“Daddy ni fa duka ma ban fahimci komai a cikin maganar nan ba sai ta cikin da ka fada. wai ciki na Nadiya take dauke da shi Daddy? Allah na gode maka Daddy kuma shine zaka hana ni auren ta Daddy? nine ai nafi cancantar na zama miijn ta tunda ga dan mu ma zai iso duniya.
Alhaji Iro ya dubi Abdulhameed yana fadin
Baka fahimci abinda nake nufi ba kenan abdulhameed? to daina Kiran cikin Nadiya naka don babu hadi ka san hakan don da da hadi da an sanar muku don haka kar ka kuma zuwa gidan nan da wata magana wacce ta shafi Rayuwar Nadiya da cikin ta amma na yarje maka kazo mu gaisa ko wata maganar ba wanna ba amma ta Nadiya mun rufe babin ta.
Cike da farin ciki abdulhameed yake akan maganar cikin nan har ga Allah yayi matukar murna abinda kuma ya san zai farantawa mom da Daddy idan suka ji Nadiya na dauke da cikin sa dole zasuyi yadda zasu yi su kawo mishi Nadiya cikin Rayuwar sa.
Suka mike suna yiwa Daddy sallama ya amsa su yana musu fatan alheri suka shiga motar su suka fice inda daddy ya kira maccid’o da zubairu ya gargade su da kar su kuma barin motar da ta futa ta kuma shigowa gidan nan don ya gama gane ciwon kai kawai Abdulhameed zai kawo mishi suka amsa da an gama mai gida
kai tsaye abdulhameed ya cewa Tsagera da ke jan motar ya wuce da shi gidan mom ya fada mata Nadiya na dauke da cikin shi
Ai kuwa suna shiga da distinguish suka fara cin karo wanda ya rungume abdulhameed yana fadin.
“Abdulhameed me nayi maka ka zabi ka guje min ? Ka kuwa san abinda Sufi yayi min da har ka zabi zaman gidan sa? da ka sani da bakayi abinda kayi ba.
“Daddy ba wannan ya kawo ni ba na san dukkan abinda Baffa alkali yayi yayi abinda ya dace ne tunda na san shi da tsayar da gaskiya gurbin ta kaine dai baka kyauta min ba da ka saka Aka sauke shi daga mukamin sa amma yanzu dubi da yake gaskiya yake tabbatar wa ya samu mukamin da yafi wanda kayi mishi sanadi. Daddy Baffa alkali dan uwan ka ne kuma kanin ka ne .ba zan ji komai ba idan ka daga hannu ka shara mishi mari ka Isa ne ko ka hukunta shi amma ba ka ja mishi tozarta a duniya irin haka ba kaga Allah ya nuna maka iyakar ka ka tozarta shi Allah ya daga darajar sa kuma har abada ba zai tab’a ganin girman ka ba bare ya kalli alherin ka sai dai sharrin ka tunda sharrin ka ya gani bai san alherin ka tunda shi wanda kayi da shi ake kallon ka alherin ka ko muguntar ka.
Haj laila ta fito jin muryar abdulhameed din Wanda ta rungume tana shafa kyakkyawwr sumar kanshi cike da kauna da soyayya tana daga gefen Rigar shi tana ganin plaster dake manne a wurin taga wurin ya soma kamewa tana fadin
“Alhamdulillahi Abdulhameed ina ma ka zauna gida na kula da kai da kaina na san nan da nan zaka ware fiye da hakan don Allah ka zauna a gida kaji,?.
“Mom wani surprised ne fa na kawo miki wanda na san zai baki mamaki.
“Good abdulhameed Allah ya sa iyayen yarinyar nan sun yarda sun baka auren ta ne surprised din?.
Ya tashi zaune yana fadin
“Ai in da basu bani auren ta ba ma mom yanzu dole su bani domin kuwa yanzu daddyn ta yake fada min abinda nayi mata tayi ciki kinga yanzu dole na aure ta tunda nine baban cikin ta.
“Alhamdulillahi Abdulhameed da gaske kake? cewar haj laila wacce take ganin Abun KAMAR A MAFARKI.
ta mike da sauri tana kama mijin ta tana fadin
“Distinguish don Allah kaji abinda nake ji kuwa? Allah yasa ba mafarki nake ba.
Duk ta rude ta gigice ta ma rasa inda zata zauna kafin ta zauna kusa da Abdulhameed tana fadin
“Fada min ya ya akayi hakan,? dan ka ko diyar ka abdulhameed tuni na gama zana su a raina shiyasa nake ganin abun kamar a mafarki don Allah fada min .
Ya soma kwance mata zaryar da yake tayi wurin uban Nadiya wanda yace mishi yayiwa Nadiya miji amma a yau sai yake buga mishi misalin da shi bai ma gane abinda yake nufi ba amma dai ya gane Nadiya na da ciki sakamakon abinda yayi mata.
Hatta da distinguish Mukhtar biro yaji wani irin farin ciki wanda yake jin bakin rai bakin fama wkan dan dan Abdulhameed da aka jima da fidda rai da samun su tunda babu ma lafiyar da zai iya haifar su Ashe Rabon na nan akan Al amarin su da Nadiya.
“Bari na tashi abdulhameed ai kuma zama bai ganni ba dole naje gidan su yarinyar Nan na karbo ta na dawo da ita nan a dauki Dr na musamman yake duba ta da cikin nata kar ya zama a can gidan nasu ba su dayki cikin da muhimmanci ba har su kasa bata kulawar da zata bawa dan cikin ta kariya tunda ba lallai su suna farin ciki da samuwar cikin ba ni kam wannan ciki ai yafi Rayuwa ta bari ka gani in shirya muje gidan Nasu.
ta mike ta haye saman don tayi shiri.
Distinguish ma hakan da matar tasa tayi yayi mishi don matukar tsautsayi ya kai su tab’a lafiyar cikin to za a samu matsala don yanzu ne rayuwar Abdulhameed take a wurin su tunda ga zuriar sa zata bayyana.
Cikin wata irin shiga ta manyan mata Haj Laila ta fito rike da jakarta wacce take cike da kudi inda kuma distinguish Mukhtar Biro ma ya fito da rafofin kudade masu yawa yana fadin
“Ku biya store laila ki daukar mata kayan bukata irin na masu juna biyu kin kuma dauki yarinyar kuje asibiti a duba ta a duba lafiyar cikin nata ki tabbatar dai babu wata matsala don wannan cikin shine Mukhtar shine abinda na dora dukkan burina laila kin san da hakan ki je idan sun yarda sun bada yar ki taho da ita nan a kula da ita sosai idan kuma basu yarda ba sai ake tura mata Dr can kullum yana duba lafiyar ta su kuma fada miki dukkan abinda suke bukata ake tura musu sai abu na karshe kar su bari wani abu ya samu lafiyar cikin nan bare aje ga rasa shi wannan kam za a samu babbar matsala.
Haj laila tayi murmushi tana fadin
“Bari mana fatan matsalar nan distinguish Allah ya raba su lafiya shine fatan mu nima ga kudi nan na dauka zan Kai musu amma bari mu fara shiga store din mu tsinci abubuwan har kayan baby ma ya kamata na fara tanada kai dai Bari muje.
Ta dubi Mustafa tana fadin
“Muje mu Mustafa kai shafik ku tsaya a gida naje na dawo .
Mustafa Tero ya mike yana karbar key din motar Haj laila irin ta matar gwamna don ba ko ina haj laila ke shiga da motar nan ba sai harkar girma da fasa taro shiyasa ma a yau ta fita da ita don a kiyaye ta. Tero ya fafari motar mai shegen gudu ya cilla a guje don su kan su suna son hawa motar nan ta mom amma bata bari sai in ita ta ga dama kamar yanzu.
A Sahad store Haj laila tace da Mustafa ya tsaya don haka a guje yake tafe saboda yana jin dadin taka motar mai tafiya kamar fitar harsashin bindiga.
Ya faka motar suka fito haj laila na gaba Tero yana biye a bayan ta suka shiga ciki suna jidar kaya.
Al’amarin da ya bawa Mustafa tsoro musamman ma aikatan Sahad din da suka san fuskar haj laila a matsayin matar gwamna a da a yanzu kuma matar sanata
Kayan da Haj laila ta jida tamkar hauka don a motar da suka zo da ita dai duk girman ta ba zata jude kayan ba dole masu store din suka tashi motar su ta loda kayan Haj laila wacce ta biya kudi cash ta Kuma yiwa yaran store din alheri mai yawa don da gaske cikin farin ciki take.
Motar su tayi gaba ta kaya ta biyo bayan su har zuwa kofar gidan Alhaji Iro
Ganin motar Haj laila irin ta fasa taro yasa aka bude mata kofa ba tare da su maccid’o sun gane mutumin da aka ce kar su kuma bari su shigo bane.
Motar kayan ma ta mara musu baya har farfajiyar gidan suka faka
Haj laila ta wuce cikin gidan kai tsaye tana fatan ta dora Ido akan Nadiya da ganin dan cikin ta.
Haj Aliya tana zaune a falo tana duba kayan lambun da ta tura a siyo mata green bean’s da kara’s
Kamshin turaren haj laila ne ya fara isowa hancin haj aliya kafin sallamar haj laila wacce take dauke da murmushi.
Da sauri haj Aliya ta dago tana amsawa har tana mata sannu da zuwa duk da bata gane ta ba amma kuma tana ganin kamar ta san fuskar amma kuma ta manta inda ta san ta
Haj Laila ta zauna akan kujera yayin da haj Aliya ta nufi fridge ta dauko mata ruwa da lemu ta dawo ta zuba mata ta karba ta sha tana fadin ta gode,
“Haj Nadiya nazo gani don Allah in tana kusa a kira min ita na ganta kafin mu dora da karatun gaba.
“Tana nan kuwa bari na taso miki ita na san tana nan tana baccin ta na ibada.
Ta wuce ta nufi sashin su Nadiya da fati ta sami Nadiya tana taunar goro tace tazo ana Magana.
Nadiya ta mike cikin ta ya fita sosai a wata biyar amma zaka ce a wata bakwai ko takwas
Haj laila ta mike da sauri tana rungume Nadiya hannun ta akan cikin Nadiya tana ta shafawa tana fadin.
“Sannu da kokari Nadiya sannu kinji Allah ya raba ku lafiya.
Nadiya dai bata san ta ba amma sai da ta gaishe ta tana amsawa da ameen.
Haj Aliya dai idon ta akan su har Nadiya ta zauna s gaban matar itama ta zauna kan kujera yayin da aka soma shigowa da kaya ana ajewa
Haj laila ta dubi haj Aliya tana fadin
“Haj ni sunana haj laila matar mai girma Mukhtar Biro wata kil ku san sunan.
Da sauri haj Aliya ta gane matar biro ce ta kumayi murmushi tana fadin
“Kwarai kuwa haj na gane ki ya gida?
“lafiya lau alhamdulillahi nazo na duba Nadiya ne in kuma Roki alfarmar ku bani ita na tafi da ita gida na don kulawa da cikin ta tunda ku wata kil ya zame muku lalura tunda nan kam kasar hausa kuna gudun abun kunya amma kuma mu a gare mu wannan cikin na Nadiya yafi mana AZURFA DA ZINARE.
“Ban katsi numfashin ki ba haj ban fa gane abinda kike nufi ba.
Ganin maccid’o sai shigowa suke da kayayyaki yasa haj Aliya ta tsayar da shi tana fadin
“Kai wai daga ina wannan kayan?
Haj laila ce ta katsse ta tana fadin
“Nice nan na kawowa jika na haj kuyi hakuri fa duk da munyi muku kutse to wallahi bamu san da maganar cikin nan ba sai yau shiyasa ma na taho don Allah kuyi mana afuwa .
Haj Aliya ta mike tana fadin, “To Bari na kira mai gidan haj shine mai iko amma ni umurni nake bi. Ta haura saman benen inda haj laila ta maida duban ta ga Nadiya wacce ta gane uwar Gayen nan ce taxo duba ta? To akan me zata zo duba ta har da da wadan nan kayan su kuma na meye?
Haj Aliya ta sauko tare da daddy Alh iro wanda yake duban haj laila
Ya zauna yana fadin
“Sannu da zuwa Haj
ta rusuna tana Fadin
“Yauwa alh barka da yamma
suka gaisa ta soma gabatar da kanta har ta Kare Kafin Daddy yace
“Allah sarki sannu haj ya mutanen gida?
“Lafiya Lau alhamdulillahi Alh dama abdulhameed ne yazo da maganar cikin Nadiya shine Al amarin yaxo faduwa ce mai kama da zama shine nazo na duba Nadiya ga kuma kaya nan babu yawa kuma muna rokon alfarma alh don Allah ka bamu Nadiya wurin mu har ta haihu don gaba daya ni da mai gida na mun dora dukkan burin mu akan ya’yan Abdulhameed sai dai kash Allah da ikon shi aka ce babu abdulhameed babu haihuwa saboda ya hadu da lalura amma da yake Allah mai rahama sai gashi Ashe haduwar su da Nadiya Allan ya kaddara mishi samun zuria shine muke neman alfarmar ka bamu auren ta tunda Allah ya saukar da wannan ayar akan su kaga shine yafi dacewa da auren ta Kuma su haifi dan su cikin aminci su rike kayan su .
Daddy ya gama sauraren ta kaf bai katse ta ba har ta dire kafin yace mata
“To alhamdulillahi haj naji dadin bayanin ki kuma na gamsu amma idan na fahimce ki saboda abdulhameed baya haihuwa ne zaku karbi dan ko diyar? kuma ma ai cikin kawai yayi mata amma dan da yake cikin ta ba nashi bane natane tunda ba aure sukayi suka same shi ba . to kar ma naja ki da nisa haj ke mace ce kin tab’a ganin inda mace ke neman aure? ko kuwa Dan ki kema naki ne bashi da ahalin uba namiji? to ki sani ba zanyi magana da ke ba ke mace ce amma idan akwai uban danki ki turo min shi sai muyi magana maganar kayan nan Kuma ki koma da su ina ganin dan cikin ta shine naku to ku bari ya iso duniya sai ku hidimta mishi da komai amma ni ma ku barni da tawa yar tunda ai sai da ta kai minzalin amfani karin yaron ku ya gani ya Kuma amfana don haka ki koma da su ki tura min uban dan ki muyi magana zaifi fahimta ta akan ke tunda ke matar aure ce.
“Ayi hakuri alh duk da na gane akwai fusata a cikin maganar ka kuma in ma ka fusata din ba laifi bane amma ayi hakuri a karbi kayan tunda nazo da su bai kamata na koma da su ba kuma in sha Allah yanzun da na koma gida zan turo mijin nawa a dai yi hakuri don Allah.
“Babu komai haj ban fusata ba Ina dai fada miki kamata ne da abinda ya kamata zamu fi fahimtar juna ni da mijin ki shine namiji dan uwa na kuma ko ba komai shi in ya bayyana a neman auren dan sa daraja ne amma ke faduwa ce ace uwa macece taxo nemawa dan ta aure kinga zaki bar kokonto cewa anya dan ki yana da uba? an san kowa yana da uwa amma ba kowa keda uba ba .
“Haka ne alh nagode amma don Allah ka karbi kayan nan.
“A a Haj bana son musu da jayayya kin tafiya da kayan ne abinda ka iya fusata ni da gaske Kai maccid’o ku kwashe su ku mayar motar maza ku kwashe su .
tuni kuwa su maccid’o suka soma kwashe su suna mayarwa mota.
“Amma Alhaji banji fadi ba da baka karbi kayan nan ba to Zan iya tafiya da Nadiya can gida na?.
“A a kije dai haj idan akwai yuwuwar zuwan nata idan mai gidan ki yazo zai taho miki da ita .
Ba don haj laila ta so ba ta mike tana fito da kudin daga jakarta ta dire a gaban Nadiya tana fadin
“Wannan dai ni bawa surukata kyauta don allah kar kace komai .
Kallon da yayiwa Nadiya ne yasa ta mike da sauri ta bar wurin yayin da haj laila ta dube shi tana fadin
“To Alh nagode wata kil kuma ka kullaci abinda ya faru a tsakanin mu amma don Allah don ANNABI kar ka haramta mana yarinyar nan da dan cikin ta idan ka duba da kyau wata kudurar Ubangiji ce ya zana hakan a tsakanin mu da su in sha Allah yau din nan uban yaron nan zai zo gareka.
“Babu matsala ki sauka lafiya mun gode
Cewar daddy wanda ya riga ta hayewa saman benen shi ita kuma tayiwa haj Aliya sallama ta wuce
Distinguish Mukhtar Biro Yana shirin fita ne motar haj laila ta shigo motar Sahad store biye a bayan su ya tsaya
Ya tsaya har suka fito yaga ma aikatan Sahad suna sauke kayan nan ya dubi haj laila yana fadin
“Ya akayi ne naga ana sauke kaya nan?
“Basu karba ba wai a dawo da su ni kuma nafi ganin suna kullace da abinda ya faru ne don shi mai gidan ma yace na tura uban abdulhameed suyi magana mace bata neman aure kai ko kudin da na bawa yarinyar nan bai bari ta karba ba .
“Yaya kika ga yarinyar tana cikin koshin lafiya da kulawa kuwa ? .
“Yarinya fa lafiya lau take amma ban hangi nasara a tafiyar tashi ba don a fussce yake gaskiya ni na fahimce shi.
“Bari naje yanzu gidan nashi duk da ina da uzuri mai karfi Amma wannan zuwan yafi uzurin bari naje naji abinda yake nufi.
Ya figi mota ya wuce zuwa gidan Alh iro
Haj Aliya ta haura saman ta samu Daddy wanda take fadin
“Kaga mutanen nan da ba tsoron Allah suke ba wai sune suka dawo suna son karbar cikin nan?