A haka Alhaji dan kyana yaci sunan sa da Ubangiji ya zaba mishi uban sa ya hau Kan layin ya Amsa sunan muhd Almustafa.
Gidan Alh yaro cike yake da Ya’ya Ya’yan da sun cimma arba in muhd Al Mustafa shine na arba in da daya kuma shine na karshe don daga kan shi ba a kuma haihuwa ba .
Dukkan wadan nan Ya’ya da Alh yaro ya mallaka baiji son wani daga cikin su irin son Al Mustafa ba Wanda duk duniya ma ta shaida Alh yaro Yana son Al mustafa abinda Kuma ya Kara assasa kiyayyar Rabi da dan ta Al Mustafa wanda shine yafi kowa shan Wahalar Yan uwa da y’an ubancin su .
A kullum Alh yaro Yana rungume da Al Mustafa kuma dukkan kudaden sa da wanda Ya’yan sa suke mishi kyauta Yana wurin kashe su ga Al Mustafa don haka Al Mustafa ya tashi ba irin tashin da yaran gidan suke ba musamman a kan kayan sakawa da cima komai yake so shi ake mishi amma duk da wannan gatan bai saka shi tashi a sangarce ba yaro ne son kowa Kuma Mai tarbiyar da ke sakawa a so shi Amma kuma a cikin gidan su bashi da kwarjini ko na naira amma kuma ga mutanen waje da aminan Alh yaro Al mustafa abin so ne musamman da Allah yayi shi kyakkyawan gaske don yaro mai kyau abin so ne ga kowa to haka Al Mustafa san kyana yake amma a cikin gidan su kurar da take dawa tafi shi alfarma.
A lokacin da Al mustafa ya soma rarrafe da son ya shiga cikin yara koma ya mika hannu a dauke shi a lokacin ne ya tabbatar da ya shigo cikin ahalin da basa maraba da shi basa kuma nufin sa da alheri bare kuma wata kauna da soyayya amma da Yake rai da alkawari kuma dukkan abinda Allah ya zanawa bawa mai tabbata ne bare kuma Al mustafa da ya zamo kafin Allah dutsen tsakiyar ruwa baka san ana Rana ba kuma kainuwa dashen Allah.
Kalubalen farko na Al Mustafa dan kyana ya fara ne daga lokacin da ya soma rarrafawa yana son shiga cikin yara yan uwan sa koma ya mika musu hannu da son a dauke shi.
Yaro ne mai son ya ganshi cikin Yara koma a dauke shi a fita da shi sai kaga yana ta dariya yana jin dadi ashe wannan shine kalubalen farko a kundin Rayuwar bawan Allah al mustafa dan kyana
Gidan yawa ne gidan su shiyasa Yara kala kala da Yan yara da matasa da manya da magidan ta shiyasa kowa ya mika hannu da nufin daukarb shi zai tafi har ya zamo ashi kyuya kowa nasa ne.
Akwai wani yaro a cikin Ya’yan alh yaro dan dakin Haj gaje ne sunan shi tukuro Dan shekara sha hudu .
Tukuro takadari ne na bugawa a jarida har ana mishi lakabi da shaid’anin haj kuma Yana jin dadin sunan shaid’anin Haj da ake ce mishi don duk wani salo na shaid’anci tukur ya san shi . tun yana karamin sa sosai ya iya tare yara Yana cire musu wando ya saka musu hannun sa a cikin Al aurar su yayi musu wasan banza. An sha dukan sa a makaranta akan wannan dabi ar ta tukuro har ya soma girma ya gane amfanin mace ga namiji ya kuma daura aniyar farke yara mata don haka wannan yaro ya zama majanuni na gaske har wanda ya saka mishi sunan shaid’an baiyi wauta ba don da gaske shaid’ani ne
Tuni turkuro ya gane mace da amfanin ta don haka ya’ya mata suka shiga tarkon sa sai dai in Bai ga wacce kirjin ta ya turo ba amma yanzu ne zai kai hannu ya latsa in ma yana da kudi a aljihun sa zai yaudaro ya kawo daki ya kwanta kuma wai Kar kuce yayi wasu shekaru A a shekaran sa sha biyu zuwa sha uku.
To wannan yaro mai suna tukuro kuma shaid’an shine ya soma ganawa Al mustafa Azaba irin ta silent killer wato a boye
Daga tsaye shaid’an Yana iya daukar Al Mustafa Dan kyana ya sako shi daga tsaye ko ya sako shi ta salla da Kai sai dai Rabi taji yaro ya kwalle da kuka haka zata fita ta dauko shi tana Rarrashin sa kuma abin yaro mai ban tausayi da dariya yana gama kukan kuma zai dafe musu yana dariya haka zasu sakee galla mishi wani rashin I’manin don shaid’an ya san kusfa kusfa ta mugunta da zalunci har ya koyawa yan uwan sa suma suke nunawa yaron nan
Haka tukuro in ya so ketar sa zai saka kafar sa da takalmi mai sawu ya take yatsun hannun yaro Al Mustafa ya darje ya murje duk don cuta da son ya saka shi kuka
Wata Rana da Allah ya nunawa Rabi wata k’eta da mugunta da tukuro yakewa dan ta sai da tayi kuka ta tausayawa Al Mustafa tana jin da tana da wani iko akan Rayuwar Al mustafa da ta sauya mishi ahali da yan uwa ta kaishi cikin Yan uwan da zasu so shi su tausayawa kuruciyar sa da Rashin gatan sa amma ya ta iya da kaddara ? Itama ta Rayu cikin kunci da Rashin gata amma tana wa Al Mustafa fatan aminci da saukin Rayuwa amma ina Alkalami yayi aikin sa har ya bushe babu kuma mai mayar da shi baya.
Al amarin ya bata Mamaki a lokacin da idon ta ya sauka Akan irin muguntar da shaid’an da Yan uwan sa suke wa yaron nata wanda kukan da ya fasa ne yasa ta fito ta Kuma ga abinda Ubangiji ya so nuna mata.
Ya’yan kuka ne masu kama da magarya sune suke gogawa a k’asa sai su nana a jikin yaron Wanda da sun nana yake kwalla ihu Ashe in suka goga Ya’yan kukar zafi suke dauka kamar garwashin wuta sai su nanawa Al Mustafa a fatar jikin shi yana ta kuka amma da ta je ta dauko shi idon ta yana yararin hawaye abin tausayin shine Al Mustafa sai son ya gudu daga gare ta ya koma cikin masu gana mishi Azaba yake yaro mai abin mamaki Al Mustafa.
Ta soma rarrashin sa idon ta taf da hawaye tana fadin
“Al Mustafa kayi hakuri wadan can ba masoya bane amma kuruciyar da tausayin ta a Raina domin Kai ke son su Amma su basa nufin ka da alheri amma ina Roka maka Allah ya baka alherin da suke hana ka ya Raba ka da sharrin da suke nufar ka da shi ya mayar musu da aniyar su.
Idan suka so muguntar su har daki zasu zo suce ta kawo shi in ma ta hana to zai kwalle da kuka dole zata kwanto shi ta mika musu tace Allah ga kayan ka kai kadai ka san Al amarin Al mustafa da yadda zai zama a duniya har ka sako shi cikin wannan ahali nasa
Al Mustafa yasha wahalar yan uwa ko nace Yan uba domin kuwa dukkan jikin sa tabbai ne na irin zaluncin da suke mishi amma dashen Allah ko Babu Ruwa yana huda.
Lokacin da yayi hak’ora wanda in yaji wuya Yake cizo lokacin ne kuma ya tab’a gallawa tukuro cizo Akan matse cibin sa da yayi yaji Azaba sai ya galla mishi cizo.
Cizon da shaid’anin haj yaji shi har cikin kokon Ruhin sa don ko da Al mustafa yake dan kad’an Allah ya zuba mishi karfi irin na mai k’ashi daya don haka ya kafawa shaid’an hak’ora bai saki ba sai da ya ciro wata jijiyar daga hannun sa abinda da yasa ka shaid’an kwalla ihu yana maskawa Al mustafa wani matsiyacin duka don yaji cizon matuka gaya.
Ai kuwa shaid’an hannu ya rure kan kace me? Sai ga kumburi yana hawa hannun dole aka nufi asibiti akayi mishi treat amma duk da haka ya jima hannu bai warke ba tamkar wanda aka Sara da takobi ba cizo ba
Wannan takaicin ne yasa shaid’an shan alwashin sai ya gota yaron nan yadda ya saka shi wannan masifar shima sai yaji a jikin sa.
Hannun tukuro ya jima bai warke ba inda kuma Al Mustafa ya sami sauki duk da bai fasa dafe musu ba don shi ya manta ma da wata wahala da yaji ta matse cibin sa da yayi fatan sa kawai a dauke shi a fita da shi ko a daga shi sama ana tullawa irin yadda suke mishi wasan mugunta amma shi sai yayi ta yage baki yana dariya wai ya samu wasa.
Ranar da shaid’an ya dauki al Mustafa hannun sa ya kama yana fadin
“Kai shege har ka san wannan muguntar ka cije ni don uwar uwar ka ko? Al Mustafa ya yage baki Yana kyalkyala dariya don bai san muguntar da ake shirin yi Mishi ba.
Tukuro ya soma matsa sangalalin hannun sa Yana tama inda zai damka shi kuma Al Mustafa Yana ta dariya har tukuro ya damki gannun da karfi da salon mugunta sai kuwa Al Mustafa ya kwalla ihu ya fasa kuka saboda Azaba.
Rabi ta fito ta karbe shi tana rurruga shi a ranta taji Ina ma zata iya fidda Al Mustafa daga gidan nan? Al amarin yaci ya kare a haka in ma banda kuruciya yaushe ana cutar ka kana nanewa?.
Ganin yadda Al Mustafa yake juya hannun ne yasa ta maida hankalin ta ga hannun nasa wanda ya soma kumburi. kan kace me? hannun ya haye suntum
Dole ta sanar da Alh yaro aka nufi asibiti da Al Mustafa wanda aka gane karaya ce a hannun tuni kuma aka gyara amma fa yasha kuka bawan Allah
Kukan da Al Mustafa yayi Bai kai wanda mahaifiyar sa tayi mishi na tausayawa halin da yake ciki ba amma kuma ta san Al amarin ba a hannun kowa yake ba yana nan hannun Allah sai tayi mishi ADDU AR Ubangiji ya Kare shi sharrin Yan uwan sa.
Tunda aka mishi Daurin karayar nan sai Rabi take goye shi ta zauna a daki don in ta fito yaga yara to zai tayar mata da bula ne Akan ta sauke shi ya tafi wurin su ita kuma tana tsoron su mayar da shi ruwa amma shi in bata sauke shi ba yayi ta kuka yana harba kafafun sa amma ta kance gara kayi wannan kukan na naki sauke ka akan kayi wanda Azaba ce zata saka ka yin wanda yafi wannan.
Tun daga lokacin da Al Mustafa ya gane cizo in yaji wahala sai ya zamo ana cutar sa yaji wuya to zai gallawa mutum cizo cizon da kuma za a jima ba a warke ba.
Alh yaro ya kan dubi Al Mustafa yace
“Mustafa wata rana sai labari kaji ko? haka ANNBIN ALLAH Yusuf ya Rayu cikin tarin Yan Uwan da basa son sa syka kuma cutar da shi amma yaya karshen ya zamo? sune a k’asan sa kuma suna cin arzikin sa saboda daukakar da Ubangiji yayi mishi to kaima sai anyi hakan akan ka Allah ta ala ya tsare ka dukkan sharri ya kuma baka juriya akan wannan Rayuwar.
Haka Rayuwa tayi ta gangarawa har zuwa lokacin da Al Mustafa ya shiga shekara uku kuma a lokacin ne Allah ya jarrabi alh yaro da jinya wacce ya kwanta ciwo ciwon da ya kara nuna mishi ahalin sa da yadda suke daukar sa ya Kuma gane masoyan sa a cikin su ya Kuma gane Wanda suke daukar sa a matsayin makiyin su musamman irin su Haj gaji da kaltume har da hauwa da kuma mafi yawa daga cikin Ya’yan su wanda sai a wuni cur basu leka shi ba bare jin halin da yake ciki.
Rabi ce a tare da shi ta kwashe amai ta wanke bawali ta kuma kama shi zuwa bandaki yayi bukata ta dawo da shi ta bashi ruwa ta bashi magani da dukkan sauran bukatu Rabi ce yayin da Al Mustafa yake katarin uban sa babu wayo bare ya gane ciwo yaci karfin mahaifin sa duk da ya san shine mai bashi kulawa ya kuma bashi dukkan abinda Yake so amma babu hankalin gane rauni na mahaifin sai dai in yaso kayan kwalam na Yara yace a bashi alh yaro Kuma ya dauka ya bashi in ma babu yace azo a siya mishi.
Manyan Ya’yan gidan ne maza suke hidimar magani da asibiti suma wanda iyayen su mata basuyi nasarar hurewa kunnuwan su ba amma wanda sukayi nasara Akan su fa sai dai su leko su wuce
Tamkar Alh yaro ya san ciwon shi ba na tashi bane sai ya soma tattare dukkan kaddarorin sa ya Kuma saka aka siyar mishi da gidajen sa da gonaki ya zamo gidan da suke ciki kawai yayi saura bai siyar ba Amma komai ya siyar ya kuma tara Ya’yan sa kaf maza da Mata ya Raba musu kudaden nan irin kason gado wanda namiji Yake tashi da kaso biyu mace ta tashi da guda daya ya Kuma baiwa matan aure kaso daya bisa takwas a matsyin Nasu
Wannan Al amari baiyiwa su Haj kaltume dadi ba duk da irin Ya’yan da suke gaban su masu yawa maza da mata da suka tashi da abinda yafi na Rabi da danta amma nasu ne ya tsone idon su .
Lallai alh yaro yayi hikima don ya san baya da k’ura zai bari akan kason gadon nan shiyasa yayi shi da Kansa
Allah ya sani yadda alh yaro ya kasa ya bawa su Sani da salisu manyan Ya’yan sa haka ya bawa Al Mustafa. kuma yadda yadda bawa su Haj kaltume haka ya bawa Rabi bai bata abinda yafi nasu ba amma sai maganganun sukayi ta yawo cewa ya bawa Rabi abinda yafi nasu ya kuma bawa Al mustafa kason da yafi na sauran Yara .
Sai kunji kunjin Mata ya tashi ana ta mayar da zancen wanda duka bai wuce yadda za a gallazawa Rabi da danta ba koma a matse ta ta fiddo dukiyar da aka bata ta danne.
Tukuro kam ya shaka ba kadan ba jinn abinda iyayen su suke fada akan rabon son zuciyar da uban su yayi don haka ya soma kulla makirci a Ranshi game da uban nasa.
Rabi dai bata da ta cewa sai dai ta barwa Allah ta kuma nemi tsari daga sharrin mutanen gidan su ta kumayi ADDU AR Allah ya bawa Alh yaro lafiya don in har k’asa ta rufe idon sa s wannan halin hakika ta shiga uku musamman maganganun da suke yawo akan son kan da suke cewa anyi.