Rabi ta fahimci Aminu shima mutum ne mai mutunci har ta yarda da karbar soyayyar sa shi kuma ya soma hidimar ta babu gajiyawa har suka so mallakar juna aminu ya fito aka tsayar da magana
Kawu garbati ya soma jan tsaki yana fadin
“Ni fa bani da komai a yanzu na hidimar aure kar ma shegen da ya jira ganin wani abu daga gareni don naji maganganu suna yawo ance na cinye gadon yarinyar nan to dama akwai bashi tsakani na da yaya mu azu dukkan gonaki da dabbobi ma ni ba a biya ni ba tunda duk kudi na shi na bawa don yayi jari ya kuma yi to saura ma na yafe amma duk shegen da yake cewa naci gadon Rabi ya same ni gida don haka ba zan matsawa kaina cewa sai nayi wani Abu ba nima bance ayo min kayan karya ba kunji ma na fada muku.
Kawu garbati ne yake ta masifa lokacin da aka zo kawo mishi goron tuni irin na mutanen da da suke kawowa in biki ya kusa
Rabi dai ba komai take wa fata da buri ba shine Allah ya sa auren ta ya zama farin ciki a gareta ba wata daula ko dukiya ba
Al Amarin rayuwa ma da Yake da ban tsoro kana take shi kuma Allah Yana tasa ashe Ubangiji ya boye gaibun sa bai kuma barwa kowa sani ba face shi din da kansa
Haka aka yi kulla kulla tsakanin mutanen kirki irin malaman Rabi da makotan kirki da suka san Rayuwar Rabi sune sukayi mata kara ta kudade wanda za ayi mata kayan madafi da labulaye da kayan girki amma in ka cire wadan nan kariman mutanen da sukayi don Allah amma kawu garbati da ahalin sa babu wanda yake da niyar bayar da hakin ashana sunyi mursisi ya tusar gaban uwar miji duk sun dage hannu Allah baku mu samu
Al Amarin da ya gigita Rabi ya kuma tabbatar mata da kaddara kowane Bawa da kalar tasa amma da yake tayi nisa a yarda da Allah sai ta hakurkurtar da ranta da zuciyar ta. domin kuwa Aminu yayi mata kayan lefe na gani na fada amma kawu garbati ko tsinken sakace bai tanada da sunan auren ta ba duk da kudaden da ya caji ahalin Aminu amma Aminu yace dukkan komai yayi farko to zai wuce Rabi yake so ba kayan da zasu biyo Bayan ta ba shi da kanshi ma yayi mata tanadi na kayan daki da komai wanda iyaye kewa Ya’yan su Ya’yan ma irin na gata ita kadai yake so a Bashi
Alkawarin Allah mai cika ne Ashe duk abinda ake tayi tsakanin Aminu da Rabi da mai kararren kwana ake yin sa domin ayar ta kullu nafsin za ikatul maut ta gama sauka skan Aminu bawan Allah wanda sai Ranar da za a daura auren su da Rabi ciwon ajali ya sauko mishi yayin da abokan sa suke ta shiri shi kuma zazzabi da ciwon ciki suka far mishi yayinda aka taru wurin daurin aure ana jiran wakilin Ango kowa ya hallara amma babu su babu dalilin su . Ana shirin bin bayan su ne sako yazo cewa Allah Mai girma da buwaya ya karbi Ruhin Aminu ana dab da daura mishi aure
Kawu garbati kam yayi kamar ruwa yaci shi don Yana son ya danne hakkin mamacin nan na kar a nemi ya dawo da abinda ya karba na auren don ya handame komai kuma baya jin zai biya haka ya nemi wanda zaiyi madadi da shi inda Alh yaro mahaifin su dan kyana yazo daurin auren don haka kawu garbati ya kebe shi yana fadin ya taimake shi ya karbi auren Rabi don tunda aka zauna ba za a tashi ba.
Alh yaro ya yarda da hakan a matsayin rufin asiri amma shi kawu garbati yana da manufa manufar sa kuma itace ko da ahalin Aminu zasu nemi a dawo musu da kayan su to Alh yaro Yana da Ya’ya masu kudi wanda ko su sun Isa su biya komai don a nan ma kawu garbati yaso yayi market sai dai abunda bai sani ba Aminu kafin ya bar duniya ya bar wasiyyar cewa dukkan abinda ya bawa Rabi yan uwan sa su bar mata kar su karbi komai hatta da kayan gado da na amfani da ya tanadar mata yace dangin sa su taimaka mishi su bawa Rabi kar su Rage komai kar kuma su karbi abinda ya bayar saboda Rabi marainiya ce kuma babu mai tausayawa maraicin ta sai na Allah don haka yana fatan abinda yayi mata ya zama sanadin Rahama a gareshi da wanna Aminu ya cika da kyakkyawar kalmar shahada .
A take aka daura auren Rabi da Alh yaro inda kuma can Rabi ke kuka da nemawa Aminu Rahama da Aminci. bata shiga wani tashin hankali ba sai da taji madadin da kawu garbati yayi da ita ba wanda ta gane abinda Yake nufi amma ta Roki Allah yasa hakan shine alherin ta da Aminu da Kuma shi alh yaro din
Dangin Aminu kam sun zama mutane domin kuwa sai da aka sami wacce ta tsaya tsayin daka don ganin an bawa Rabi komai da ya zama don ita marigayi Aminu yayi shi . kuma sanin da akayiwa kawun ta garbati na zalunci da kama karya yasa aka tsaya har sai da aka kai kayan Rabi gidan Alh yaro aka kuma danka mata wasiccin marigayi Aminu.
Wannan kaya da aka kawo Rabi da su sune suka tashi k’ura a gidan malam yaro wanda ya ke sanar da matan nasa uku yadda al amarin auren ya taho amma suka ce ina ! akwai kamshin munafunci a cikin maganar sa da Yake Allah yayi mishi budurwar zuciya shine yaje ya auro yar cikin sa koma jikar sa kuma yayi mata kaya na kece Raini.
Tun daga wanna bayani da yayi musu sai suka dauki Karan tsana suka dorawa Rabi wacce take biye sau da kafar mijin ta da abokan zaman ta amma bata barranta daga sharrin su ba bare Kuma Ya’yan su da suke aunawa Rabi zagi koma suce zasu doke ta. amma da Yake ba mai son tashin hankali bace bata ma tsayawa bare ta kula kuma ba zata tab’a fadawa Alh yaro ba bare iyayen su mata da sune suke saka su ko kuma a tsawatarwa yaro ko don goben sa basa yi su kam.
Haka rabi tayi wannan haihuwar ta farko wacce tasha da kyar dalilin doguwar nakuda dan yazo babu rai don ya mutu ne tin a ciki ita Kuma tayi jinya ta warke ta koma hidimar ta amma daga cikin kishiyoyin ta ba a samu wata guda daya da ta yarda da musuluncin ta ba tace mata Rabi ya Kika kara ji da jiki? sannu bata hada su ba amma da yake mai ilimi fitila ne Rabi duk Safiya sai ta zaga dakunan su ta gaishe su in sun so su Ansa in Basu so ba kuma su watsar da ita.
Alh yaro Yana son Rabi musamman yadda take mishi biyayya inyace tayi tayi in yace ta bari ta bari don haka yake mata dukkan abinda take so kai wanda bata ce tana so ba ma yi mata yake sai hakan ya ke Kara Rura wutar kiyayya a tsakanin abokan zaman ta don sun san kudaden da akewa Rabi hidima da su daga aljihun Ya’yan su Alh yaro ke roro su don ma wani abun suna tsoron da da ba haka ba.
A wata shekara ne Alh yaro yasa daya daga cikin Ya’yan sa Wanda Yake babban ma aikacin gwamnati ne yace a biyawa Rabi kujera bana taje ta sauke farali tunda iyayen ku duk sunje sun koma sun kuma je umrah amma banji dayan ku yana nufin yiwa yarinyar nan kara ba duk da irin girmamawar da take muku a matsyin ta na matar uban ku amma take muku biyayya irin ta Yar cikin ku don wanene bata gaishe wa irin gaisuwar da ya’yan ku ma basa muku irin ta to bana so nake a biya mata itama ake kiran ta Haj Rabi.
“To baba in sha Allah yadda kace haka za ayi .
“Yauwa sani Allah ya yi maka albarka ai ka gane ko sani ? Su iyayen ku basu da hankali ne basa son Kuna yin alheri musamman ga yarinyar nan da suke daukar ta kishiya duk basu ganin hidimar da take musu da girmamawar da take musu ni kuma na san halin kows daga cikin su zuciyar yarinyar nan babu mugun nufi a tare da ita to ko babu komai alheri ga mai alheri ai Ramako ne don Allah don ANNABI sani kar ka yarda da yan ubancin da iyayen ku mata suke rura muku ko bayan numfashi na kuyi zumunci Allah zai tserar da ku daga musibun zamani ku Kuma so juna ku taimaka wa Yan uwan ku don dan uwan ka shine yake taimakon ka daga inda wani da ba dan uwan ka ba ya taimake ka to daga Ranar ya zama dan uwan ka don Allah kune manya kar ku bari iyayen ku su zuga ku ku kasa cimma alheri a duniya da lahira kaji na fada maka .
Ina wuta a jefa Rabi jin sani ya biya mata kujera sai haj kaltume uwar gida ta soma tijara da masifa don nemawa kai janhurun masifa wai har da hawan jinin ta ya taso don wahala akayi asibiti da ita amma duka babu abinda aka fasa sai dai Rabi bata huta ba har Allah yayi mata tafiya taje ta sauke farali tayi ADDU A tayi roko ga Ubangiji da yayi Rahama ga ruhin aminu da mumunai bayin Allah da suka rigaye mu gidan gaskiya
Ta dawo makka cike da murna da farin ciki yayin da alh yaro yake duban ta yana tambayar ta yadda ta samu aiki tana sanar dashi komai tayiwa yan gida tsaraba ta kuma yiwa su kawu garbati wanda ya Rufe ta da masifa yana fadin ta zama butulu tunda ta Sami duniya amma ta mance da shi bayan shine yayi mata hanyar arzikin
Kuka tayi tayi baiwar Allah don ba sana a take ba amma kawu Yana ganin tana da kudi bata Aiko mishi bayan ita kadai ta san yadda take Rayuwa a gidan nan.
Ciki na biyu da Rabi ta Samu har ya shiga wata na takwas sahura Yar Haj kaltume da taji abinda uwar ta ta fada mata akan Rabi na karya da gaskiya amma dai mafi muni shine biyan hajjin nan shine karshe don haka a dubu sahura taxo gidan ta kuma Rufe Rabi da duka tana fadin sai dai Alh ya tsine mata amma babu mai hana ta dukan Rabi
Da cikin ta rufe ta da duka bata barta ba sai da taga jini ya tsinke mata kafin ta kyale ta tana haki tana fadin sai ta zamo ajalin ta .
Aka kwashi Rabi zuwa asibiti inda nakuda ta taso mata babu shiri ta haife ban cikin ta wanda yazo shi a wahale don yaxo babu lafiya har ana saka shi a kwalba amma da Yake ba mai tsawon numfashi bane ya koma ga Ubangiji.
Alh yaro da ya zo ya samu labarin komai daga haj gaje mai biwa haj kaltume wacce ta Rattaba mishi komai karya da gaskiya har da karin gishiri don tana son a tadawa kaltume da sahura haxo ai kuwa Alh yaro yace ba zai tsinewa sahura akan abinda tayi ba amma in sha Allah in dai Rabi bata da hakkin ta in sha Allah sai anyi mata fiye da abinda tayi.
Ai kuwa ba a Rufa sati ba mota tayiwa sahura dauka daya daukar da ta karye kafa har ta zamo gurguwar karfi da yaji alh yaro ya soma fadin
“Allah kuma ai ba ya zalunci tunda ya haramtawa kansa shi sai Dan Adam mai karfin hali.
Daga haka magana ta mutu babu wanda ya kuma tayar da ita Rabi kuma ta koma Rayuwa cikin godiya ga Ubangiji wanda dukkan abinda ta gani ta yarda ta amince Rubuce Yake. in ba haka ba ita da ta tsara Rayuwar ta da aminu amma mutuwa tayi Mata shigar sauri dole ta godewa Allah don ta san komai yayi farko karshen sa na zuwa fatan dai Rahamar Allah ta tabbata ga masu I’mani.
Ciki na uku shine Wanda Ubangiji ya zana zai zo duniya duk kulli da kitimirmira da gulma da munafunci da kwainane da makircin masu yi basuyi nasara ba sai da alkawarin Allah ya cika
Ciki na uku shine cikin da aka haifi Alh Dan kyana cikin da aka same shi ya kuma faku har sai da ya kai wata biyar inda kuma akace Wai ba a yarda ba don an gama gane in Rabi ta haihu a gidan nan akwai matsala don haka uwar gidan tsakiyar mai suna Haj hauwa tace bata yarda ba sai dai ko Rabi ko tayi ta Rayuwar ta ita da abinda zata Haifa don haka aka ce ta haihu mu gani .
Sai gashi Allah da iyawar sa ya kaddara zuwan Dan kyana wanda nakudar sa ma ba Mai tsayi Rabi tayi ba sai ga shi ya iso duniya Babu ciwo babu zafin nakuda sai dai kukan sa akaji sai aka rika rige rigen zuwa duba Rabi sai kuma aka ga yaro yana tsala kuka amma babu wacce ta shiga don bayar da taimakon ta ga Rabi ko Dan jaririn ta sai suka yo baya ana mamaki babu wacce ta taimakawa Rabi wacce ko cibi bata iya yankewa ba sai da Alh yaro ya shigo gidan ya samu matan nashi suna kunji kunjin haihuwar ne ya shiga dakin Rabi ya same ta tana Rike da yaron mai shegen kyau wanda kana kallon sa kaga uban sa sak don haka shine ya Kira ungowar zomo wacce ta gyara yaro ta kuma kamawa rabi ta gyara ta inda kuma gida ya dauki maganganun kishiyoyin Rabi amma dai alkawarin Allah baya tashi kuma mai cika ne duk nisan lokaci.