Skip to content
Part 42 of 99 in the Series Azurfa Da Zinari by Hadiza Gidan Iko

“Abdulhameed, mutum kamata ya dace da karya ko magana biyu?  Yaya za ka kalle ni idan na yi maka alkawarin karya sai kazo sai kaji an daura auren Nadiya da wani ba kai ba? tsohon banza ko kuwa makaryaci mayaudari? to ko kusa ko alama kar ka saka ran auren Nadiya don babu hadi kazo a makare.

“Ka tausayawa halin da zan shiga daddy don Allah kar kayi min haka Daddy.

“Abdulhameed be a man Kaji? Idan so ya zama cuta to hakuri ne maganin wannan cutar da ace kazo tun kafin yau da na yi maka alfarmar da ka roka don na gane ko babu komai ka dan san hakkin shari a ta a fara neman izinin iyaye kafin a xo to amma yanzu idan nace na janye daga wanda na bawa na baka yaya shi wancan zaiji ya ya kuma zai dauke ni ? kaddara kaine wanda na bawa auren Nadiya sai kaji na janye na bawa wani me zaka dauke ni? to mu bar wannan maganar abdulhameed don kuwa tauna ta ma yana nufin akwai yuwuwar a janye din amma a bar kwarya a gurbin ta .

Hawaye ya soma wanke fuskar abdulhameed yayin da Mustafa ma ya soma rokon daddy alfarma amma maganar shi daya ce suyi hakuri a bar maganar.

Duk naci da jajircewa basuyi nasara ba har ta kai Alh iro ya mike yana fadin zai shiga cikin gida

dole kuwa suka mike suka juyo gida Abdulhameed cike da tashin hankali

Tsagera ya faka motar a farfajiyar gidan Baffa Alkali Haj laila ta fito tana rike da jakarta ta manyan mata first lady koman ta irin na Yan gayu da nuna alfahari hannayen ta cike da zobunan ZINARE haka sarka da yan kunne ZINARIYA mai daraja

Haj Safiya ta tarbe ta suka gaisa duk da haj laila akwai dagawa da jin Kai wmma Haj Safiya babu shiga sabgar da ba tata ba shiyasa ma take rike da girman ta tafi karfin raini tunda bata watsar da darajar ta ba in haduwa ta kama zasu hadu a agaisa don haka suka gaisa da haj laila wacce ta san don Abdulhameed tazo tunda na zuwan take ba.

“Abdulhameed na ciki kuwa Safiya?

laila ta fada tana kallon Haj Safiya

“Anya kuwa gaskiya sun fita don abdurrahaman ya zo yake ce min na bawa su Abdulhameed key din mota to na basu banji kamar sun dawo ba amma bari na duba miki shi jiki ma ba lafiya amma sai yawo.

“Uhum Safiya yaron nan baya jin magana daga gadon asibiti fa yake amma ya hana kanshi zaman lafiya akan wata yarinya bana ko shakka can ya tafi .

Safiya ta fice tana fadin

“Sai ADDU A ka haife su ne baka haifi halin su ba

ta duba sashin nasu a rufe ta dawo ta fada mata basu dawo ba.

tana nan zaune suna magana har zuwa lokacin da motar su mustafa ta shigo haj Safiya ta daga labule ta hango sune ta zauna tana fadin

“Gasu nan laila.

Da sauri Haj laila ta mike tana fadin

“Bari na ganshi safiya damuwa ta ciwon nan nashi amma shi baya gani banda yana da sauran numfashi da yanzu fa yana dab da cimma wata uku.

Ta fice tana nufar inda sashin nasu yake

A kwance ta samu Abdulhameed wanda yayi kwanciyar kife wato ruf da ciki Mustafa na gefen shi yana bashi baki .

ta shigo da sallama Mustafa ya mike yana mata sannu da zuwa amma abdulhameed bai ko motsa ba.

“Mustafa Ashe nan kuka taho kuka bar mu da tashin hankali da jimami?

Abdulhameed ya tashi zaune yana duban mamar tashi yana fadin

“Mom naje gidan su Nadiya amma Daddyn ta yace min wai yayi mata miji mom in dai ba zan auri Nadiya ba to banga amfanin zamana a duniya ba wallahi don ba zan iya ganin wani ne ya aure ta ba.

Haj laila ta dafa kanshi tana fadin

“Kayi hakuri tunda kana son ta Abdulhameed nayi maka alkawarin sama maka ita amma yanzu mu wuce gida ina son ka kasance kusa dani don naga yadda kake shan magani nafi son naga ka warke koma meye sai ayi .

“Ba zan koma gidan ku ba mom nan zan zauna a gidan Baffa alkali don shi na San zai iya amfani da hikimar sa ya je ya rarrashi mutumin nan Amma Daddy zai nuna karfin iko ne har komai ya lalace kamar yadda ya lalata shi to ba zan koma gidan ku ba. magani kuwa ba zan kuma shan sa ba don da na gane mutumin can da gaske yake ba zai bani auren Nadiya ba to wallahi ku rika kallo na a matsayin matacce don zan mutu ne ko ban shirya mutuwa ba .

“Don Allah ka bar irin wannan maganar abdulhameed in ka mutu Kuma ni ba zaka hango min irin halin da zan shiga ba? yanzu ma da kayi wannan mutuwar ta wucin gadi kaga irin bala in da na shiga ne? ka bari ni zanje gidan su yarinyar na nemi uban ta in ma wanda suka bawa auren nata ya kamata na nema duk zanyi in yaso sai na siyi soyayyar tashi yayi mata kudin tsiya na fansar maka kar ka damu kanka don Allah kaji? .

“To ina jiran ganin kokarin da zakiyi min mom amma maganar na kwantar da hankali na ma bata taso ba.

Da Haka Haj laila taiwa Haj safiya sallama ta wuce .

Kimanin kwanaki arba in da yin shari ar Nadiya da Mukhtar Biro aka wayi gari manyan alkalan biyu sun amsa kiran Allah wanda sune suke da hannu akan komai . mutuwar da ta tayar da hankali matuka gaya ta Kuma jawo Rasa jigon tafiyar.

Aka shiga yaya za ayi ya za ayi akan maye gurbin su? Dole sunan Sufi biro ya fito don shi din gwani ne Kuma zakakuri matuka gaya. sai dai an shiga kunjin kunjin cewa saukakke ne an sauke shi Kuma daga cikin masu mutuwar ne ke da aikin rattaba a sauke shi yau ga shi sun bar duniyar sun kuma bar mukamin da sukayiwa rukon alewar yara ashe ita duniyar bata ta da tabbas kana tsska da sharafi zata watsar da kai kamar yadda tayiwa wadan nan masu kullin makircin

Sai aka shiga kulle kulle don an zaga an kuma zagawa amma babu kamar ya Sufi biro dole aka gama zaune zaunen aka rubuta sunan shi aka aike mishi da takardar girman da ya same shi wanda ba don an so ba sai don Allah mai fidda rabo ko da ba a so ba

yana gidan gona yana ganin yadda ake fidda kaji da kwai kullum harkar tasa gaba take yana kuma mamaki da yadda al amarin Ubangiji yake wanda babu mugunta ga Ubangiji sai dai bawa ya mugunci kansa

Kiran wayar tashi ya same shi inda ake neman sa  a court appeal

Bai dauki kiran da wani muhimmanci ba don sai da aka gama mishi aikin shi a gidan gona ya koma gida yana cin abinci haj Safiya tana fada mishi zuwan haj laila ganin abdulhameed.

yayi murmushi yana fadin

“Sun dawo kenan ? ai kuwa gobe zan saka manu ya fidda min zabi da kwayaye na Kai musu an jima ba a hadu ba . ya gama cin abincin ya shiga sashin su Abdulhameed ya samu abdurrahaman da mustafa da shafik suna fira yayin da abdulhameed yake bacci.

su duka suka gaishe shi ya amsa yana tambayar jikin abdulhameed suka ce yana samun sauki tunda yana shan magani.

Ya duba abdulhameed ya fito

ya manta da kiran da akayi mishi a court appeal har ya kwanta bayan ya gama lissafin kudaden sa na kwai da kaji.

Washe gari kuwa ya na gida ya sa manu ya fidda zabi da kwayaye yace a gyara su a shirya yanzu zai shigo zai karbe su manun ya amsa tuni kuwa aka gyara zabi da kwayaye masu yawa don Hhaka yana zuwa kuwa an gama aka loda mishi bayan mota ya nufi gidan yayan shi Mukhtar Biro da kayan karamar arziki.

Alhaji iro yabi bayan su Abdulhameed da Mustafa Tero da kallo har suka fice yana mamakin halin dan yau. Ina ma ace uban sa ne yazo nema mishi auren ya gurfana a gaban shi? dama haka Allah yake ikon sa ragowa. kuma tana da dadi don Allah ne kadai ya san inda zaka hadu da wanda ga ragewa ko ka tsanantawa

Ya shiga ciki yana fadawa haj Aliya yadda sukayi da Abdulhameed da irin magiyar da yake mishi akan ya bashi auren Nadiya.

Haj Aliya ta muskuta tana fadin

“Ni kuwa daddy sai naga da ka yarda ma da bashi auren ko babu komai shine wanda ya san kowace ce ita babu gori babu jawabi kuma ma Daddy ai ka bari magana baya ba sai ka sanar da shi cikin da ya bayyana sakamakon abinda yayi mata ba?.

“In bashi auren Nadiya kike nufi aliya? Tayi maza ta amsa da tabbacci.

“Bai cancanci auren ta ba Aliya na hango hakan da tazara mai tsayi shiyasa ba abinda zai yuwu bane ba kuma zan soma ko da comfearing ba . ke ko a mafarki naga hakan zan yi saurin karyatawa don ban shirya hakan ba .

“To maganar cikin kuma fa,? da kayi mishi magana wata kil ya yarda ya karba kaga kayiwa dan ko diyar gata zasu tashi suga uban su wanda zai hana a kira su shege.

“Sai kuma kika manta Aliya shin meye shegen? ai dan da babu aure ya samar ? to su din meye In ba shegen ba? kar ki sauyawa zancen manufa haka yake kuma in ma ya karba din kina zaton wata daraja ga dan? kuma sau tari ma namijin da ya samu mace irin haka bai faye yarda ya karbi abinda kaddarar ta bayar ba don zukata cike suke fal da zargin anya nasu ne ? kuma ko ba wannan ba Shari a ma uwa mace ta barwa abinda haduwar su ta so  ko a gaban kotu za a ce na mace ne da dai aure ne sai uba namiji ya zama mai da amma in dai haduwar titi ce irin haka to dan mace ne in da uba namiji ake baiwar irin wadan nan Ya’yan Aliya to ta ina za s samu shegen? ai kowa zai zama dan uban sa ne  ba na uwar sa ba don haka bama zai ji zancen ciki ba yaje na sallame shi cikin ta kuma ta haife ta bar mana shi a nan muna so Allah ne ya kaddara zuwan sa duniya ta haka ba kuma zan zubar ba wata kil akwai hikimomin Ubangiji akan zuwan nasa .

Haj Aliya ta sauke ajiyar zuciya tana fadin

“Kuma haka ne Allah yayi mana mafita.

Suna nan zaune Kaisar ya fito yana fadin

“Mama Ina fati ?

haj Aliya tace bacci take.

“Don Allah a tada ta mama Nadiya ke son faten tsaki da yakuwa da manja.

“Jeka ka fadawa Ade tayi mata amma ta yaya banda rashin adalci mutum yana bacci a tashe shi?

Kaisar ya dubi haj Aliya yana fadin

“Mama bata son na yan aikin ne shiyasa ni kuma ban iya ba ne da nayi mata.

Kwalla ta cika idon Alh iro yayin da haj Aliya ma sai da taji wani abu ya yanki zuciyar ta kafin ta ce

“To taso fatin Kaisar Allah ya raba da wannan jidalin wai tallar turmi a ka

Ya wuce cikin dakin haj Aliya yana tashin fati daga baccin ta ta bude idon ta a tsorace tana duban shi.

“Please my sister taso don Allah sweetie ce ke son faten tsaki irin mai yajin nan da yakuwa please taimaka min ki yi mata kinji?

Wani Abu ya tsaya a kirjin fati har ya tokare mata wuya amma ta maze cike da juriya da boye damuwa tace

“Ok to bari na fito.

ya juya yana fadin

“Thanks my dear

tabi bayan shi da kallo yana ficewa dakin sai kawai taji hawaye na tsere a fuskar ta . baya neman ta sai a hidimar Nadiya. baya jin kunyar fadawa Nadiya kowane irin suna a gaban ta  duk bata iya controlin din kaunar sa a gaban sa ko yaushe cikin fidda alamun son sa a zuciyar ta take amma ya take ya mutusiye baya ko son nuna mata ya fahimci halin da take ciki

ta share hawayen ta tana sauka daga kan gadon ta shiga toilets ta wanke fuskar ta ta fita ta nufi kitchen tana Aikin ta na jin yadda zuciyar ta ke kuntata a tsakanin kirjin ta har ta gama ta kwashe ta nufi dakin nasu inda ta iske shi ya tarawa Nadiya kayan kwalama kala kala a gaban ta amma abun haushi fuskar Nadiyar a kirne babu dariya ba fara a

Ta aje a gaban Nadiyar sai fa shine yayi mata sannu amma ita giwar sai yatsuna fuska take tamkar taga tutu

ta fice daga dakin don nan yake wuni yana gantalewa ita kuma tana zuba iko shiyasa ma fatin ta zabi zaman dakin mama ta basu wuri.

Haj laila tana komawa gida ta fadawa distinguish abinda abdulhameed ya fada da yadda yake zaune a gidan Baffa Alkali a cewar ta ta raina kulawar da yake samu don dai  shi din ne in baiyi niyar abu ba baya yi.

“Kin tara’s da Sufin a gida?

Ta kada kanta tana fadin

“Baya nan sai dai Safiya har suka dawo kuma yake fada min uban yarinyar yace ba zai bashi auren ta ba ni Kuma nayi nufin zube kudi na na nema mishi yarinyar nan ko da kuwa zasuyiwa yar su kudin tsiya ne zan zube AZURFA DA ZINARE na siya mishi ita amma ina ganin don baiga tsinin idon ka bane ko don wata alfarma da ka iya nema wurin ka zai baka auren yarsa .

Ya dube ta yana fadin

“Ni fa duk ba wannan ne damuwa ta ba laila yadda yaron nan zai rayu babu haihuwa yarinya ma ya same ta ya gama don na san uban ta ko baiga kima ta ba zan tura wanda zai ga kimar su ya bashi duk karyar banza ce da yaga kudi yanzu ne zai sauyawa zancen manufa duk kudin sa ai bai kai gwamnati ba

Sai suka shiga yaya za ayi a kautar da abdulhameed daga wancan balakin na rashin haihuwa inda suka soma bibiyar likitoci da masana kiwon lafiya amma dai maganar guda ce musamman ma takardar da suka taho da ita daga washing ton

Washe gari kuwa sai ga motar Sufi biro Sufi mai Shari a motar shi ta shigo gidan dan uwan nashi inda mai gadin ne ma ya bude mishi kofar don ya san shi matuka kuma kallo daya zakayiwa Mukhtar da Sufi ka gane yan uwa ne don kamar su daya su hudu sai fa ummulkhairi da ta dauko kamar mahaifiyar su smma su duka kamar mahaifin su ce a tare da su

Sufi ya futo yana bawa mai gadin hannu suka gaisa kafin ya soma sauke kayan da yazo da su a mota mai gadin ya soma jida yana shigar da su har ya kwashe kafin mai shari a ya fito da fararen yan Abuja guda biyar ya baww mai gadin ya karba yana godiya.

<< Azurfa Da Zinari 41Azurfa Da Zinari 43 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×