Skip to content
Part 75 of 75 in the Series Azurfa Da Zinari by Hadiza Gidan Iko

Ranar juma Alhaji yaro ya tashi jiki ya motsa inda Alhaji Sani ya iso ya sami jikin ya motsa har yana cewa a koma asibitin Amma Alhaji yaro ya dakatar dashi yana fadin

“Sani ai asibiti basu da tasrifin komai sai Wanda Allah yayi don haka ni Kam kuyi hakuri . Ga Amana nan zan baka don na yarda ba zaka tab’a cin amanar ba ga Al mustafa nan ga uwar sa sani na barsu a hannun Allah na barsu a hannun ka in ka bari aka cuce su Kaine ka cuce ni kuma alhakin su zai zama Akan ka.

“In sha Allah alh babu mai cin amanar su na Kuma dauka in Sha Allah.

“To Allah yayi maka albarka yayiwa Yan uwan ka ya juma shiryi Wanda Basu gane ba tun kafin lokaci ya kure musu.

A wannan rana dukkan Ya’yan na Alh yaro sai da ya gana da su yana musu nasiha ya Kuma yafe musu ya kuma bar wasiccin Al Mustafa a garesu a matsayin sa na karamin su ya kuma ce duk wanda yaci amanar sa da shi da mahaifiyar sa to ba zai yafe musu ba.

Wannan wasiccin ma ya kuma tayar da hazo har ya fusata shaid’an Wanda yayi nufin aikewa da uban nasa kiyama don yaci mutuncin Rabi da danta Al Mustafa.

Karfe biyu na dare Allah yayiwa Alh yaro cikawa a hannun Rabi yana kuma rike da nustafa wanda mutuwa batayi musu hanzari ba

Ya cika cikin irin cikawar da kowane musulmi Yake fata wato kalmar shahada ya maimaita fiye da uku kafin Allah ya amshi Ruhin sa cikin sanyi babu magagi babu shure shure. Ubangiji ka azurta mu da mutuwar shahada don mutuncin manzon Allah kayi Rahama ga ruhin musulmi maxa da Mata kasa su cikin aminci.

Wani irin sanyi ya shigi Rabi hawaye take fiddawa tana tuna alherin Alh yaro Wanda kaddara ta hada su a dare daya amma ya mutunta ta ya bata matsayi irin wanda bata zaci samu ba amma a yau Allah ya yankee numfashin sa ya koma gare shi ko yaya Rayuwa zatayi da ita nan gaba kuma?

tana dafe da kumatu tana hawaye tare da jimami sai taga Al mustafa ya mike daga jikin Alh yaro tamkar Wanda aka tsorata ya fita da gudu zuwa waje.

Ta mike tana dauke kwallar idon ta tabi bayan Al mustafa don ta kamo shi.

tukuro da ya biyo dare ya fado dakin Alh yaro ba tare da tunin komai ba ya jawo filo ya danne Kan Alh yaro da ke kwance ba tare da sanin abinda Yake kokarin yi Aya ta gabace shi kullu nafsin za ikatul maut kuma tayi Aikin ta don haka sai tukuro ya danne kan Alh yaro da karfi yaki saki da fatan sai yaji ya daina numfashi.

Rabi da ta kamo Al Mustafa wanda ta kula a firgice yake duk da ta kasa gane abinda ya firgita shi sai ta rungume shi tana tofa mishi ADDU A suka dawo dakin alh yaro inda taga abin mamaki tukuro akan gawar mahaifin sa inda ta gane nufin sa.

Tayi tsaye a bayan shi tana share hawaye har zuwa lokacin da Al Mustafa ya saki ajiyar zuciya inda motsin sa yadawo da tukuro har ya yarda Alh yaro ya daina numfashi ya kuma juyo yaga Rabi zaune ta dafe kanta sai kuma tsoro ya kama shi Amma da Yake ya iya shaid’anci sai ya juya yana shirin fita sai kuma ya juyo Yana fadin.

“Da kin bari naji wata magana ta fito akaina har ke sai kinbi bayan shi inda yaje sai kin gano shi.

Ya fice da sauri yana bacewa daga inda yafi ta inda kuma gaj hauwa ta ga komai na tukuro.

Washe gari gida ya dauka da koke koken mutuwar Alh yaro kuka ake kamar irin na wanda  akewa son nan ya mutu .

Tukuro yana cikin wanda suke kuka da fadar sun shiga uku yayin da haj hauwa ke kallon tukuro Tana son fashewa.

Haj kaltume kuwa da take ta kururuwa babu abinda take fadi sai

“Lafiya lau muke da shi jiya jiya  amma ace yanzu ya mutu ? wane irin ciwo yayi tsakanin jiya jiya da dare zuwa safe ace ya mutu? Me ake son cewa? har ya mutu shi daya babu wanda yaji ko ya nema? To wallahi ban yarda ba sai an fada min yadda akayi mutuwar nan daga shi sai Rabi duka yaushe ne yayi mana Rabon kudi? Kuma sai ace ya mutu?

Sai gaj gaji ta karbe da fadin

“Dole kuwa a tuhumi Rabi tunda tana ganin danta daya mun fita yawan zuria ba dole koma meye zai faru ba? Mu kam mun shiga uku an mayar damu zaurawa an mayar da Ya’yan mu marayu wallahi nima ba zan yarda da wani abu bayan wannan ba dole a tuhumi Rabi.

Sai suka sake kecewa da kuka suna tuma a k’asa suna faduwa wasu ma har da  tashin aljanu.

Aka rufu akan su yayin da ake can ana hada gawar alh yaro nan kuma ana koke koken mutuwar har da tashin aljanu

Aka samu suka sauka sai kuma haj gaji ta mike tana cacumo Rabi tana damkewa take fadin.

“Wallahi wannan makirar ce ta kashe Alh kuma kudin da ya Raba ma in aka matse ta sai ta fiddo wasu.

Haj kaltume ma ta dafa mata suka soma kace nace kamar ba gidan mskoki ba.

Rabi tana rungume da Al Mustafa tana kuka tana jin sharrin da suke shirin kala mata wanda bata da alaka da shi.

Aka fito da gawar Alh yaro aka fice daga gidan yayin da su haj kaltume basu daina cece kuce ba tamkar ba gidan makoki ba .

Kan kace me ? haj gaji da Haj kaltume sun rufe Rabi da duka suna fadin sai ta fadi abinda ta bawa Alh ya ci ya mutu.

Haj hauwa ta mike tana karbar Rabi wacce suka fasawa baki har da yaga mata riga sai kuka take ta na rike da Al mustafa wanda yake ta kuka ganin uwar sa ma tana kuka.

Haj kaltume da Haj gaji suka dubi haj hauwa wacce ta karbi Rabi daga garesu tana watsa musu wani mugun kallo don itama akwai adawa mai tsanani tsakanin su da su haj kaltume.

“Wai ku duk wannan wa azin da ya sauka a gidan nan bai zame muku izina ba sai kun nuna jahilci? to kar wanda ya kuma dukan Rabi idan kunce an kashe Alh a gidan nan ba zan musa muku ba amma ba dai Rabi ba Ina ce a cikin ku har da wacce ta haifi iblis a gidan nan? to ku tuhumi Ya’yan ku in kuma Baku da labari ni Ina da shi ku bari a adawo daga binne Alh ni zan fiddo muku wsnda ya kashe Alh amma Rabi kar wacce ta kuma dukan ta wallahi duk sharrin da kukayiwa baiwar Allah nan kuma duk shirun ta da kawaicin ta baku ji ku tausaya mata ba? dukkan abinda Ya’yan ku sukewa dan ta wace shegiya a cikin ku ta tab’a kawowa kara ? To ya Isa haka.

“Me kike nufi?  cewar Haj gaji wacce ta daki kirji da karfi tana duban haj hauwa.

“Da hausa fa nayi maganar nan har sai an sake tamabayar me nake nufi ? to zan fadi abinda nake nufi in ma baku gane ba jakan mata masu kama da tunkiyoyi ku kam kunfi kama da dabbobi wallahi fiye da ace mutane ne ku anyi muku mutuwa amma tamkar kunzo cin kasuwa? to a biyo ni a sha labari in ma mutum baya Jin hausa zan fahimtar da shi da kowane kalar yaren yake ji wallahi.

Ta fada tana jan Hannun Rabi suka bar wurin ta Kai Rabi daki tana Bata Baki don tausayin ta take ita da Al mustafa. ta  sauya kayan da suka yaga Mata  suka dawo rumfar tsakar gida inda aka kafa zaman makoki yayin da Haj kaltume da haj gaji kuma suka balle hancin tsiya haj gaji na fadin sai anyi mata bayanin da take bukata da kuma zagin wulakancin da hauwa tayi masu sai tabi kadin sa.

Mutanen da suke ta zuwa gidan makokin bai hana su fahimci abinda su Haj kaltume da Haj gaji da ke watsa Rashin mutunci ba wanda suke watsawa Haj hauwa da Rabi wacce ko karar haj ma ba sa mata saboda bak’in ciki.

Al Mustafa yana jikin uwar sa a wannan makoki wanda zaman sa yafi Kama da zaman jiran ta fashe ta kuma fashen din  don babu abinda ake sai tozarta Rabi da danta yayin da manyan Ya’yan Alh yaro mata suke biye a bayan iyayen su mata wurin son wulakanta rabi daidai da abinci wannan sai an nunawa Rabi bare ce ita a gidan sai kuma an jawo abinda za ayi mata habaici ko gori.

Manyan Ya’yan Alh yaro maza sun hada da Alh auwalu Alh Sani Alh salisu Alh Rabiu da alh hamisu alh Hadi Alh nura Alh abubukar Alh Usman Alh Aliyu sai wanda suke biye s bayan su . dukkan wadan nan ma aikata ne da yan kasuwa shiyasa komai akayi a gidan Alh yaro na game da hidimar gida to  sune suke yin sa yanzu ma da suke waje wurin zaman makoki sune komai da ake yayin zaman kuma dukkan su Ya’yan nashi mazan nan da na zano Sani shine wanda ya zamo baya daga cikin halin da iyayen su mata suka tsoma kuma shi din dan dakin haj kaltume ne Yana kuma da kudi sosai . haka salisu shima yana da Rufin asiri shi kuma dan dakin Haj gaji ne yayin da Haj hauwa take da alh nura da Alh hadi suma bakin gwargwado suna da Rufin asiri tunda yan kasuwa ne yayin da su Alh auwalu da Rabi u duk na Haj kaltume ne kuma su irin mazan nan ne masu shiga harkar mata shiyasa suke da kabilanci a zukatan su Kuma in iyayen su mata suka hana su yin alheri ko da Alh yaro yace suyi ba zasuyi ba saboda suna biye bayan iyayen su mata .

A ranar da akayi Rasuwar Alh yaro  da dare bayan kafa ta dauke ne  mutane sun wuce sai yan gidan isu isu  haj gaji ta ta kira alh Rabi u tace ya tattaro mata dukkan Ya’yan gidan don mutuwar Alh ba mutuwa ce ta Allah da ANNABI ba akwai coge a cikin Al amarin amma hauwa tana son fada mata a cikin ya’yan gidan ne wani ya kashe Alh.

Ai kuwa bai tsaya ba ya gayyato dukkan yan gidan inda haj kaltume ma ta mike tana fadin.

“Kai Isa jeka ka kira min hauwa tazo ta fada Mana abinda take nufi da maganar da ta fada  .

Haj hauwa ta fito kafin ma a kira ta don taji abinda ake fada don haka ta fito tana fadin.

“Bama sai an kira ni ba tunda naga kun matsu da neman magana.

Suka zuba mata ido har ta karaso tana fadin

“Kunce a cikin gidan nan ne aka kashe Alh to na yarda amma ba dai Rabi kuke nufi ba? to wanda ya kashe Alh yana nan ciki don haka ya fito tun kafin na fiddo shi in kuma bai fito ba to shaid’anin cikin gidan nan shine da wannan Aikin.

Haj gaji ta kwarawa haj hauwa ashar tana fadin.

“Matsiyaciya ta nan kuma kika hudo ? to na Rantse miki da Allah sai kotu ta Raba mu akan wannan sharrin da kikayiwa tukuro ke baki ga naki shaid’anun ba na cikin dakin ki? Ina ce asiya har cikin shege Kika zubar mata a boye? to in sha Allah zai kinga shaid’ani a haular ki ni ban haifi shaid’ani ba .

Sai ga tukuro ya mike yana kuka yana fadin.

“Ni za ayi wa sharri bayan an ingizani ? to ai saka ni akayi kuma sai ayi min sharri?.

“Kai ya Isa haka don Allah kar ku jawo mana masifar da har gidajen radio sai anjimu Alh dai ya tafi to ADDU A yake bukata ba janhurun masifa ba.

“Ina za a bar wannan maganar? wallahi ba zan kyale wannan sharrin ba kuma bakuji abinda tukuro ya fada ba cewa saka shi akayi? to ku tambaye shi mana wa ya saka shi? kai tukuro wa ya saka ka ka ka kashe alh? kuma me aka saka kayi? .

“Don Allah haj a bar maganar nan tunda ba abin alheri bane .

“Kai hamisu rufe min baki wallahi sai anyi ta bakuji dan uwan ku take shirin batawa suna ba? tashi ka fadi abinda aka saka tukuro kar ka Rufawa kowace shegiya asiri fige ta zigidir.

Shaid’an ya mike yana cewa

“Nifa haj  hauwa ce tace zata bani kudi in naje na kashe Alh a cikin daren jiya shine nace mata ba zan iya ba tace har kudi zata bani in na kashe shi wai yayi Rabon son zuciya to gara ya mutu sai ta tayar da Rabon da yayi tace sai an sake ni kuma nace ba zanyi ba shine fa tace to zata kala min sharri idan banyi ba ai zata saka haruna danta to shine fa tace nine nayi abinda harunan yayi.

Alh sani ya make bakin tukuro yana fadin .

“Rufe mana baki dan iska wannan maganar da jin ta shirya ta kayi ko aka shirya maka waye bai san ka ba akan shaid’anci?.

“Kai sani kar ka kuma dukan sa wallahi uban waye kake nufin ya shirya mishi?  Bakaji abinda yace tace mishi ba?.

Haj hauwa ta saki baki tana kallon tukuro da mamakin wannan makirci da ya shirya ko aka shirya mishi  bata ko shakka uwar sa ce ta shirya mishi hakan.

Wuri ya ya mutse ana ta hayaniya  haj kaltume tana fadin

“Haba gaske matar nan take dukan kirji Ashe ta San tudun da ta dafa to akwai hadin baki tsakanin ta da Rabi duk yadda akayi sunyi wata bak,’ar kasuwa kuma nan gaba kad’an zata bayyana .

Haj hauwa ta mike tana fadin

“Ni nafi karfin nayi muku sharri wallahi amma ga Rabi nan ganin Ido na naga tukuro a dakin Alh ya danne mishi kai da filo kuma ga Rabi nan itama ta gani.

“Ahaf ba gashi ba? dama ba yanzu nace akwai munafunci a tsakanin hauwa da Rabi ba ? to gashi nan suna son cewa tukuro ne ya kashe Alh.

<< Azurfa Da Zinari 74

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×