy ya kira alh Sule ya fada mishi an Basu sallama nan da nan kuwa yazo ya kwashe su a mota suka bar asibitin

Suna tafiya mashin na sauke Kaisar ya shiga ciki yana tambayar dakin da alh iro yake inda likitan ne ya bashi tabbaccin yanzu suka bar asibitin ya sami sallama don haka  ya juyo zuwa gida

Da fati suka fara cin karo a gida  wacce taja tayi turus tana kallon shi da wani irin tsoro ta zuba mishi ido shima ya zuba mata ido ya soma takawa da nufin zuwa inda take amma zuciyar ta a dake take kallon shi inda ta ji a ranta ko fatalwar Kaisar yayi bai zamo abin gudu a gareta ba don zatayi fatan fatalwar sa ma ta zama abin debe kewa a gare ta.

ya miko mata hannu babu ja ta mika mishi nata har ta na bin shi da runguma tana fadin

“Sai yaushe zan daina ganin ka a mafarki na Kaisar? sai yaushe zuciyar kauna zata rufe babin ka a rayuwa ta? zanyi fatan ace mafarki na ya zama gaskiya Kaisar yadda nake ganin ka a mafarki ka zama na gaskiya ido da ido.

Da sauri ya soma girgiza ta yana fadin

“Babu mafarki fati me nake ji kina fada ? wace irin zuciyar kauna? zuciyar kauna daya ce tana kuma wurin Nadiya fati kin kuma sani yadda zuciya ta ta mutu akan Nadiya.

tamkar wacce ta tashi daga bacci haka fati tayi firgigit ta ware idanun ta akan Kaisar. tamkar saukar tsini da kaifi a zuciyar ta jin abinda ya fada

Hawaye ya soma ta idon ta ta dube shi tana fadin

“Ko a zahiri ko a mafarki Kaisar ko kai dinka na zahiri ko kuma fatalwar da nake hasashe don Allah don ANNABI zan zubar da ajina na fada maka irin son ka da Ubangiji ya zuba min a zuciya ko da bai zama samu ba to na sanar da kai don ka sani zan mutu ne da soyayyar ka a raina ko da kuwa fatalwar ka ce nake magana da ita ina son ta shaida hakan in kuma kaine din ka rike wannan har bayan rai. “Ban gane abinda kike fada ba Fati? What do you mean?

“Don’t worry, I just wanted you to how special you are..”

“Fati ke yar uwa ta nake kallon ki. little sister my blood pressure. Don Allah kar ki kawo wani abu bayan wannan . Nadiya nake so irin son da zan kyautar Mata da numfashi na kema kin san hakan rai na da Rayuwa ta duka na fansar domin ta me kike zato? me kika dauki son da nake mata?.

“I say don’t worry, just forget it…” Kafin yace wani abu ta tare shi da fadin

“Don Allah kaine ko kuwa dai mafarki nake yi? Ta yaya akayi hakan bayan hanging dinka da na tabbatar da idona?.

<< Azurfa Da Zinari 32

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×