“Mama? Daddy? Don girman Ubangiji kuyi min afuwa wallahi ban san abinda yake faruwa dani ba ban san komai ba .
Daddy da yake share zufa yace
“Babu komai uba na ai shi aure ruhi ne da shi ko kai ko uwa ta idan ajalin dayan ku ya sauko to dole mu karbi kaddarar hakan ai gama ta gama kuma uba na Allah ya tsayar a haka abinda kawai nake jiye maka shine sharrin mace da makircin su don na soma shinshinar al amarin yarinyar nan da kake so don sai daga baya na gane ta kusa ta girme ka kuma ma meye dalilin auren ta har buyu da yake rabuwa? Astagfurullah Allah zato zunubi ko da ya kasance gaskiya amma ina zaton wani abu a cikin duhu. .
“Daddy bani da lafiya wallahi wallahi ban san me yake faruwa dani ba don Allah kuyi min ADDU A.
Daddy ya dafa kanshi Yana mishi ADDU AR har ya kare kafin alabo yace
“Daddy Baffa da Inna sunyi fushi dani har Baffa yana shurin ya la ance ni don Allah daddy ka rufa min asiri ka basu hakuri wallahi ban san abinda yake faruwa dani ba.
“Dole ne su dauki kaddara uba na kaji kwantar da hankalin ka Allah yasa hakan shine alherin.
Ana cikin hakan sai ga Nadiya ta shigo falon yayin da Abdulhameed Yake biye a bayan ta sai wasu mata guda biyu Yan kungiyar human rights masu Sanye da kakin aikin su inda Daddy da mama da duk Wanda Yake cikin falon ya mayar da hankalin shi a kan su yayin da Nadiya ta zube a gaban Daddy da mama tana kuka tana Fadin.
Daddy gani gareka mama kuyiwa Allah ku yafe mini wallahi ban zaci rayuwa zata zo min a haka ba.
“Ni dai na yafe shikenan? To amma yadda na fada miki baki da muhalli a gida na kuma takardar ki tana nan Kaisar ya bayar ko na saka shi ya baki don na gama gane fitar ki cikin ahalin mu shine zaman mu lafiya don haka ga takardar ki itace kawai abinda yake tsakanin mu in kuma kina son kiji abinda na soma fesa miki to Bismilla wata kil ta cikin abunda zan fada miki ma ki banbance tsaba da tsakuwa da yadda kika faro don ki gane kinyiwa duniya daukar nauyi sai kika ji bata kai leda nauyi ba.
Daddy Alh iro ya dubi Abdulhameed wanda ya shaida dan gidan distinguish Mukhtar Biro ne sai matan nan biyu da suke tare ya kara fusata yana nuna Nadiya da take Kuka cike da nadamar zuwan wannan ranar wacce daddy Yake Shirin juya Mata baya.
“Meye naki na jawo min wannan yarok gida na? Su kuma wadan Nan mutanen a me kika zo min da su?
Matan nan an human rights ne sukayi maza suka ce
“Kayi hakuri Alh muna da Dalilin zuwa ne ka saurare mu ko na minti Sha biyar ne please.
“Idan dai tare kuke da ita bani da lokacin sauraren ku don yadda na Rabu da ita a farko shi yake nufin har yanzu ma mun rabu ba kuma zan sake sauraren ta ba Abu daya ne a tsakanin mu shine musulunci wmma bayan haka babu wani Abu don ko zumunci ba zanyi da yarinyar nan ba.
Abdulhameed ne ya fito da takardar da sukayi yarjejeniya da Nadiya Akan ya fidda ita daga prison ita Kuma zata bashi yan biyu Wanda tun a can America kungiyar human rights din ta shiga ciki ta Kuma zama witness shiyasa aka bugo stamp aka turowa Reshin su da Yake bauci shiyasa suka taho don tabbatar da kowa ya cika alkawarin sa.
Daddy kayi hakuri dalili ne ya kawo Ni gidan nan ga takardar da mukayi komai a Rubuce ga kuma shaida nan tun daga America shiyasa nazo da an bani abinda yake nawa ba za ku sake saka Ni a idon ku ba.
Ya fada Yana mikawa Daddy takardar wanda ya karba Yana dubawa.
Fati da Alabo kam bak’in cikin halin da suke ciki bai barsu ba sai ga Nadiya mai tafe da wani shirin film.
Kaisar ya shigo gidan ya kuma iso falon mama inda ya iske falon dam da mutane har da Nadiya wacce kallon ta ya haddasa mishi bacin rai don tuni yarinyar nan duk Yadda Yake son ta ta gama fice mishu a rai sai kuma ga Daddy yayi atakin din sa Akan cewa sai ya sake ta tunda ta tsallake k’asa zuwa America har ta shiga Venus suka kuma ganta cikin shiga ta rashin kirki don haka bai ja ba ya Rattaba mata saki daya Amma daddy yace sai ya cike biyun ya zama uku don sukara nissan tazara da haramta ga juna.
Ya yi sallama ya shiga ya zauna yana duban Fati da Alabo duk da yana cike da son ya tambayi Fati khalifa da Siyama amma ganin Nadiya wacce ke kuka kashirban yasa ya saurara .
Daddy ya Gama duba takardar wacce take tg yarjejeniya akan a fanshi Nadiya ita kuma ta fansar da Yan biyu ko kuma Abdulhameed ya rike ta har sai an biya kudin sa ko kuma an bashi Ya’yan sa . Takardar da akayi da hukumomin da suke manya a america Kuma suke da karfin kwatar yanci a ciki harda human rights wacce a yanzu ma tafe suke tare da su .
Daddy yayi murmushin takaici yana duban Abdulhameed yana fadin
“Wai abdulhameed anyi muku wahayi da ya’yan nNan ne da kuka makale uhin numfashin ku akan su? Tuni nake ta ta maimaita muku magana kun kasa ganewa sai kace ba da yaren hausa nake muku magana ba? har abada fa babu wanda ya Isa ya karba muku ya’yan Nan ku rika rike wannan ku da Yan biyu fa sai dai ku gansu ba dai suzo gunku ba. Kuma da take baka Ya’yan don ta fanshi kanta ashe yaran suna da rana a gare ta? To itama bata da wani hurumi akan su tunda ba zaci ta tab’a nufin su da wani alheri guda daya ba bayan na daukar cikin su da haihuwar su wannan ma don bata da yadda zatayi ne tunda bata so ba . To mu rufe wannan babin in har kunyi da ita fansar Ya’yan ta ko ita kanta sai nace maka kaje da ita ka rike wata kil ma kun samu don Ni dai ba zata kuma zama a muhalli na ba tunda ta zama yadda ta zama nima na zama don haka Ina maka albishir din yan biyu dai ga Mai su nan har a kiyama Babu mai karbar su daga gareshi
Ya nuna Kaisar yana fadin
“Amma ita kam kuje da ita idan da akwai amfanin da zatayi muku tayi ni da kaina ma zan iya kawo muku ita har gida don nan din daga taimako ne ba haular ta bane .
Abdulhameed da Bai zaci hakan ba ya zaci daddy zai tsorata da takardar Nan amma sai yaga ko a jikin shi da kuma abinda ya. Fada akan Nadiya wacce kukan nadama ya kasa tsayawa.
Yan kungiyar kare hakki suka soma rarrashin Daddy akan ya fahimci abdulhameed da Kuma takardar da suka zo da ita.
Ya daga musu hannu Yana fadin
“Ai na fahimta yanzu ba Yan biyu ko ita kanta ne fansar kudin da ta karba ba? To na yarda nayi giving up din ita su tafi da ita a madadin kudin su Yan buyun ne dai ba zasu samu ba ko da kuwa har da su a cikin abinda ta karba amma ita ni da kaina ma zan iya mika ta.
Abdulhameed ya mike Ranshi a bace don shifa Yan biyu yake so ko ta wane irin hali . don Haka ya dubi Daddy Yana fadin
“Ni fa kudin mutum biyu na biya ta Yaya kuma za a bani daya? .
“To ai ga shi a rubuce Yan biyu ko ita kanta Nadiya kaga babu dalilin da zan dauki Ya’yan da ba nata ba na Baku ai kun san kyauta da abin wani mugunta ce ba Kuma za ayi hakan ba ita dai ai a matsayin su biyun take don haka kar kaja mana zance da tsayi daya a cikin uku ka nema ka kuma samu.
“Gaskiya ba zan karbi wannan ba ni a Yara biyu na biya ta kudina ba a Karan kanta ba in ma na so magana ai har da ita kanta duka a ciki.
“To Abdulhameed zan so ka so maganar nan ai mun saba faduwa da tashi a gaban kotuna da ku sai mu maimaita meye bak’o? ni zan so ma ka tura min uban ka don shine daidai da ni.
Ai kuwa Abdulhameed ya daga waya ya kira distinguish Mukhtar biro ya soma fada mishi abinda ke faruwa na Hana shi yan biyu.
“Ya hana yaran ne shi iron ? To kar ka bari yarsa ta kubuce maka ka dawo da ita in yana son yarsa dole ya bani yaran Nan nasan ma in ya gane hakan da sauri zai nemo ka ya baka Ya’yan nan.
“Ba fa zai fahimta ba Daddy gara kawai kazo ayi mai yuwuwa don ya fada ba zai bayar da Ya’yan nan ba.
“Haka yace shi iron? To bari nazo don gyatumin sa ina ganin sai mun Bawa hamata iska ni da gayen ban ko zai kiyaye ni wallahi kuma ko baya kaunar Allah sai ya bada Ya’yan nan bari nazo naga karshen rashin kunyar sa bani minti talatin gani nan zuwa.
A can Misau kuwa khalifa ya tsale da kukar yayin da Siyama ma ta Karbe suka uda Inna Hajara wacce ta kwashe su tana rurruga amma suka ki shuru .
Baffa halilu kam da yake zaune a tsakar gida ya zuba uban tagumi har da Yar kwallar da take rego idon sa yana dauke ta da hab’ar rigar sa Yana tunanin butulcin Alabo da irin wannan gigitaccen sakin irin na haramiya da ya wanka har saki uku rus .
Ya jiyo kukan yaran da ya kaure a dakin Hajara don haka ya mike da sauri Yana fadin
“Hajara baki bata yaran Nan bane ta tafi da su?.
“Wallahi malam bacin Raina bai bari na tuna da su ba sai yanzu da yaron nan ya fara kuka kafin na Ankara da su a dakin kaga yarinyar nan ma ta kama tana taya shi.
“Subhallahi bari ko yar madarar nan ce na Samo a Basu wata kil yunwa suke ji.
“A a malam madarar nan fa itace ta zamo ciwon yarinyar nan har aka daina bata ita .
“To Hajara yaya zamuyi da su ? zamu zuba musu ido ne suna kuka?.
“Malam dole tafiya ta kama mu mu bisu bauci da yaran nan tun Bamu dauki alhakin su ba.
Da sauri Baffa halilu ya koma daki ya dauko makullin motar da ya jima bai tuka ta da kanshi ba sai dai Alabo ya tuka shi da ya koma bauci ma sai dai mutanen arziki su ara su hau shi Baffan ma baya zuwa ko ina daga wurin wiki sai gona amma yau ga dalili yaja zai tuka ta har bauci.
Haka Inna Hajara ta yayo yaran suka dauko hanya tana faman jijjigar su har ta samu sukayi shiru.
Sun iso bauci ne a lokacin da falon daddy yake cike da mutane su Nadiya da mutanen ta da Kuma irin jumurdar da take faruwa ta Abdulhameed bai yarda ba sai an bashi yan biyu.
Inna Hajara ta shigo tana sallama inda idon ta ya fada akan alabo wanda take cike da shi ta wuce inda yake tana fadin.
“Kana nufin ka bashi takardar don kaine uban Mara’s mutunci? Kana nufin a bainan nas ka kayi rashin albarkar da ka tsinto akan titi? To karbi nan karbi yaron nan kai kanka ai kasan kaci uwar karya ka kwana da yunwa tunda aure zakayi Kuma ka datse igiyar ai sai dai ko ka kaiwa uwar matar ka yaron nan ta rike maka shi amma ba binta ba wallahi in kuma ka kuskure zaka hadu da bacin rai karbi na ce maka !
Ta fada da amon sauti yayin da alabo ya karbi khalifa yaron yana tsala kuka yayin da shima alabon yake fidda hawaye.
“Wai da gaske ya bada takardar ne?
cewar Baffa halilu wanda ya shigo yana duban Daddy.wr
“Kai bari na ga idon ashin kirkin ku in ga shegen da zai fuskance ni da ita . Munafukin yaron nan har ya iya irin wannan wulakancin? ni akayiwa haka? .
“Haba Yaya Halilu me ye abin tashin hankali don Allah irin wannan? Yanzu idan dayan su ne ya mutu ku kalubalenci wa? Ku zauna ba case din uba na ne ya dame ni ba irin na wannan yarinyar Daddy ya fada yana nuna Nadiya.
“Kai kenan iro ni kuma ta yadda yaron nan yake Shirin tozarta ni koma na ce ya nunawa duniya babu wanda ya iss da shi to za ayi yadda yake so don ni kam wallahi Zan yafewa duniya shi.
“Haba Yaya halilu me yasa zaku saka jahilci a cikin Al amarin nan? .
“Wannan ne jahilci iro ? To shi meye sunan abinda yayi? Ilimi ko kuwa rashin kirki? cewar Yaya Hajara wacce take ta dauke kwallar idon ta ta kasa hada ido da kowa.
Haj Aliya ce ta ke fadin
“Haba Yaya Hajara don Allah ku sha ruwan Sanyi komai fa yayi zafi maganin sa Allah ne.
“Don Allah kyale Ni Aliya wai komai sai ace Allan bayan mutane shaid’anun kansu ne ? shi yanzy wannan wawan har akwai wani kuskure da za ayi mishi uzuri a nan?.