Kan kace me? Laulayi mai zafi ya riske ta ta na faman kwara amai abinda yaja hankalin Kaisar kanta ya Kuma kwashe ta zuwa asibiti duk da shi da kanshi yaji s jikin shi ciki ne da ita yayin da murna da farin ciki suka cika shi musamman ma da likitan ya tabbatar mishi da hakan.
Ita kam Nadiya a rikice take tana kallon likitan da tashin hankali ciki ? cikin ma na wannan fakirin matsiyacin dan aikin GIDAN su? da sake wallahi ai zata dukan kirji tace Ya’yan abdulhameed uban su yana da matsayi da daukakar uban sa duk da ba aure ne ya bayar da su ba amma cikin Kaisar tace me akan matsiyaci fakiri kuma dan aikin gidan su? da sake wallahi.
Da wani irin matsiyacin fushi Nadiya ta fice daga asibitin ta bar Kaisar wanda yake cike da farin ciki da godewa Allah wanda zai cika mishi mafarkin sa na samun rabo tsakanin sa da Nadiya.
Ya mike da sauri yana bawa likitan hannu sukayi musabaha ya fito amma bai ga Nadiya wacce tana fitowa ta tare napep ta nufi asibitin da ta San za a zubar mata da cikin nan don bata shirya haihuwa da Kaisar ba haba wannan sbun kunya ne a gare ta banda haike mata da yake kuma ace tayi cikin shi wane irin abun kunya ne wannan?
Ta isa asibitin ta kuma zayyane abinda take bukata wato zubar da ciki .
aka auna ta ganin baiyi kwari ba yasa aka bata kwayoyin magani ta taho .
Kaisar duk ya rude rashin ganin Nadiya ya kuma zo gida bai ganta ba abinda ya kara rikita shi ya shiga neman ta amma bai yi nasarar ganin ta ba har ya hakura ya dawo bakin kofar ya tsaya da fatan ya ga ta inda zata biyo
Ya tsurawa hanya Ido har zuwa lokacin da napep ya sauke ta yaga lokacin da ta shigo ya biyo bayan ta har zuwa sashin su.
“Kin tayar min da hankali Nadiya Ina kika tsaya ne?
Ta ajiye jakar magunguna tana mishi wani shegen kallo tana gadin
“Hankalin ka ya tashi ? to sai ayi yaya don hankalin ka ya tashi? Kuma inda naje ma ai zan iya fada maka tunda ba tsoron ka nake ji ba asibiti naje don s zubar min da cikin nan don Kai kanka ka san ba zan iya daukar cikin fakirin matsiyaci irin ka ba wallahi dole na zubar da shi sau dubu garan min cikin farko da nayi ko ba komai uban su dan babban gida ne kuma ba fukara u bane .
Cike da tashin hankali yake kallon ta don ya razana da maganar zubar da cikin da ambata.
“Kar kiyi min haka Nadiya don Allah don ANNABI kar ki zubar min bani da kowa sai shi .
Tayi wata dariya ta rainin hankali kafin tace
“A baka da kowa sai shi kake so na lalace a haihuwar sa? da kana da wani abu sai nace muyi tsada ka biya ni na haife maka tunda kana so amma ni kam rariya nayi nufin kaishi ba kuma zan fasa . to baka da komai kai kanka damu ka dogara fakirin ka matsiyacin ka sai na lalace a haihuwar ya’yan ka? Idan har kana son na haife maka cikin ka to ka nemo kudin ka muyi tsada ka biya ni kudin kudin rainon ciki ka kuma biya na haihuwa ni kuma zan tsaya na haife maka dan ka na baka na kara gaba in kuma baka da kudi baka da hanyar kudi to Ina mai tabbatar maka da wannan cikin ba zai kuma kwana biyar a jiki na ba don haka zanyi maka alfarmar baka sati daya ka shiga ka fita ka samo kudin biya na in kuma aka wuce sati baka kawo min kudin nan ba to kake kallon cikin nan a matsayin mafarki kuma mataccen da aka hak’awa kabarin bunnewa ta haka zan Gane Kai ZINARE ne ko AZURFA idan har ka kawo kudin nan to lallai maganar daddy ta tabbata kai din ZINARE ne to inga hakan a bayyane.
“Na siya in dai wannan shine bukatar ki nawa ne zan biya kudin rainon cikin da na haihuwar? In sha Allah zan siya na biya a fada min kudin yanzu na tura ko kuma na kawo cash duk wanda kike so haka za ayi ranki ya dade.
“Me zai hana na fada maka tunda zaka iya biya? kudin rainon ciki milyon biyar na haihuwa kuma milyon goma in ka shirya sai ka bani milyon sha biyar in kuma ka taya ko ka nemi ragi na fasa wallahi sai dai kaji na zubar a rariya.
“Kai ai ni arha ma yayi min sweetie na kara miki ma milyon biyar su zama ashirin .
Ta dube shi da wata irin razana don batayi zaton hakan ba abinda tayi zato ta san bashi da ko dubu dari in ma rance zzai nema ba zai iya samun milyon goma sha biyar ba sai gashi da Arashin kara mata milyon biyar.
“Account zaki bayar na tura miki ko kuwa cash zan kawo miki?.
“Bana son cash don na san wurin daddy zaka je ka aro su ga account details nawa ka saka min su don in aka wuce yanzu wallahi na fasa wannan damar ta yanzu ce kawai shima don na san karya ce kawai taf a cikin ka Banga ta inda zaka nemo kudin nan ba don haka ban yarda ka matsa ko ina ba yanzu zaka saka min su naji saukar su cikin account Din.
Ta fada tana mika mishi account details din
Yayi murmushi ya karba yana fadin
“Ko nan da awa daya ba zakiyi min alfarma ba sweetie.
“Ko minti sha biyar ba zan iya yi maka alfarma ba sai na kure karyar fakiri matsiyaci irin ka.
“To Alhamdulillahi llazee bi ni imatuhi tatummussaliha
Ya fada yana tab’a wayar shi ya shigar da account details din yayi ya gama ko minti biyar ba ayi ba Nadiya taji karar shigowar sak’o wato alert
da sauri ta duba wayar ta kuma ga kudin kwance a a cikin account din.
Ta dube shi cike da mamaki amma ta kasa cewa komai.
“Yanzu zan samu Daddy na fada mishi yadda mukayi idan har want abu ya samu cikin nan Nadiya.
Ya murza yatsun hannun shi sukayi Kara amma dai bai karasa furtawa inda ita da kanta ta karasa sauran maganar m.
Ya fuce ya barta da baki sake
bai jima da fita ba ya dawo shi da Daddy da Haj laila
tana nan zaune inda ya barta don ya gama hade mata lissafi. abinda take tambayar kanta Ina ya samu wadan nan kudin? waye shi da daddy yake kiran shi da ZINARE?.
Daddy ya zauna yayin da Haj Aliya ta kasa zama tayi tsaye tana kallon Nadiya da mamakin bakar zuciyar ta .
“Menene gaskiyar abinda Kaisar ya ke fada min a yanzu Nadiya? cikin shege ne kike iya dauka ki Raina a kyauta amma cikin auren sunnah shine ba zakiyi hakan ba sai an biya ki? wai ke wace irin mutum ce ? ke nawa aka biya uwar ki a daukar naki cikin? kin fa fara Isa ta wallahi Allah ya sani hakuri na ya fara karewa akan ki ina tsoron nayi Miki abinda zai dame ki duk da tausayin ki da neke ke ba kya tausayawa kanki to bani wayar taki nan in maida mishi da kudin shi in kuma kika ce ba haka ba wallahi kema sai biya kudin wahalar da akayi miki ba uwar taki kawai zaki biya ba ke naki lissafin mai tsayi ne dashi ko za a saka ki kasuwa ba xaki iya biyan shi ba.
Daddy ya karbi wayar Nadiya ya duba account din ta yaga kudin da Kaisar ya tura mata don haka take ya mayar wa Kaisar da kudin say account din sa don su duka ya san account nombar kowa ya tura kudin yana wurga mata wayar yana fadin
“Ciki kuma ki zubar zan baki mamaki wallahi zubar da cikin nan shine nadama ta karshe da zakiyi a rayuwar ki .
“Daddy da baka karbar mata kudi ba hakkin ta ne na kuma bata.
“Kai fita idona shiyasa ta Raina ka an gaya maka komai ne ake biyewa mace ? In kuwa kace haka zakayi da gudu zata auna ku wutar jahannama don wannan yarinyar da ka gani tafi iblis shaid’an ci .
Daddy ya fice yana fada Haj Aliya ma da mamaki ya hana ta magana ta bi bayan Daddy.
Nadiya ta dubi Kaisar tana fadin
“Kayiwa kanka kanka dama ni na san manuba ce wannan kudin kuma wallahi na gama da Kai ciki kuma a yanzu kan idon ka zan sha maganin da zai bi rariya.
Ta figo ledodin maganin ta fito da kwaya biyar ta auna a baki tabi da ruwa duk kokarin da yayi don ganin bata Kai maganin baki ba sai dai ya makara tuni ta kora da ruwa ta hadiye.
wani irin sanyin jiki ya ji dole ya sallama ya kuma karbi kaddarar hakan ya fice yana jin kanshi yana sarawa.
Yaji duniyar tayi mishi zafi har ga Allah ya dora rai da cikin nan amma dole yayi hakuri wata Kil bashi da rabon samu ne.
Ya fita zuwa waje duk da bai san inda zaije ba amma ko babu komai dai zaiyi nesa da Nadiya wacce ya soma jin tsanar ta a yau.
Ya fice daga gidan ya nufi titi sai ji yayi an ce Allazi wahidun Allah da GIRMA Yake.
Ya jiyo yana ganin dattijon yana nufo shi yana dogara sandar sa .
“Kar ka damu yaro kaji Allah shine gatan ka .
cewar dattijon wanda ya fara fadar hakan da haduwar su.
Ya duk’a yana gaishe shi ya kuma fito da kudi yana mika mishi.
“A yau dai ba zan karbi kudin ka ba yaro Kai baka gajiya da kyauta ne?.
“Ayi hakuri a amsa baba ayi mana ADDU A.
“Kar fa ka damu don naga ka damu sosai akan zubar da cikin nan da zatayi kar ka samu damuwa ka barwa Allah koman ka in sha Allah ba zatayi nasara ba ka kwantar da hankalin ka yadda Allah ya so haka akeyi babu wanda zaiyi abinda Ubangiji bai zana ba koma gida kaci gaba da sabgogin ka.
“To Alhamdulillahi baba nagode da karfin gwiwar ka Allah ya kara lafiya.
“to ameen ameen yaro Nagode Allah ya jikan iyayen ka mutanen kirki in sha Allah yadda suka zama mutanen kirki suka haife ka dan kirki insha allan sai ka wanzar da mutanen kirki ta tsatson ka .
Ya fada yana wucewa Kaisar yana amsawa da ameen ameen.
Ya komo gida ya shiga sabgar shi da yan biyu inda kuma ya jiyo Nadiya tana waya tana fadin
“Nifa Dr har yanzu ko d’igon jini ban gani ba bare fitar want ciki kuma fa babu ciwon komai.
Yana jin ta bai dai tanka ba har yaji tana fadin
“Kwaya biyar na sha gaba daya yanzu kan sai dai na Sha goma na gani .
Ya fito falo yayin da su Ramadan suke hawa jikin shi suna sauka suna kuma jawo kayan barna suna game kishi Kaisar Yana ta janye su suna komawa amma suna ganin Nadiya suka koma jikin aisar suna lafewa tsoron ta suke ji basa ko zuwa inda take .
ta jawo kayan magungunan ta ta soma banka har da over duk Kaisar yana kallon ta amma tamkar shukar dussa babu wani labari har tsayin wata da kwanaki sai ma girma da ciki yake karawa.
Keena ta dubi luba tana fadin
“Ke kika ce aikin ba I’mani kamar yankan wuka amma dubi yaudarar da yayi min,? sati nawa yau da cewa Kaisar xai zo bai zo ba?. to in aikin bai samu ba ba sai s bani kudi na ba?
luba ta dube ta tana fadin
“amma kuwa kece lambar farko da ya kamata ace kin bada shaidar aikin ba I’mani tunda yayi miki kin gani kawai dai ina Jin yanzu ne dai aka samu akasi.
“Kuma duk akasin ya kasa samuwa sai da akazo kan abinda nake so? babu fa abunda ba zan iya akan Kaisar ba luba in nace miki komai to Ina nufin komai wallahi.
“To keena ai sai kije ki same shi kiyi mishi bayani ni ai na miki mai wuyar tunda na nuna miki hanya.
“Dole na san abinyi luba tunda ba zan iya hakura da Kaisar ba.
Wayar keena ta dauki tsuwwa tana dubawa taga shaid’an ne yake kiran ta taja baya da sauri kamar wacce kunama ta gallawa harbi.
“Inna lillahi wa inna ilaihir Raju un shegen mutumin nan yaga lokacin da na diba ya wuce bai ji ni ba gashi nan yana kira na Luba me zan ce mishi?.
“Dauki ki fada mishi kina hanyar jos don in ba haka kika ce mishi ba to ba zai barki ki sarara ba.
Wayar ta tsinke aka sake bugowa keena ta dauka tana fadin
“Ina kan hanyar isowa shaid’an ka saurare ni .
“Na fa gama gane yaudara ta kike sakina Anya kuwa kin san ni ? to kar ki bari na fito miki a shaid’ani na don zaki Kare ne har babun ki idan kin san ba zaki iya kwangilar da na baki ba to turo min kudi na.
“Haba dai me yasa kake tunanin zan yaudare ka? Ai babu wannan a tsakanin mu komai dare ka saurare ni yau in sha Allah a jos zamu kwana.
“Na dai fada miki in kin san yaudara ta kike gara ki sauwake wa kanki na gaya miki don har yanzu baki san waye shaid’an ba to wallahi kina dab da sanin waye ni.
Ya tsinke wayar shi ya bar keena da sakakken baki ta dubi luba tana fadin
“Kiji min mutumin nan yana neman tayar min da wuta .
“Da Allah rabu dashi dabara tana kare mana ne,? In ma ya sake kira kice mishi ya saurare ki .