Skip to content
Part 76 of 78 in the Series Azurfa Da Zinari by Hadiza Gidan Iko

Alhaji Sani ya soma magana yana cewa,

“Gaskiya bana jin dadin irin wadan nan maganganun da akeyi a gidan nan don Allah a barsu bana son jin su koma waye ya kashe Alh mun barshi da fitar Rana da faduwar ta amma saboda Allah ace uban mu ya kwanta ya mutu a yau ko kwana daya bai samu ba amma ace an tashi irin wannan maganar Anya ba abin kunya ake shirin ja mana ba? In na waje yaji haka muce me? to bama son wannan maganar koma waye yaje shi da Allah .

“Kai fa dama ba wani son gaskiya kake ba Sani ta Yaya za a bar irin wannan maganar ace wani wanda yayi shi da Allah? In kai ka yafe sai akace sauran yan uwan ka ma sun yafe? to tunda kai ka yafe ja gefe ka bar wanda bai yafe ba ya nemi hakkin sa ni dama tunda na ga hauwa ta shige cikin lamarin Rabi tayi kuru kuru na san sun kulla wani mugun k’ullin gashi kuma ya fito.

Cewar haj kaltume.

Alh Sani ya dubi mahaifiyar tasa yana fadin

“Haj idan babba bai kashe wuta ba bai kamata ya rura ta ba don Allah a bar maganar nan matukar dai gano wanda yayi abun nan ba zai dawo da Alh ba to in kuka matsa da buncike to zaku binciko abinda ba ku zata ba don ta iya yuwuwar a kusa da ku Abin yake koma a dakin ku to don Allah a bar maganar nan.

“Shin an barta Sani tunda har anzo gabar da kake son karya ta ni  a gaban makiya na amma ka sani hakkin wanda bai yafe ba Yana kanka tunda ka hana yayi motsi kwatar hakkin sa a cikin wanda basu yafen ba har dani a ciki kuwa.

Haka Sani ya kora kowa daga wurin ya kuma ce duk shegen da ya kuma tayar da maganar daga cikin kannen sa zai sha Mamaki.

Kwana ki uku da yin Rasuwar hankalin Rabi da danta al Mustafa ya tashi kallo daya zakayi musu ka san basa cikin hayyacin su babu abinda Rabi take tunani irin makomar ta a gidan Alh yaro . Ba kuma ita take dubawa  ba sai Al Mustafa da take tausayawa fiye da irin tausayawa kanta da take shine abin tausayin tunda babu mai tausayawa kuruciyar sa da Rashin gatan sa .

Ranar da akayi kwanaki bakwai da rasuwar ne Haj kaltume  tace a raba gadon gidan don tana son ta saka Sani ya siye mata  kason hauwa da gaji da  na Rabi a hade mata  tayi kiwon kaji .

Akayi Rabo kowa ya samu kason sa da na Ya’yan sa dakuna da filin tsakar gida da bandaki wasu ma har da Karin wasu sassa na cikin gidan kasancewar gidan Alh yaro  babban gida ne sai dai yawan Ya’yan ki yawan kason ki don haka sai ya zama Rabi itace kawai ta samu kason dakin da take a matsyin tumunin ta da na Al Mustafa. wannan Daki shi kadai Rabi ta tsira da shi babu bandaki babu wata kofa ko da ta kofar gidan ce ta shiga kason haj gaji wacce tafi yawan Ya’ya ta kuma san dama haka suke jira su tozarta ta.

Alh Sani ya shigo kofar Rabi wacce ta tabbatar da sani baya daga cikin wanda suke kallon ta da wani Abu face alheri shiyasa take mutunta shi matuka gaya tun lokacin da ta shigo gidan nasu Bai tab’a mata kallon banza ba don shi tausayin ta ma Yake musamman da yaji dalilin da aka bawa baban su auren ta dalilin mutuwar masoyin ta Aminu kuma ta karbi uban nasu duk da tsufan sa babu raini babu wulakanci . don haka shima sai yake bata matsayin matar uba.

Ya shigo ya samu tana  share hawaye Allah kadai yasan tarin damuwar ta musamman skan al Mustafa.

“Subhallahi haj me yake faruwa? Ayi hakuri haka Rayuwar take.

Shi kadai ne yake mata karar kiran ta da haj.

Ta share hawayen ta tana fadin

“Babu komai baban Fatima ina tausayawa rayuwar Al nustafa ne .

“Kar wannan ya dame ki insha Allah ko bashi da kowa yana da Allah bare kuma gani duk da ba ni da tabbacci akan yau din bare kuma gobe.

“To Nagode baban Fatima dama Ina shirin zuwa gidan ka ne don na fada maka zan koma gidan kawu na tunda nan din dakin nan kawai nake dashi babu kofa babu makewayi  kaga zamu takura shine zan koma gidan kawu na ga kudin nan zan baka ka ajiyewa Al mustafa da wannan dakin da ya gada ka ajiye mishi rai da rayuwa duka suna hannun ALLAH in Allah ya raya shi a siya mishi ko fuloti ne .

“Ba za ayi haka ba haj nima abinda ya kawo ni kenan tunda kinga yanzu su haj suna cewa a ja musu katangu a Raba tsakanin ku alhalin sun san babu inda ko kofar da za a shigo nan  amma ga nan bayan nan na siye shi zan huda miki kofa ayi miki bandaki da sauran wurin amma kar ki bari wani ya san anyi hakan don Allah.

Hawaye ya sake wanke fuskar ta .

“Nagode Baban Fatima Allah ya jikan lahirar Alh da haj ya duba bayan ka .

“Babu komai Nagode.

Haka akayi aikin kofofin su haj kaltume wacce take jiran taji Rabi tace zata siyar da dan dakin da ya zamo kason su don saboda haka dama tace a ja musu katanga don ta san Rabi ko kofar fita bata da ita dole zata nemi mafita in tace zata siyar sai ita kuma haj kaltume tace Sani ya siya ya hade mata ta yadda zata jirga gaji da hauwa sai gashi Taji Wai ana Aiki a harabar da sani ya siya.

Babu shiri ta zagaya bayan inda taga an Hado ta kofar Rabi ana shirin fidda wani gida.

Ta soma tambayar masu Aikin wanda ya saka su suka tabbatar mata da alh Sani ne ya saka su ai kuwa tazo ta figi wayar ta tana kiran shi .

“Kai  wai a me kake kallon  matar can ne? A kan wane dalili kakewa matar nan wannan aikin? me kake nufi ne wai ? ko kuwa kana son nuna min Aman uban ka ne zaka lashe saboda baka da mutunci.

“Haba Haj don Allah kun girma da irin wannan maganar ku daina sakin magana haka kawai wannan maganar ni ta bani kunya wallahi.

“Kai ba wannan na tambaye ka ba naga ana aiki a shiyyar Rabi ta cikin harabar ka meye dalilin hakan?.

“Kudin gadon su ne ta bani tace na siyar mata da adadin inda za a fidda kofa shine na yankar mata  mukayi ciniki ta siya.

“To ban yarda da wannan cinikin ba maza ka mayar mata da kudin ta nata wurin nake so ka siyo min amma wannan harabar bata mallaki kudin siyen ta ba Kuma kai da yake kanka a kulle Yake duk wanna kudin da ta danna maka da sunan siyen fili baka gane hakkin mu ne da ta danne ba? a nawa kudin nata Yake da har take siyen fuloti? to kar ka yarda sani na gane akwai kamshin munafunci a lamarin ka zan baka mamaki wallahi.

Haka Haj kaltume tayi ta tijara tana masifa  har Sani ya dawo ya same ta tana auna mishi harara.

“Saboda Allah haj in ba a tausaya wa matar nan ba sai a barta ta mutu? nifa babu abunda tayi mini Kuma Banga tana muku wata rashin kunya ba.  ta kuma bani kudin ta tace na yankar mata inda zata fidda kofa sai nace ba zanyi ba? yanzu da mukayi ciniki ma kina fadar hakan Ina kuma ga na tausaya mata ko don albarkacin dan ta da ya zama dan uwa na?.

“Kai ya ishe ka haka kaji? Akwai munafunci a cikin maganar nan . don meye yarinyar nan zata zo cikin mu ta rashe? waye   tsarar ta ?wanda ya hada ya kuma  Raba ba sai ta kama gabanta ba? ko kuwa tana nufin yadda kake daukar takalifin gidan nan lokacin Alh yana raye yanzu ma da baya raye zaka ci gaba da hakan? To kar ka yaudari kanka wallahi ko ruwa ban yarda kake siye ba kowace shegiya dan ta yayi mata hidima wacce bata da dan da zaiyi mata hakan ta komawa dangi da Yan uwan ta . Itama waccen kaje kuyi cinikin dakin ta ka siyo min shi a hade min nan ita kuma ta Kara gaba.

“Haj yau Ina Alh da ya tara ku? Babu shi wata Rana muma zamu mara mishi baya  mutuwa fa bata buga kofa haka ma likkafani bashi da aljihu don Allah don ANNABI dukkan abokan zaman ki da wacce tayi miki alheri da wacce tayi miki sharri ki saka mata da alheri  duk ki manta abinda ya faru a baya a fuskanci abinda yayi saura na sauran Rayuwar yanzu dai dubi Alh yau duk fadin duniyar nan babu inda zamu je mu gan shi sai dai mu nuna tudun k’asar kabarin sa to Haj don Allah abinda ya wuce ya wuce .

Fadar hakan kawai sai Haj kaltume ta fashe da kuka tana fadin

“Na shiga uku na lalace Sani ni kake fadawa haka? Eh in ma nema na akayi an same ni  magauta suna shirin cin nasara a kaina.  to  ka shiga taitayin ka don wallahi mun kusa mu samu matsala har ni zaKa cewa nayiwa kishiya afuwa? Ka kuwa san wahalar su da naci ba lokacin kishi ba halan ?  to yanzu ne zan Rama abunda ba zan iya yafewa ba .   babu shegiyar da zan dagawa kafa ko nayiwa sauki wallahi . babu  Alh yanzu  ya bar duniya ba   duk shegiyar da ta ce min kulle zance mata  cass kuma wancan aikin ka mayarwa matar nan da kudin ta dakin ta nake so ka siya min in rika zuba shara a ciki don ta Gane nice saman ta  . itama kuma ta komawa dangin ta koma ina ne ta koma amma bana kaunar na bude ido na na ganta a gidan nan suma saura da sannu zan saka ka siye minn nasu kason don kishiya ta gane nice dai a saman su wallahi . amma sai in  ka yarda nice uwar ka za ayi hakan in kuma ka sauya wata uwar ne da ni sai ka fada min  don na sani .

“Allah ya huci zuciyar ki in sha Allah yadda kike so haka za ayi haj.

“In da yadda nake so kake ai da ba haka ba da duk gidan nan sai an Rika sunkuya mini  ana mini fadanci amma ina fada kana karyata ni ko ince ga yadda za ayi kayi min wa azi sai kace ka fini sanin Allah ne? to tun kafin a haifi uwar mai sabulu balbela take da hasken ta.

“Kiyi hakuri yanzu zan mayar mata da kudin ta in sha Allah dakin nata ma zan siya miki shi .

“To in gani a k’asa shine zan yarda kana son mu Rabu lafiyar.

Ya bata hakuri sosai har ta sauka tana saka mishi albarka da taji zai siyo mata dakin Rabi.

Ya sami Rabi wacce ya fada mata abinda Haj mahaifiyar sa tace amma ya Roki Alfarmar tayi hakuri a madadin dakin ta zai bata gidan sa da yake jajere wanda babu nisa da nan unguwar kuma gidan yafi na su haj kaltume tsari amma kudin su ita da Mustafa zai siya musu floti har ya bukaci da ta kawo kawu garbati ya zama shaida saboda halin Rayuwa.

Rabi tace

“Wallahi ba sai na kawo kowa ba baban Fatima ai kawu garbati idan yaji da flotin nan yana iya cinye shi kai na yarda da kai kaine uban Al mustafa a yau da gobe don haka kar ka bari Al amarin mu ya zama bacin rai ko silar samun sab’ani tsakanin ka da Haj wallahi a kyauta ma zan iya bada dakin nan tunda na San kabari na jira na don haka ni ce da Godiya don kayi min alfarmar da dangi na basu yi min ba.

“A a ba zaki bata a kyauta ba sai dai gidan da zan baki ya zama madadin dakin kin kudin ku Kuma in sha Allah da an samu flotin zan zo na Kai ki ki gani.

Ai kuwa ba ayi sati ba Rabi ta shigo yiwa su haj kaltume bankwana tana fada musu ta saida dakin ta zata koma gidan kawu garbati don alh Sani yace kar ta nuna wa haj kaltume yadda sukayi kawai tace mata ta siyar ne saboda babu kofa kuma babu bandaki dama hakan aka shirya hakan kuma ake so.

Dukkan sashi sashi na abokan zaman nata sai da ta zaga ta sanar da su tashin  nata don fita hakkin makotaka.

Gidan da Rabi ta koma sai ya zamo gobarar titi a jos don Allah yayi nata sakayya da sauri gida abinda ke gida kuma Alh Sani bai fasa bawa Rabi tallafi ba na abincin da zata ci ita da yaron ta Al mustafa bai kuma kasa basu kulawa irin wacce wanda ya karbi Amana yake bayarwa ba . don haka sai Rabi ta kama sana a don yanzu kam aure tsoro yake bata sai ta kama sana a ta siyi fridge tana siyar da ruwan sanyi da kunun Aya almajirai na mata talla kan kace me? Allah ya daga martabar Rabi ta soma kama kudi Al Amura sukayi mata sauki Al Mustafa kuma ya soma samun kulawa ta sosai har Alh sani ya saka shi makaranta nursury yana kuma hidimtawa karatun nashi yayinda zaurawa sukayiwa Rabi caaaa da son su aure ta amma kuma da yawa ta san akwai dalilin su na auren nasu amma ita kam Bata muradi.

Ya akayi? Ya akayi haj kaltume ta samu labarin gidan da Rabi take ciki na Alh Sani ne? sai ga ta afujajen wurjanjan ta iso jajere tana gwama numfashi ta fado gidan babu ko sallama don ji take tamkar ta shake Rabi ta huta da wannan bak’in cikin da sani yake shirin kunsa mata.

Yadda haj kaltume ta fado gidan babu ko sallama tamksr wacce aka jefo daga sama ne   ya firgita Rabi wacce tayi saurin karanto ADDU AR neman tssari kafin ta gane haj kaltume ce.

Ta mike da sauri don da guduwa zatayi saboda a duke take tana zubawa almajiran tallar ta kunun Aya da zobon jinja don haka ta cika fararen manyan bokitai almajiran zasu dauki talla wacce da sun dauka kamar sun juye nan da nan zasu dawo su dauki wani.

“Sannu da zuwa Haj

Ta fada tana shimfidawa Haj kaltume tabarma ta kuma kawo mata zobon jinja da kunun aya Mai sanyi ta aje mata amma bata zaune ba sai karewa gidan kallon take tana mamaki da jin bak’in ciki yana sukuwa a zuciyar ta .

“Kece da sannu ba Ni tunda idon ki ya rufe Kika kasa tuna Sani dan dan Alh yaro ne har kike shirin buga runs dashi to in ma wani siddabarun kikayi mishi nayi miki alkawarin saita ku ke da shi .

“Haj alheri ne ya hada mu kuma shine a tsakanin mu tunda ko Babu komai Mustafa ya zama dan uwan Ya’yan ku. Ba zan iya ce muku komai ba saboda baban Fatima yayi min alheri kuma ko ba komai ni matsayin iyaye nake daukar ku don haka mutumin kirki shine yake kallon kowane mutum a mutumin kirki don haka ni kam abinda ya wuce ya wuce .

“Zage ni kawai tunda babu dama a dake ka koka . “Ke yanzu nan kina nufin wannan gidan shine a matsayin akurkin dakin ki da bai wuce bandaki ba? Sai kuma ance kinci kudin marayu ki kawowa mutane kabli da ba adi kamar wacce aka yaye a gidan bil ama dan ba ura? To ga amana ta fara matsar ki kuma dukkan wani shiri naku ke da sani  ya dawo kunne don haka in har kin san gidan nan na Sani to tattare komatsan ki ki koma gidan garbati ai ke kanki kin san tunda Alh ya mutu to ko tsinke ba zan kuma yarda Sani yayiwa wata shegiya daga cikin ku ba dama na shirya wulakanci mai kalar ruwan omo wallahi Duk wacce tace min kulle zance mata cass don haka kar ki bari na gane bakar kasuwar da kuke Shirin kullawa ke da sani don ni Kam zargin ku nake wallahi.

Haj kaltume ta daga waya ta kira alh Sani tace yazo yanzu yanzun nan gidan Rabi tana jiran shi duk ma abinda Yake ya ajiye shi yazo.

Haka kuwa Alh Sani ya ajiye tarin ayyukan da suke gaban shi ya taho Yana neman tsarin Allah daga wannan kira na mahaifiyar sa don ya tabbatar da ba lafiya ba.

Alh Sani ya shigo gidan ya Tara’s da Rabi tana fidda hawaye ya zube a gaban haj kaltume yana gaishe ta ta soma kare mishi wani banzan kallo mai kama da kana kyankyamin mutum ba tare da ta amsa gaisuwar sa ba.

“Me nake ji a gari yana yawo akan wannan gidan? kaima nan haka da kai ka iya irin wannan Rashin mutuncin na maza? To bari na tuna maka In ka manta kowace ce Rabi matar alh yaro ce wacce ta wanki gawar sa ya tafi kiyama ta kumayi mishi takaba itace kake son cewa wani Abu? kai maza sai a barku da rashin tsoron Allah kam.

Ya dubi mahaifiyar tasa cike da tashin hankali yana fadin

“Haba haj haba haj . Yanzu kece da wannan da maganar? wallahi ban zaci jin hakan daga bakin ki ba shi zato zunubi ne ko da kuwa ya zamo gaskiya na zaci shaidar alheri daga gareki tunda kin san kuruciya ta da samar taka ta duk banyi wani Abu ba sai yanzu da na soma Tara zuria.

“Yo maza har wani tabbacci gare ku? Ai network din layin sadarwa yafi ku tabbas don haka maza ka bani bayani meye gaskiyar abinda nake ji akan wannan gidan? kai yanzu duk wannan bai sa ka gane Rabi ta wawuri kudin marayun Ya’yan mu ba? In da ance an mata sharri yanzu da ta siyi wannan tartsetsen gidan shima bai zama abun tuhumar ba?

<< Azurfa Da Zinari 75Azurfa Da Zinari 77 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×