"Ba zan so ka da yarinyar nan ba Kaisar saboda nasan matsala ce a cikin rayuwar ka kai ne kake son yarinyar nan Kaisar amma ita ba son ka take ba . na gane hakan ne tun da tayi shiru da bakin ta bata nemi hana ka shiga halakar da ka saka kanka ba. ko makiyi ba a cutar da shi da cutar da ba tashi ba amma Kai dubi abunda tayi maka Kaisar anya wanda yayi maka haka ba zai iya soka maka wuka ka mutu saboda kiyayya ba,? na ji dadi da zuciyar ka ta yardar maka ina son. . .