“Uhum uba na kenan kukan na meye? kar dai kace min kukan rashin nawa ne kake nuna min yadda zakayi shi in na bar duniya? A a kar muyi haka da kai mana uba na? kaifa jarumi ne shi kuma jarumi ba a ganin kukan sa don kuka kasawa ne ragunta ne kuma ma in ka cire jarumtar shi kukan mutuwa fa jahilci ne ba nuna soyayya bane in anyi shi nuna soyayya na nan a ADDU A wa mamaci ita gaskiyar soyayya . to zan roke ka uba na ko na mutu don Allah kar kayi mini kuka ka roka min Allah amincin sa da amincin ANNABI MUHD sallalahu alaihi wassalam in kai kayi kuka uba na to hamza da yake kanin ka shi da babar ku da binta wazai rarrashe su har ya basu baki ? hakika akwai magagi da maye ga wanda ya rasa uwa ko uba ko ma dan uwa ko wani jigo soyayya ce ke magagi har ayi kuka amma mafi A ala juriya da tuna ita mutuwa ga musulmi aminci ne kuma hutu ga Wanda yace amantu billahi rabba . sau tari mune mukewa mutuwa kallon azaba ga wanda ta dauka bayan aikin mutum shine mabudin sa ga makoma guda biyu . Kuma mutuwa ibada ce da kowa sai yayi ta alhalin ita din Rahama ce muddin mutum musulmi ne mai I’mani . a wannan duniyar ma Uba na da tashin hankalin cikin ta kadai ya ishe mai I’mani yaushe bawa ke mike kafa? kullum fa ka bude Radio sai kaji wani sabon Al amari da zai saka zubar hawaye ai bawa yayi fatan cikawa da kyau da I’mani uba na kaji? Allah ta ala ya rufa asirin musulmi yayi mishi mafita akan wannan rayuwar in kuma tafiya tazo fatan mu kyakkyawa kyakkyawa tare da aminci share hawayen ka Allah ne gatan mu mu daku.
Alabo ya share hawayen shi ya mike yana fadin
“To Baffa wata ma nine zan riga ka tafiya in na tafi ayi min gatan ADDU AR nan nima.
“Bana fatan hakan uba na nafi son na barku kamar yadda muma namu iyayen suka bar mu muna musu ADDU A kuma kuyi mana ya’yan ku suyi muku kuma Allah yayiwa Rayuwar ku albarka ya hana ku ganin kuncin da yake a cikin wannan duniya.
“smeen ameen Baffa Nagode Baffa Allah ya yaja da rai.
“To ameen uba na yasa zanga ranar auren nan naka ni kam buri ya cika a wanna rana naga auren uba na.
Alabo ya wuce cike da kunyar Baffa wanda ya zamo wani irin uba mai tsayuwa akan ya’yan sa mai son abunda suke so ya kuma tausayawa na kasa dashi. kafin kaga fadan Baffa halilu za a jima in kuma ya fara to zakayi mamaki don ya iya fada baya yi dai. ya dasa wata irin kauna da soyayya a tsakanin shi da alabo wanda yaci sunan mahaifin su shine suke ce mishi slabo su kuma suce ubana . bayan alabo akwai hamza wanda su biyu ne maza Ya’yan Baffa halilu
Kwanaki uku alabo yana gabatar da sallar neman Alkhairin Allah a game da auren nan yana kuma jin kara gamsuwa da son auren yayin da Baffa halilu ma yadda alabo yaji shima haka yaji don haka alabo ya sami Baffan ya fada mishi yadda yaji a ranshi na gamsuwa da auren . sai dai akwai abinda ya gani wanda bai yarda ya fadawa Baffan ba na ganin wata tazara da zata gitta tsakanin shi da fati amma dai duka ya tattare komai ya mikawa Allah.
Baffa shima ya sanar dashi gamsuwar da yaji don haka yace yaje ya samu Baffan shi iro ya fada mishi in yaso kome kenan dama shine mai shige mishi gaba ko yana raye ko ya bar duniya. don haka ya tura shi bauci wurin Alh iro.
A ranar da Baffa ya ce yaje ya sami Baffan nashi a ranar alabo ya dauko mota ya nufo bauci.
Alh iro yaga Alabo ya tarbe shi yana fadin
“Uba na kaine tafe ? yaya su yaya halilu da yaya Hajara?
Alabo ya zube a gaban shi yana gaishe su shi da haj aliya wacce ta cika mishi gaban shi da kayan tarba kafin ta basu wuri shi da Baffan nasu.
“In ce dai kuna lafiya uba na?
“Eh lafiya lau muke Baffa dama munyi wata magana ne da Baffa shine yace nazo na same ka na sanar da kai ba shi ne zan fadawa ba.
“Allah yasa ka samo mata ne uba na don har na fara imagine din sama maka mata amma dai na dakata don baka damar ka.
“Baffa in har ka sama min zan karba sai na sje nawa muradin Baffa tunda na san zaku fini hange.
“A a yba na gara dai a barka ka darje ka sami wacce hankalin ka ya kwanta akan ta.
“to Baffa na gode amma kayi hakuri don Allah da abinda zan fada maka wata kil maganar ba zatayi maka dadi ba kayi hakuri Baffa.
“Kar ka damu uba na ai zan fahimce ka raina ba zai baci ba in ma ya baci zan nuna maka yadda zaka gyara tunda har yanzu da kuruciya a tare da ku ita kuwa kuruciya sai ana hakuri da ita fads min kaji uba na?.
Alabo yayi k’asa da kanshi yana fadin
“Baffa dama ni fa fati nake so na dade ina son ta amma sai na kasa sanar mata shine na fadawa Baffa shi kuma yace kaine mai nema min aure a ko ina ne don haka nazo na same ka na fada maka.
Baffa yayi murmushi Yana fadin
“Alhamdulillahi alhamdulillahi uba na hamdan kaseeran naji dadin wannan maganar taka kuma dama auren da nake maka magana a yanzu dama har ga Allah na yanke hukuncin hada ka aure da fati amma ina gudun kar ya zamo an shiga hakkin wanin ku sai kawai na barwa Allah ikon shi uba na tunda Nadiya tayi aure hankali na ya koma ga fati da wanda ya dace da ita duk wanda zan hango sai naga kaine kafi kowa dacewa da ita sai gashi Allan ya taya min ya hada zukata to amma ka tuntubi ita fatin da wannan maganar? .
Da sauri alabo ya kada kanshi yana fadin
“A a Baffa ban sanar da ita komai ba ko shi Baffa cewa yayi kar na tayar mats da hankali.
“To alhamdulillahi uba na hakika fati tana maka kallon dan uwa kuma Yayan da suka fito ciki daya in har ka tunkare ta da wannan maganar wata maganar zata fito har ta nemi sanin wacece ita? Idan kuwa ta san wacece ita to dole ma magana zata fito har kan Nadiya abinda kuma ba zan so ba don su duka zasu nemi sanin su waye su? to ka barwa cikin ka wannan maganar amma kuma ni nayi maka alkawarin kaine mijin fati smma Kar kace mata ga yadda zuciyar ka take jin ta don zaka jawo magana uba na ka barni zanzo missu din na sami yaya halilu sai muyi magana amma ka saka ranka a inuwa in sha Allah uba na kaine mijin fati.
Alabo yayi murmushi yana fadin, “na gode Baffa Allah ya kara girma yaja da rai.
*****
Tun ranar da Kaisar ya yi mata wannan wulakancin ta daura aniyar bashi mamaki matukar dai ya kuma gigin tab’a ta don haka ta tanadi kakkaifar wukar ta wacce take nufin warbe shi idan ya kuma haike mata yayi mata fyaden
Bai kuma kula ta ba har tsayin sati biyu yana ta hidima da twins wanda suke cikin wata na biyu sunyi girma na ban mamaki ga wayo da suke dada karawa yayin da uwar su kuma take dad’a nisa da su don yanzu kam no-no ma sai ta so ta Basu in bata so ba sai dai su wuni suna shan madara. tuni Kaisar ya zage da hidimar su wankan su da sanya pampers da cirewa duk ya kware Kuma Yana yin kokari matuka gaya wurin siya musu sutura pampers da madarar NAN tana karewa zai kawo wata. tuni kuwa su Ramadan suka kyalewa Nadiya nonon ta don sau dubu zata dungura musu shi a yanzu ba zasu karba ba ko kuwa sun gane babu tabbas a nata ne shiyasa suka kama dahir din madarar su ? ko kuwa ma dai madarar tafiye musu nonon? To Allah dai shine mssani amma tun basu cike wata uku ba suka barta da kayan ta abinda dama take so shiyasa ma take musu kurullah don wai kar tsotsa ya kayar mata da kirji sai gashi a arha ma sun bar mata kayan ta a tsaye yayi ta tssyuwa fuye da mil ma .
Ranar da Kaisar ya kuma kwana da Nadiya irin wancan al smarin ne ya kuma faruwa ta kasa katabus har ya tabbatar da ya gamsu ita kuma taji kamar an daure ta duk da kakkaifar wukar da tayiwa masauki a karkashin fulon ta wadda taso yana nuna mata maitar sa ta jawo ta ta shatale mishi wuya amma sai taji kamar ya daure ta dauri kuma irin na goro bata samu zarafin wani kokari ba sai da ya nutsa har yana sauka daga gadon kafin ta cacumo shi ta rike tana kuka tana fadin
“Me kayi min ne haka? Wane siddabarun da kulunboton ne kayi min? yayi murmushi yana duban ta bai iya ce mata komai ba sai fuskar ta da ya shafa yana fadin
“I love you too my dearest.
Ya fige rukon da tayi mishi ya wuce ya barta tana mamakin karfin bawan Allah nan wanda ta gama raina ajawalin sa amma duk lokacin da ta shiga hannun sa tana jin jiki duk da ta gama tabbatar da bai kyale ta haka nan ba sai da yayi mata wani abu wanda ta gama yarda sihiri ne.
Kaisar ya Isa sashin su haj Aliya Yana fada mata zai je gombe gaishe da su baddo da kawu yayari don ganin watan azumin Ramadan yana dab ya kuma Kai musu abunda ya samu
Haj Aliya tayi mishi fatan alheri ta kuma bayar da suga da shinkafa tace ya kaiwa tsohuwa baddo kakar sa inda ya nuna mata kayan da daddy Alh iro ma ya bayar yace a kaiwa yan Billirin duk da ya fada mishi shima zaije misau a yau din Haj Aliya tace ai ya ma tafi yana can
Da haka shima Kaisar yayi mata sallama ya fice inda yake ta tunanin Yaya zaiyi da su sha aban da Ramadan? wata zuciyar tace ya tafi da su sai kuma yaga zasu sha wahalar jijjigar mota sai kawai ya kawo su wurin haj Aliya ta Karbe su tana musu wasa suna kallon Kaisar da Yake jin zaiyi kewar su haj Aliya ta dube shi tana fadin
“Yaran nan fa Kaisar wallahi sun gane ka dubi fa kallon ka suke daga wanna kallon sai kyuiya .
Yayi murmushi yana fadin, “Ba zasuyi ba mama bari na tafi sai na dawo.
Suka yi sallama ya fice ya dauki mota ya hau hanyar gombe. karfe biyu na rana ya iso garin gombe kasancewar juma a ce yasa ya tsaya a babban masallacin juma a na garin gombe yayi sallar juma a ya tashi zai koma mota ne yaji an ce allazi wahidun Allah da GIRMA Yake.
Da sauri ya juyo sai ya ga dattijon yana dogara sandar sa da sauri ya nufe shi yana fiddo kudi zai bashi.
“Baba barka da juma a.
Dattijon ya juyo yana fadin
“Yauwa barkan mu dai yaro kaine a nan?
Ya duka yana gaishe har ya bashi kudin wanda ya karba yana godiya.
Kaisar bai tambaye shi komai ba don ya yarda ba mutum bane tunda ya ganshi a bauci yanzu kuma gashi a gombe babu inda ba za a ganshi ba .
“Karbi wannan maganin yaro kasha da sunan Allah in sha Allah Ubangijin yayi maka kariya yarinyar can ba zata samu damar cutar da kai ba tunda gata can tana neman yadda zata kashe ka smma Allah ya fita kuma duk abinda tabaka ka karba kaci in sha Allah ka gama da ita.
Ya karbi ruwan maganin yasha yayiwa dattijon godiya ya wuce inda yaga tsohon ya shige cikin jama a daga nan bai kuma ganin shi ba ya b’ace b’at don haka baiyi mamaki ba ya wuce Billiri.
Fitar kaiser daga gidan ne ya bawa su keena da ta gama haukacewa akan Nadiya da Kaisar. da kyar ta iya kwana garin ya waye ta dauko su luba da safina suka nufo gidan Alh iro da fatan su shigo sashin can suga wacece? sai dai duk zuwan da zasuyi zasu tara’s da Kaisar a bakin kofar ko kuma a bakin get wanda dole zai mayar da su . shiyasa suka kasa samun shiga sashin can
Duk da haka basu hakura ba suka jaraba suna ta zarya har dai a ranar ta yau suka shigo gidan ba su ganshi ba ai kuwa da sauri suka fita motar suna shiga ciki inda maccid’o ke wa luba kallon mayata don ta cije shi shiyasa ma bai basu matsala ba suka shige
Kai tsaye suka afka sashin nan suna tura kofar wacce take a bude duk da basuyi zaton samun ta a bude ba.
Nadiya tana zaune tana kukan keta haddin da Kaisar yayi mata sai ganin su luba da keena tayi akan ta ta mike da sauri tana rungume keena tana Kara fasa kuka don takaici .
Kukan ta ya Rikita su keena .
“Subhallahi Nadiya me yake faruwa ne,? me kike yi ne a nan? ance an miki aure ? meye gaskiyar haihuwar da ake yayatawa kinyi?.
Duka keena ta jero mata wadan nan tambayoyin tana duban ta yayin da Nadiya ke ta sheka kuka tana jin tamkar su keena ne maganin matsalar ta yayin da su safina sukeb ta kallon ta da son ta asu amsar tambayoyin da keena ta jera mata .
Suna cikin zaman ajon da ya aure su ne suka ji Haj aliya ta shigo bakin kofar tana kiran Nadiya don ta karbi su Ramadan . Nadiya ta mike tana amsawa ta fice ta Isa bakin kofar ta karbo yaran shiyasa haj Aliya bata ga su keena ba don da ta gansu tabbas zata auna su waje don ta gama yarda kawayen Nadiya bara gurbi ne rubabben kwai . ta karbi ya’yan ta juyo ita Kuma haj Aliya ta fice don bata son zuwa sashin don kame girma yanzu ma kawo yaran tayi shiyasa.
Nadiya ta shiga da su Ramadan da sha aban abinda ya gigita su keena ganin identical twins din suka warci yaran suna fadin
“Wai twins ne kika haifa? waye uban su ? waye mijin naki ba dai gayen nan dan aikin gidan ku ba? Nadiya ta dubi Keena da wadan nan tarin tambayoyin wanda sukayi matukar bata haushi har ta tanka a zafafe tana. “Haba keena sai kace dai a kiyama wadan nan tambayoyi? ni na rasa ma inda kuka samo wannan labarin.
“Samira Mustapha ce ta ce ta ganku a asibiti kin haihu da muka zo nan gidan naku kuma mamar ku tace kinyi aure sai ga gayen nan wanda Kika ce dan aikin gidan ku ne mun gani yana rike da daya daga cikin yaran nan ni abinda kawai nake son sani Nadiya da gaske kinyi aure? Kuma waye mijin? Nadiya ta goge hawayen idon ta tana fadin
“Da gaske ne keena nayi aure kuma wannan gayen da nake fada miki dan Aikin gidan mu shine daddyn mu ya aura min .
Keena ta dafe kirji tana gwalalo idanu tana fadin, “Inna lillahi wa inna ilaihir Raju un ni kam shiga uku ta same ni Nadiya. Nadiya ta dube ta tana Fadin
“Kar ki damu keena na san kina son kaiser ni din kuma ba son sa nake ba in har kin shiryawa auren shi ni bani da matsala don wallahi ba zan iya zama da dan aikin gidan mu ba kaskantacce irin shi wallahi naci baya ko a idon ku kawai bare kuma duniya ta shaida.
“Alhamdulillahi kawata ni Kam na shirya auren shi tunda ma har ba zama zakiyi ba ni kam naga wuri fatan zaki Kama min har na shigo don wallahi tunda na dora Ido na akan gayen nan har yau din nan ban huta da azabar son sa ba.
“Kar ki damu keena ni fa kin dade da sanin show ne abinda zuciya ta take so kuma har gobe shi nake so. “To Alhamdulillahi sai mu kamawa juna har mu cimma buri ki kama min na shigo nima na kama miki ki fice kije ga muradin ki.
“Ara min wayar ki keena na kira show mun jima bamu hadu ba don rabo na da fita har na manta.
Keena ta bata aron wayar ta kira show akayi ta soyayya yana tambayar ta me yake faruwa ne yake neman layin ta yaji shi a rufe? Ta fada mishi an rufe layin ta ne kuma babu waya wurin ta yace zai aiko mata waya da layi zai hada mata komai.
“Nagode Darling zan turo keena ma ta karbar min.
Da haka sukayi waya cike da kewa da soyayya ta bawa keena wayar ta.
Keena ta dube ta tana fadin, “Kin shirya rabuwa da gayen nan ko kuwa akwai lokacin da kika tsara kike jira lokacin yazo?
Da sauri Nadiya ta dubi keena tana fadin, “Wallahi ko yanzu zan samu na rabu da shi Ina murna don Allah kadai yasan yadda nake ji yadda kika san Ina kan kaya haka nake ji in yanzu na samu na zulle so nake.
“To bani hankalin ki nan na Baki datar da zaki sami hakan . duk abunda kika san baya so shi zakiyi ta masa da zaki yarda ma har show din naki ya kamata ki rika kawowa nan na tabbatar da ba zai lamunci wannan ba ni kuma yanzu ki bani lambar wayar shi da ta motar shi shikenan.