Wata irin gigitacciyar fargaba da tashin hankali suka saukarwa Kaisar da ya zubawa fati Ido itama ta zuba mishi nata idon yana yararin hawaye.
“Fati? ashe baki rufe babin abinda nace mu rufe ba? kina nufin sai da kika kai maganar nan a gaban Daddy fati? da ke daddy ya daura min aure ne,? ba na fada miki ra ayi na akan Nadiya ba? me yasa kikayi min haka? ke yanzu kin zabi in da baki da muhalli ko na zaman. Kukan fati ya hana shi karasa sauran maganar yana kallon ta da wata irin fusata tamkar yayi bal da ita amma karimcin daddy ya hana yayi hakan ya yi shiru amma yana kokoawa da zuciya da kuma numfashi.
“Kayi hakuri yaya Kaisar tuni na bunne abinda nake ji a cikin kirjina da zuciya ta tunda na gane babu abinda nake ji g zuciya ta ga taka zuciyar. ni ban sanarwa da daddy komai ba wallahi babu abinda na sanar mishi.
“Auren wa to aka daura In ba ke ce kika kulla wani abu ba? Fati Ina son na Kara jaddada miki Nadiya nake so babu wani gurbin da wata mace zata samu a zuciya ta matukar ba Nadiya bace. Ina son nayi na kallon ki a matsayin yar uwa ta amma ba masoyiya ba ki rike wannan kar wata alaka ta biyo bayan wannan ki sani ki kuma kara sani Nadiya nake so.
Ya karasa maganar a fusace don ranshi ya fara sanar mishi daddy ya aura mishi fati ne wata Kil kuma ta zaga ta fadawa daddy tana son shi don tun kafin ta furta ya gano ta . don Haka d wani irin haushi da takaici ya shiga cikin gidan ya sami Nadiya tana zaune gefen gado yayin da al Hassan ke gefe yana kuka amma bata ko nuna ta san da mutum a wurin ba bare ta dauki yaron ta rurruga shi yayi shiru.
Da sauri ya karaso yana aje Al Hussain ya dauki Al Hassan ya soma jijjiga shi har yayi shiru kafin ya dubi Nadiya da take tab’a wayar ta wacce ta jima bata bude ba.
“Yanzu kina zaune kina jin yaron nan yana kuka amma kikayi banza da shi Nadiya? Ta dago tana sauke mishi wani banzan kallo tana fadin
“To meye naka ne a cikin in nayi banza da shi? Uban sa ne kai ko kuwa cikin sa kayi ko haihuwar sa? kai ka fa fara Isa ta da shisshigin ka na son cusa kai ba kwarjini ban so kar ka sake na fada maka ka fita harka ta dan anace sarkin naci.
Yayi murmushi yana fadin
“ta yaya zan iya fita harkar ki bayan banayi sai da ke? ai naci ma ban fara ba sweetie sai naga kin bani yar baby irin wannan kuma fada min uban twins in ba ni ba? Ko kuwa kina son fada min akwai wani uban su bayan ni? to in ma wancan dan iskan ne yayi kad’an ya amsa sunan uban su in dai ina numfashi.
Taja wani matsiyacin tsaki tana fadin, “Ni kam na hadu da masu bibiyar kurwa bana ko shakka ka hado iri da masu maita da lashe kurwa shiyasa ma akayi ka dan kad’an.
Yayi dariya yana fadin, “Ai ban ma fara maita ba Nadiya sai ranar da Ubangiji ya cika min burin mafarki na na ganki a gefe na a matsayin matata a ranar zan nuna miki maita don sai na sud’e ki na lashe tas.
Haushi yayi kamar ya kashe ta don yadda yake nuna mata tabbaccin sa akan hakan.
Ya ajiye mata Al Hassan da ya gama kukan ya jefa Yan yatsun shi biyu a baki yana tsotso inda Kaisar ya gane yunwa yake ji sai dai uwar su bata da I’manin tausayawa kuruciyar su sai Allah ya zuba musu hakuri matuka gaya in ba haj aliya ta yi tsaye kan ta ba ba zata basu no-no ba ganin hakan yasa Kaisar ya siyi madarar jarirai ta NAN da ya kula suna jin yunwar zai jona kettle yayi ruwan zafi ya dama madara ya basu don haka yanzu ma ya jona kettle ya hada ruwan zafi ya dama madara ya soma bawa twins suna dadddaka idon su akan shi suna kallon shi shima yana kallon su har suka koshi sukayi gyatsa sai bacci.
Hawaye ne kawai suke gudu a fuskar ta. me tayiwa so ne haka da zafi da ya kasa karbar ta? me yasa ne bata tako nasara irin wacce Nadiya ta tako ba? taso ace ta iya jarumtar ciro son da ya shiga zuciyar ta ta watsar amma ya ta iya ? al amarin ba a hannun ta yake ba. Ta dago kanta da sauri jin an dafa kafadar ta sai kawai sukayi ido hudu da keena da kuma luba wanda suka shigo gidan da son ganin fatin don su sami lambar wayar Kaisar su kuma nemi address din Nadiya a jama are sai kawai suka ga fatin tana kuka duk da sun hango Kaisar din a tsaye gaban ta har ma sun jiyo wasu daga cikin kalaman shi.
“Subhallahi sister me yake faruwa? Cewar keena da ta dafa kafadar fati.
Da sauri fati ta soma share hawayen ta tana fadin, “Babu komai.
“Don Allah lambar gayen nan nake so ko zan samu a wurin ki?
cewar keena.
Fati tabi ta da kallo don kuwa bata bukatar a fada mata dalilin neman lambar ga wannan kawa ta Nadiya mai budadden idanu, don haka tace babu waya a hannun Kaisar.
“Amma kuwa da mamaki yanzu nan duk haduwar shi bashi da waya? Fati da ta gaji da Jin su ta juya tana fadin
“Bari na sanar mishi kuna son ganin shi mana ? Suka bita da kallo har ta shige luba na fadin, “Nifa na karanto wani Abu a cikin idon yarinyar nan bana ko shakka tana son gayen nan fa keena kun Kara yawa itama tana ciki kina zaton zata iya Baki lambar wayar sa? amma ari mu gani idan ta turo shi to zato ne kawai ba hasashe na ba idan kuma bata turo shi ba to ta nuna kanta.
Keena da taji shock akan maganar luba ta k’ame baki sake . tana dakon soyayyar shi wata na taya ta? ba zai yuwu ba wallahi.
Kaisar ya fito cikin wani arashi don fati dai bata fada mishi ba don ya tsuke fuska baya ko son kallon ta ita kuma ta kame kanta don kar ya kira ta da marar zuciya wacce ke so a inda ba a son ta.
Kallo daya yayi musu ya watsar da su ya wuce abin sa cike da izza da daurewar fuska.
Keena kan taji shakkar shi matuka gaya yayin da luba tayi karfin halin cewa
“Ina wuni?
bai juyo ba yana shurin wucewa luba ta sake cewa
“Ana magana
Ya tsaya yana juyo su inda luba ta finciki hannun keena suka nufe shi.
“Don Allah wani taimako muke so kayi mana kawa ta ce ta yada wayar ta bamu san inda ta yada ita ba shine muke son ka ara mana wayar ka zamu kira.
“Bani da waya amma kuje ga masu gadi can ku nema .
Ya wuce bai kuma ce musu komai ba ya bar gidan suka bishi da kallon wannan fa zaiyi tauri da yawa.
Keena taja hannun luba suka fice suka bar gidan cike da takaicin rashin Samun nasara
Kaisar ya shigo falon na haj Aliya inda daddy da mama suke zaune da tarin goro da minti da dabino.
Ya tsuguna a gaban su gaban shi yana faduwa don ya gama yarda auren shi da fati Daddy ya daura.
“Kaisar bani hankalin ka Ina so nayi magana da kai ina fatan zaka fahimce ni?.
“Zan fahimce ka daddy duk yadda kayi dani ina godiya don na san ba zaka tab’a cutar da ni ba kuma abinda uba zaiyiwa dan sa Daddy shi zakayi min .
“Alhamdulillahi Kaisar kasan naje Gombe jiya na dauko kawun ka yayari da sada ba don komai na dauko su ba don su shaida daurin auren ka na kuma kira Yaya halilu wanda shine mai baka auren.
Bai karasa ji ba ya gasgata zancen cewa fati aka daura auren shi da ita duk da bai so hakan ba amma ba zai bawa daddyn kunya ba.
“Kaisar naso ka fahimce abinda nake nuna maka na fin da kayiwa Nadiya fati itace matar ka amma ka kasa ganewa to alhamdulillahi na daura auren ku da Nadiya ba don komai yasa nayi hakan ba sai don yan yaran nan da na tabbatar kaine gatan su kuma kana son Nadiya in ba ita ba banga alamar zaka fiddo wata mace da sunan matar aure ba amma ba wannan ne makasudun ba makasudun yana ga yan mala ikun Allah nan da na gama gane uwar su batayi maraba da zuwan su duniya ba kuma babu kauna a tsakanin su to wannan shine babban dalili amma bayan hakan ni na san Nadiya ba alheri bace a cikin rayuwar ka tunda duk dan halal hallacci Yake amma ita sam batayi maka wannan halacci ba to Kaisar yanzu Nadiya ta fita idda kuma da anyi suna zan gyara muku sashin can ku zauna a can don ba zan so nayi nesa da ku ba don na san yarinyar nan ciki da bai idan kukayi nesa dani akwai matsala.
Wani irin farin ciki ya sauka akan zuciyar Kaisar ya rufe idanun shi yana fadin
“Alhamdulillahi Allah alhamdulillahi daddy ka gama min komai ka kuma cika min MAFARKI na in sha Allah auren mu da Nadiya shine silar daidaituwar komai in sha Allah.
“to Allah ya sa sannan kuma yanzu ya kamata ka soma shirin fara aiki ka zabi kamfanin da yayi maka amma wanda yake nan kusa da gida amma da gari lafiya sai nace legos ko kaduna shi yafi kamatar ka.
“to daddy duk yadda kayi yayi daidai.
Ya fito yana farin ciki inda yayi karo da fati tana shirya kayan abinci sai yaji kunyar yarinyar irin yadda ya gaggaya mata magana ashe bai fahimci manufar kukan ta ba? kuka ne irin na nayi asarar abinda nake so ? ashe ba hargagi take so a wannan lokacin ba irin rarrashi?.
Ya ruko ta irin rukon da bai tab’a yi mata irin shi ba ita kuma sai taji wata wuta tana fizgar ta har bata yi kokarin kwacewa ba.
“Sister fati please and please don Allah ki yafe ni kinji? wallahi sai yanzu naji ban kyauta miki ba ashe na munana miki zato ? don Allah don ANNABI ki yafe min ashe yadda nake kallon al amarin ba haka yake ba.
Hawaye ya sake kecewa Fati ta soma kada kanta tana fadin
“Babu komai komai kaga ya faru dama Allah ya zana zai faru wani baya auren matar wani haka wata bata auren mijin wata kowace da abokin burmin ta ka dauki dukkan al amarin a matsayin imagin function.
Motar distinguish Mukhtar biro ta faka a kofar gidan Alh iro ya kuma sauke gilas din motar yana kiran maccid’o wanda ya taho da sauri yana gaishe shi ya amsa kamar ana mishi dole ya dubi maccid’o yana fadin
“Iron yana nan ne?
Maccid’o ya amsa da yana nan.
“Ce mishi yana da bak’o a waje.
Da gudu maccid’o ya auna cikin gidan ya sanarwa Alh iro yana da bak’o.
“Ungo makullin seat room maccid’o sauke shi na san dai biro ne.
Haj Aliya ta dube shi tana fadin
“Mutanen nan fa babu alheri a tare da su daddy da ka daina sauraren su ni wallahi na gaji da ganin su.
“Barni da shi Aliya duk rashin kirkin su sun isa su shigo nan ciki su dauki Ya’yan Nadiya ko ita kanta?
ya fito inda ya sami distinguish Mukhtar biro zaune akan kujera.
Ya mika mishi hannu sukayi musabaha Alh iro yana fadin
“Kaine akace bak’on dama?
“Nine babu ko wai iro me nake ji ana fada iro? har yarinyar nan ta haihu amma ka kasa sanar damu?.
“Ku a wa za a sanar muku? wai duk maganar da nayi muku a baya kai da matar ka baku fahimta bane? da hausa fa nayi maganar nan biro da wane kalar yaren ne kuka fi fahimta na juya harshe don na ganar daku?.
“Da kowane harshe kayi magana muna ganewa iro amma mun fi fahimtar ayi mana yadda muke so amma in akasin hakan ya wanzu to bama gane komai sai nuna karfin ikon mu ta kowace fuska don ganin mun mallaki abinda muke so.
“to biro ku baje karfin ku da ikon ku ku kwaci Ya’yan nan duk da na San sune suka kawo ka ni kuma ka rike wannan a ranka ko na mutu wadan nan yaran sai dai su dubi wasu ahalin ba dai ku ba da ace kazo ne ganin su yan buyun da na kawo maka su ka gansu amma tunda iko da karfin kwanji kazo sakawa babu shegen da ya Isa ya mallaka maka Ya’yan nan in bakayi sannu ba allura ce zata tono garma .
“Haka kace? .
“Haka nace in baka ji ba ma in sake maimaita maka in kuma akwai shegen da ya Isa ya karbar maka su to na ganshi .
“Zaka gan su kuwa iro tunda duk wata hanya ta sulhu da masalaha na biyo ta amma sai wulakanci mai kalar ruwan hoda kake .
“Ai baka ga wulakanci mai kalar ruwan hoda ba biro sai ka nemi shiga hurumin yaran nan da kayi hikima ma da ka tsaya ka ga yaran nan ko da kuwa kallon da zai zamo na farko da karshe ne don Ina mai tabbatar maka da ko a hoto ba zaka ga yaran nan ba.
Alh iro ya daga waya ya kira Kaisar yace ya kawo mishi yan biyu a falo.
Minti uku sai ga Kaisar ya shigo da yaran cikin farin kaya sai kamshi suke
Alh iro ya karbe su yana dorawa distinguish Mukhtar Biro a cinyar sa yana fadin
“Duba su da kyau ka kuma yi musu ADDU AR samun ingatacciyar Rayuwa ba irin ta lalataccen dan ka ba jibi ne sunan su in kun sami time kuna iya zuwa rad’in suna don tuni uban su na sama yayi musu huduba da sunan da yayi mishi dadi .
Distinguish Mukhtar biro ya zubawa yaran ido suna tuna mishi da kuruciyar abdulhameed kuma gasu identical twin suna jiran daya sai ga biyu .
“Kayi musu ADDU A don Ido guba ne naga ka tsira musu ido kana zancen zuci in ka gama gani bani su na mayar gida in ADDU AR ba zata samu ba.
“Na baka ka mayar? karfi ya cinye maka iro in kana da shi na gani.
Cewar distinguish Mukhtar biro wanda ya tashi tsaye yana rungume da yaran cikin babbar rigar sa.
Daddy yayi murmushi yana fadin
“Haba dai biro ai karfin ka bai Isa ya kwaci Ya’yan nan a gidan nan ba kai ko a waje kuwa wallahi kaci uwar karya ka kwana da yunwa gara in hauka kake ka bari ka bar gidan nan kafin ya tssar maka.
Distinguish ya mike yana shirin ficewa daddy ya mike yana kiran maccid’o wanda ya danno aguje yayin da distinguish ke shirin fita .
“Kai maccid’o ku karbo min yaran nan hannun wancan mutumin zai sace Ya’yan mutane.
Aguje maccid’o ya nufi distinguish da ya bude mota yana zuba yan biyu a bayan mota yayin da maccid’o ya sauka akan distinguish yana shirin damukar shi ya daga shi sama zai maka da k’asa amma daddy ya dakatar da maccid’o wanda yake aunawa distinguish Ashar.
“Kar buga shi maccid’o ya baka jariran nan kawai ka kawo min rabu da shi.
Maccid’o ya hankada distinguish Mukhtar Biro can gefe ya fada ragwagwam ya bude motar ya kwaso yan biyu ya kawowa daddy wanda yace mishi ya kaiwa Haj Aliya su.
Distinguish ya tashi daga faduwar ashin kirkin da maccid’o ya watsar da shi yana duban kayan shi da sukayi k’ura har rigar shi tana yagewa ya dubi Alh iro Daddy yana fadin
“Ni ka sanya ayiwa wannan wulakancin ko? to wallahi tallahi zaka amsa kira kotu inda zaka gane ka tabo abinda yafi karfin ka wallahi sai kayi nadamar abinda kayi ni ka sa akayiwa hakan ko? to ka saurari martani. Abdulhameed kam ya rikicewa iyayen sa fiye da rikicin sark’ a dole yan biyu yake so fiye da rayuwar sa Yana son su dawo hannun momi daga hannu alh iro shiyasa bai iya bari Haj laila ta dawo ba ya nufi kasuwa shi da Tsagera suka jibgo siyayyar kayan jarirai tari guda abun kamar ba hankali.
Tsagera ne wanda aka tura kai kayan amma sai gashi da su ya koma Daddy ya maido shi yace basa so
Haj laila tana zaune a falo tana jiran dawowar distinguish Mukhtar biro sai kuwa ga shigowar motar shi taji ya shigo a guje yana dannawa mai gadi horn har ta soma jiyo hargagin sa abinda ya tabbatar mata da basu kwashe da marar arziki ba don shi fushin kaza huce kan dami ne da kaji yana tijara to wani ya tabo shi sai ya sauka akan wani.
Yadda taga rigar shi da kurar k’asa har ma ta yage ga kuma bakin shi a fashe k’asan leben shi ma ya haye da kumburi .