Keena ta rungume luba tana fadin
“Ki bari don Allah ?
“Ah ! kina mamaki? Ai yanzu karyar maza ta Kare keena sai dai in baki san dawan garin ba amma yanzu don mace tana son namiji ai sai in bata so ta same shi bane amma da kinbi ta k’asa sai dai kiji ana wata maganar ba wannan ba kin manta ne da hadiza bakura ? .
“An gama magana luba nima kam hakan zanyi Amma kafin nan sai na fara tallata mishi kaina in ya karba shikenan in kuma bai karba ba sai na biyo mishi ta bayan gida.
“Ai kuwa kar ki tsaya tallata mishi kanki don ke da kanki kin san ga wacce yake so wato Nadiya wacce ban fidda zaton saboda soyayyar tata ya shiga gidan su a matsayin dan aiki don haka gara kawai ki tafi kanki tsaye don yarinyar nan tayi mana fin da ya wuce zaton mu wallahi shiyasa nake bak’in cikin duk inda muka shiga sai tayi population din da bamuyi ba in banda manufar nan keena ai da tuni wani zancen ake ba wannan ba. na kasa manta gorin da Nadiya tayi min shiyasa nake son ganin kukan ta in kuma rama abinda tayi min don ba a taba wulakanta ni irin wulakancin da tayi min ba .
“manta luba ai ni yanzu mafita nake nema akan ta don kudin can da akayi min alkawari sai naci su Yasin sai kuma ga sawun giwa tsuntsu biyu kenan da dutsi daya bari na Kira ta naji .
Keena ta sake kiran wayar Nadiya amma wayar a kashe don haka ta mike tana fadin
“Tashi muje gidan su luba har na gano sweetie na .
Luba ta mike tana fadin
“wai safina bata dawo bane jiya?
“Ina zata dawo can ta kwana kin san mutumin nata da maita don yau ma ba lallai ta dawo ba.
Suka fito suka shiga motar keena suka nufi gidan Alh iro gidan kudi.
Keena da lubabatu da kuma safina yan mata ne da suka hadu da Nadiya a makarantar high institution wato jami a . duk da kasancewar su keena ba karatun ne a gaban su ba illa sheke aya shiyasa karatun nasu baiyi wani abun kirki ba kullum cikin dawo da su baya ake har yau din basu kammala ba kasancewar ba karatun ne a gaban su ba sai burin su wanki maza a sheke aya shiyasa basu damu da zaman hostel ba don gidan da suke ciki a hostel yake a makarantar maza kuwa wannan ya Aje wanna ya dauka . tun a lokacin karatun Nadiya take tare da su duk da ita kam tana da kokari amma farkon haduwar su Nadiya tayiwa luba wulakanci saboda su suna son mace mai kyau a cikin su a cewar su karin girma ne saboda ko yaushe suna harka da maza
A yanzu haka akwai wani mai kudi da yake a garin Jos ana ce mishi shaid’an saurayin keena ne ya kawo mata ziyara a makaranta ya kuma dauke ta zuwa hotel din da ya sauka suka watse suka lalace bayan ya maido ta makarantar ne kuma yayi kicibus da Nadiya wacce yaji ya mutu a son ta har ya tanka ta cikin salon su irin na yan bariki duk da keena taji wani abu mai kama da kishi don tana wankar shaidan kudi ba na wasa ba amma sai ta maxe don ta san Nadiya yar gadara ce .
Ai kuwa sai ga Nadiya na wanke shaidan da tijara har tana tambayar shi ya san ko waye uban ta? To yaje ya tambaya in bai sani ba ya sani .
Shaidan yayi murmushi don ya tabbatar da gaske son yarinyar ya kama shi musamman m da ya koma Jos ya kasa sukuni har kasuwar keena na neman mutuwa don tun da yaga Nadiya ya mace .
Keena kam har jos ta iske shaidan ganin kwana biyu baya ko kiran ta shi kuma ya fada mata gaskiya yanzu yarinyar nan yake so Nadiya kuma yana neman hanyar da zai same ta ko da sau daya ne idan ya farke ta bukatar shi ta biya . daga karshe dai ya bawa keena kwangilar kawo mishi Nadiya ya biya ta shine ya bata kyautar mota ya kuma yi mata alkawarin manyan kudade idan har tayi nasarar kawo mishi Nadiya shine dalilin da suke jikin ta da son cika wannan burin. sai Kuma ga sawun giwa ya take na rakumi keena tayi gamo da soyayyar Kaisar ko yaya zata Kaya musu?.
Motar keena ta faka a kofar gidan alh iro suka fito zuwa kofar don ba a barin su shiga ciki sai fa in Nadiya tace su shiga.
Suka shiga keena na ta wara idanu taga ko zata hango Kaisar sai kuwa ta hango shi zaune a karkashin inuwar umbrella yana rike da Al kur Ani yana karatu sai kawai keena ta nufe shi tana sallama.
bai amsa ba sai da ya kai Aya.
Ya dago yana kallon ta tayi murmushi tana fadin
“Yaya na sannu da kokari don Allah a saka ni ADDU A Ina da bukata wurin Ubangiji ya biya bukatu.
ya kare mata kallo shigar ta kadai ta fallasa mishi ita a marar kunya don haka sai ya kawar da kanshi don yaga sai kara tura kirji take da son lallai sai ya ga abinda zata ja hankalin shi.
“Nagode
kawai ya fada yaci gaba da karatun shi.
tana shirin zama kusa da shi ne ya rufe Al kur anin ya wuce ta ya barta nan zaune inda dariya ta kama luba ta kuwa kyalkyale da dariya har keena ta taso da yar kunyar ta suka nufi cikin gidan suka samu Haj Aliya wacce ta tarbe su tana musu maraba.
Sun gaisa keena ke tambayar haj Aliya Nadiya da suka daina samu a waya shine suka zo su duba ta.
“Ayya ai kuwa bata nan taje jama are shiyasa baku same ta ba kuma bana jin wayar tata a kunne take shiyasa sai dai in ta dawo
Suka mike sukayi wa haj Aliya bankwana suka taho luba na dariya tana tambayar keena yadda sukayi ta kuma fada mata .
“Ai na gaya miki kawai kibi ta k’asa kina gida zai sallama miki yace ke yazo nema kudi kawai zaki tanada mu fasa Niger.
*****
tunda Alh garbebe ya sami shiga wurin yakumbo halima yake faman sauke wa yakumbo Halima kayan arziki dangin kayan lambu dangin tattasai da tumatur albasa kabeji Nadiya kuwa idan akwai wanda ta tsana a duniya to garbebe ne Wanda wahalar aikin gona ta mayar tsoho har kanshi ya dauki farin gashi. Ko yaushe yana gona ko lambun shi yana siyar da albasa kabeji karas tattasai tumatur ga kuma motocin shi na sufuri kudi kam akwai su ga Alh garbebe amma fa ba naci bane don burin kaf yana ga yadda za a kara habaka harkar noman damina da na rani amma fa gidan shi babu yunwa haka kuma yana siya musu sutura duk sallar idi ko ta layya sai dai shi kam babu hutu a tare da shi kullum cikin aiki yake haka ma yan yaran shi maza matasa su uku duk suna tare ana aikin lambu ko na gona
tuni kuma ko da suka zo yaji abinda daddy yace na ya tura manya ayi magana ya soma siyen kayan aure irin na birni don a cewar sa matar da zai dauko yar birni ce
Mai hali bai bar halin sa ba Nadiya bata bar wulakanci ba sai dai in ba a zo inda zatayi shi ba .
garbage yazo da dare Nadiya na jin shi tayi banza da shi har sai da yakumbo tace
“Wai ba kece naji hafsa tacewa garbebe yana soro yana jiran ki ba? kin tashi ko kuwa sai na iske ki ?
Nadiya ta tashi tana fidda kwalla ta wuce soron garbage ya tarbe ta yana rarrashin ta ta dube shi a tsiwace tana fadin
“Da Allah dakata min malam kake min surutu sai kace carbi wai ban ce maka bana son ka ba? wane irin naci ne da kai ? to wallahi tun wuri ka shafa min lafiya ka kuma je ka fadawa waccan matar ka fasa aure na in kuma ba haka ba duk abinda ya same ka ita taja maka shi wallhi.
Alh garbebe yayi murmushi yana fadin
“Babu komai ai ni na ganki nace Ina son ki ba ita ta hada ni da ke ba komai zakiyi min Ina son ki Nadiya masoyiya ta.
ta mike tana tsirta mishi yawu a fuska abun haushi sai taga ya lakace yawun ya ai baki ya lashe yana fadin zakin yawun nata.
ta wuce ta bar shi yana sambatun kaunar ta haushi na k’ara kamata tana kuma k’ara saka yadda zata jefa yakumbo halima a cikin hadari matukar ta dage da auren nan.
Cikar watan ta biyu a garin jama are Nadiya ta wayi gari tana sheka amai saboda kamshin kuli kulin da take toyawa yakumbo halima wacce ta taho tana fadin
“Wane irin wulakanci ne haka kike kwara min amai a gaban kuli kuli salon kisa ace k’amu k’amu nakeyi a kayan sana a ta?
yakumbo halima ta balbale Nadiya da masifa yayin da Nadiya kuma take ta kakarin amai a dole yakumbo ta karbi soya kuli kulin ta Nadiya kuma ta kwanta zazzafan zazzabi ya rufe ta Wanda yaja ta har kwana biyar a kwance yayin da alh garbebw kuma ya shigw sunturin kawo mata kayan dubiya wasu kuma daga lambu yake debo mata su
Amai ya matsawa Nadiya komai ta kai baki sai ya dawo ga zazzafan zazzabi shima ya ki sauka dole alh garbebe ya bawa yakumbo Halima kudi yace a kai Nadiya asubti musamman aman da ya matsa nata bata iya cin komai ya zauna mata sai ta amayar da shi ga shi kuma jikin ta ya saki amai da tafiya da ruwan jiki
Dole kuwa yakumbo ta shirya suka nufi asibiti da Nadiya wacce jikin ta yayi taushi sai hajijiya ma da take gani kamar zata fadi dole yakumbo Halima ke rike da ita har suka Isa asibitin.
Sun Isa Asibitin general hospital dake cikin garin jama are yakumbo ta tafi yankar tikitin ganin likita wato hospital card, ta dawo da katin ta zauna zaman bin layi Nadiya kuma amai ya hana ta sukuni sai kwara shi take duk da babu komai a cikin ta sai yawu kawai da kakarin amai take don komai ta saka baki dawowa yake.
Ta dawo ta tara’s da Nadiya tana kwara amai wata mata dake kusa da ita tana ta mata sannu . yakumbo ta zauna tana fadin
“Ai jiki magayi tuni nake fada musu wannan man da yajin da suke dankara suna ambamar shi kamar ba gobe in shawara da basuri ya tashi tambayar su zasu gane Allah daya yake ba kuma a jingina shi da kowa gashi nan shawara tayi miki mugun kamu har kina neman daukin likita .
Matar ta dubi uakumbo jin tana fadar wai basur da shawara ita kam kallo daya tayiwa Nadiya ta gano al amarin da yake tare da ita smma ga tsohuwar na kiran basur da shawara ga alama bata kawo hakan a ranta ba to in likitan ya sanar da ita gaskiyar sl amarin yarinyar meye zai faru? Sai tayi gum da bakin ta don fadan da babu ruwan ka yafi dadin kallo kuma ita wa ya aike ta shiga hurumin da ba nata ba?
layi ya matsa har aka zo kan yakumbo suka shiga ita da Nadiya likita na tambayar abinda ke damun Nadiya yakumbo Halima ta cabe tambayar ta soma kora mishi bayani.
“Menene fa likita ban da shawara da dan kanoma? In suka dafi mai da yaji basuyi mishi da kyau ambamar sa suke kamar ba gobe shine ya taso mata sai kwarara amai take .
likitan ya dubi yakumbo ya kuma dubi Nadiya wacce a kallo daya mutum da aikin sa ya gane
Yayi murmushi yana fadin
“To Inna bari mu gani a duba ta sosai in basur din ne.”
Ya soma auna Nadiya wacce ya bukaci tayi fitsari ta kawo
Yakumbo tabi likitn da kallo jin yana neman fitsari don ta san abinda hakan yake nufi amma ta zuba Ido da hanci tana saurare
Nadiya ta yo fitsari ta kawo a kwalba likita ya tura su dakin awo suka dawo ya karbi takardar gwajin yana dubawa kafin ya dubi Yakumbo yana fadin
“Inna ina mai gidan nata yake ne?
yakumbo ta jiyo tana fadin
“Mai gida na ko kuwa mai gidan wa?
ya kada kanshi yana fadin
“Mijin ta ita marar lafiyar nake nufi don a yi musu barka don amarya dai ta kusa zama mama ciki na wata biyu da sati biyu.
A rikice da tashin hankali
yakumbo ta daki kirji tana fadin
“Kai banji abinda kace ba likita wai me kake fada ne haka ? daina zolaya ta duba dai da kyau
Likita da ya tabbatar da dama dole akwai lauje cikin nadi tunda yaji tsohuwar tana fadin basur da shawara ya san bata san komai.
“Inna ina nufin ciki ne da ita ba shawara ba ba ta da miji ne,?.
yakumbo ta katse shi da kwara ashar saboda kidima
“Gidan ubanwa ta ganshi? budurwa ce gal a leda ashe ni ina can sake da baki galhoman wofi har abunda ya faru ya faru yau ni na shiga uku na kasa fita ni halima.
Sai kuma ta dubi likitan tana fadin
“Kace wata nawa?
ya maimaita mata wata biyu da sati biyu.
“Oh ni halima wane irin balak’i ne wannan da sammakon asubshin farko? yar amana ce fa aka kawo min ? wai likita wane irin ciki kake magana don Allah? cikin haihuwa ko na ba haya? likitan ya tabbatar mata da hakan sai kawai yakumbo halima ta fashe da kuka tana fadin.
“Yau ni da wane idon zan dubi iyayen yarinyar nan ace sun bani yarsu lafiya kalau daga gyaran tarbiya sai kuma ace na lalata abunda ma bata yi iskanci a gaban su ba sai a guna ? wannan ai shine zaton wuta a mak’era a ganta masaka.