"Ta tayar maka da hankali uba na wallahi ban san tazo gidan nan ba sai yanzu na ganta Ina ake tayarwa ango hankali da asubar farko? cewar daddy Wanda ya fada yana zolayar Alabo.
Yayi murmushi yana fadin
"Wallahi daddy ban san bata gidan ba sai yanzu da naje tashin ta salla don tun jiya da muka hadu ta ganni shine ta rufe daki taki ta bude duk cewa da nake ta tsaya taji abinda zan fada mata bata yarda ta tsaya ba.
"Ban san tazo ba uba na ka yafe ni da na san tazo komai dare sai na. . .