Skip to content
Part 61 of 64 in the Series Azurfa Da Zinari by Hadiza Gidan Iko

Ango na gefe yana kallon yadda abokan sa su Kaisar suke ta shiga da fita don fidda shi kunya . Kowa ya bude baki zai ce a nuna mishi wannan Ango amma sai Kaisar yace baya gari amma in Sha Allah anjima ko gobe zai bayyana

Fati ta kwana cike da bege da son ganin mijin nata bakin ta dauke da ADDU AR alheri gareshi da auren su amma har a washe gari da ya kama Ranar walima bata saka shi a idon ta ba sai can yamma tana tare da kawayen ta na garin misau wanda suke ta shirin komawa misau Kaisar ya iso yana fadin

“Yan matan amarya sun shirya ne ga motar da zai mayar dasu misau in kuma suka bari ta wuce to Sai gobe kuma .

“Mu kam muna nan sai mun siyar da bakin Amarya mun kulle kudin mu tukuna cewar hadiza babbar kawa.

“Ke kam wannan baki da kirki duk da angon bai iso ba smma kike maganar siyar da baki? to ungo don Allah ku fito a mayar da ku .

Ya aje musu kudin Yana fadin ga mota can tana slow wacce tabari aka barta sai dai cikin kudin bakin kawar ku da kuka siyar zakuje tasha ku dauki mota don nan gidan dai babu wacce zamuyiwa alfarmar kwana zuwa gobe don daga Ango sai smarya kawai zasu kwan a gidan su gara ma kuyi harama in kuwa ba haka ba sai dai mu kai mutum gidan bak’i ya kwan.

“Ai fa da gaske kake to tunda kuma ka biya kudin bakin Amarya ai a kasa ma zamu iya komawa misau alh Kaisar Ina Yan biyun ka Ya’yan wmarya? ni kam Ina son yaran nan musamman ma naga kayan ku iri daya.

ta fada tana daukar jakar ta suka fice Kaisar yana fadin

“Suna can suna hutawa sun gaji kun gajiyar da su .

Aka kwashe kawayen fati sukayi sallama tana kewar su har da hawaye tana bayar da sak’o ga innar ta da Baffan ta har da Yaya alabo.

Kaisar da ya dauko alabo tare da abokan shi don zuwa rakiya dakin smarya yana fadin

“Aiki kuma ya rage naka Ango sai ka mu dai munyi mai wuyar saura kuma ya rage naka .

Sukayi mishi caaaaa har suka iso gidan nashi Kaisar yana fadin

“To Amarya ga Ango na kawo ni kam aiki na ya kare sai a sallame ni na tafi nawa gidan .

Fati tayi maza taja mayafin ta ta lullube kanta ruf yayin da ta soma jin maganganun su suna tashi gaban ta ya shiga sarawa yanzu ne zata hade da Angon? wace irin karba zaiyi mata?.waye ma shi Angon da kuma kamar da zata ganshi?

Kaisar ne yace ta fito inda kuma daya daga cikin su ya amsa da cewa amarya ai ango ne ke take mata baya dole Ango ya shiga ya fito da ita

Tana zaune ta soma jin takun tafiya abinda ya kuma Kara fadar da gaban ta don ta tabbatar da angon ne yake nufo ta.

Takon tafiyar da taji yana nufo dakin nata yasa zuciyar ta bugawa tare da karar takun wanda take ji na mai amsa sunan Angon nata wanda takun sa kadai ya tabbatar mata da cikakken namiji ne wanda takun sa ke  amsa amon sautin tafiya.

Sassanyan kamshin turaren shi ne ya sauka akan hancin ta wanda yayi matukar tafiyar mata da hankali ta kuma jin dukan kirjin ta yana kara bugaww saboda jin tsayuwar sa akan ta abinda ta tabbatar da kare mata kallo yake saman ta zuwa k’asan ta wata kil ya hango abinda bai masa ba a tare da ita wata kil kuma ya nuna mata alfarma yayi mata ya karbe ta a hannun Daddy tunda ba shi yace yana son ta ba.

Bata dire wannan zancen da ta dauko ba taji zaman mutum a dab dab da ita har jikin su yana gugar juna kafin taji wani tattausan hannu ya sarke yan yatsun hannun ta masu dauke da jan lallen rani wanda ya kwanta a saman farar fatar ta ya kai hannun nata a bakin shi yana kissing yana fadin.

I’m so sorry my dear.

Ya fadi maganar da wata husky voice yana bata hakuri wanda bata san ko hakurin meye ba . amma dai duk da a rikice take sai da ta gane hakurin rashin bayyanar sa gareta ne tun farko.

Hucin iskar bakin sa da ya sauka a fatar hannun ta shi yaja mata jin wani abu mai kama da shock .

Bata karasa tantance komai ba taji ya rutsa ta yana zagaye ta da hannayen sa zuwa jikin shi yana  kara maimaita kalmar ban hakurin da yake ta bata.

“Wai ko bata ciki ne ko kuwa Ango ya samu Amaryar sa ne ya bar mu nan zube ? to ko mu wuce sai zuwa safe ma gaisa?

cewar bakari abokin Alabo.

“Kai kuma wa ya fada maka ana magana? Ai sai shiru kurum ka sani ko ana wani dan k’us k’us din ne? bar su su gama su fito ai tafiya zamuyi.

Ya Kara rungumar dk yayiwa fati yana rada mata a kunne cewa suje su sallami bak’in can ita suke jira.

ya mike yana daga ta cik yana kara rad’a mata ko ya dauke ta?

tayi saurin girgiza kanta don tana cike da tunanin muryar tashi da muryar wa ma tayi mata Kama ? amma bata iya ganewa ba yana rike da hannun ta ya kuma ruko ta ya Kara a jikin shi har falon da yasha manyan kujeru har saiti biyu na jemammiyar fata Yan Italy

Kaisar ne ya bude da ADDU A bayan yace su Karanto salatin ANNABI MUHD sallalahu alaihi wassalam suka cika da ADDU A suka shafa inda bakari ya dora da nasiha da fatan alheri da rike ibadar aure wacce Allah ne yace ayi ba iyaye ba don haka hakuri da juriya sune cikin ta har Allah ya iyawa ma aurata

Sun yiwa fati kyautar kudade kafin sukayi musu sallama suka wuce

Ya raka su har motocin su yana musu fatan alheri da godiya mai yawa sukayi sallama suka wuce shima ya rufe gidan yana jin bugun zuciyar shi akan yadda zai fuskanci amarya da dogon sharhin da zai biyo baya idan ta fahimci karatun.

Ya same ta a inda ya barta shine ya zauna dab da ita yana fadin

“I’m sorry to say my dear.

Ya fada yana janye mata lullubin da yake kanta yayin da tayi k’asa da kanta bata nemi su hada Ido ba saboda Al kunya irin Tata.

Ya tsura mata ido yana jin yadda son ta yake sukuwa a zuciyar shi Wanda Yake jin tamkar ya hadiye ta ya huta.

Ya rike hannun ta yana kallon jan  lallen rani wanda zanen shi ya kawatu a idon shi yayin da wata majaujawa da taja shi ya kai bakin shi da nufin ya sumbace ta sai kawai ta ta dago da wani irin tsoro tana kai ganin ta a fuskar shi sai ta soma hango fuskar yayan ta Alabo a kan fuskar Angon.

Ta mike da sauri tana kara kallon fuskar wanda yake gaban ta cike da rudani da tashin hankali.

“Zo ki zauna mana dear? what is wrong?

muryar shi ta fito mata radau  a yadda ta san shi yaya Alabo.

“Ya.ya.ala.booo.

taja sunan cike da tashin hankali tana nuna shi da yatsa.

“Cool down my dear zo kiji na fada miki komai naga kin tayar da hankalin ki don Allah nutsu kiji abunda baki sani ba.

“Ah A a yaya Alabo me nake don Allah ? mafarki nake ko kuwa hauka? waye mijin da ake min magana? kai? don Allah ce min imagin.

ta fada cike da tashin hankali tana son ji daga gareshi.

“Yi hakuri mu zauna my dear.

“Ba zan iya zama ba sai ka fada min waye mijin da su Baffa suka bani ? Ina ake haka yaya ya auri kanwar sa ? nice nayi hauka ko kuwa Daddy ne yayi batan kai? shima Baffa sai ya kasa tayar da shi? kai ba gaske bane wallahi sai dai mafarki.

“Zo na fada miki komai please Amma cool down please.

“Kaine miji na yaya Alabo? don Allah ka fada min eh ko A a kaina ya kulle da yawa amsa kawai nake so ka bani kaine mijin da daddy ya aura min ? .

Ya kada mata kanshi Alamar haka ne.

ta toshe kunnuwan ta tana kada kai Alamar bata so hakan ba.

Sai kuma ta fashe da kuka tana kwasawa da gudu zuwa daki ta mayar da kofar ta rufe tana kuka da wani irin tashin hankali.

Ya mike da sauri yabi bayan ta yana tura kofar amma yaji ta a rufe.

ya soma bugawa yana fadin

“Fati don Allah bude na fada miki komai don Allah ki daina kukan nan wanna fa ba wata matsala bace .

Bata iya sauraren shi ba tana kuka tana ganin meye za a hada ta aure da dan uwan ta?  .

Duk dukan kofar da yake bata iya budewa ba yayin da kukan ta ya dame shi jin shi yake har tsakiyar zuciyar shi.

Ya koma dakin da yake nashi ya dauki wayar shi yana kiran wayar Baffan su halilu amma wayar a kashe yayin da fati kuma da taji ya daina dukan kofar ta bude da nufin ficewa daga gidan ai kuwa taga baya kofsr sai kawai ta wuce zuwa kofar da ya rufe ta bude ta fice abunta.

Ya jima yana kiran wayar Baffa amma bai same ta ba sai kuma yaga ba zai iya kiran daddy ba ya fads mishi komai ba sai ya ajiye wayar ya shiga toilet ya sakarwa kanshi shawa yana jin sanyin Ruwan Yana sauka kanshi amma cike yake da tashin hankali musamman yadda daren farkon shi ya kasance da hanyar da zai bi don shawo kan matar sa Rabin ruhin sa wacce ya rayu da kauna da soyayyar ta sai dai wani shamaki da yake neman tauye farin cikin da ya ke ta fatan tabbatar sa.

Ya gama wankan ya fito wanda yaso ace fati tana kusa dashi a wannan lokacin.

Ya fito ya dubi ledodin kayan siyen bakin da su Kaisar suka tara musu na zabbi da kayan fruit har da sassanyar madara amma ga alama kayan zasu kwana da tsami Amma sai ya zauna Yana jin ba zai bari su kwana da tsmi ba shi sai ya ci tunda Amarya ma ta garkame daki .

Yana cin kayan arzikin su yana kallon kofar dakin fati Wanda yake a rufe yana jin ina ma zata yarda ta fito taci abin nan kar ta kwana da yunwa? amma yasan ba zata fito ba dole yaci ba don suna mishi dadi ba sai don kar su zamo asara

Ya koma dakin shi ya daura alwala yana tayar da salla wacce yake ta neman dauki da neman albarkar aure ya kuma sa komai ya zama sauki matar shi ta fahimci komai da akayi ba ayi shi cikin jahilci ba

Fati kam da ta fice daga gidan kai tsaye ta nufi gidan daddy duk da tazarar dake tsakanin su haka ta shari kafa ta soma debar fegi har ta iso duk da daren da ya soma

ta wuto su maccid’o da suke Shirin datse gidan ta wuce zuwa dakin ta don tuni haj Aliya ta wuce dakin daddy ita kuma ta fada kan gadon ta tana aikin kuka kuma babu wanda ya ganta don haka tasha kukan ta kafin ta Bawa kanta magana ta tashi tana daura alwala ta haye sallaya tana fadawa Ubangiji kukan ta da damuwar ta.

Babu wanda ya san gidan ta kwana sai da mama ta sauko daga bene sukayi kicibus da fati ta soma rafka salati tana fadin.

“Ke me nake gani haka ? Kece ko kuwa idona ne?

fati ta soma kuka tana rungume mama tana fadin

“Mama yaya Alabo ne aka daura min aure dashi? .

“Shine mana fati kar dai kice min zaton ki ne kika tabbatar har kika baro gidan mijin ki? Kar ma kice min nan kika kwana? haba fati? kin san iyayen ki ba zasu yi abinda ba daidai ne ba  ko sun Sha giya ai ba zasu baki mijij da bai halatta da auren ki ba uba na ai mijin ki ne na halal don Allah tashi ki koma gidan mijin ki tun kafin daddy ya san kin zo nan uba na miji ne irin kowane miji da kika gani  ba za ayi abu a cikin jahilci ba fati kinji don Allah kiyiwa mijin ki biyayya zanzo har gida na fada miki waye mijin ki a gareki ko shi Kika tambaya ma zai fada miki ai kin san yaya halilu da daddy ba zasuyi abunda bai zama shari a ba share hawayen ki kinji? mama ta kare da rarrashin Fati.

Daddy da ya soma saukowa yana jin su ya soma fadin

“Fati nake gani ? ni na san za ayi haka amma kamar yadda mamar ku ta fada miki uba na miji ne kamar kowane miji koma fiye da sauran wasu mazajen don uba na yafi na kowa Fati .

Suka daga kai suna kallon daddy da yake saukowa.

Alabo da sai dab asuba ya gama sallolin sa har aka soma kiran assalatu kafin ya mike ya bada farali ya juma a zaune yana jan carbi kafin ya mike ya nufi dakin fati don ya tayar da ita sallar asubahi

Ya soma dukan kofar amma baiji motsin mutum ba . ya kara bugawa inda yaga kofar ta yi baya alamar a bude take sai ya tura ya shiga Yana baza Ido amma bai hange ta ba shine har toilet amma bata ciki .

Sai hankalin shi ya soma tashi ya shiga zagaye gidan da sunan neman ta amma ko kyallin ta babu  sai ya fita zuwa gidan Daddy don can yafi zaton ta .

Ya tashi mota daga shi sai jallabiya ya nufi gidan Daddy

Fati da take dauke kwallar ta tana kallon mama da daddy da suke nufin auren ta da Yaya Alabo halastacce ne to ita din wacece? ba innar ta ce ta haife ta ba ? Ko kuwa zuwa akayi da ita ko kuwa shi yaya Alabo ne ba dan su ba?.

Ta sunkuy da kanta Daddy yana dafa kanta yana fadin

“Fati kinyi bajinta sosai amma na san dole zuciyar ki zata raya miki wani abu shiyasa ma na boye miki amma ki sani ke da alabo kuna da wata tazara wacce ba zata haram ta muku auren juna ba don haka ki rike wannan a ranki alabo mijin ki ne wanda zakiyiwa biyayya kuma Kar gane shi ne mijin ki da kikayi yasa ki rage komai na game da biyayyar sa kinji?.

Ta share hawayen ta tana fadin

“To daddy in sha Allah nayi maka alkawarin hakan.

Alabo ya shigo gidan hankalin sa a tashe amma ganin fati a gidan yasa hankalin sa ya kwanta ya duka a gabansu mama da daddy yana gaishe su Yana kallon fati da kanta yake kas.

<< Azurfa Da Zinari 60Azurfa Da Zinari 62 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×