Skip to content
Part 71 of 71 in the Series Azurfa Da Zinari by Hadiza Gidan Iko

Daddy yayi murmushi Yana fadin

“Ni na fahimci abinda baku fahimta ba Yaya. Amma kuyi hakuri ni da kaina ne zan fahimtar da ku.

“Bama sai ka fahimtar damu ba iro ni na gama yanke hukunci wallahiu kuma a yanzu zan zartar da shi nine ban binta madaurin auren ta to yaron nan sai dai ya nemi mai shayar mishi da dan shi amma binta ba zatayi ba ya kaiwa uwar matar sa kamar yadda Hajara tace koma waye ma ya kai mata. sannan dukkan wata alfarma da kayi mishi sai ya barta wallahi ya fita a dukiyar ka ya fita a gidan da ka saka shi y fita a motocin da ka bashi kai komai sai yaron nan ya barsu wallahi tunda abun duka ba mutunci to zamu k’are ne a rashin mutunci .

Baffa halilu ya mika mishi hannu yana fadin

“Bani makullin motar ka ka kuma bani na gida da kamfani kai hatta Ragunan da kake sakawa sai ka cire su ka bani dan iska marar kirki .

Alabo ya soma laluben aljihu ya futo da key din mota da na gida da na kamfani duka ya mikawa Baffa Halilu yana fidda hawaye yana fadin.

“Baffa don Allah kuyi min afuwa wallahi bani da lafiya ban san abinda Yake damu na ba don Allah kar ku la’ance ni .

Daddy ya karbi makullan yana fadin

“Yaya halilu ni kuma ai nine uban uba na don haka in ka karbe koman shi ni kuma zanyi mishi wata suturar wacce ta zarce wannan . wai duk kalaman yaron nan baku fahimta ba ne? yace muku bashi da lafiya bai san abinda yake faruwa dashi ba ba zaku duba maganar sa ba? To kuyi mishi uzuri baku yi mamakin auren nan nashi da yadda ya taho wuta wuta ba? to na gama gane akwai wani Abu a k’asa to maganin ba zaiyi wahala ba tundw an fahimci ciwon yanzu mu aje wannan matsalar gefe ni na fahimci abinda baku fahimta mu koma ga abinda ya Tara wadan nan mutanen ko baku lura da su bane?.

Sai a lokacin Baffa halilu ya soma karewa mutanen kallo ya ga Nadiya yaga Yan human rights ya kuma ga abdulhameed.

“Me kuma ya faru?

Baffan ya tambaya yana share hawayen idon sa don kuma jikin shi yayi sanyi.

Daddy ya mika mishi takardar da abdulhameed ya bashi ya karba yana dubawa.

“Hakuri na ya kare akan yarinyar nan shine zan bude abunda na rufe a yau yaya halilu ku kun San komai amma ita bata sani ba kuma bata san kowaye Kaisar ba to tunda al amarin ta ya zama haka ni kam na gaji da hadiyar bak’in cikin ta kuma don in nunawa Kaisar da Abdulhameed kowace ce Nadiya da ita ma ta gane matsayin ta in kuma damka ta ga wanda ta fansar da kanta garesu in ma suna ganin zan bisu ne Akan ta sai nace sunyi kuskure gara ma da ta karbi fansa In sun so su bautar da ita ko su sayar da ita a baiwa su rike kudin su duk yayi musu daidai bani kuma da janhuru akan hakan gara ma da Allah ya tara mu duk da taron ba wanda zance mai dadi bane Amma na san kaddarar bawa bata tab’a kauce mishi na kuma karba na kuma godewa Allah yasa wani alherin ne zai same mu ko ya sami uwa ta da uba na.

Kowa ya nutsu yasha jinin jikin shi yayin da Inna Hajara ke ta shre hawaye tana fyace majina da hab’ar hijabin ta . fati da Alabo ma da tasu damuwar musamman ma shi da yake rike da khalifa wanda akace Fati ba zata shayar mishi da shi ba.

Wayar Abdulhameed ce tayi tsuwwa ya kuma duba sai yaga daddy ne wato distinguish Mukhtar Biro.

ya mike ya fita inda Daddy ya karbi khalifa daga hannun Alabo ya mikawa fati yana fadin

“Yunwa yake ji yaron nan bashi yasha

ta karbe shi ta koma ta zauna .

Abdulhameed ya fito inda distinguish yaci burki a kofar gidan Alh iro ya kira wayar Abdulhameed ya fito yana fadin

“Ka fada mishi in bai bayar da yaran nan ba tasa yar zamu dauka? to koma ka fada mishi nazo ya fito in ya kai jan wuya.

Abdulhameed ya dawo yana fadawa daddy ga Daddyn sa yazo.

“Ku shigo kawai ai da Rabon shima zaiji abinda zaiji ku shigo nan.

Abdulhameed ya fita suka shigo tare da distinguish wanda yake fadin

“Iro ba a nuna maka takardar human rights ba ne halan? to yarka ta fansar da kanta ko Ya’yan ta Abdulhameed ya fanso ta don Haka cikin biyu wallahi dole ka dauki daya ko dai ka bani Ya’yan da kayi mini manuba ko kuwa wallahi na sa a rufe yarka tun daga nan har datissara don haka in kana son yarka sai ka bani Ya’yan tunda ai an fada maka mugun abun da ta yi aka Kama ta shine abdulhameed ya fanshe ta daga kisan da ake shirin gabatar mata a yanzu ai ni nayi maka alfarma ba kai kayi min ba tunda kudi na sunyi maka rana.

“Babu ranar da kudin ka zasuyi min biro har Abada kuma yan biyu dai sai dai ka gansu da idon ka irin haka gasu can gun uban su amma ku kam sai dai ko ku mutu da begen yaran nan amma ko a mafarki kuka gansu Allah ya Isa .

“To ni kuma zan rike yarka wallahi duk ranar da ka shirya karbar ta sai ka kira ni ka bani Yan biyu.

“Bari a hado maka kayan ta biro ka wuce da ita na barma ita har a alkiyama ba a fansa ma na baka ita ba a kyauta na baka ita kudin da kuka fanso mata zan iya mayar maku Alamma yan biyu dai albarka wallahi yadda ma aikin Allah ya barranta daga wuta haka zaku barranta da Yan biyu.

“Daddy nayi nadama wallahi a yau Ina jina a tsirara don Allah ka fada min ko ni wacece don zuciya ta tana dab da bugawa na gama gane haye nayiwa ahalin ka Daddy don Allah wacece ni ? meye dangantaka ta da ku ? daddy sanar min asali na tun kafin duniya ta sanar min .

“Dukkan su a nan sun san asalin ki amma ke da Kaisar baku sani ba kuma shima baki san ko waye shi ba duk da na sha fada miki shi din ZINARE ne ke kuwa AZURFA to a yau zaki san waye shi kuma ta Yaya ya zama ZINARE ke kika zama AZURFA? To da ke da wanda bai sani yanzu zaku sani Kuma duk abinda kikaji a ciki da wanda yayi miki dadi da wanda bai miki dadi ba Rayuwar ce tazo da haka .

TUSHEN LABARIN DA ASALI.

“Mu biyu ne iyayen mu suka haifa ni da Yaya na halilu wanda muka zamo yan biyu Kuma sunan mu ma iri daya ne wato ibrahim

“A shekarar 1988 ne muka  sami kammala karatun mu har aka tura mu service wato bautar k’asa inda ni na samu posting nab zuwa garin Jos wato Plato inda na ke koyarwa a makarantar Yan mata ta gaba da primary.

Alh Dan kyana wani shahararren mai kudi ne a garin Jos wanda Allah ya bude hannun sa da zuciyar sa ya zuba masa alheri matuka gaya ya Kuma zama madubi a garin Jos don duk Wanda ya kwana ya hantse a garin Jos to ya San da zaman Alh dan kyana saboda taimakon da Yake da kuma irin alherin da yake a garin Jos har jama a da yawa suke son Alh Dan kyana.

Alh Dan kyana kyakkyawan mutum ne na kin karawa tun a kallon farko zaka fahimce bafullaccen Gombe ne sai dai bashi da tsayi sosai kuma bashi da kiba shiyasa ake ce mishi dan kyana wanda ya zamo almajiri ne wanda yazo almajirci daga gombe aka kawo shi Jos inda yasha yawon almajirci har bauci da Yola amma da Yake Allah shine arrazaku sai ga dan kyana yayi arziki Mai yawa a garin Jos kuma inda ya burge taimako Yake yi a gidajen marayu da asibitoci da tsangayu na karatun Al kur Ani a garin Jos da kuma tallafawa matan da aka mutu aka bar musu marayu. Kai taimako mai yawa alh dan kyana yake yi a garin jos har makotan garuruwan da suke makota ka da jos an san dan kyana an kuma san alherin sa don Sai dai in baiji ana bukata ba.

Ya mallaki kamfunna ne masu yawa na sarrafa fulawa shinkafa takin zamani Kai abubuwa masu yawa har da harkar man fetur Alh dan kyana ya hada kuma dukkan abinda ya saka gaba sai Allah yayiwa abin nan albarka kuma kullum arzikin sa haba ka yake sai dai Allah ya azurta alh dan kyana da mutane mara’s tsoron Allah wanda suke zagaye da shi masu son su danne daukakar Alh dan kyana koma su karbe rahamar da Ubangiji yayi mishi . ga kuma Yan uwan sa da suka kasance yan uba wanda yasha wahalar su amma bawan Allah da arzikin yazo sai ya jawo su a jiki don a tafi tare da su amma abinda Alh dan kyana bai sani ba shine Yan ubanci yayi mazauni a zukatan dangin sa wanda sune suke zagaye da shi kuma basa son yana aikata dukkan wani alheri wa al ummar garin jos ashe suna jin haushi kuma da gaske suke.

Alh dan kyana ya tashi cikin gidan da ake tsantsar yan ubanci domin kuwa ya tashi a cikin yan uwan sa masu tarin yawa don shine D’a na karshe a gidan su wato auta kuma mahaifiyar sa itace mace ta karshe a gidan wacce ta haifi ya’ya uku kuma biyu suka rigaye mu gidan gaskiya tun suna jarirai sai Dan kyana wanda asalin sunan muhd Al mustafa amma tun yana karamin sa ake ce mishi dan kyana har kawo girman sa da kuma daukakar da Ubangiji yayi mishi

Mata hudu ne a gidan su Dan kyana mata uku duk suna gaban mahaifiyar sa don ita mahaifiyar sa an bawa mahaifin sa auren ta ne a lokacin da girma ya kama shi don matan sa duk sun haife ta Ya’yan su ma manya sun girmi mahaifiyar Dan kyana amma duk da wannan fin da sukayiwa mahaifiyar dan kyana da haihuwar ta da sukayi sau fin dubu bai hana su kulla wani irin kishi mai tsanani ba da Yar da suka haifa sama da a kirga

Mahaifiyar dan kyana ta sha wahalar kishiyoyi matuka gaya har zuwa lokacin da tayi haihuwar farko dan ya koma saboda bakar wahalar da ta sha ta doguwar nakuda alhalin matan kishiyoyin ta sun fuskanci nakuda take amma aka kasa samun wadda zata dubi Allah da zuciyar musulunci ta ta taimakawa baiwar Allah nan duk da biyayyar da take musu sau da kafa dukkan kuma abinda za a ce tayi tun daga na sharri zuwa k’age da kutungwila zata bayar da hakuri ba tare da ta musa ko ta karyata ba amma duk da haka Bata barranta daga sharrin su ba bare ranar taimako tazo a taimaka mata

Kwanan ta uku tana fama da nakuda baiwar Allah amma babu wanda yayi nufin ce mata sannu bare taimako

A cikon kwana na hudu ne Alh yaro mahaifin su Dan kyana ya gane Rabi bata da lafiya ai kuwa da Yake mutum ne mai zafi ya shiga fada yana nuna bacin Ranshi ya kuma kira manyan Ya’yan gidan maza Wanda mafi yawan su ma aikatan gwamnati ne wanda su ke daukar takalifin gidan Nasu amma fa iyayen su mata basa son hakan kuma ba don komai suke hakan ba sai don tsabar kishi da mugun hali. Da kafin Rabi tazo yasu yasu ne suke muguntar su . amma lokacin da Rabi ta shigo gidan sai suka mayar da mugun halin su Akan ta saboda suna ganin Alh yaro ya jawo musu abin kunya ya jawo wa Ya’yan sa abin fada ace ya auro yar cikin sa koma jikar sa

Sai kuma ya zamo Rabi ta shigo gidan da sa a wacce tayi sa ar ne tare da kyakkyawan halin ta da dabi un ta wanda yasa dattijon yaji Yana son ta fiye da sauran matan nasa uku da ya kwashe shekarun kuruciya da su Wanda basu da kirki ko na sisi ga mugun halin tsiya wanda suka dora Ya’yan su akai har da yawa daga cikin yaran nashi basu ganin mutuncin sa saboda iyayen su mata sun dora su a keken bera don kawai ya karbi auren Rabi sukace Ina wuta su jefa shi

Al Amarin Rabi mai ban mamaki ne da tausayi domin kuwa marainiya ce wacce ta tashi Babu gata haka kuma marikin nata azzalumi ne wanda ya cinye mata gadon ta da sunan shi yake ciyar da ita wanda yake kanin mahaifin ta inda ta gaji dabbobi da gonaki a gun mahaifin ta Amma kawun ta garbati ya lashe komai kuma Rabi bata samu Rayuwar yanci a gidan kawun ba sai ma takura da tsangwama da tayi ta haduwa da su  amma da Yake Rabin Rabin ce wacce Ubangiji ya azurta da hakuri duk sai ta kawar da kanta ta barwa Allah komai ta ci gaba da karatun ta na boko da islamiya wanda ya fidda ta daga mafi yawa na kunci da takura

Allah gwanin adalci kuma arrahamanu sai ya hada Rabi da masoyi daya tamkar da goma wato Aminu wani ma aikacin banki Wanda Yake son Rabi saboda kamun kanta da sanin mutuncin kanta

Aminu ya soma son ta ne tun lokacin da akayi musabakar karatun Al kur ani mai girma anan  yaga Rabi ya kuma nemi izini wurin kawu garbati wanda yace yazo yar ganta

Tun daga nan Aminu ya fahimci kalar ayuwar da Rabi take ya kuma daura aniyar fidda ta daga damuwar da zata dame ta.

<< Azurfa Da Zinari 70

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×