Tafiya mai nisan zango daga bauci zuwa jamhuriyar Niger mota ta sauke luba da keena a garin jibiya ta jihar katsina daga jibiya kuma mota ta dauke su zuwa Niger.
Keena tayi mamakin yadda akayi luba ta san wannan wuri amma kuma da ta tuna itama yanzu gata dalili yayi dalili ta sani
Dajin Allah ne guda wanda babu gida ko alamar akwai wani mai ruhin numfashi sai tarin itace da sarkukin daji
Keena kam tsoro mai tsanani ya kamata amma ta dubi luba da take tunkarar wata katuwar itaciyar bishiyar kuka mai girman gaske wancce duk tafi itacen . . .