Skip to content
Part 7 of 80 in the Series Azurfa Da Zinari by Hadiza Gidan Iko

“Tero? Shugaban jami’an DSS din ya fada da sigar tambaya yana kallon Tero wanda yake cije lebe da hasaso irin rashin kirkin da zai girbawa yarinyar nan da ta Sa aka kawo shi wurin nan . don sai yaji a yau ba zai iya bacci ba matukar bai lalubo muguntar da zai shiryaww kahira ba.

“Kai don Uban ka sunan ka nake tambaya kana fada min sunan yan iska meye Tero in ba tattaccen dan iska ba?

Shugaban jami’an nan ya fada a fusace yana zarowa Tero idanun shi masu kama da anyi b’arin kwai a titi.

Tero ya dube shi jin yana auna mishi zagi ya kuma kufula zuciya tazo mishi iya wuya ya dubu shugaban Yana harara shima a fusace ya ce,

“Ba ni da wani suna bayan wannan haka na tashi naji ana kira na indai ba yanzu ake son a sauya min wani ba.

“Me ye ya hada ka da yar GIDAN KUDI? “Wacece? ni ban san ta ba in kuma wacce tace ku kama ni ce uban gida na ta zaga ni kuma naso naci uwar uwar ta ya hana Ni.

“Ka kuwa san wacece ka zaga har kake shirin kai hannun ajikin ta da sunan duka?

“Ina zan sani tunda banje neman taimako wurin ta ba?

“Ka iya kalaman ka nan ba wurin da ake kawo mana wasa bane zakayi nadamar maganganun ka.

“A yanke min hukuncin laifin da nayi mana za a zaunar dani ana zagi na? Ni dai ai na san banyi komai ba ni an san ko Ni waye ? Idan don na zagi yarinyar can ne to ai gutsun uwar ta ma zan yage wallahi ko za a bari na ci uwar ta ne in yaso sai a hade laifin nawa ayi min hukuncin gaba daya? don wallahi sai naci gindin babar yarinyar nan don uban uwar ta yar ta shegiya kawai.

A fusace shugaban jami an ya kifawa Tero mari yana fadin, “Don uban ka ka san wacece kake mata wannan zagin? to uban ta yana iya siye uwar ka da uban ka har da zunuban su kuma sai ka san ka zage su.

“Uban uwar su ita da uban nata kaima uban uwar ka dan ta shegiya kuma na rantse maka da Allah idan ka kuma zagi na bare ka kai hannu a jiki na da sunan duka nayi maka alkawarin ba zaka sake awa uku a kan matsayin da kake a kan shi ba wallahi sai an watso ka idan kuma kana musu sake zagi na don Uban uwar ka.

Mamaki ya kashe shugaban jami an daga zaune ganin irin zagin tsamar naman da Tero yayi mishi ya tabbatar da idan bai taki wani abu ba bai Isa yayi shi ba. sai ya shiga karewa kayan jikin Teron kallo tun daga kan rigar jins din shi da turaren da yake tashi a jikin shi har zuwa agogon dake daure a hannun shi da facing cap din da takalmin timberland dake kafar sa amma kuma sai wata zuciyar ta sanar dashi iskanci ne irin na matasa marasa tarbiya .

Tero ya kafa mishi nashi idanun yana auna mishi harara tamkar zai kai hannu ya make shi.

Shugaban yaja  wayar shi dake gefen computer dake kan tebur din gaban shi Yana laluben wata lamba ya kuma danna Mata kira. Muryar Nadiya ta bayyana tar a wayar tana fadin.

“Hello? Shugaban ya amsa Yana fadin, “Ranki ya dade ya kike so ayiwa wannan yaron da aka kawo ?

“Adamu kar ka bari dan iskan nan ya kai labari bana so ya fito daga hannun ku Ina so daga nan sunan shi ma ya bace a duniya kamar yadda nake son a batar dashi sai dai uwar sa ta haifi wani amma bana son yana yawo a duniya zan turo maka kudi ko nawa kake bukata matukar zaka batar min da dan iska.

“An gama ranki ya dade ya fada yana ajiye wayar. Ya mike yana kiran garzali. Garzalin ya taho da sauri yana fadin,

“Yes Sir.

“Garzali ku dauki wannan yaron ku kai shi gidan dutsi a saka shi a daki mai lamba ta dari da ashirin .

Tero da ya tabbatar da idan aka kaishi gidan dutsin nan hakikatan ya gama amsa sunan mai rai za a kashe shi ne kamar yadda tsinanniyar yarinyar nan ta nema don haka sai ya daka tsalle yana fadin

“Na rantse da Allah sai nayi muku sanadin barin wannan kakin tunda haka kuke aikin ku kudi suke siye gaskiya bayan karya.

Ya zaro wayar shi da nufin yayi kira garzali ya fige wayar inda nuhu ya shigo ya Tara’s da hargagin Tero wanda suka danne aka bugawa Tero handcuffs.

motar Boss ta iso office din na DSS ta faka suka fito shi da tsagera inda suka ga kattin sun rungumo Tero wanda yake hankoron kwacewa suna danne shi suna shirin dannawa mota.

da sauri Boss ya karasa wurin motar yana fadin

“Ku sake shi !

duka jiyo su duka har da Tero da bai zaci ganin Boss ba sai da yaji amon sautin sa.

su garzali da nuhu sukayi turus don sun san ko waye Hameed mukhtar .

Dole kuwa suka saki Tero wanda boss ya mika misu hannu yana fadin

“Ina key din handcuffs din nan?

da sauri kuwa nuhu ya ciro daga aljihu ya mikawa boss ya karba yana bude handcuffs din ya mika musu key din.

“Muje wurin oga ranka ya dade don ya san kai kaxo don yace mu kai shi gidan dutse cewar garzali

suka nufi office din shugaban

Nadiya da ta mike da sauri Jin adamu ya kira ta akan dan iskan nan Wanda yayi mata zagin rashin kirki

Ta dauko jakarta mai cike da kudade dama bata jima da yin wanka ba ta saka kayan ta ta fice ko fati bata san fitar ta ba ta nufi office din DSS

yadda ta shiga ma aikatar tana tayar da Kura yasa aka soma darewa ana bata hanya har ta faka motar tana dauko jakarta tafito da katon gilas din ta  wanda ya mamaye fiye da rabin fuskar ta ta manna a fuska tana shirin fita wayar ta tayi tsuwwa ta jawo ta sai taga show ne yake kiran ta akan wata vedio zasu dauka a wakar shi ta hipop kuma yace tare yake son suyi vedion mai dauke da wakoki sha biyu inda kuma ta yarda ta Amince don haka sai ta dauki wayar suna magana da show.

Boss ya shiga office din shugaban DSS wanda ya tarbe shi da farin ciki har yana bashi hannu suka gaisa yana duban Tero yana fadin

“Ko ka san wannan ne Hameed?

“Dan uwa na ne Mai gida .

“Amma bai fada min ba ban san shi ba wallahi ai da ba ayi haka ba kai me yasa baka fada min haka ba?

shugaban ya fada yana duban Tero da yake cije lebe amma bai tanka shi ba sai ma tsaki da yaja.

“Ai babu matsala Hameed kuje kawai a gaishe min da distinguish .

Boss ya juya yana ajewa shugaban kudi suka fice su duka har da shugaban wanda yabi su wai zaiyi musu rakiya.

tana cikin motar tana waya da show motar su Boss ta wuce ta inda ta gane motar har ma ta hango Tero tare da boss din sun fice .

taa fito daga motar tana bin bayan motar da kallo inda ta ga har da rakiya adamu yayi musu?.

“Late me  five minutes show I will call you back.

ta fada tana katse wayar ta nufi office din shugaban da sauri.

“Waye naga ya fita kamar dan iskan yaron can?

ta fada a maimakon sallama inda shugaban ya dube ta yana fadin

“Ranki Ya dade yaron nan fa ba zai yuwu a yadda kike so ba don shima ZINARE ne irin ki don tuni na soma nadamar kama shi musamman da ya soma zagi na yana kuma maimaita zagin da yayi miki na gane ya san abinda ya taka wata kil ma gaba da gabanta wai aljani y taka wuta don regamar Nigeriar nan tana hannun iyayen su madafun ikon kaf yana wurin su ni ina tsoron ma kar yaron ya bata min suna.

“Waye uban sa a duk garin nan da Nigeria? Ta yaya na fada maka wulakancin da yayi min ka sallame shi ? ta mike a fussce ta figi jakarta ta fice tana jin tamkar ta fashe saboda bak’in ciki ko banza dai ya k’aska’ntar da darajar ta inda ake kunya ta ta.

<< Azurfa Da Zinari 6Azurfa Da Zinari 8 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×