Keena na fitowa tayi arba da malam Ango wanda rana ta iske shi yana ta hada uban zufa amma bai damu ba ya kasa motsawa daga inda yake idon shi kur akan kofar hostel sai kawai yaga keena ta fito ya kuwa mike da sauri ya nufe ta yana fadin
“Sakeena ke nake ta jira wallahi hankali na a tashe yake matukar ban ganki ba don Allah ki tausaya min mana ga dan karan rake na ruko miki.
Wani abu mai kama da tausayin sa ya tsurga mata ta dube shi tana karba tana fadin
“Nagode baba wmma don Allah ka fahimta mana? ai kai musulmi ne ko ?
Ayayi maza ya amsa yana murmushi don yadda yaga fuskar rahama a fuskar ta a yau ba kamar ranar nan da tayi mishi jajayen idanu ba.
“Kwarai kuwa ni musulmi ne sakeena.
batayi mamakin yadda akayi y san sunan ta ba tunda dukkan al amarin kaucewa hanyar Allah ce.
“Kayi hakuri baba don Allah ni din matar aure ce ina da miji ka kuma san a shari ar mu ta musulunci babu bibiyar macen aure ga wanda yake mai hankali irin ka tunda kaima na sani kana da iyalin nan kuma ba zaka so ganin wani Yana bibiyar su ba haka ne,,?
ta tambaye shi ya kuma amsa mata da haka ne.
“To don allah kayi hakuri ka daina bibiya ta kar ka jaza min matsala tsakani na da miji na .
“To na fahimce ki sakeena amma Allan ya Sani ba zan iya daina bibiyar ki ba don ni da kaina ban san inda soyayyar ki take a zuciya ta ba abu ne dare daya wanda ban shirya mishi ba don haka sai dai mijin ki yayi hakuri har Allah ya yankee min ko kuwa shi ya hakura ya bar min ke.
A fussce keena ta kalle shi jin abinda yake fada.
“Wato duk lallamin ka da nayi don mu rabu da kai lafiya baka gani ba ko? to billahilazi na kusa na kwakkwara maka ruwan ashar tunda baka san na cikin shago ba ya Ina nuna maka ban son ksna zuwa nan kana wani kara likeww da makaleewa? to Allah ya sa na kara ganin ka nan kofar wallahi sai na saka anyi maka zigidir an kuma baka kashi .
ta juya zata shige sai kawai taga malam Ango ya bita da sauri yana fadin
“Wallahi sai dai kisa ayi min duk ma abinda za ayi min in ma kashe ni ne duk ayi akan ki ba zan ji komai ba wallahi I love you bila adadin .
A guje keena ta kwasa da gudu malam Ango kuws ya rufa mata baya shima a guje yana son kamo ta.
Ai kuwa keens ta kwalla ihu ta maido kofar ta datse .
Ihun keena ne ya taso luba daga baccin da take ta fito tana haduwa da keena tana mayar da numfashi irin ta sha da kyar din nan .
“Ke da waye keena,?
luba ta tambaye ta .
“Ni kam luba ke kika jawo min wannan janhurun masifar ni da waye banda wancan nataccen da tsautsayi ya zaboro min? dubi fa wai rake ya kawo min duk yadda naji tausayin sa na so ya gane hanyar jirgi daban da ta mota alma kamar na kara Iza shi har da neman kamo ni luba wallahi dole gobe mu dauki hanyar Niger don na rantse da Allan kin gama kwanciya kiyi bacci ni ina fama da bak’in ciki wallahi kinci uwar karya kin kwana da yunwa.
Luba ta kyalkyale da dariya tana fadin
“Wannan soyayya keens ta gaske ce kullum da abinda za a ruko miki yau awara gobe rake,? kai don Allah kija zaren yayi tsawon mana wata Rana dakwalwar kaxa za a kawo mana bani raken na tsotsa tunda kin tayar da ni daga bacci na in kuma kin shirya gobe mu dauki hanyar Niger ai in ba komawa mukayi ba ai ba zaki barni na huta ba .
“Ai wallahi ko ban shirya ba sai na shirya gara da kika bada kai bori ya hau amma wallahi da kin gama bacci irin na mutane dai sai dai ko kiyi na zomo.
cewar keena wacce ta watsawa luba raken da aka data aka zuba a leda.
Washe gari kuwa suka daaka sakamakon suka dauki hanyar Niger a motor haya don haka kafin azuhur sun Isa Niger dajin da ba I’mani yake.
A yau kam sun tara’s da wasu mata a tare da ba I’mani wanda ya na ganin su ya kyalkyale da dariya ana fadin.y
“Ta kwabe kenan,? ai tini na hango hakan.
Suka zube a gaban ba I’mani luba tana karanta mishi kuskuren da aka samu na bayar da lambar mota da ba ita ce ba .
“Me kike so ayi yanzu ? cewar ba I’mani wanda yake hararen su luba da Keena.
Keena da taji hushin tambayar tayi maza tace.
“A mayar da aikin kan shi wancan da muka zo don shi mana shi wancan ai tsautsayi ne yasa akayi hakan dashi yana nan yana nace min sai kace jela duk inda nayi yana biye dani don jiya ma banyi bacci ba sai faman muguyen mafarkai nake da shi har yana biyo ni daki na?.
Ba I’mani ya kara hade fuska yana fadin
“Ba za a iya jiya aikin Nan ba tunda ya riga ya kama inda aka aika shi sai dai ku dauki kaddara amma me ya sa kuka kawo lambar motar shi bakuyi bincike ba?.
“A a fa gaskiya ba I’mani ba haka nake so ba ni fa ga wanda nake so ta yaya wani jemammen tsoho zai dafe min yana min jelen zarya har da wata shegiyar awara da rake? kawai ni yanzu ka san yadda zakayi dani a juya aikin nan ya koma kan Kaisar haka nake nufi kuma don haka nazo nan din amma me zai kawo ni in na san babu biyan bukata.
Cewar keena da tayi maganar a fussce.
“Ke hattara ki san abinda zaki fada ba za a juya Aikin ba sai menene,,?
shima ba I’mani ya fada a fussce yana nuna keena da yatsa.
“Ayi hakuri ba I’mani bata san ka bane.
Cewar luba da ta tabbatar zai yiwa keena wani shaid’ancin ne tunda ya nuna ta da Yatsa.
“Barta na sanar da ita waye ni tukuna kafin ta koyawa harshen ta linzami.
Yana buga ruwan da suke gaban shi sai ga keena an daga ta a sama ta rabu da k’asa kuma ta tsaya cik a saman iska tana wulla kafafu.
“A nan zata kwana tunda bata da kunya ai baki fada mata wurin ba I’mani ta zo bane? shine take min rashin kunya,?.
“Ayi mata hakuri ba I’mani kawata ce don Allah ayi hakuri.
“Zata ci arzikin ki amma da a yau din ta kwana a dajin nan taga aljanu mara’s I’mani tunda itama nan ta iya rashin kunya.
Ya nuna keena da yatsa sai ga keena ta fado k’asa tum tana mayar da numfashi tana kwalla.
.
“Godiya take ba I’mani yanzu a taimaka mana ko karya wancan aikin ne ayi in yaso sai mu sake biyan wasu kudin a sake mana sabon aiki don Allah a taimaka ba I’mani.
Cewar luba wacce tayi maganar tana kwantar da murya cike da ladabi.
“Wannan aikin naku fa bashi da makari sai an sadu ko dai ayi aure ko kuma ayi zina cikin biyu daya za ayi kafin ya kare in Kuma ba haka ba to haka za a tsaya kullum yana makale da ita yanzu haka ma gashi can yana jiran dawowar ku don haka tana da zabin abinyi ku tashi ku bani wuri na gama da ku.
Yana gama fadar hakan ya bace daga inda suke suka daina ganin shi inda keena ke fadin
“Ni kam luba ke kika cuce ni wallahi.
“Da na taimaka na kawo ki shine na cuce ki ? ke baki ga laifin ki ba sai nawa kike gani ? uban wa ya nuna lambar motar nan in ba ke ba? har da ashariya kika durawa uba na bai tab’a samun tagomsshin ADDU AR alheri daga gareki ba duk ma abinda ya faru ba ke kika jawo kayan ki ba? ai yanzu sai muje ki kiyi zabin daya cikin biyun da ya zana ko dai ki rufe Ido ki aure shi ko kuma kawai ki bashi kanki kuyi zinar .
“Wallahi ba zan yi ko daya ba ni zan kalli wannan jemammen tsohon har na yarda na bari ya tab’a jiki na? Allah ya sauwake wallahi wallahi ba zan yi ko daya ba.
“Amma kuwa ai gara shi da ba allah tunda shi ko banza banji yana wari ba kuma duk k’azantar sa yana duban gabas babu datti a tare da shi .
Keena ta dubi luba tana fadin
“Har anzo nan gabar da zakiyi min gori? lallai kin cika tsinanniya luba tunda har kikayi min wanna sanadin smma ba komai watan bakwai shi ya jawa shamuwa.
“A a keena sai fa in kinso kiga laifi na amma meye abin gori a nan? daga fadar gaskiya sai cibi ya zama kari kari kuma ya zama kababa? .
“Kar fa ki gaya min maganar banza luba don wallahi yanzu ne zamu fasa tangararen bala I da ke .
“A a Allah ya baki hakuri keens da nasan hakan ai da ban fara kawo ki ba ni gani nayi kamar mafita na kawo miki smma kiyi hakuri.
“Kifa saurara min luba ya ishe ni haka don Allah ki kyale ni da wannan banzan surutun naki ki barni kawai da wannan tsinannen zindikin mushirikin macuci shima in duddurawa uwar sa ashar.
“A a keena kin manta abunda yayi miki ne kike neman zagin sa? to wallahi rufawa kanki asiri nice zaki zaga ki zagi banza ba smma shi wancan kar ki soma don ba banza kikaji ana ce mishi bai da I’mani ba kar ma ka ja wa kanki wallahi kame bakin ki .
“Uban uban uwar shi shege tsinanne Allah ya isa kudi na wallahi .
Da sauri luba ta finciki hannun keena suka auna a guje saboda hayakin da ya soma sauka a dajin abinda ya tabbatar wa da luba ba I’mani ne yake shirin wanzuwa a gaban su don haka tuni keens ta kame bakin ta daga aunawa ba I’mani ashar.
Da kyar suka fice suna shessheka.
Da Haka suka dawo bauci inda kuma suka tara’s da malam Ango yana zaman jiran su amma keena ta juya bata ma shigo hostel din ba tace da mai napep din ya juya da ita zuwa hostel din su surayya inda ta tare a can suka daina haduwa da malam Ango wanda yake cikin tsananin damuwa da rashin ganin keena wacce ita kuma take cike da tata damuwar ta rashin cikar buri akan Kaisar.
Washe gari masu tsaron kofar gidan Alh iro suka wayi gari da gane baki sun shigo gidan inda su maccid’o akayi shirin ko ta kwana suka fito da makamai akayi sabon washi su adda da barandami tsitaka da awartaki duk an fito da su ana sauraren dare.
Dare na rabaww kuwa su zarto suka diro a gidan Alh iro ai kuws su maccid’o da sukayi kwanton bauna aka hade da su zarto.
Kamar shiri su maccid’o sukaji ana kama kwanon rufin gidan da son haurowa dama SUNYi shiri tuni don haka suka kwashi kayan fadan su barandami tsitaka da Adda da gariyo suka nufi ta bayan da aka hauro sai kawai ga su zarto suna durowa ai kuwa fusatacci irin su maccid’o da gwarma da zubairu suka soma dauki ba dadi duk da su zarto suma da nasu kayan fadan amma ba su da shiri irin na su maccid’o don haka tuni suka soma sauke musu aiki suna sarar su. Tuni kuwa suka nemi matsera suka soma kama katangu suna haurawa shi kam zarto da maccid’o ya kusa saukewa kafada da kyar ya sha don ma karfin hali irin na muguye da taurin ran tsiya
Kaisar da ya kai Nadiya jama are bai baro jama are ba sai magaruba ya isowa bauci kuma ya zame wurin king wanda ya yada zango a nan a cewar shi ba zai koma gidan ba har sai su Daddy sun dawo
Kwana biyu da Kai Nadiya jama are ya dauki king suka tafi jama ark don duba Nadiya ya kuma kwasar mata kayan bukata rututu.
Suna tafe a mota kings Yana ta zuba masifa akan nacin Kaisar ga Nadiya duk da ba wani son shi take ba.
Kaisar yayi murmushi yana duban kings yana fadin
“Kayi hakuri king ba laifi bane laifin zuciya ta ne da ta kasa hakura da soyayyar Nadiya Kuma a raina nake jin na kusa cimma buri na tunda har gobe ban daina mafarki da na aure ta har ta haifa min baby girl ba.
“Dalla malam jeka kayi wanka ni wannan makauniyar soyayyar taka wallahi ko a labari kirkirarre ban tab’a Jin kalar sa ba ko da so ya zama cuta hakuri sai ya zama magani.
“Karya ne king wallahi wanda yayi misalin nan bai dora kwarya gurbin ta ba comfearing to your self ni da na jaraba maganin hakurin cutar so bai min magani ba don na kai kalmar inda kuka dora ta ta ma sai naga bata hau daidai ba .
“Sai kayi ta kayan wahalar ka kai kadai amma ka sani na tsani yarinyar nan sau fuye da na fada wallahi bana son mutum gadararre mai izgili da dagawa kai kuma sai nace Allah ya cika maka mafarkin ka don ban san s a me ake nuna maka shi ba.
“Ameen king amma don Allah kar ka tsane Nadiya ni Ina mata uzurin kuruciya in na aure ta kana tsanar ta ai ba zanji dadi ba.
“Sai dai kar kaji dadin malam amma daina tallata min ita ta bata rawar ta da tsalle ne a wuri na iyakata da ku idanu amma shirgin ta ma kar ka saka ni ko a yanzu mukaje ni ba ma zan fito daga mota ba kaje kayi abinda zakayi ka gama.
“Karya fa kake yasin sai mun shiga ka gaida yakumbo Halima wallahi yo me kenan muzo tare ka coge a kwar gida?.
Sun isa jama are lafiya yakumbo halima ta tarbe su da murna har ta kawo musu dan waken da take ta siyarwa king kuwa da Allah yayi mishi masifar son dan wake yayi ma yakumbo Halima gaisuwa ta sosai har yana fadin
“Wallahi ina son dan wake Yakumbo ni dai duk cikin abincin duniya dan wake ne nawa.
Ai kuwa yakumbo ta samu abokin fira suka yi ta magana da king yayin da Kaisar ya shiga wurin Nadiya dake kwance akan gadon yakumbo halima ya aje mata kayan da ya ruko mata ta dube shi tana fadin
“Su mama basu dawo ba ne har yanzu ko kazo mu koma ne,?.
Ya dube ta yana fadin
“Kara hakuri dai sweetie sun kusa dawowa yaya babu dai wata matsala ko ?
Ta yamutsa fuska tana fadin
“Ni kam ban san me ya sa Daddy ya hana a zubar da cikin nan ba ni da na san haka ake wahala wurin ciki zan yarda nayi shi ne? ko kwanciya nayi ayi ta harbi na a cikin ? amma Daddy ya matsa ba za a zubar ba ni kam an cuce ni wallahi.
“Kar ki damu ko ni ba zan so a zubar ba sweetie in ma baki son baby ni ina so in ma kince a biya ki wahalar nan wallahi zanyi hakan.
ta dube shi a wulakance tana fadin
“Da wane kudin ne zaka iya biyana? kudin aikin da ake biyan ka gidan mu sune zaka biyani da su ? .
“Sweetie ni fa ba dan aiki bane ki gane hakan in don kina min kallon dan aikin GIDAN ku yasa kika kaasa karbar soyayya ta to ni ba dan aiki bane .
“Kaji matsalar ka karya da son boye talauci don kaga na tsani matsiyaci shine zaka fake min da karya? to koma waye kai baka mallaki kudin biya na ba ka gane wannan i bana son harka da matsiyaci gara ka gane wannan.