Skip to content
Part 56 of 62 in the Series Azurfa Da Zinari by Hadiza Gidan Iko

*****

MISAU.

Alabo kam yayi matukar jin dadin dawowar fati misau ko ba komai zai kafa gwamnatin sa yadda yake so  sai dai yadda yaga fati din ne abin ne bai mishi dadi ba don kamar tana cike da wani abu sunke a cikin zuciyar ta

Inna Hajara ta tarbi fati tana fadin

“Ta Rasulu kece tafe ? ta fada tana murnar ganin ta amma dai ganin yadda jikin ta a sanyaye yake amma da yake fati bata da hayaniya ga zurfin ciki da take da shi

Baffan ta ya dawo ya same ta yayi murmushi yana fadin

“Oyoyo ga binta sannu da zuwa yaya mutanen gidan da Baffan naku? komai lafiya lau Baffa suna ta gaishe ku . to madallah binta kun sha bikin Nadiya kema Allah ya fiddo miki naki rabon na alheri kema kiyi auren ki.

Alabo da ya tsura mata ido yana son ta fahimci sak’on da yake cikin idon shi amma kanta a k’asa bata dago ba bata kuma ce komai ba sai dai ta amsa a zuciyar ta

Kwanaki biyu da zuwan ta misau ta kara rama mai yawa kallo daya zakayi mata ka gane tana cikin wani hali. Inna Hajara ta na kallon ta tana mamakin abinda yake damun ta. kwanaki da yawa al amarin na fati babu sauki dole Inna Hajara ta same ta  a daki sai Kuma ta same ta  tana kuka abinda yayi matukar tayar da hankalin Inna Hajara wacce ta rungume fati  cike da tashin hankali tana fadin

“Haba ta Rasulullahi yanxu har akwai wani da zaki boye min? ni ko da na ganki naji a jiki na kamar kina da damuwa don Allah fada min abinda yake damun ki kinji? In sha Allah babu abinda ba zan iya yi miki ba in sha Allah zan miki maganin damuwar ki .

Fati ta share hawayen ta tana tunanin fadawa innar ta gaskiya ko kuwa zata barwa ranta sirrin ta ? da kunya ta fadi cewa tana son Kaisar ya bar ta? gara kawai ta barwa ranta ta barwa Allah in ya so sai ya yi mata magani koma ya yaye mata baki daya don haka ta shirgawa innar karya cewar bata da lafiya sai ga Inna Hajara ta rude tana ta shiga tana fita da nema mata magani dole ta wartsske ta shiga sabgar gaban ta yayin da alabo kuma ya shiga hidimta mata babu ji babu gani duk da ba son hakan take ba don tana mamakin yadda yayan nata yake mata.

A fusace distinguish Mukhtar Biro ya dawo bauci daga Abuja tafiyar da yake jin ta fiye da nissan barin duniya.

Babu abinda yake maimaita wa sai kalaman dan uwan sa mai shari a Sufi biro wai  basu da hurumin komai akan Ya’yan abdulhameed

Bai tab’a gane yadda Sufi yake kallon shi ba sai a yau din da yake tabbatar mishi da diyyar ran da zai biya lallai ya zame mishi dole ya raba kowane irin zumuncin ne tsakanin shi da Sufi tunda dan uwan ka ba zai iya rufa maka asiri ba sai ma ya kama a wulakanta ka to ko sune ya kawo shi duniya a yau ya barshi bari kuma na har abada bare ciki daya da  suka fito

Ya matsu ya iso gida bauci don bai ma tsaya saurare Alkalin da suka daura gurmin su na manuba ba bare don yana ganin an so a cuce shi tunda in da ya san Sufi ne zaiyi shari ar zai yarda ya danna kudin shi ? sai gashi don an raina mishi wayo da hankali an kasa karba mishi Ya’yan Abdulhameed kuma ana maganar shine zai biya wasu uwayen kudi na diyyar rai wanda dole zasu girgiza tattalin arzikin sa har da wani bashi account details din kotu .

Ya iso bauci yana danna horn da karfi abinda ke nuna mai gida yana cike kenan da zafi ko tijara

Da sauri mai gadin ya bude kofar yana son dora idanu akan mai gidan ya kuma gano fuskar nan tamkar hadari ya gan gamo yana shirin saukar da ruwan sama.

Ya fito a motar yana buga kyauren motar tamkar dai shi ya kar zomon

Mai gadin ya bishi da kallo har ya shige cikin gidan yana fadin

“Allah shi kare balaki mai gida ba kanta kenan sai huci kake ko wa ya tabo shi? Yanzu haka shi da matar gidan ne kai mata na wulakanci a duniya su kuwa maza da mulki dubi dai kamar zaiyi abin kirki amma da ta murza gashin baki sai kaji dan bawan Allah yayi muiy.

Haj laila da taji shigowar motar distinguish yana Danna horn ta san ba a samu yadda ake so ba sai ta mayar da hankalin ta akan kofar shigowar ta kuma ji yadda ya banko kofar ya shigo kallo daya tayi mishi taji gaban ta ya fadi .

Bai tsaya a falon ba ya haura saman benen shi ta bi shi da ido kafin ta bude fridge ta dauki ruwa mai sanyi da lemu ta bi bayan shi.

Hannayen shi a goye a bayan shi ta kafa mishi kofin ruwan ya kuma shanye yana zama yana kallon ta ta soma bashi hakuri da kalamai masu sanyi har ya soma sauka sai kawai taga hawaye yana sauka a fuskar shi abinda ya tayar mata da hankali matuka gaya ta sake bashi baki tana tambayar shi ba asi.

“Laila haka dama dan uwa ke zama makiyi? ban san yaya akayi shari ar nan ta fada hannun Sufi ba ya kuma tozarta ni ya bawa duniya damar da zata kalubalen ce ni har yana fada min nine ma zan biya Alh iro kudin haddi kuma ni da Abdulhameed bamu da hurumin komai akan Ya’yan yarinyar can laila a yau ko Sufi ne uba na dole na yankee dukkan wata alaka da zata Kuma hada ni da shi tunda na gama gane baya sona baya iya rufa min asiri baya kuma kishin duniya ta ganni zigidir to meye amfanin shi gareni?.

“Shi Sufin ne yayi mana haka Mukhtar? to ba za a iya dauke shari ar daga Abuja ba nee a mayar da ita wani gari? ni kam ba zan boye maka ba ba zan bar Ya’yan nan a hannun mutanen nan ba wallahi sai an bani su ko ba a kaunar Allah.

“Dukkan dabara ta da hikima ta laila ta kare duk hanyar da nasan zan bi don ganin na kwaci Ya’yan nan smma kofar a kulle ga zarto ma shiru har yanzu babu wani bayani ni kam in har na mutu a yanzu laila ko wani ciwo ya far min a yanzu laila ki shaida bak’in cikin Sufi ne ya kashe ni kuma ko na mutu zan bar wa Abdulhameed wasiyyar ya dora gaba da Sufi har datissara  ku kuma tabbatar mishi da shine ya kashe ni in kunso ku kyale shi in kun so kuma ku nemi hakkin ku amma s yau nayi nadamar kasancewa tsatso daya da Sufi zan kuma tabbatar mishi da na yanke dukkan wata alaka da shi har duniya ta tashi.

Haj Laila kam tafi shi shiga tashin hankali don ta gama zana yaran nan a gaban ta amma a wannan karon dole ne ta kullaci dan uwan mijin nata wato Sufi don tana ganin shine yaja mata wannan bak’in cikin.

Haka wannan gida suka kwana hankali a tashe yayin da Abdulhameed kuma ya samu labarin yadda aka kwashe na yana shi auren Nadiya da kuma hana su ya’yan kuma duka daga Baffa alkali wato Sufi

Shima ya shiga tashin hankali wanda ya zarta nasu don shi kam ciwo ne ya tashi dama abu ga wanda ba cikakkiyar lafiya ba sai ga ciwo ya dawo har da kwara aman jini ga Abdulhameed Mukhtar biro. dole Kuma distinguish Mukhtar Biro da Haj laila suka aje tasu damuwar gefe suka rungumi ta gudan jini Abdulhameed wanda al amarin nashi sai godiyar Ubangiji don yayi nisa da yawa har ana shirin fita dashi waje amma dai cikin hikimar Ubangiji ya soma samuwa amma dai jiki babu dadi

Hankalin Mukhtar biro ya kuma tashi ya hade dukkan abubuwan da suke faruwa yana auna su a mizanin hankalin sa amma sai amsar duka tazo mishi a mutum daya tak wato dan uwan shi Sufi biro wanda duka wata matsala shine ummul aba isin jawo mishi ita tunda daga abu daya sai ga abu goma.

A fusace ya mike ya bar asibitin ya nufi gidan mai shari a Sufi biro.

Sufi yana gida bauci don duk weekend yana baro garin Abuja ya dawo bauci cikin iyalan sa yayi hutun karshen mako kafin ya koma can Abuja duk da anyi mishi tayin komawa birnin tarayya amma yace yafi son garin sa na bauci don haka baya jin wahalar zuwa da dawowar.

Yadda Mukhtar ya shigo gidan kadai zai nuna maka Babu lafiya don yadda ya faka motar har yana tayar da k’ura ya kuma fice daga motar zuwa cikin gidan babu ko sallama ya danna kanshi Sufi ya dago kanshi yaga dan uwan shi ne ya mike yana fadin.

“Brothe .

“In ka kuma ce min brothe zan auna maka Ashar wallahi nemi dan uwan ka a wani wuri Sufi amma ni ko kaine uba na a yau zan yanke alaka da kai tunda sanin ka bai amfana min komai ba sai bak’in ciki da tashin hankali to nayi kaicon kasancewa tare da kai  in kuma ka yarda na ganka a harka ta zan wulakanta ka ne da duk kalar wulakancin da yayi min .

Ya figo wani katon hoton ilage wanda suke su biyar Mukhtar Sufi abubakar da Usman sai ummulkhairi hoto ne da aka wanke manyan size har biyar don haka a kowanen su kaje gidan shi a falon shi zaka riski hoton don haka Mukhtar ya figo shi ya maka da k’asa gilashin ya tarwatse ya kuma fincike takardar hoton ya yage saitin inda yake ya kece shi gutsi gutsi ya watsar yana fadin.

“Yadda na fidda kaina daga kai da duk abinda ya shafe ka  haka nake so ka fidda kanka daga ni babu ni babu kai bare zuria ta ko a hanya bare naji ka kama sunana abakin yan wallahi zanyi maka alkawarin wulakanci mai daraja ta farko.

“Kayi hakuri Mukhtar tunda kace kar na kuma hada kaina da kai amma banajin zan iya hakan Mukhtar. wallahi tallahi ban tab’a jin nayi nadamar aiki na ba irin yau da kake fadar ka yankee alaka dani . amma har a yanzu ba zanyi nadamar tabbatar da gaskiya gurbin ta ba ina rokon kayi min afuwa wallahi ko akan abdurrahaman ko sumayya ne san tabbatar da gaskiya matukar na gane basu da gaskiya to zan basu sakamakon rashin gaskiyar su duk da na san abinda nayi Akan abdulhameed ne ya ja min hakan wallahi da na san shiga ta aikin nan zai zama silar samun sab’ani tsakanin mu na rantse maka da Allah da ban shige shi ba amma Allah ya san manufa ta akan abinda baya maka dadi na mara maka baya a danne hakki da gaskiya to Ina hangen ranar da AZURFA DA ZINARE ba zasuyi mana amfani ba. ba zan ce kar kayi abinda zuciyar ka ta raya maka ba amma ina mai tabbatar maka da lallai ni bana daga cikin masu yankee zumunci in kai ka Yankee ni insha Allan zan kulla shi .

“To ka kulla shi din don allah kaga yadda zan wulakanta ka irin wulakancin da baka tab’a ganin anyiwa wani ba bana son ka Sufi bana son ka rab’e ni bana son zuriar ka da ahalin ka su rabe ni babu ni babu kai kar matar ka ko Ya’yan ka su danganta kansu dani ko ahali na idan akayi hakan zanyi rashin mutunci mun rabu rabuwa ta har abada ka rike wannan a ranka.

Ya juya a fusace ya fice da sauri yayin da Sufi ya zubawa fasasshen gilashin da ya tarwatse frame din hoton su wanda suke su biyar zuriar da iyayen su suka bari suna alfahari dssu da zumuncin su yau sanadin aikin shi na shari a ya tarwatse komai.

Hawaye ya soma fita a idon Sufi yayin da haj Safiya take rabe a gefe jikin ta a sanyaye tana jin duk abinda yake faruwa amma bata da damar tofawa.

“Kayi hakuri Alkali Allah ya huci zuciyar sa amma kar kayi nadamar tabbatar da gaskiya gurbin ta don ba nadama bace nadama tana nan ga dora karya gurbin da ba nata ba kuma ba nan ne abin damuwa ba sai bawa ya kasance a inda babu mataimaki sai Allah da ayyukan sa . zai gane abinda ya kasa ganewa .

Yasa tissue yana dauke kwallar idon sa yana fadin

“Nagode Safiya da wannan karfin gwiwar hakikatan nadama tana ga ranar da Babu AZURFA DA ZINARE ga Wanda ya aikata son ransa in sha Allah zan tabbata akan turbar da ba ni na dora kaina ba Allah ne ya dora ni zanyi ADDU A don na damu matuka gaya akan abinda yaya Mukhtar ya fada min wallahi safiya banji dadin maganar da ya fada min.

“Babu dadi amma Allah ne shahidin bawa ya kuma san abinda zukata suke sakawa.

da haka haj Safiya ta bashi magana mai dadi har ya sanyaya fiye da zaton sa.

*****

Alabo ya durkusa a gaban Baffan nasu halilu yana gaishe shi ya amsa yana fadin

“Uba na yaya ne? Yaya aikin naku?

Alabo ya soma  sosa sumar kanshi yana fadin

“Baffa aiki lafiya lau alhamdulillahi.

“To masha Allah Allah ya kara daukaka uba na.

Alabo yayi shiru yana jin kunyar maganar da ya kawowa Baffan don yana jin nauyi.

“Yaya ne uba na ? ko akwai matsala ne ?.

“A a Baffa dama wata magana ce nake so na fada maka amma Ina jin nauyin ka Baffa.

“Kar ka damu uba na fada min kaji zan fahimce ka ka dauke ni kamar abokin ka kaji,?.

“To Baffa dama naga kwanaki kun tab’a cewa zan auri Nadiya amma ni har ga Allah a lokacin akwai wacce nake so ne Baffa kayi hakuri don Allah shiyasa nace bana son ta .

“Ayya uba na kar ka damu babu komai ai komai ya wuce ba gashi tayi auren ta ba? kaima ka fiddo wacce kake so in sha Allah Baffan ka zai nema maka auren wacce kake so.

“Baffa dama ni fa fati nake so shine nace bari na fara fada maka duk abinda kace haka za ayi.

Baffa yayi shiru kafin yace

“To uba na kace zaka tayarwa yarinyar nan da hankali uba na don fitar wannan maganar shine zai ganar da ita wacece ita don tana kallon ka a wanda kuka fito ciki daya to amma wannan ba damuwa bane uba na matsala tana nan ga binta musamman idan bata ji zata iya karbar ka a miji ba ka san babu wanda zamuyi wa dole daga kai har ita Ina fatan baka Kai ga furta mata ba?.

Alabo ya kada kanshi yana fadin

“Ban fada mata ba Baffa sai dai na jima da tattala son ta a raina .

“Allah yasa hakan ya zama alheri ai zamu so wannan hadi uba na amma ka bani lokaci nayi istikhara mu fara da neman zabin Allah kaima ka daure ka fara muga ni .

“to In sha Allah Baffa nagode Allah ya kara lafiya nagode sosai Baffa Allah ya bar min kai .

“Kayya dai uba na in ka ganni a duniya lokacin ne baiyi ba wanda suka fini daraja ma sun wuce nima lokaci nake jira yadda mutane da yawa suka rasa magabatan su  muma haka zaku rasa mu Uba na fatan dai kuyi mana gata na tuna mu da rako mu da ADDU A shine babban gatan da zakuyi mana.

Kawai sai Baffa halilu yaga alabo yana fidda hawaye yana kuka don hasaso ranar da zai bude ido yaga gawar mahaifin sa mai kaunar sa da gatanta sa.

Baffa halilu yayi murmushi ganin hawaye a fuskar  Alabo.

<< Azurfa Da Zinari 55Azurfa Da Zinari 57 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×