Skip to content
Part 43 of 99 in the Series Azurfa Da Zinari by Hadiza Gidan Iko

Ya shiga da sallama haj laila ta amsa mishi tana fadin

“Alkali Kaine tafe ? Sannu da zuwa

Ta fada tana juyawa ta bude fridge tana kwaso mishi lemuna  yayin da distinguish Mukhtar ya fito jin laila na ambatar alkali

fuska a murtuke ya fito ya zauna Sufi yana fadin

“Kai laila duk ina zan kai wannan ?

Ya dauki kofin yana kaiwa baki yasha kafin ya aje yana duban ya’yan nashi  yana fadin

“Brothe barka da Safiya.

Distinguish ya daga mishi hannu yana kara kirne fuska.

Haj laila tace

“Yaya mai jiki? Anaje jiya ai .

“Yana samun sauki alhamdulillahi laila Kuma shine kukayi tafiyar ku ke da mijin ki kuka barmu bamu san abinda yake faruwa ba sai da abdulhameed yazo naji komai? .

“Kayi hakuri alkali hankali ba kwance ba shiyasa bamu sami zarafin fada ba Allah ya kara girma Alkali

Ya amsa da ameen kafin ya nuna kayan da yazo da su yana fadin

“Ga albarkar gidan gona nan ku saka albarka babu yawa muna bukatar ADDU A

Haj laila ta amsa tana Fadif

“Masha Allah kayi gidan gona ne Alkali?

ya amsa da wani ma yake kan samarwa a yanzu tunda Allah yayiwa Abun albarka.

Mukhtar ya dube shi amma bai ce komai ba bare yace ya gode

Haj laila ce tayi ADDU A ta kuma nemi albarkar Ubangiji har tana nuna wa mijin nata wanda yace ya gani.

Wayar Sufi ta dauki tsuwwa ya fiddo ta yana ganin lambar babban alkali yuguda ya dauka da sauri yana gaishe shi inda yugudan yake mishi albishir da matsayin da aka bashi na maye gurbin mai mutuwa na birnin tarayya Abuja.

Da yake wayar a bude take duk suna jin abunda aka fada inda Mukhtar yabi shi da ido har ya gama godiya yana fadin zai shiga Abuja zuwa jibi in sha Allah

Ya gama wayar Haj laila tana ta fadin congratulations alkali.

Ya dube ta yana fadin

“Laila ai bana Jin zan karbi mukamin nan gara kawai su bawa wani ni kam tunda na gano sirrin da yake cikin kiwon nan kuma ai na gama da aikin gwamnati zanje Abuja ne nace su bawa wani ni kam na kama dahir.

Mukhtar bai iya boye firgitar da yayi ba  don shi da kanshi ya gane gaba ya kai dan uwan nashi.

“A a don Allah alkali kar kayi haka ai sai a hada taurar biyu a tauna in ka mayar ai baka gode ni imar Allah ba tunda ya fika sanin wanda kake son cewa a bawa ya baka .

” A a laila gara na zauna a haka nayi kiwo na ban sab’a da yan uwa na ba ban saba da mutanen gari ba baki ga har yanzu mijin ki kullata ta yake ba ? baki ga ko magana ya soke min ba,? to gara na zauna a haka wani baiji haushi na ba Akan aje gaskiya gurbin ta don matukar ina kan aikin Shari a to abinda mutane basa  son ne zanyi ta tabbatar wa don ba zan yarda da danne hakki da cutar marar karfi ba dole a daidai ta sahu laila kamar yanzu da aka kashe rai saboda abinda akayiwa abdulhameed shin shi wanda ya aka kashe an kashe banza kenan? Tto ki sani matukar ina kan aikin Shari a sai brothe ya biya iyayen yaron da aka kashe diyyar dan su tunda ga nashi yaron kinga a yanzu yana fushi idan na tabbatar da gaskiya gurbin ta ba sl ba zai wuce hakan ba? to kinga gara kawai na hakura tun banyi wacce za a yi min ta rayuwa ba.

Mukhtar ya dube shi Jin abinda yake fada don shi da kanshi yana tambayar kanshi yaya matsayin shi wanda aka kashe din ? sai ga Sufi yana mishi tambihi da nuna shine zai biya diyyar ranshi.

Sufi ya mike yana fadin

“Ni dai na wuce sai gani na biyu ina kuma duban hanyar zuwa ayi min cinikin kwai da kaji ko zabi.

Haj laila ce kawai tayi mishi fatan alheri amma distinguish ya mutu a zauna yana tsoron kar Sufi ya karbi mukamin nan ya tabbatar da abinda ya fada

A cikin kwanaki biyu Sufi ya karbi mukamin sa wanda bai so hakan ba sai da yan uwan shi da matar sa haj safiya suka matsa mishi kafin ya yarda ya amsa matsayi kuwa mai daraja na justices inda aka bashi katon gida a Abuja da mota irin ta manyan alkalan da albashi mai daraja a duk watan duniya.

Yakumbo Halima ta iso garin bauci duba Nadiya ita da hafsa Haj Aliya ta tarbe ta tana musu maraba

Nadiya ta fito daga daki tana yiwa yakumbo barka da zuwa yakumbo halima kuma ta zuba mata ido ganin cikin ta ya soma girma

yakumbo ta rike baki tana fadin

“Yau na shiga d’aka ba maza haka cikin yarinyar nan ya fita yaya sliya? Ke duba min ciki kamar na watanni bakwai ni halima wannan abu kamar na cin rabon kiyama?.

“To ya za ayi halima ai rabon zuwan wani bawan Allah ne nima giman cikin nan yana bani tsoro to smma ikon Allah ya wuce mamaki.

“Ikon Allah to Allah yayi mana magani ai ni kuma duk jiki na yayi sanyi Wai anjefi kaza da gishiri tace jiki na yayi sanyi kuma.

Alh iro ya fito yaga yakumbo halima yana fadin

“Halima ce a gidan?

ya zauna tana fadin

“Nice kuwa Alh nazo duba Nadiya ne naga wannan ciki mai kama da ana hura shi .

Yayin murmushi yana fadin

“Ni na zaci ma Alhaji Garbeben naki ne ya turo ki karba mishi abunda ya bayar.

“Ai Alhaji Garbebe ko ta kofar gida na baya bi yanzu tunda nayi mishi burga amma banda haka Kam da har kudin man da ya zubo yaxo nan sai an biya shi to da yake na san kan tsiyar sai nace hukuma zamuje yayi bayani ai tunda ya arce  bai Kuma ko bi ta hanyar gidan ba tunda yasha da kyar a waccan shari ar amma da yazo yana fadin na cuce shi kuma ba zai yarda ba sai na biya shi yo Alh ana biyan kyautar saurayi da budurwa ne? .

Haj aliya da Alh iro sukayi ta dariya yakumbo tana fada mishi yadda suka kare da Alhaji Garbebe.

“Al Amarin nan ya dame ni luba wallahi na kasa samun sukuni a zuciya ta komai nakeyi bawan Allah nan nake gani yana min gizo har Yana bayyana a idona  gashi kuma ban ga zaiyi saukin kai ba don da ganin shi zaiyi jin kai baki lura da kallon da yayi min ba ne? daga amsa sallamar fa bai dora da komai ba sai ma wani banzan kallo da ya bini da shi duk da nayi zaton zai karewa sura ta kallo amma bai ma hada ido da ni ba yasha wani matsiyacin kunu kamar yaga kayan banza.

luba ta kyalkyale da dariya tana fadin

“Ai keena har yanzu waka kike ne ba abinda Kika fada ne a zuciyar ki ba  shiyasa har kika tsaya neman wani yarda da aminci amma da da gaske kike kin kuma tanadi karafan banki tuni zamu fasa nijar na kaiki inda ake share hawaye amma da yake wake kike keena kuma ga Alama kina jin dadin rera ta shiyasa nake kallon ki.

“Wace irin magana kike luba? Ko da yake na miki uzuri baki an abinda yake sinke a cikin zuciya ba shiyasa baki ga halin da nake ciki ba wallahi ba karamin tashin hankali nake ciki ba na rasa yadda zanyi wallahi.

“To ga yadda zakiyi in dai da gaske kike  ki fiddo kudi mu fasa Niger.

“To ai inda gizo ke sakar ke luba babu lambar sa kuma ga wannan yar wulakancin bata garin bare mu sami lambar shi a wurin ta.

“Wannan duk mai sauki ne keena lambar wayar sa ko ko motar  ba zamu rasa samun wata ba ko wurin yarinyar nan ta gidan su Nadiya zamu iya samun ta yanzu kina da kudi a hannun ki?.

“Kudi ba zasu zama matsala ba luba duk da bani da isasshen kudi a account amma bari na tambayi shaid’an na san ko nawa nake son zai bani cikin kudin aikin nan in na gama sai ya fidda kudin sa ya bani ciko

Ta figi wayar ta tana dannawa shaid’an kira

Kara biyu tamkar yana zaman dakon kiran ya cabe ko da yake har zaman dakon ma yana yi don ya kafawa yarinyar kwadayin son ya latsa ta duk da rashin kirkin da ta tata mishi amma yana makale da son ta .

“Ya akayi keena ta samu ne?

“ta kusa ta samu dai shaid’an kudi nake so ka tura min don sai na hada da wasu mutanen da dole na sallame su don ni da su luba munyi kadan gaskiya shine nake son ka tura min kudi .

“Bani da matsala da kudi keena amma kin san bana son bata lokaci daga nan zuwa yaushe zan Kira ki ? .

“To yanzu haka dai tana jama are aka ce to can jama aren zamu bita kaga ga kudin transport ga na kunji kunjin abubuwa kar ka damu ni da kaina zan kira ka da naga komai ya zama ready.

“To kamar nawa kike so?

Keena ta dubi luba da son ta nemi nawa zata nema?

Da sauri luba da ta gane abinda take nufi ta ware mata yatsun hannun ta uku alamar dubu dari uku.

“Ka tura min dubu dari uku ma ta Isa in da yuwuwar na nemi ka Karo sai na fada maka amma yanzu dai bani 300k mu gani.

“Baki da matsala ke dai yi kokari kafin watan nan ya kare ki kira ni nazo na farke yarinyar nan.

Keena ta dubi luba tana fadin

“SATA zata saci SATA ni da shaid’an yana son wata nima ina son wani bari mu gani ni da shi wa zai riga cimma nashi burin duk da ta hannun shi zan kwantalo kudin samo nawa muradin shima kuma nice zan zaboro masa nasa muradin.

Safina da take kwance tana waya sai da ta gama ne ta dubi keena tana fadin

“Amma kuwa lamarin ki da mamaki keena ni na san bakya son mutum sai da dalili wanda ba zai wuce ki wanke shi ba amma wancan me zaki wanka a tare da shi in banda wahala,? dan aiki ne fa .

“Safina ai na karyata kaina akan gayen nan don na gane so da yaudara.

“To Allah ya sauwake miki amma gaskiya kin kira wahala shine har da zuwa Niger don nemawa kai wahala? ai ke mai dan wani abu akewa wannan wahalar keena wanda bai da komai in kika kashe kudin ki akan sa me kenan? babu riba kenan sarin kosai kin kashe baki mayar ba bare kici riba sai faman kayan soyayya kike uwa tanatabara? kai lallai sannu ya jiki? Allah ya katse miki wahala don kin mata sallama saura kiris kuma ta amsa miki.

“Ba komai safina Allah ya Rubuto miki wannan wahalar kema kiji yadda ake ji .

Suka sheke da dariya su duka har suna tafawa tsakanin luba da safina.

Karar shigowar sak’o a wayar keena ne ya katse su suka dube ta suna fadin

“Alert?

Keena ta duba taga kudin da tace shaid’an ya tura  mata ne sune ya turo.

Tayi murmushi tana kwara ihu tana nunawa safina da Luba, 300k kwance a wayar ta.

“tashi ki gani Luba ai banga sauran zama ba wallahi sai naga yadda cinikin mu ya fada ni da gayen nan siye ko bari albarka muje na fidda kudin nan luba kafin na samo lambar gayen nan koma ya za ayi a yau sai na samo daya ko ta motar ko ta wayar sa  muje muje oya oya my dear.

suka fice keena na aunawa safina ashar.

Bak’in da aka sanar da Daddy Alh iro yayi sune suka saka shi ya fito da sauri don yace a bude musu kofar da yake saukar bak’in

Yana shigowa kuwa yayi turus ganin abdulhameed da Mustafa har da shafik Wanda shima ya biyo a wannan karon.

Ya ture mamakin sa a gefe ya shiga yana fadin

“Abdulhameed ne ? Sannun ku da zuwa Mustafa waye wannan shi kuma?

ya fada yana nuna shafik.

“Shafik ne Daddy shi ma dan uwa na ne.

“Masha Allah sannun ku da zuwa

Suka sauko suna zubewa a gaban shi suna gaishe shi ya amsa yana tambayar Abdulhameed jiki ya amsa da sauki.

“Madallah madallah Abdulhameed ya ya ne,?.

“Daddy alfarmar nan dai ce na dawo na sake roka don Allah don ANNABI a dubi halin da nake ciki.

“Abdulhameed mun rufe babin maganar nan fa tun ranar nan ko ? ka sani ni din kaifi daya ne ba wai bana magana biyu bane tunda ni ba littafi bane amma abinda ba zai yuwu bane kake zuwa da shi na fada maka na bayar da auren Nadiya a inda ba zan kwato na baka ba don Allah ka gane hakan bana son ma ana maimaita maganar . ka sani kai din a matsayin D’ana kake a yanzu har abada ma to amma yawan tuna min wannan maganar ka iya sawa na dakatar da zuwan ka gidan nan ka gane,?.

“Na gane daddy amma halin da nake ciki nake so ka fahimta wallahi Daddy na jaraba yin hakurin nan amma na kasa don Allah Daddy ka dubi rauni na.

“Abdulhameed mu daina jan maganar nan bari na fada maka wani abu da baka san shi ba in kuma baka wuka da nama don ka yankee hukunci inga idan zakayi adalci.

“Ko ka san yadda mahaifin ka ya dauki fansar son a bi mishi kadin jinin ka da mukayi zaton ka mutu  ? anyi bincike sosai aka kuma gano Nadiya ce ta kashe ka mahaifin ka yace sai an kashe ta da tabbatar mata da haddi duk da an gane kayi mata fin karfi yayin tayi kisan . ba wannan ne abin mamakin ba abdulhameed sai da aka yankee wa Nadiya hukunci amma mai kaunar ta da son ta ya karbi haddin ta ya kuma karbi laifin ta yace shine yayi ba ita ba . aka Kuma tabbatar mishi da rataya aka kashe shi sai gaka ka bayyana abdulhameed. kafin nan yarinya nan ta sami ciki sakamakon abinda kayi Mata Amma yace duk a haka yana so bai kasa ba bai fasa ba . sai ace wani nashi yana son ta shin idan kaine alkalin da zaka yankee hukunci zaka bata wanda ya rasa dan uwan sa ta silar ta ko kuwa wancan da aka so kashe ta saboda shi kuma ga shi ya bayyana,? kai in takaice maka ma cikin da take tare da shi a yanzu yana nan yana dawainiyar da kai ne ya kamata ace kanayi.

Cikin wata irin kidima da razana abdulhameed yake jin Daddy yace Nadiya na da cikin sa akan abinda yayi mata.

<< Azurfa Da Zinari 42Azurfa Da Zinari 44 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×