Skip to content
Part 66 of 66 in the Series Azurfa Da Zinari by Hadiza Gidan Iko

“Kaisar yarinyar nan kuwa tana samun nono isasshe? Tambayar da haj Aliya ta jefa wa Kaisar wanda bai boye mata ba ya fada mata gaskiya cewa ita Siyama ma bata tab’a dandana no-non uwar ta ba saboda kuwa ta fada bata tsani yan biyu ba irin tsanar da tayiwa Siyama saboda tayo kamannin uban ta.

Haj Aliya ta wuce tana rike da siyama a hannun ta tana fadin

“Nice banyi maka adalci ba Kaisar da na barka da hidimar yaran nan nice nafi kamatar na rike maka su amma banyi hakan ba ka gafarce ni nayi zaton al amarin yarinyar nan mai sauki ne ashe ya wuce tunanin mu.

Daddy ya dubi Nadiya ya kuma dubi Kaisar amma ya kasa cewa komai ya wuce yana dauke kwallar idon sa .

Nadiya ta mike ta na duban Kaisar.

“Duk abinda ka gani ka tuhumi kanka tunda nace ka sauwake min baka ji ba to ai kuwa ba zaka ki gani ba wallahi .

Ta wuce ta shiga dakin ta ta sauya kaya ta kuma wanke jinin da mama ta fashe mata kai ta fice daga gidan kai tsaye kuma ta zarce wirin show wanda suka soma tsara yadda tafiyar zata kasance amma show ya tabbatar mata da sai ta san yadda tayi ta kashe auren ta don ba zai yarda a kuma Kama shi da laifin ya shiga hakkin aure ba.

“Ya fa kasa sakin nan show babu abunba banyi mishi ba shiyasa ma kawai na fito don ba zan kuma komawa gidan can ba kar Allah ya bashi ikon saki yayi ta rike igiyar auren har a tashi al kiyama.

“A a dear ba zan yarda na sake fadawa hannun hukuma skan wani abu da ya shafi auren ki ba na yarda zan tsaya miki a komai amma banda lamarin aure tunda har takardar record ke akwai a kotu in na kuma me kike zato? kawai ki sami wata hikima kiyi ko ki ja mishi wani katon sharri ko ki kai karar sa ki nemi sakin ki zaifi miki sauki.

Nadiya tayi murmushi tana fadin

“Ka kawo data show billahilazi yanzu zan kullawa gayen nan janhurun masifa wanda zai gammace uwar sa bata kawo shi duniya ba.

ta mike tana fadin

“Yanzu nan da sati biyu ne tafiyar America? to ni fa bani da wasu kudade masu nauyi show ga gyaran da zanyi shima mai shan mai zanyi.

“Kar ki damu wannan duk can zasuyi miki komai kyauta ke dai ki gama da gayen can kawai don ko ina zamuje ba za a ce matar aure na kawo ba tunda kina da yancin ki a hannun ki .

Nadiya ta fice daga studion show kai tsaye ta shirya kullawa Kaisar sharri wanda zai cinye shi har karshen rayuwar sa don ita kanta sai da taji tsoron abinda take nufin yi amma da yake shaid’an yayi mata futsari a zuciya bata ja ba ta fidda wayar ta tana Kiran nomber sirrin da ake kira don bada bayanan sirri ta kuma sanar da inda za a zo da wanda za a nema da kuma abinda ta fada wato bandit.

ta gama wayar tana kyalkyale wa da dariyar mugunta don ta gama gane ba karamin gurmi ta hada ba.

tana cikin dariya ne wayar ta ta sake daukar tsuwwa inda ta ga nomber sirrin da ta kira ce suka kira ta suna son ganin ta a office din su. bata ji ko darr ba ta fuce zuwa office din ta Kuma bada bayanin Kaisar da irin sharrin da ta kulla mishi .

“to shi din waye naki da har kika gane yana cikin yan ta addar bandit kuma tun yaushe kika lura da halin da yake ciki? daya daga cikin jami an ya tambaye ta.

“Na gane hakan ne ta yawan wayar da yake wacce yake kebe kanshi yayi ta baya son a ji abinda ya ke fada da kuma irin kudaden da yake facaka da su sai kuma fitar dare da rufe fuska amma sauran bayanin in kuka rutsa shi tunda aikin ku ne zaku san yadda zakuyi mishi guga .

“To yanzu idan muna son mu kama shi ta yaya zaki iya taimaka mana?.

A nan Nadiya ta bayar da  details din Kaisar nombar wayar shi da kamannin sa da inda za a same shi.

Suka sallame ta suna cewa idan akwai yuwuwar su neme ta zasu yi hakan.

A ranar kuwa aka kira Kaisar wanda aka soma tambayar sa shine kaiser? ya amsa da eh aka ce sako ne za aka bayar a  bashi ina za a same shi? ya fadi inda yake wato chemist din nurul huda don yazo Siyawa siyama madara ai kuwa bai sha mamakin sak’on da ake magana ba sai da yaga motar DSS ta faka a gaban shi sun kuma zarge shi sunyi gaba da shi abinda kuma ya tayar da hankalin mai chemist din wato alh nura fari wanda yake da kyakkyawar alaka da Kaisar da alh iro don haka ya kira wayar Alh iro ya sanar dashi abinda ke faruwa ai kuwa hankali a tashe daddy ya bazamo wurin Alh nura fari suka bi bayan su Kaisar amma a ranar ance ba za a saurari komai ba sai an gama bincike wanda sai ya kai jibi.

Haka kullum daddy zai zo ya kawowa Kaisar abinci amma har yanzu idanun su basu hadu ba kuma ba a bada damar ganin shi ba

Kwanaki hudu rus kafin magana ta fito wacce aka sanarwa daddy cewa ana zargin Kaisar ne da zama dan ta adda wanda yake fakewa cikin al umma.

Daddy yaji maganar wani iri har yana kwarewa yana dafe kirji yana ambatar kalamar Inna lillahi wa inna ilaihir Raju un.

“Bandit? waye mai wannan kokarin? wallahi tallahi yaron nan bashi da alaka da abinda ake tuhumar sa amma lokaci zai yi alkalanci a soma binkice .

Daddy ya dawo gida Yana kuka yana fadawa haj Aliya wacce ta ke duban Daddy tana sauraron abinda Yake fada mata.

“Uhum sharri kayan kwalba in sha Allah zai koma inda aka aiko shi bands zato yana zunubi da nace yarinyar nan tayi kokari Tana dab da cin miki.

“Wace ? Nadiya?

daddy ya tambaya a rude inda zuciyar shi take sanar da shi ko shakka babu yarinyar nan zata iya aikata mugun nufi  wanda yafi wannan .

A rikice daddy ya soma binciken yadda al amarin Kaisar ya faro sai ga shi ya samo komai ta yadda aka kira jami an  bunciken sirri da aikin da aka sanar har da lambar Kaisar din Kai daga karshe ma sai ga lambar Nadiya ta bayyana a matsayin wacce itace ta kawo zancen da kuma irin yadda ta kawo maganar da abubuwan da gani a tare da shi na waya da kuma fitar dare da boye kamanni .

Daddy kam idan akwai ranar da yayi nadamar sanin Nadiya da kusantar ta da yayi.

Daddy ya dawo gida ya na samarwa haj Aliya dukkan abinda ya faru tayi murmushi na takaici wanda ya taho da hawaye a idon ta tana fadin

“Allah ya sani munyi komai domin zatin Ubangiji amma dubi sakamakon daddy? sharri? sharrin ma irin wannan wanda zai Kai mutum a mahallaka? amma babu komai bata san rayuwa bane dukkan abinda kake son ganin ya samu dan uwan ka to akan ka Allah zai fara sauke shi don ka san shi Allah din ba azzalumi bane in sha Allah sai gaskiya ta danne karya ! Sai adalci ya danne zalunci! sai musulunci ya danne kafurci  wanda bai  San duniya bane yake haye mata irin hawan da yarinyar can tayi mata ni kam daddy a yau da a gidan marayu muka  dauko yarinyar can da sai dai nace ka yafe min amma wallahi sai mun mayar da ita kuma nayi nadama ba yar kad’an ba  wallahi .

“Kiyi hakuri Aliya duk yadda kike ji a kirjin ki a yau nafi ki ji amma na san kwarya ta gari tana Ragaya haka Kuma AZURFA DA ZINARE darajar su da banbanci wata Kil watan kunyatar yarinyar nan ne ya tsaya.

Tuni aka soma bincike wanda ta hakan ne za a gano waye Kaisar ta hanyar mutanen da yake mu amalanta da kuma muhallin sa wanda dole zai nuna wani Abu da ya shafe shi.

Da gidan shi aka fara wanda a ranar da aka fara bunciken a ranar ne kuma Nadiya da show suka dage daga Nigeria zuwa America don saura kwani biyar a shiga show up Venus don haka Rubutacciyar takarda Nadiya ta bari a gidan ta fice abunta don babu Wanda ya San bata gidan sai a ranar da aka fara bunciken Kaisar Wanda aka taho tare da shi zuwa gidan aka soma buncike yayin da daddy da Kaisar suke a tare ana ta bankade komai na gidan da son a gano wani sbu da zai nuna shi a matsayin dan ta adda. ana  cikin haka ne aka zo kan takardar Nadiya wacce daddy ne ya dauke ta ya duba ya kuma bawa Kaisar shima ya duba ya kuma bawa mama ita.

Allah gwanin adalci bai so ya wulakanta Kaisar ba ya kuma so wanke shi akan bak’in fentin da aka so shafa mishi don haka ko allura ba a samu a gidan ba bare wata wuka ko bindiga dole aka koma dashi aka shiga neman wanda yake tare da su wato abokan sa su king har da su Alabo wanda suma bincike ya koma kansu har da muhallan su  aka kuma tabbatar da babu komai suma irin na laifin da aka so kama su da su ba don haka aka koma neman Yaya za ayi? dama in da an samu kayan laifin ne aka kuma tabbatar da yana da hannu a cikin abunda ake tuhumar sa shine za a mika shi kotu to babu komai amma duk da haka ba a saki Kaisar ba ana ta bin hanyoyin da za a bi a binkito wani abu akan Kaisar inda kuma Daddy da mama sukayi ta ADDU AR Allah ya shiga cikin lamarin yaron ya kawo mishi mafita.

Keena kam sai aunawa ba I’mani ashar take musamman idan ta tuna da kudin shaid’an da ta karba wanda yasa ta dole ta kashe waya ta kuma yi hijira daga hostel ta koma wani gida don boye kanta. sai dai me ? A wannan dare da keena ta gaggallawa ba I’mani mari bata kwana lafiya ba domin kuwa dare nayi ta soma jin koke koke da iface iface a saman rufin dakin gidan da take wanda ya tayar da ita daga bacci.

Al amarin da bai faku ko ya goge a zuciyar ta ba kai tsaye ta gane surkullen ba imani ne dama ko da suka taho luba na ta fada nata cewa kinyi ganganci keena da kika mari mutumin can bai da I’mani yasin kuma na san ba kyale ki zaiyi ba.

Sai gashi taji ana mata gad’a a aman rufin dakin abinda ya tsorata ta matuka gaya.

Luba ma da take kwance a dakin don bata tafi hostel ba a cewar ta ta gaji da uban gudun da suka debo a dajin ba I’mani shiyasa ta kwanta a nan a she da rabon itama ta karda.

Keena ta kai hannu tana daure zanin ta da tayi daurin kirji wanda tsoro ya sa ya kusa ficewa daga daurin kirjin ta mike a tsorace yayin da luba ma ta farka a firgice tana kallon keena da itama tashin hankalin ta ya bayyana a fuskar ta .

“Daga Ina nake jin wannan sukuwar ? halan shegun magunan nan ne suke baje kolin iskancin su a dare su hana mutane bacci?.

cewar luba wacce take duban keena.

“Ke luba wannan iskancin ya wuce mage yasin wnya kuwa ba shegen tsohon najadun can bane da Yake fadar zan gani ba?.

Bata dire zancen ba suka ga ana jijjige rufin dakin kafin suka ga hayaki yana shigowa dakin kuma suka rasa ta Ina hayakin ya shigo kafin suka ji karar ihun da aka kwartsa wacce ta tabbatar musu da hakikatan ba I’mani nee.

Wutar da ta soma sauka ita ce ta saka keena da luba kwantsama ihu suna neman mafaka amma karfin hali yasa keena ta soma kwasar kayan ta da suke dakin ta na fitowa da su gudun lashewar wuta

Luba ma ta taya ta sukayi ta rido kayan suna neman matsera gudun wuta ta lasa amma Ina sun dai rage amma wuta kam ta lashe kayan Keena wacce ta ciji yatsa tana fadin.

“Luba kinga abinda tsinannen tsohon nan yayi min? ya dake ni kuma ya hana ni kuka? Ya cinye min kudi babu biyan bukata kuma don uwar sa ya bini da bita da kulli? na rantse miki da Allah ba zan kyale shi ba sai na rama wulakancin nan da yayi min haka kawai a mare ni kuma a tsinka min jaka?.

“Keena ki rabu da mutumin nan dama na fada miki ba lallai ya kyale ki ba kuma a yanzu ga abinda ya faru to in ba neman janhurun masifa ba mai zai mayar da ke wurin shi? .

“Ai luba sai na nuna mishi nima na iya tsiya da jawo balaki mai kaca ya cinye min kudi kuma yace ba zanyi magana ba har ya jawo min asara da yo min cinnen wuta? To hatta wannan kayan da ya kona min sai yayi nadamar abinda yayi wallahi.

“A a Keena ki kyale mutumin nan yaji da Rashin I’manin sa amma in kika ce zaki koma kiyi mishi wani abu to tamkar kin kuma kiran wani balakin ne.

“Ai sai dai ko na kira shi luba amma wallahi sai na komawa zindikin mushirikin can gobe goben nan wallahi don ya gane ba banza wofi nake ba wallahi luba ko ni ko shi sai daya yayi ta Rayuwar sa.

Ta wuce tana duba yadda wuta ta lashe mata katifa da wasu sauran kayan ta banda ta kwaci wasu kayan ta daga wutar da har ita bata tsira da komai ba.

Haka ta koma dayan dakin ta kwanta cike da bak’in ciki shima sai me? kamar ana jira suka kuma jin ihun nan da iface iface kan kace me? wuta ta sake bayyana inda sukayi ta ambama mata ruwa har sukayi nasarar kashe ta amma nan ma ta lashe kayan Keena da yawa.

<< Azurfa Da Zinari 65

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×