Skip to content
Part 6 of 23 in the Series Azurfa Da Zinari by Hadiza Gidan Iko

Mama ta dubi Nadiya cike da mamaki jin tana fadin ba zata yi girkin ba.

“Ba zaki yi girki ba kika ce? Sai kuma tayi shiru ta kasa maimaita abinda ta fada amma kuma a k’asan ranta haka take nufi ta yaya za a ce tayiwa dan aikin gidan su girki in ba son a muzanta ta ba?

Mama ta mike ta figo shareriyar bulaliyar tana fadin “Yau zanga iyakar rashin mutuncin ki Nadiya.

A fusace ta nufo ta zata make ta da gudu Nadiya ta nufi kitchen din tana dora tukunya tana fadin, “Saboda Allah mama ko break first banyi ba zaki saka ni yiww wani katon wofi girki salon kisa ya raina ni ya ke daukar kanshi wata tsiya?

Mama ta tsaya a bakin kofar kitchen din tana fadin, “Wallahi ba zaki bar  kitchen din nan ba sai ki girka dukkan abinda kika san kin baiwa karen can don ba zanyi sammakon wofi ba kina can kin shanya baki kina bacci baki taya ni ba kuma kice ba zance wani abu ba kinci uwar karya wallahi kin kwana da yunwa  kuma babu ke babu cin wani abu har sai kin kammala dukkan girke girken ai kin san dai yawan kayan abincin da kika zubarwa kare ko? To maida niyya don ba zan matsa ko Ina ba sai kin kammala komai.

Hajiya Aliya taja ta dake lamba. Tuni Nadiya ta soma girki kasancewar akwai kayan girki na zamani tuni tayi bakin gas uku shiyasa tayi sauri amma kuma dukkan girke girken da take yi babu wanda bata saka mugunta ba. daga wanda ta faki idon mama ta afka gishiri sai wanda ta zabga yaji don a cikin naman kan saniyar ma har da zu kero ta zuba inda kuma zata saka suga sai ta zuba gishiri inda zata saka gishiri kuma ta zuba suga abinda bata sani ba mama na kula da ita bata sani ba ne shi ramin mugunta gajere ake gina shi in kayi mai tsayi kai ne ka fada. Ta kashe gas tana hade fuska don idan akwai wani Abu da Nadiya ta tsana a rayuwar ta to girki ne shiyasa fati tayi mata zarra a wurin iya girkin itama haj tafi son Fati ta taya ta sikin duk da tayi kokari matuka gaya wurin ganin ta koyar da Nadiya da Fati nau oin girke girke kuma tuni suka iya  don mace babu iya girki ai ta zama wacce ta rako  mata, “Na gama Mama ta fada tana gimtse fuska, “Sai ki dauko kayan can ki wance ki zuba komai a muhallin sa ki taka ki Kai mishi in yaso sai kizo ki karya ai duk wanda ya hana uwar sa bacci shima kuwa ai ba zai rantsa ba.

A dole ta wanke kwanukan ta soma zuba komai tana murmushin muguntar da ta san tayi har ta gama inda mama tace ta rage sauran abincin ta kuma rage ta dauka ta fita. Mama ta bi ta da kallon tausayi fitowar kaisar kenan daga toilet yana tsane ruwan dake jikin shi Nadiya ta shigo tana mishi kallon raini.

“Kai masoyiya ta wani girkin kika yi min ko kuwa Mama ce ta saka ki?

“Ita Mamar uwar ka ce n da kake Kiran ta da mama? Ko kuwa samun wuri ne don ka ga an baka wannan dakin wanda duk zuriar ku babu mai arzikin mallakar sa? To Nemo jahilar uwar ka  a inda ka baro ta. Yayi murmushi yana fadin, “In na cewa mamar ki mama ta ai banyi laifi ba ko? mamar ki tawa ce in bakiyi sannu ba ma sai na fiki fada a wurin ta. Taja tsaki tana fadin, “Matsiyacin banza Wanda talauci yake shirin gajiyar da uwa da uba kayi maza ka gama ka wanke min mota zan kuma aike ka kasuwa don ni ko a wankin da aka dauke ka ba zanyi iya baka kaya na ka tab’a ba don ni kam kyankyamin ka nake wallahi bare har na baka undies dina nonsense kawai. Tana shirin ficewa ne taga ya mayar da kofar ya rufe yana kallonta yana murmushi yana fadin,

“To ki sauya min aiki mana uwar daki na ai saboda ke fa aka dauke ni aikin nan dukkan aikin da kike so nayi miki shi zanyi komai wahalar sa kuwa.

“Me kake nufi da rufe kofar Nan? “Ina nufin nuna miki I love you. Ya matso dab da ita ya rungume ta rungumar da tazo mata a ba za ta ya kuma kai bakin shi a nata yayi mata kiss duk da taso nuna jarumtar hana hakan amma taji tamkar ba shi ne ya kankame ta ba don haka sai da ya sake ta don kanshi kafin ya soma bude abinda ta kawo yana fadin

“Dole ne naci abincin da kika girka da hannun ki darling I love you.

Ya debo kwan da aka hada da dankali ya kai bakin shi amma yaji gishiri zau amma a haka ya hadiye  bai nuna ba sai ma yayi ta cin abincin a haka tamkar baiji aibun da yake cikin abincin ba sai ma yabawa da yake.

Ita kam babu abinda take sai tofe tofen yawu saboda kiss din da yayi mata a baki da sauri ta murda key din kofar ta fice don tana jin amai yana shirin kwace mata mana na zaune a falo ta shigo ta wuce dakin su zuwa toilet tayi ta wanke baki da maclean da kumfar sabulu har ta gama ta fito falo tana jan kayan break haj ta dakatar da ita tana fadin, “Ai babu kason ki a nan ciki sai dai ki dauko cikin wanda kika girka.

“Mama wancan fa bashi da dadi. Sai kuma tayi shiru ta kasa karasawa.

“Na san bashi da dadi amma a haka kin san bashi da dadin kika kaiwa kaisar? To wallahi baki da wani kaso a cikin abincin gidan nan a yau sai wancan da kika girka tun daga safiya har zuwa dare gara ma ki gane cewa mugunta bata da wata rana ketar gwaiwa Mai ita take kashewa don haka wancan sauran abincin shi zaki ci yanzu kici da rana da dare ma ki dunduma amma Ni ko fati ke ko su Ade sukayi girki babu rabon ki a yau dai wallahi sai dai ki kwana da yunwar ki kuma ko kofar falon nan kin gama fita.

Nadiya ta koma kitchen tana bude sauran abincin da ke akwai tana tunanin wane zata iya ci daga ciki? amma ta gane babu wanda zata iya ci sai kawai ta fice daga kitchen din ta koma daki tana fidda kwalla haka kuma mama take nufi don ko da rana bata yarda Nadiya ta shiga kitchen din ba haka kuma ta kasa ta tsare a falo inda fati ce ta kaiwa kaisar abinci yana tambayar ta Nadiya abinda yayi matukar tsorata ta duk da ita da kanta ba zata ce ga dalili ba da dare ma haka inda duk sake a falo har da kaisar da daddy da Mama da fati ana ta fira daddy ya dubi Fati yana fadin ina nadiya ? Tace tana daki yace a Kira ta tazo falo ta zauna ayi fira da ita ta fito ta zauna kamar wacce aka cewa dago sai kawai idanun su suka sarke da juna ita da kaisar ya zuba mata shanyayyun idanun shi ta galla mishi harara tana kawar da kanta gefe. Daddy ya dubi kaisar yana fadin “Kaisar gobe zamu fita kaga kamfani ko zaka iya aiki? In kuma ba zakayi aiki ba tunda ka gama karatu sai a nema maka aiki ko?

Nadiya ta dubi Daddy Jin wai zai kai shi kamfani wai waye wannan mutumin? wane irin sihiri yayiwa daddy ne?

“Daddy duk abinda kace shi za ayi  amma da ka barni na rika tuka su nadiya a mota ina kaisu duk inda zasu je. “Haba haba kaisar ka zama direba ? ba zai yuwa ba.

“Allah kuwa Daddy zai yuwu ina so ne na ke hidimar su da kaina aiki kuma ko ban gaba sai a nema min in kuma bani da inda zan kai su a ranar sai nazo kamfani.

“Uhum kaisar ko dai Nadiya ta.

“Allah ya sauwake daddy na shiga tukin wannan matsiyacin ba wanki yace ka dauko shi ba shine ma har yake da zabin aikin yi? Daddy wannan yaron fa mayaudari ne me yasa ka yarda ka kawo shi gidan nan? A jiya fa muka hadu dashi a wurin party yake min karyar banza shine yazo har ya samu shigowa gidan Nan wallahi Daddy ban yarda da shi ba yazo ne kawai don ya yaudare ka kura ce da fatar Akuya.

Daddy yayi k’asa da kanshi yana jin kunyar maganganun yarinyar nan mama ma haka.

“Ba kece na yiwa kashedin kiran wani da wannan sunan matsiyaci ba? me yasa ke baki son a zauna lafiya? kar ki kuma aibata kaisar domin kuwa shi ZINARE ne ke kuma AZURFA kin san duk darajar AZURFA bata kai ZINARE ba ko ? To ki rika kallon kanki a matsayin AZURFA kaisar kuma ZINARE na baki satar amsa don haka kar ki kuma ce mishi matsiyaci don ni da kaina ne zan nuna miki fushi na in kuma nuna miki taxarar ku ke da kaisar in kuma nuna miki banbancin AZURFA DA ZINARE  kuma daga yau kin daina shiga mota ko kiyi drybin da kanki tunda haka kaisar yake so haka za ayi ke daga yau ma shine mai zartaswa a gareku ke da fati sai ki koyi yadda zaki girmama shi sakarai dabba dake  tashi  daga nan ki bani wuri mutuniyar banza. Da wani irin tashin hankali ta mike tana son sanin waye wannan kaisar din wofin da har yake zama mai zartaswa a gareta?

<< Azurfa Da Zinari 5Azurfa Da Zinari 7 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×