Ya gama wayar ya ajiye yana zaton yayi hikima amma sai Abdulhameed yace
“Daddy ba haka ya kamata kayi ba. In kayi haka ai zaka sake bata al amarin ka da uban yarinyar nan ni nafi ganin ka sa a dauke Nadiya daga garesu kafin su zubat mata da cikin ta In yaso sai mu bar Nigeria ni da ita kai da mom in yaso idan ta haihu mu karbi dan mu dawo kome za ayi sai ayi amma yanzu in suka bata maganin da cikin zai zube kafin aje a kama su fa? kuma in anje ga hukumar anya mutumin nan ba zai kayar damu ba ? kuma in anje ga hukumar kace me yayi mana? In kace cikin yarsa kake so da yace zai zubar da wane sadakin na samu amsa sunan uban cikin,? To Daddy sake shawara don zaka jawo mana mu rasa abinda ni da kai muka dora ruhin numfashin mu.
Da wani irin tsoro kuwa distinguish ya ke duban haj laila da abdulhameed don ya gama yarda abinda abdulhameed din ya fada shine kawai mafita.
“Na gamsu kuwa da wannan maganar abdulhameed don zanfi son ace uban yarinyar nan ya kai mu hukuma akan laifin mun saci yarsa mun bar Nigeria da dai ace kaine ka kai shi hukuma don zai zubar da cikin ta gara ka ma sauya shawara wallahi gara mu fice da yarinyar nan zuwa k’asar da bai san inda muka nufa ba yafi sauki da ya kashe mana jikan da muka dora rai.
cewar haj laila wacce dyk ta rude ta kidime.
“Ai ko yanzu bata baci ba laila bari nace in sun kwaso ahalin iron su fidda min mai cikin su ajiye ta a wuri na musamman kinga daga nan sai mu fice da ita su kuma asake su ba zamu dawo ba sai ta haife kinga zamu rike namu mu mayar mishi da tashi in ya bada auren ta shi ya so in kuma bai bayar ba ma mu dai mun tsira da dan ko diyar shari a kuma na shirya yin ta daga nan har zaila .
Ya dauki wayar yana kiran commander amma yaji wayar is swech off ya sake kira nan ma a kashe sai kawai ya figi makullin motar ya fice ya bar haj laila da abdulhameed cikin zullumi da tashin hankali mai tsanani.
Wani matsiyacin kallo Nadiya ta aunawa Kaisar mai kama da zata juye idanun ta a k’asa.
“Banji me kace ba? ta fada tana mishi kallon wofi.
Yayi murmushi yana shafa sumar kanshi yana fadin
“Cewa nayi yane fa yau ne ranar zuwa awon nan ki shirya muje na kai ki ko kina sane da yau ne.
ta ja tsaki tana hararar sa take fadin
“Wai kai a wa ? kuma a me kake min wannan shisshigin don Allah? ka fini son rayuwar tawa ne ko meye ? to ba zanje ba dan iya na garin dan iyau.
“Yi hakuri ranki ya dade mu je a duba min baby na da lafiyar su.
“A gidan uban wa suka zama naka? wai kai don Allah ba ka da zuciya ne ?.
Ya kuma yin murmushi har yana daraww.
“Ina naga zuciya akan ki sweetie? wallahi tuni na ajewa kare ya dauka skan ki babu abinda ba zan iya ba kuma kina mamaki ne da nace baby nawa ne? a komai Nadiya zan iya fansar da Rayuwa ta akan abinda ya shafe ki kamar yadda nayi ta ryuwa ta don tseratar da taki rayuwar. don haka cikin nan ma Nadiya nawa ne har abada Ina son shi ba kuma zan ki shi ba ko da kuwa duka duniya zata juya mishi baya ke ni zan hana shi ma sanin waye shi don ni zai bude ido ya gani ya kuma kira ni da daddy ko Abba saboda gatan da zanyi mishi irin na wanda uba keyi ne my sweetheart so sorry walk up mu je asibiti.
Ta zuba mishi ido tana ganin kokarin shi matuka gaya na jajircewa akan ta da wl amarin ta sai dai har gobe bata ji yayi mata bajintar da zata yaba mishi ba bare taji ya kai wanda zata kalla a matsayin masoyi bai Kai ba har yanzu.
Taja tsaki tana kwantawa akan gadon ta ta bar shi tsaye rike da katin nata na asibiti.
Ya mika hannun ya riko hannun ta yana matsawa yana fadin
“Yi hakuri ranki ya dade muje na yau sai ki kulle zuwa gaba daya kinji ?
ta fincike hannun ta a fusace tana fadin
“Kar ka kuma rike min hannu malam kaji bana son iskanci.
“Ai Ni ba dan iska bane Nadiya akan ki ne kawai nake hakan .
Haj ta shigo tana fadin
“Ita da wa nake jin tana daga murya Kaisar?
Ya dubi haj Aliya yana fadin
“Mama asibiti na tuna mata da zuwa yau ne ranar awon ta shine wai ba zata je ba .
“Kuma kai da yake sauna ne ka tsaya tana daga maka murya baka kwakkwada wa kahira mari ba Kaisar ? to ka koyi yadda ake koyawa irin ta ladabi da kace Eh tace A a ka jibgi Yar banza ta haka zata gane tarbiya.
“Haba mama da cikin za a dake ta? Ai ita mace bata kamaci duka ba musamman ga namiji wanda zai ware kwanji yayi dukan ko za ayi mama ai da hab’ar riga ya kamata ayi kamar za a share musu k’ura.
“Ai kuwa wahala bata karewa namijin da zaiyi hakan ba Kaisar amma dai kai ka zama jajirtacce, ta dubi Nadiya tana fadin.
“Shi ne yake kallon cikin ki a abinda zai hana a jibge ki amma ni wallahi ba cikin da daya ba ko cikin yaya goma ne da ke zan nadeki ne na nadi wofi tashi kibi shi sakarai dabba da ke . banda Kaisar din ma da yake dan halal ni yaushe zan lalace wurin shegen cikin ki har kin sami mai kulawa da ke kike iskanci? wanda ya kamata ma ya yi miki hidimar da yaron nan yake miki ma bai san halin da kike ciki ba sai shi amma kike wulakanci yadda kike so ai shi ya fi ki ma wallahi da ya san shegen cikin ki amma yake tattala lafiyar ku banda shi ke son kije ai ni don ta ni ki tabbata a yadda kike uban wa kikayi wa?
Dole Nadiya ta mike tana jan baki gaba suka fice
Motar Kaisar taki tashi ga alama karfen nasara ne da bashi da tabbas dole ya barta ya karbi key din ta malam Ango Nadiya naja mishi tsaki har da su zagi dai ta hada suka fice a motar suka nufi asibiti.
Fitar su babu jimawa sai ga jami an tsaron Soji sun iso gidan Suna neman alh iro
Maccid’o ya sanar mishi ya fita inda aka sanar mishi ana son ganin su shi da ahalin sa duka a barikin sojin
Kan kace me,? Haj Aliya da Alh iro har da fati an wuce da su barikin Soji.
Keena da luba da suka fito daga banki sun fidda kudin da shaid’an ya tura musu zasu nufi gidan su Nadiya kenan motar ta zo ta wuce su inda idon keena ya fada kanta ta kuma ga Kaisar da yake jan motar tayi maza ta daki luba da karfi tana nuna mata motar da kuma Kaisar.
Luba ta bi hannun keena da kallo kafin ta finciki hannun ta suka danna mota suka marawa motar su Kaisar baya.
“Don uban ki luba maza ki daukar min lambar motar kiyi sauri kar ya shige cikin go slow ki barni da cizon leben da yatsa.
Luba da take rike da waya tuni kuma luba ta dauki lambar motar ta kwafe a wayar ta tana fadin
“Na dauka keena huta dannawa tsoho na ashar don uban ki yana kabari baki bishi da ADDU A ba kike zagin shi .
“Yi hakuri kawa ta bana cikin hankali na ne shiyasa amma yanzu tunda kin dauka Allah yayiwa Boss din ku rahama ya yafe mishi.
“Mtss! Luba taja tsaki tana fadin, “Wahalalliya kawai.
Keena ta juya kan motar suka dauki hanyar gida sukayi shirin zuwa nijar ina da zasu bi motar haya don tafiyar tafi karfin su a motar su daga bauci zuwa Niger akwai tafiya don haka suka tafi a motar haya.
Distinguish ya sami wayar commander yake fada mishi kar a hade su wuri daya a aje su kowa da wirin sa don akwai mai juna biyu a cikin su .
Alhaji Iro yana zaune a inda aka ajiye su shi da haj Aliya da fati yana fadin
“Uhum ni zanga wanda ya Isa ya saka ni abinda banyi niya ba Aliya.
“Saboda ka ce mishi haka ne wai yayi mana wannan wulakancin? ni yau naga ikon Allah wannan fin karfi haka?
Ya lalubi wayar shi yana fadin, “Ina Nadiya da Kaisar?
Haj Aliya tace, “sun tafi asibiti awo.
“Alhamdulillahi bani wayar ki aliya na bar tawa a gida.
Ta mika mishi wayar ya lalubi lambar Kaisar ya kira ya kuma dauka.
“Kaisar kuna Ina? Ya tambayar. “Daddy muna asibiti.
“to in kun gama kacewa Nadiya nace ku tafi jama are sai na ce ku dawo kana ji na?
“Daddy me kuma zatayi a jama are?
“Akwai wani dalili ne da nake son ta faku Kaisar ka tabbatar da ka kaita jama are kaima ka tsaya a can zan kira ku kaji?.
“Eh Daddy bari na bata ka fada mata don zata iya cewa ba zata je ba.
Ya mika mata wayar Daddy ya fada mata zuwa jama are ba don ta so ba ta amsa.
Suna gamawa kuwa suka dauki hanyar jama’are rayukan su cike da neman dalilin wannan tafiya
Distinguish Mukhtar Biro ya iso barikin sojin tare da haj laila da abdulhameed inda ya iske alh iro tare da haj Aliya sai kuma fati.
Commander ya tarbi distinguish Mukhtar Biro tare da matar sa haj laila sai abdulhameed wanda yake dogara sandar karfe irin ta Ya’yan manya.
Distinguish ya dubi haj laila yana fadin.
“Wannan itace Nadiyar ? Ya fada yana nuna Fati?
Ta kada kanta tana fadin
“Ba ita bace.
“Saboda haka ne ka sa aka kawo mu nan? Cewar Alhaji Iro.
“Eh don na na gane sai nayi maka hakan ne zaka gane akwai maza a gaban ka Ina ka kai yarinyar nan iro?
Daddy yayi murmushi yana fadin “tana can inda za a zubar mata da cikin nan in don hakan yasa akayi min wannan tozarcin to ka makara kuma zan nemi hakki na a gaba.
Da sauri haj laila ta dafe kirji tana fadin, “Inna lillahi wa inna ilaihir Raju un ya kashe ni sai ta soma kuka.
Alhaji Iro ya dubi commander yana fadin
“Ban fa san abinda nayi ba aka kawo ni nan idan don wanna ne kotu zamu hade da shi a sallame ni in Kuma yana da wata magana yayi a sallame ni.
“Babu wata magana sai ta a saka ka fiddo min yarinyar nan in kuma ka zubar da cikin ta ne to wallahi ka shiga matsala har Rayuwar ka.
“Daddy me yasa zaka sa akawo su nan ? kasa a sake su don banji a raina zai zubar da cikin nan ba ya fada ne kawai.
“Daddy don girman Allah da gaske ka sa an zubar da cikin Nadiya?
Abdulhameed ya fada idon sa fall kwalla.
“Ba a zubar ba abdulhameed amma ina mai tabbatar maka da za a zubar din kaga dai wulakancin da mahaifin ka ya kuma yi min ko? banda wanda yayi min ya kuma kawo ni wurin soji sai kace nayi mishi SATA?
“Ka yi hakuri Daddy don Allah kayi hakuri.
Ya juyo yana kallon uban yana fadin,
“Kaga ni ko Daddy? kaga abinda kaja? sai da nace maka in kayi haka kara lalata abun zakayi to ka sa sake su .
“Ba zan sa a sake su ba abdulhameed sai munyi komai a rubuce ta yadda hukuma zata zama witness da na nemi cikin nan na rasa zamu dasa shari a da shi daga nan har datissara.
Abdulhameed ya tsaya sai an sallami Alh iro da iyalan sa yayin da distinguish ya ce sai anyi rubutu don suma su Commander su zama shaida
Dole dai aka sallami su Alh iro inda distinguish kuma ya rubuta takarda ya bayar ajiya s matsayin shaida
Yakumbo Halima kuma sunyi ban tafin makafi ta taho duba Nadiya don haka Daddy yace da Kaisar su juyo gida kawai
Yakumbo Halima ce ke ta masifa tana fadin
“Ni kam da ina nan shegen mutumin nan yazo babu abinda zai hana na cacume shi da kokowa don wulakancin nashi ya wuce malaman gari azo har gida da soji kamar an kama wani dan bandit? In banda ma rashin kunya dan nashi ya keta haddin yarinya kuma ake maka bita da kulli? kaima Alh sai da nace maka a zubar da cikin nan kaki da an zubar da yanzu sai menene kuma? .
“Ba zan zubar bane Halima saboda kisan kai ne kuma bamu san waye wanda Ubangiji zai halitta ba wata kil wani shehin malami ko wani bawan Allah mai daraja anya ba har da kashe kashen nan bane abinda ya hana duniya zaman lafiya? to ko da basa son shi halima ni Ina so bare kuma suna so na kuma gane suna so shiyasa zanja su a k’asa wallahi kuma ki sani babu wanda ya Isa ya karbar musu dan nan ko waye shi . baki lura ba ne,? Da Allah ya tashi yiwa cikin yarinyar nan gata ba sai ya jarrabi uban da rashin haihuwa bayan ya illata yarinyar nan? to duk haukan da suke kenan kuma wallahi karya suke su fada min sadakin nawa suka biya da dan su zai amsa sunan uban cikin Nadiya? kuma wannan wulakancin da yayi min zan nemi hakki na wallahi.
Abdulhameed fada yake sosai akan abinda uban sa yayi don dama tini ya hango ya Kara rikita al amarin gashi kuma ya damalmala shi .
“Daddy ka lalata al amarin nan don haka na fidda ka zan saka Baffa Alkali na san zaiyi nasarar da bakayi ba na Kuma san adalcin da Baffa Alkali yayiwa baban Nadiya dole zaiji kunyar musa mishi alfarmar da zai nema don haka Daddy na cire ka ka barni da Baffa Alkali wanda na tabbatar da zai shawo kan komai.
“Kar ka sake ka saka min Sufi a cikin sabga ta Abdulhameed don wannan mutumin na rufe babin sa In kuma ka saka min shi a harka ta da kai da shi duk zanci uban ku wallahi in kuma ka musa kaje ka sanya min shi din sakarai dabba da kai mahaukaci wanda bai san ciwon kansa ba har Sufi ne abin rike wa a gare ka masoyi? to ni Sufi baya cikin mutanen da suke masoya na taki kad’an ma zan nuna mishi kowaye shi a wuri na.
Abdulhameed yayi murmushi yana fadin
“In kun samu sab’ani da dan uwan ka daddy nima mun samu sab’ani kenan? wallahi Daddy ko cewa kayi Baffa alkali makiyin ka ne ni a masoyi yake wuri na babu abinda ya shafe ni da matsalar ku tare na ganku cikin ku daya ko kokowa kuke kai da shi zan dauke kaina ba zan shiga tsakanin ku ba don haka ko neman aure na zan tura Baffa Alkali ne zan tura ba kai ba shine Mai min komai ba kai don haka yanzun nan zan same shi na sanar mishi Daddy sai dai kayi hakuri.
Ya fada yana juyawa yana dogara sandar sa ya fice inda distinguish Mukhtar Biro yabi bayan Abdulhameed din da idon shi cike da mamakin yaron.