Skip to content
Part 34 of 35 in the Series Azurfa Da Zinari by Hadiza Gidan Iko

“Kai dai ayi sha ani uban gida na amma wannan yarinyar ba kuruciya bace akan ta sai dai wulakanci abu kad’an fa zata ce ma mutum matsiyaci gori a wurin ta tamkar a kanta aka saukar dashi zagi da mari ko Kai ka yankewa k’asa cibiya bata jin wahalar yi maka ko kai din sau nawa tana maka? na dai kula kamar kana son ta ne don kallon ka ma kadai gare ta ya nuna hakan.

Kaisar yayi murmushi yana shafa kyakkyawwr sumar kanshi wacce ta kara fidda mishi sirrin kyawun sa ya dubi malam Ango yana fadin

“Wai yanzu nan malam Ango har ka hango soyayya a idanu na? ai lallai ka san sirrin soyayyar malam Ango hala kasha fama da ita a lokacin kuruciya?

Malam Ango yayi murmushi yana fadin

“Kai raba ni da wannan zancen uban gida na ai abinda ya wuce ya wuce yanzu ta masara da shinkafa nake soyayya ai ta masu jini a jika ce irin ku amma ni kam fata ta bushe mutuwa ta soma barbada min gishirin mutuwa a ka ai soyayya sai ta ma aikin Allah da iyaye kuma amma mun rufe babin waccen  ta mimi mimi da baki .

Kaisar yayi murmushi yana mamakin yadda soyayyar Nadiya bata tsaya a zuciyar sa ba sai da ta fito idanun shi har hankalin masu hankali ya kai gareshi suka gane .

tafiya mai nisa kafin suka shigo garin jama are kafin suka sake daukar hanya Kaisar yana ta kallon garin bauci da kana nan hukimomin sa masu burgeww da sha awa har motar malam Ango ta faka a kofar gidan yakumbo halima wacce a lokacin karfe biyu da rabi na rana ne benci na a waje mutane kwastomomin yakumbo hali masu cin danwake suna rike da robobin dan waken suna ta aunawa malam Ango ya yi sallama a soron gidan inda anan yakumbo take girka katuwar tukunyar ta wacce ake jifan dan waken  sai kawai Kaisar ya hango Nadiya gaban murhu tana ta sakun dan waken jikin ta yayi butu butu da garin dan waken wanda ta tankade ta kuma kwaba ta ke jifan dan waken yayin da yakumbo take zaune gefen Nadiya tana zubawa masu siye  ta zuba mai da yaji ta karbe kudin ta ita kuma Nadiya ta saka ya dahu ta kwaso ta juye a Katuwar robar dake gaban yakumbo cike da ruwa ita kuma take tsama tana sallamar kwastomomin

Malam yayi sallama ya shigo yakumbo ta dago kai tana amsawa tana fadin.

“Kai malam Ango nake gani ? kamar ka san ina zancen gidan nan naku a raina wallahi sai gashi Allah ya kawo min kai to sannun ku da zuwa kai da bak’o ?

Kaisar ya zube a gaban ta yana gaishe ta don bai san ta ba amma kamar ta da mama yasa ya gane yar uwar ta ce don haka yake jin zai iya girmama ta don mama amma banda haka irin azabtarwar da malam Ango ya fada mishi da wacce ya gani a yanzu ace Nadiyar sa ce da jifan dan wake a irin wannan katuwar tukunyar ? zafin wuta ma ai ya isa ya cutar da ita .

“Sannun ku sannun ku bari a zuba muku dan wake tukun yau dai Allah yayi zaka ci dan wake nan malam Ango yaushe rabon da kazo irin wannan lokacin?

Malam Ango yayi murmushi yana fadin

“Kin kuwa san ranar wallahi har mafarkin sa nayi ai yakumbo Allah ya hore miki sanin sirrin girki haka na fadawa haj tace wai santi dai nayi ni kuma na san abinda na sani kar ma ace zazafen nan da wainar kosai.

yakumbo tayi murmushi tana fadin

“lallai ko na dai zance santi kake malam Ango .

ta zubo dan waken mai yawa Wanda ta doro musu har da jan magi mai star ta kuma kwalala musu mai da yaji.

Atuni kuwa malam Ango ya soma aikawa ciki yana cewa Kaisar

“Kai ai matar nan ta iya girki wallahi shiyasa mutane suka dafewa kayan sana ar ta komai nata kaci dadi gareshi hatta da kuli kulin ta gishiri gareshi. haka kosai bare koko uwa uba dan waken nan ai malam akwai dadi Yasin

Kaisar yaci ba don kambama shi da malam Ango keyi ba sai don Nadiya ce ke jifar sa Amma da duk dadin da malam Ango yake fada ba zai ci ba.

tuni kuwa malam Ango da Kaisar suka share dan wake inda yakumbo ta kawo musu ruwan fiyo wota tana zama tana fadin

“Yauwa malam Ango dama ina shirin zuwa gidan naku cikin satin nan don akwai wani makocin mu da ke can kasa wanda yayi min magana akan yarinyar nan Nadiya matar sa ce Allah yayiwa rasuwa ta bar shi da yan marayun Ya’ya har bakwai shine yace yana son yarinyar nan ni kuma nace babu matsala in akayi hakan ma an rufa juna asiri tunda a can kam garin naku yarinyar nan ba zata auru ba tunda har Dan gidan halilu aka bawa amma uwar sa tayi tsallen tsinka tsumma tace bata yarda ba to shi garbebe duk yankin nan ma akwai mai noman shi ? motoci ne da shi ake mishi sufuri samun irin su ai rabo ne tunda shekaran da ta wuce yaje dakin Allah ya sauke farali amma da yake yarinyar nan Allah yayi a tambaya da ita shine take min kukan munafunci wai bata so to biye mata za ayi? shine nake so idan kaje ka fadawa shi Alh kace mishi ga yadda akayi wata kil nan da karshen satin nan zan rako shi gaisuwa .

Nadiya da taji hakan ta soma matse hawaye inda kuma yakumbo ta soma lailaya mata ashar tana fadin bata san ciwon kanta ba da me tafi garbebe da har zata ce bata son shi?

Malam Ango ya amsa yana saukewa Nadiya kayan ta da suka zo da su duk da ganin Kaisar da Nadiya tayi babu wata maraba ta kirki kallo daya ma tayi mishi ta kawar da kanshi shi kuma babu abinda yake sai lissafin Al amarin Nadiya da ake fadar wai wani can garbebe yana son ta.

Kaisar ya ajewa yakumbo tsaraba ya dubi Nadiya Yana Fadin

“Dan zo mana na ganki minti biyu?

ta mike ta fito ya kare mata kallo ta na duban shi da son taji abinda zai ce mata.

“Yanzu kin gamsu da irin wannan rayuwar my sweety? naso na yi wani abu a kai amma naga matar nan da gaske take ke yanzu kina da ni har ake maganar hada ki da wani bakiyi wani motsi ba?

ta soma fidda hawaye amma bata ce komai ba.

Ya saka hannu aljihu ya fito da handkicif yana dauke mata kwallar ta yana fadin

“Daina kuka bari mu koma gida zan dawo na tafi dake gida kinga yadda kika koma kuwa? ai my sweetheart baki da miji sai ni  in sha allah kar ki tayar da hankalin ki zan dawo soon.

ya mika mata abinda ya ruko sukayi wa yakumbo sallama suka wuce shi da malam Ango.

*****

Abdulhameed kwance a gadon asibiti yayin da distinguish ya iso a ranar ya kuma zo ya samu jikin da kyau an dinke inda wukar ta huda. an kuma cire mishi wayoyin da aka makala mishi  yana saukar da numfashi cike da nutsuwa inda likitocin suka bada tabbaccin gobe zai iya bude idon shi

Ai kuwa a ranar distinguish Mukhtar Biro tare da mai dakin shi haj laila sun kwana suna tattaunawa a game da ciwon abdulhameed.

Washe gari kuwa misalin sha biyu na rana abdulhameed ya bude idon shi yana sauke su akan Haj laila wacce take rike da hannun shi tana kallon shi ya juya yaga Tero da daddy yayi murmushi kafin ya maida idon shi ya rufe

Bai kuma farkawa ba sai dab da magaruba inda yake son yayi magana a tada shi zaune amma bakin yayi mishi nauyi da kyar ya samu ya ce a tada shi amma babu wanda yaji abinda ya fada saboda muryar shi tayi k’asa sosai ba a Jin abinda yake fada

Sai da likitan yazo ya duba shi ne ya ce a samo mishi ruwan tea a bashi a kuma tayar da shi zaune a jingina mishi filo

Washe gari sai ga boss har  yana mikewa Tero yana rike dashi yana kuma magana fes

Ya na rike da kofin ruwan shayin yake duban Tero yana fadin

“Tero ina Nadiya? Ina fatan su mom basu yi mata komai ba?

Haj laila ta dube shi tana fadin

“Wacece haka kuma Abdulhameed?

Distinguish ma ya dube shi yana fadin

“Wai yarinyar nan yar gidan iro kake magana?

“Eh daddy Ina fatan dai bakayi mata komai ba? wallahi daddy yanzu nake jin son yarinyar nan ko don na tab’a ta ne naji abinda naji a tare da ita? ni kam a nema min sallama na koma Nigeria na nemi yarinyar nan Daddy kunce ko yar wa nake so zaku aura min to Daddy ita nake so ayi min aure don wallahi idan ban auri yarinyar ban ba zan iya rasa rayuwa ta don yanzu ne na gane so  da abinda nake so .

Distinguish Mukhtar Biro tare da matar sa haj laila suka dubi juna cike da tsoro da firgici Jin abinda yake fada ta yaya zasu koma gaban Alh iro suce neman auren Nadiya suka zo ya basu bayan distinguish ya shiga ya fia har an sauke haddi akan dan gidan iron? ta yaya ma zasu nuna dan su ya bayyana bayan an kashe musu nasu dan ? lallai abdulhameed yana shirin jawo musu janhurun masifa gashi kuma s yanzu lafiyar shi ake nema bare ayi mishi jan Ido ? bama wanna ba sun san shi kaifi daya ne in yace eh to baya sauyawa ta yaya zasu soma bashi magana ya sauya daga yar gidan iro ya koma wacce ba za a ji kunya ba? Malam Ango ya isar da sakon yakumbo halima ga Alh iro na shigowa neman auren Alh garbebe ga Nadiya.

Daddy ya gama jin komai yayin da Kaisar yake zaune yana sauraren su bai ce komai ba yana jiran jin amsar Daddy akan auren wani wofi wai shi garbebe ga Nadiyar

Daddy yayi murmushi yana fadin

“Alhamdulillahi malam Ango amma  kuwa naji dadin wannan maganar wallahi  ashe zuwan yarinyar nan jama are ma alheri ne dama ni haka naso wallahi gara yarinyar ban ta nemo miji a can wata shiyyar  Allah ya kawo su lafiya ni banda kar nace na barwa Halima komai ai da nace in dai ta Yaba da mijin Nan to na bar Mata wuka da nama to dole harkar aure sai da maza in dai ana so al amarin yayi daraja .

“Daddy ka kuwa ga yadda Nadiya ta koma ? don Allah daddy ku tausayawa yarinyar nan wallahi baka ga katuwar tukunyar da na iske tana jifan dan wake ba ga wutar itace tamkar gidan buredi ko zafin wutar nan ya isa tashin hankali Daddy don Allah ka sauwake mata zaman garin can wallahi baka ga yadda Nadiya ta koma ba Daddy in kukayi mata haka fa Allah zai muku hisabi yarinyar nan akwai kuruciya a tare da ita kuma tsakanin ku ma sai Allah yayi muku hisabi to kar ku biyewa halin ta don Allah kuyi hakuri ku dawo da ita gida wallahi tana wahala a can malam Ango fa yace min babu aikin da batayi wai har da kuli kuli da Koko da kosai har da dan wake duk ita keyi gashi kuma an kawo maka zancen wani bagidaje mai ya’ya har bakwai don Allah daddy ta yaya zata iya tafiyar da yaya bakwai? kuma naga sai murna kake daddy tamkar dai kuna shirin kai Nadiya bola ku zubar saboda kun gaji da ita ?.

Daddy yayi murmushi yana fadin

“Ai ko ba komai dai ta kara wani ilimin ta kuma koyi abubuwan da bata iya su ba. kuma ni yanzu Kaisar ba zan rika amfani da maganganun ka don gane abinda kake son nuna min ba . saboda na san ba a cikin hankalin ka kake magana ba kana magana ne a cikin maye maye kuwa irin na soyayya don haka wannan mijin da Allah ne ya zaba mata ba ni ba kadai ya Isa ka gane shine daidai da yarinyar nan tunda ni dai Allah na bawa zabi gashi kuma ya zaba don haka ni nayi murna Kaisar ko babu komai akwai hikima da Ubangiji ya saka a hakan duk yana daga cikin ta gane rayuwa da gane rayuwa bata dorewa akan yadda bawa ya zana ta ko yake son ta kasance mishi yau da kai gobe kuma sai labarin ka  Allah ya tabbatar da alheri yanzy ne yarinyar nan tayi miji irin wanda nake mata fata ko banza dai bai zamo daga cikin wanda zata gorantaww talauci ko alfarmar gidan su ba kuma ya’yan shi da kake magana ai zata iya tarbiya ne da ya’yan wani ne kafin nata suzo kaga zata gane tarbiya d yadda ake yin ta.

Kaisar kanshi a kasa yana sauraren Daddy har ya kare kafin yace

“Daddy me yasa baka sona da Nadiya? Daddy na san kana kauna ta hakikatan banda na san hakan da nace nine baka so Daddy tunda baka son abinda nake so to amma na san kana sona amma sai ka kasa so min abinda nake so.

<< Azurfa Da Zinari 34

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×