“Ga uwa ta ga uba na oyoyo da iyaye na” cewar Daddy.
Yayin da Alabo kuma ya zube a gaban mama yana gaishe ta ta rike hannuwan shi tana fadin
"Uba na kuna lafiya ko? Yaya kuke? ya amsa mata da komai lafiya ta ce to Alhamdulillahi haka nake son ji uba na Allah yayi muku albarka yasa kuyi zumuncin da ya zarce na iyayen ku.
Fati ta rungume Daddy tana fadin
"Daddy nayi kewar ku Kai da mama gobe ma misau zanje na gano Baffa da Inna ta .
"Kai masha Allah Allah ya kaimu da rai da lafiya haka. . .