Motar Tero ta faka a kofar get din gidan Alh iro yayin da maccid’o Yake duban Tero a kallo daya ya gane shine wanda Alh iro yace kar su kuma bude mishi kofar gidan ko ya dawo sai gashi kuma suna gani.
Tero ya soma danna horn da son azo a bude mishi kofar amma su maccid’o sukayi kunnen uwar shegu da shi yayin da gwarma ya mike zai bude amma maccid’o yace mai gidda ya hana wancan yaron shigowa ku kalle shi da kyau don ku gane shi.
Haj Laila da ta kule da ganin wulakancin masu gadin ta soma balbalin bala’i tana nuna su maccid’o wanda suka tashi suna kallon ta sanin ko wacece yasa maccid’o ya karasowa yana fadin.
“Kiyi hankuri hajiya mai gidda na yace kar mu Kuma bodewa wanga kofa ko ba gaskiya ba.
“Saboda kun tab’a kama shi yayi muku sata ko kuwa me da har za a ce kar a kuma barin shi ya shigo? In ba dalili da yayi dalili ba har ku komawa Ubangiji ba lallai ku saka yaron nan a idon ku ba da Allah ni bude min kofa mu shige.
“A a Haj gaskiya ba zamu arya dokar mai gidan ma tunda gidan sa ne kuma yace kar a bar shi ya shigo mu yaushe zamuyi hakan tunda akan hakan ya aje mu? Cewar gwarma.
“Wai akan wannan gidan kuke mana wulakanci ? kun kuwa san ko wacece ni ? Zubairu yayi Maza ya amsa ta da fadin.
“To ko wacece ke Haj ai ba gidan ki bane ba kuma cewar ki zamu bi ba ta wanda ya ke da gidan ce ya kuma aje mu Yana biyan mu kinga kuwa ai babu wani da zai zare mana idanu.
Haj laila ta dube shi tana jin banda akwai abinda ya kawo ta da yau wancan ya gane wacece ita. Ta juya a fusace tana fadin, “Kai Mustafa jira ni a nan na shiga na fito harka dai duk in ta hada da talaka ne sai ya nuna maka tsiyar sa in ba kaddara ba yaushe kamata irin wannan gajan mai gadin yake da damar sakin baki a gaba na yana magana kama ni da ba rike first lady nake kuma rike da na matar sanato amma ake gayan bakar magana haka? kamar ni da alfarma ta da mukamin miji na.
Ta fita a motar ta nufi kofar shiga nan ma zubairu ya tare yana fadin
“Ai haj tare kuka zo da yaron nan wata kil kema irin abinda ba a so a tare dashi kema kina da shi gara kawai ku koma tunda tare kuke In kuma kina son shiga gidan nan sai kin sanarwa mai gidan in ya yarda ku shiga haka kawai wasu mara’s tsoron Allah da I’mani suka zo nan suka dake lamba suna fadin wai sun biyo wata yarinya ta shigo nan gidan ashe ashe mutanen nan mugaye ne sai da suka shiga suka fito sai ga magana an juya ta to kuma muka sani ko irin wadan can mutanen ne,?
Haj laila taja baya tana kallon zubairu cike da mamakin maganganun da ya fada.
“Kai ka san ko wacece ni kuwa? zan sa a wulakanta ka wallahi bude min kofar nan.
“Nifa ban san ko wacece ke ba bana kuma bukatar na sani yan mata gida ne dai nace ba zaki shiga ba da ke kadai na gani da na bude miki amma tunda kika zo da wanda aka kindayawa doka to wallahi ni dai ba zan bude ba sai dai ki koma ki bari har mai gidan ya dawo ko kuma ki kira wayar sa in naji yace a barki ki shiga to da gudu zaki shige.
Maccid’o ya mike yana fadin
“Kai dan zubai bari na hwadawa haj in ta san ta sai ta shiga tunda ba ita anka ce kar ta shigo ba.
Ya wuce da sauri yana shiga cikin falon yana sallama haj Aliya ta amsa mishi tana fadin
“Ya akayi ne maccid’o?
Ya zube a gaban ta yana fadin
“Haj mai gidda kwanaki ya nuna muna wani yaro yace kar mu sake barin shi ya shigo nan niya to shine yazzo nan niya shi da wata mata tana hwada da b’ace b’ace ita da dan zubai shine nace bari nazo na hwada miki.
“to maccid’o ai shi mai gidan shi ya ce kuyi hakan don haka duk wanda ya hana Kar ku sake ku barshi amma jeka ka tambaye ta kace nace daga Ina take ? In ta fada maka kazo ka sanar min sai na kira shi na fada mishi in ya yarda ta shigo sai ku bude mata.
Maccid’o ya mike yana cewa
“An gama Hajiya.
Ya dawo yana fadawa Haj Laila yadda ta ce ya fada yana jiran amsar ta.
“Ka ce haj laila ce matar distinguish Mukhtar biro.
Ta fada a zazafe don a ganinta an tozarta ta.
Da sauri maccid’o ya koma yana cewa Haj Aliya.
“Haj tace ko matar struggle Mukhtar biro?
haj Aliya tayi murmushi tana fadin
“Ko dai matar distinguish?.
“Haka fa haka tace
“To bari na kira Daddyn maccid’o yadda yace sai kaje mata da amsa.
Haj Aliya taja wayar ta tana kiran layin daddy Alh iro ta kuma same shi tana fadin
“Daddy fatan kun sauka ?
Ya amsa mata da yanzu dai suka shigo garin gombe.
“To masha Allah an Isa lafiya alhamdulillahi dama matar mutumin nan ce taxo su maccid’o suka hana ta shigowa saboda tazo da yaron da kace kar su kuma bari ya shigo.
“Matar Mukhtar biro ko? Ya tambaya ta amsa mishi .
“Su bude mata ta shigo amma kar ki bari taga jariran nan Aliya in ma zaki iya ki nuna mata babu wata haihuwa da akayi a gidan in ma ta nemi ganin Nadiya kice mata bata Nigeria don da gaske nake Aliya na harmta musu auren Nadiya na kuma haramta musu Ya’yan da kaddara ta kawo.
“Zan iya mana daddy ai duk yadda kace haka za ayi.
“Yauwa to aliya ta shigo kawai ki nuna mata baki san zancen da zata zo da shi ba don naji a raina sun sami labarin haihuwar Nadiya ne.
“to shikenan daddy.
ta aje wayar tana duban maccid’o tana fadin
“Maccid’o ku bude musu kofar su shigo.
Ya juya ya fice yana fadawa zubairu ya bude mata kofar
Haj laila da take d’aci wai an bata mata rai ta taka da kafar ta wacce bata son taka k’asa ta wuce Ta bar Tero a bakin get
ta shiga da sallama haj Aliya ta tarbe ta tana fadin
“Sannu da zuwa
Haj laila ta zauna tana fadin
“Haj haka kuka bar masu gadin nan suna shuka rashin kirki kala kala? banda nan gidan ne da a wani wuri ne shegen mai gadin can ya fada min wannan maganar da na sa an kama min shi don uban sa kamar ni da mukamin miji na da girma na da karishma ta ace wulakantacce kamar mai gadi yana keta min haddi da wadan nan maganganun? to ya ci albarkacin ku wallahi .
“Kiyi hakuri haj akan aikin su suke kuma mai gidan ne yace musu haka ba laifin su bane.
Suka gaisa da haj Aliya tana fadin
“Kuma Haj sai ku ki sanar mana da haihuwar Nadiya saboda Allah? ai ko babu komai an gama zama daya .
“Haihuwa kuma ? cewar Haj aliya wacce tayi tambayar kai ka rantse da Allah bata san maganar ba.
“Eh mana Haj don Allah Ina baby suke na gansu nayiwa yarinyar nan barka da arziki.
“Ni fa ban gane abinda kike magana akai ba Haj wai wa ya haihu.
“A a Haj zaifi kyau dai muyi magana daya abdulhameed yaje asibiti ya dawo yana nuna min hotunan jarirai gasu ma a waya ta Ina jin har da ke ma a cikin hoton.
Haj laila ta zuge jakarta tana fitowa da wayar ta tana nunawa haj Aliya hotuna ta karba tana dubawa ta kuma tabbatar da hakan ne amma waye wannan abdulhameed da bata San shi ba? Ta mikawa Haj laila wayar ta tana fadin
“Haj kin san dai ba zanyi miki karya ba ko? To Nadiya ma bata Nigeria fa to ta Ina wani ya ganta har ya dauki hoton karya ya tura miki? zan fi yarda dai ko can inda take ne don anyi za a zubar mata da ciki wata kil a asibitin ne amma ke a Nigeria ne aka ce miki ta haihu?
Haj laila ta dubi haj Aliya tana fadin, “Haj kenan ni dai na san ko zaku yanke alaka damu baku Isa yanke alaka tsakanin abdulhameed da Ya’yan sa ba tunda na kula al amarin kuna son saka kulli a cikin sa to zamu biyo ta bayan gida tunda na kula har yanzu kuna nan akan bakan ku.
“To Haj bayan gida fa yana nufin tsiya da tashin hankali? to kar ku soma mu da aka cuta bamu biyo ta bayan gida ba sai ku,?.
Kaisar wanda bai san bikin da ake ba yafito da yaro daya nade a tawul yayin da haj laila ta mike tana fadin
“Wannan kuma me ye? Ta fada tana nuna Kaisar wanda yake shirin wucewa amma haj laila ta tsayar da shi ya tsaya yana gaishe ta bata iya amsawa ba ta bude fuskar yaron mai sunan alhassan taga fuskar abdulhameed sak tayi murmushi tana fadin.
“To Haj shi kuma wannan da na gani meye? har da manuba haka?
“Ba manuba bace haj kune kuke shirin biyo ta bayan gida a yanzu don ku gane mu tuni muka biyo ta bayan gidan don haka wannan ma da kika gani tsautsayi ne kuma na farko da karshe shine kadai abinda zaki iya kardawa . nifa na rasa abinda kuke nufi haj ? wai yarinyar nan sau nawa kuka aure ta da kuke binbinin ta da halin da take ciki? ko kuwa don ba akai ku hukuma bane neman kadin keta haddin da dan ku yayi mata ba? to amma yanzu ni ba zan ce komai ba magana tana hannun uban ta amma in dai cewa zakuyi kuna son Ya’yan can ne sai hace muku albarka ba a siyar ba ko ni kuwa daga yanzu zan bawa masu gadin can umurnin kar su kuma barin ki ki shigo gidan nan.
Haj laila ta mike tana murmushi tana fadin,
“To Haj sai nace Allah ya bawa mai rabo sa a nima ba zaki kuma gani na a gidan ku ba amma ki sani wallahi tallahi dole ky bada ya’yan nan tunda dai duniya ma zata shaida hakan zaki ce na fada miki tunda duk hanyar arziki mun biyo amma baku yarda ba to zamuyi amfani da madafun iko.
“To hajiya muna jira .
Haj laila ta fice cike da fusata tana cewa mustafa Tero ya tashi mota su tafi .
Distinguish Mukhtar biro da ya dawo gida yana jiran dawowar matar tashi haj laila sai kuma gata ta dawo a fussce tana zuba ruwan tijara.
“Yaya ne basu yarda ba har yanzu Ya’yan nan na abdulhameed ne?.
“Ina fa suka yarda? kai kaga irin wulakancin da masu gadin kofar gidan Alh iro sukayi min? wai har sak’o ya bari akan kar a kuma barin motar mustafa shiga gidan nan? Kai a yanzu ma matar shi sai da takare min wulakanci tana fadin nima ba zata bari na kuma shigowa gidan ta ba. bayan ta nuna min bata ma san da haihuwar ba sai gashi Allah ya tona mata asiri naga wani ya fito da jariri.
“Dole na nunawa mutanen nan karfin iko laila don na gane da gaske suke ba zasu bani Ya’yan nan ba ni kuma wallahi ba zan bar musu su ba na yarda na biya dukkan chajis din da za ayi min akan keta haddin da abdulhameed yayiwa yarinyar na biya na karbi ya’yan nan.
“Nima haka nace gara kawai mu nuna musu karfin iko su bayar da ya’yan nan ko basa so .
Da sauri kuwa ya ja waya yana kiran wani alkali a garin Abuja ya sanar mishi kullin da yake so a kulla don a karbar mishi Ya’yan nan amma zai nemi alh iro in ya fahimce shi kalas in kuma bai fahimce shi ba to za a kawo shi inda bai Isa ya musa hakan ba .
Keena ta dubi luba tana fadin
“Wai luba ko kin kara jin rangal rangal da mai kalangu ya fada rijiya?
Luba ta dube ta tana fadin
“Ban fa gane ba keena?
“Dan dattijo nake miki nufi mana mai mota? kwana kusan nawa rabon da na saka shi idona? wallahi har na soma manta shi Kai gaskiya dole muke shan wahala duk wanda ya bar Allah sai Allah ya barshi.
“Wai maganin malamin nan na surayya? Eh mana ai tunda na bashi shi nima nayi sati biyu wallahi bakiji yadda naji kamar an sauke min wani gungumemen dutsi a kirji na ba .
“Kai amma nayiwa mutumin nan barka ya sha da kyar wallahi tsoho kamar wannan Yana bulayin soyayya?.
“tashi zakiyi luba yanzu gidan su Nadiya zamuje na samo lambar wayar gayen nan wurin yarinyar nan ta gidan su Nadiya ai barin hali sai mutuwa dole na komawa ba I’mani tunda abin nasa kamar yankan wuka ne don yanzu kam na gama yarda da daukar lambar mota sai na kira naji dahir tukuna .
Luba ta mike tana fadin
“Ni kam Ina tsoron ranar da wancan shaid’an din zai waiwaye ki idan ya gane ba sikin sa kike ba.
“Ai kwantar da hankalin ki har address din Nadiya a jama aren zamu karba tsuntsu biyu zan jefa da dutsi daya.
Suka fice zuwa gidan Alh iro.
Sai dare Alh iro ya dawo daga Billirin gombe inda suka taho da kawu yayari yayan mahaifiyar Kaisar ne sai kuma kanin ta mai suna kawu sada .
Kaisar ya ga zuwan mutanen biyu a gidan nasu ya tarbi daddy yana musu sannu da zuwa
Kawu yayari ya kalle shi yana fadin
“Baturen ingila baddo tace a gaishe ka tunda ka yada ita wata Kil baturiya ka samo .
Yayi murmushi yana fadin
“tuba nake kawu yayari zanzo ai .
“ta yafe tace sai an aika mata da kayan dannar kirji.
Suka wuce ciki inda daddy ya sauke su a daki na musamman aka shiga sauke musu kayan tarba Haj Aliya tana ta musu sannu da zuwa tana tambayar su baddo da sauran yan uwa
Washe gari sai ga yaya halilu ya iso tare da wasu dangin su alh iro kasancewar ranar ta juma a gaba daya suka hadu motoci suka kwashe su zuwa masallacin juma a wanda ana gama shi Kaisar ya taho saboda ya bar Al Hussain yana amai jikin shi kuma ya yi zafi don haka asibiti yake son kai shi don haka ya juyo gida ya kuma dauki al Hussain ya nufi asibiti aka duba Al Hussain aka ce za ayi mishi allura saboda zazzabin da Yake jikin shi amma Kaisar yace in da magani a bashi fatar shi da jikin shi ba zai iya daukar kaifin allura ba dole aka sama mishi magani na ruwa tun a nan hospital din ya diga mishi a baki kafin ya iso gida inda ya sami gidan cike da bak’in daddy ga kuma su kawu yayari zasu wuce gombe.
Ya dubi su kawun da suke rike da goro mai yawa suna fadin
“Mu zamu wuce Kaisar Allah ya tabbatar mana da alheri.
“Kawu kuzo jiya kuma ku koma yau? haba sai kace ana korar ku?.
“to ba mun gama abinda ya kawo mu ba,? Auren ka ne ya kawo mu an kuma daura mun baro ayyukan mu a gida.
“Gaban shi yayi wata irin faduwa jin yace auren shi ya kawo su an kuma daura. Aure? da wa to?.
Kafin ya gama hada uku da biyar tuni sun shige mota malam Ango yaja su suna daga mishi hannu.
Ya fito mota yana rungume da Al Hussain yana ta sauri zai shiga ciki yaji meye ake wanda bai sani ba?.
Fati wacce ta taho idanun ta na zubar da hawaye itace sukayi taho mu gama suka zubawa juna ido yayin da zuciyar shi take karanta mishi auren fati daddy ya bashi?