Skip to content
Part 79 of 80 in the Series Azurfa Da Zinari by Hadiza Gidan Iko

Kwana biyu alhazai suna ta niyyar komawa gida don suna madina ma basu ko baro can ba  Rabi ta soma mura sanadin ruwan sanyi da ta sha ai kuwa mura tace Salamun alaikum . Kan kace me ? Rabi ta soma fita hayyacin ta dole akayi asibiti da ita . Kwanaki hudu Rabi na fama da ciwon da mura ce farkon sa amma sai ga ciwo ya koma na cikin kirji

A cikon kwana na biyar ciwo ya tashi har ana Rufuwa akan ta

Jawahir ce tsaye akan ta duk abinda aka bukata itace duk da mafi yawan magunguna ma kyauta ne

A cikin dare afuwa ta samu ga Rabi har sukayi fira da jawahir wacce take fadawa Nigeria take so ta koma ta gano Al Mustafa don haka daga kwance ta fara shirin samun Visa jawahir na fada mata visa ba zatayi wahala ba masarauta zata kafalshe ta ma a na ta tsaya mata.

  sai dai Ashe  kana taka Ubangiji yana tasa tasa kuma itace tabbas

Lafiya lau Rabi ta kwanta amma tashi sai dai a tashin da gawar ta Al amarin da ya kidima jawahir tana ta kuka don sunyi sabo da Rabi tana jin ta tamkar yar uwar ta musamman idan ta tuna yadda ta rayu

Kuka sosai jawahir take tamkar yar uwar ta haka take jin Rabi amma yaya bawa ya iya da Al amarin mutuwa? ta zama gado in har ana gadar ta mun gaje ta

Allah arrahamanu wanda yayiwa Rabi baiwa ta Rasu a garin manzon Allah aka kuma wanki gawar ta zuwa makabartar bak’i A ALLAH ta ala yasa makwancin GIDAN IKO ya zamo a bak’i A tare da Yan uwa mu sami rabon alherin da Rabi ta samu lallai mai hakuri yana da babban Rabo ga dai inda Rabi Allah ya mata sakayya da alheri ko ba komai tana garin da babu kamar sa a duniya har da lahirar ma .

Jawahir bata da lambar wayar Mariya don haka babu wanda ya Sani sai da suka koma gida ne aka tattare kayan Rabi akayi parking din su inda a wayar Rabi ne aka samu lambar wayar Alh Sani wanda aka bugawa aka sanar dashi

Alh Sani ya samu labarin rasuwar Rabi da inda tayi  rasuwar da suturar da akayi mata a birnin Madina

Jikin shi yayi wani irin sanyi yana jin duniya a bakin komai take ba .

Jawahir ce ta tattare komai na Rabi ta turowa Alh Sani tun daga suturun ta zuwa kayan da ta siya zata zo gida Nigeria har zuwa albashin aikin ta fuka aka turowa Alh San

Alh Sani ya zubawa Al Mustafa Ido ganin yadda yake ta wasan sa cikin yara bai san wani sabon maraicin ya kuma samun sa ba . Tausayin yaron ya ratsa shi ya soma share hawayen sa

Dole alh Sani ya mike ya isa gidan kawu garbati don ya sanar dashi amma akayi Rashin sa a bai same shi a gidan ba sai dai matan sa ya barwa sak’o in ya dawo a sanar da hi rassuwar Rabi

Kawu garbati ya dawo ya samu labarin rasuwar Rabi sai ya kama masifa yana fadin

“To me ya kawo ne nata shi sanin? ko kuwa zaice ba a aiko da sak’o ba? ke zulai maza ki kira min mariya a can makkar kice tayi maza maza taje gidan da Rabi take ance gidan Masa udu ne sarkin makka ko? to maza taje ta karbo Mana dukiyar da Rabi ta Samu in ba haka ba ai a baitul mali za a zuba ta alhalin mu muna nan muna Allah ya baku mu Samu.

Ai kuwa a take aka kira mariya taka sanar da ita abinda kawu garbati ya fada

Mariya hankalin ta yayi matukar tashi jin rasuwar Rabi ba komai take tunawa ba sai hakuri da yakana irin na Rabi da irin abunda kawu yayi mata yanzu shikenan tata ta kare Allah yasa tana cikin dausayin Aljanna.

Mariya ta isa gidan wurin ummu Nauwal wacce ta fada mata sak’on da kawu ya aiko ta ummu nauwal kuma ta fada mata an turo komai nata har da kudin Aikin ta Duka an turawa Alh Sani

Mariya ta dawo tana kiran zulai ta fada mata an turawa Alh Sani komai ai kuwa kawu garbati ya mike yana fadin

“Ni na san akwai manuba a cikin Al amarin nan bari na same shi naji abinda Yake nufi da kawo min bak’in labarin mutuwa amma ya danne kayan mai mutuwa

Alh Sani yazo gida ya fadawa su haj kaltume Rasuwar Rabi haj hauwa ce kawai tayi mata fatan samun aminci a kashewa amma Haj kaltume motse baki tayi tana fadin

“To akan ta aka fara mutuwa ne da kake wani kwaso jiki ka taho kai ga wanda kanwar uwar sa ta mutu? to Allah ya jikan musulmi sai me kake so nace?

Dole Alh Sani ya taso ya dawo gida inda ya Tara’s da kawu garbati ya dake lamba yana jiran dawowar sa .

“Sannu kawu yanzu kazo ko ka jima?

“Nafi awa uku a nan Ina jiran ka dama nazo ne na samu sak’o shine akace har da dukiyar ta aka  Aiko shine na biyo sawu.

Alh Sani ya dubi kawu garbati yana fadin

“Wace irin dukiya kuma kawu? kayan ta ne sai dan abunda ba za a rasa ba muje na bude maka store ka kwashe

Ya bude store inda ya fitowa da kawu garbati da komai na kayan Rabi da wanda zata zo ganin gida amma kudin ta kam bai sanar dashi komai ba don ya san halin kawu garbati sarai kuma ko ita marigayiya ta sanar dashi kar ya sanar da kawun abinda tace a ajiyewa Al Mustafa don babu I’mani s tare da kawu garbati don haka alh Yace yace abinda aka aiko kenan.

Kawu garbati ya soma tijara yana fadin

“In dai anso adalci kayan mamaci na magada ne kuma duk wanda yaci abin maraya to wuta bal bal yake ci .

Alh Sani ya dubi kawu garbati yana fadin

“Haka ne kawu ashe ka san hakan kayi sama da fadi da na marainiya? to ayi ta matashiya ga masu cin hakkin marayu Allah ya sakawa duk wanda aka cuta.

Sai kawu garbati ya balle hancin tsiya yana tijara yana masifa yana fadin

“Kai yanzu nan har kaine zaka fada min haka ? waye bai san abinda kai kayi ba? to har yaron nan Al Mustafa ka bani shi ka kuma damka min kayan gadon sa tunda baka da amana.

“A a kawu Al Mustafa fa ai dan uwa na ne kai kuma a wa zan baka shi ? Da kana da wannan zuciyar zumuncin da akan uwar Al Mustafa zan fara gani smma shi ai nine nashi kai kuma s me kake? Da ka so hakan tun kafin yau ya kamata ace kazo ka duba yaron nan ko da baka bashi komai ba smma yanzu dubi abinda kake cewa na baka shi na baka gadon sa anya ba irin yadda kayiwa uwar sa zakayi mishi shima ba? to babu mai baka yaron nan kawu sai dai ko ka kaini gaban Alkali.

Da haka kawu garbati ya taho yana aunawa Alh Sani zagi kuma haka ya wawashe  kayan Rabi ya kira tani dillaliya ta siye komai ta bashi kudin sa bai kuma bawa kowa komai ba hatta zulai da take ta cewa ya basu suturun Rabi amma duk ya kad’ar da komai ya dafe kudin sa ya watsa aljihu ko naira biyar bai yiwa Rabi karar bada sadakar da zata amfana daga kayan ta da ya kadar ba.

Kwanaki biyu Alh Sani yaga Al Mustafa duk yayi sanyi baya shiga cikin Yara yayi wasa ya jawo shi a jikin shi Yana tambayar sa.

“Al Mustafa me kake so ne?

Ya dago kanshi yana kallon shi kafin yace

“Baba a kaini wurin Inna ta .

Hawaye ya tsinkewa Alh Sani ya rasa amsar da zai bashi amma Dole ya soma Fadin

“Kayi hakuri Al Mustafa mai yankee kauna ta  Raba tsakanin ka da innar ka sai dai ko ka ganta a cikin baccin ka amma kayi mata ADDU A Ubangiji ya fi mu sani akan Al amarin yau da kuma goben mu Allah ta ala ya baka hakuri Al Mustafa ya baka juriya ya kuma sa ka zamo sanyin idaniyar iyayen ka kaji?

Ya fada tana shafa kanshi yayin da yaron yayi shiru ba don ya fahimci abinda ake fada ba.

kwanaki da yawa Al Mustafa yana yawan cewa a kaishi wurin innar sa amma sai hanne da alh Sani su dauke hankalin sa da wata maganar ko abin wasa.

Tun yana maganar har ya daina sai dai Allah ne kadai ya san adadin bege da kewa da yaro Al Mustafa dan kyana yake ciki amma da yake Allah Al musawuru ne sai ya yarjewa Al Mustafa aminci mai yawa ya kuma duba maraicin sa aka bashi baiwar ilimi da karatun Al kur Ani mai girma tare da na bokon abinda ya nunawa Dija Al amarin na Ubangiji ne sai ya zamo ko a cikin Ya’yan nata Al Mustafa yayi musu zarra don one position ne nashi yayin da Ya’yan ta ke dauko bayan bayan sa ta ko ina Allah ya daga darajar Al Mustafa dan kyana inda kuma Dija ta soma Jin haushin hakan Amma Bata da wata hanya da zata nunawa yaron mugunta domin kuwa hanne ta zama uwa ta sosai ga Al Mustafa komai yi mishi take musamman yanzu da ta ta gama tabbatar da maraicin sa gaba da baya wani lokacin ma a cikin kudin da alh Sani yake biyan ta take wa al Mustafa hidima don a danta take jin sa shima  ya Kama ta a matsayin uwa . ALLAH kenan Mai tsarawa bawa Rayuwa . da Rayuwa.ta zama littafi da wani bawa ba zai iya karanta nashi ba sai dai ya rike shi yayi ta kuka Allah kayi mana kyakkyawan karshe duniya da lahira.

Al Amarin yaro Al mustafa sai ya Rikewa Dija makoshi ya kasa wucewa .

Mace ce ita mai mugun son kanta bata so ace a komai an wuce ta sai dai ita ace ta zarce kowa . Sai ta manta da Al Amarin Ubangiji ta kuma manta da yatsun hannu ma ba tsayin su guda ba bare Rayuwar duniya da babu tabbas.

Al Mustafa yaci gaba da zuba baiwar da Ubangiji yayi mishi ta karatu da kokari duk da shekarun sa bakwai amma hatta da Fatima Yar Dija ta farko Al Mustafa yafi ta Sani akan Al kur Ani bare Kuma a koma fannin boko tamkar dai ace yaron yasha wani fahami sai Dija ta gaji da zaman yaron a gidan musamman saukar Al kur Ani da yayi ya shiga hadda yayin da Salim kuma yake a izo biyar .

Alh Sani yayi musu alkawarin duk wanda ya dauko one position a makaranta ya kuma yi kokarin karatun Al kur Ani zai siya mishi keke

Al Mustafa da yayi nasarar dukkan samun wannan kokarin sai Alh Sani ya darzo mishi Keke nai daraja da tsada wanda sai Ya’yan gata domin kuwa keke ne mai danjoji wanda yake sakin wuta ga tsuwwa Yana yi yana fadin thank you Daddy.

Zuwan wannan Keke na Al Mustafa ya ruda Salim da muhd wanda suka tsale da kuka suna tuma suna faduwa a dole suma sai an siya musu irin keken Al Mustafa.

Alh Sani ya kama Salim da muhd yana Rarrashi yana cewa

“Baku ga kokarin da yayi ba ne Salim? Ai na fada muku kuma idan kukayi irin nasa zan siya muku sai ku dage ku bada himma  duk mai son irin keken Al Mustafa yayi karatu sosai kuma kai Al Mustafa da ka gama hadda mashin zan siya maka  Yar besfa.

Ai sai su Salim da muhd suka sake barkewa da kuka suna dira kafa

Dija kam ta gama zuwa wuya don ta gama gane Sani yana son maida Mata Ya’ya baya ya fifita Al Mustafa akan Ya’yan sa

Ta taho da fushin zuciya tana kama Salim da muhd da suke ta kuka tana fadin

“Yanzu saboda Allah abinda kake min a gidan nan akwai adalci a cikin sa ? don menene Zaka siyawa yaron Nan Keke ka hana su ? Har bare yafi dan gida a wurin ka ? To gaskiya ba zan dauki wannan abin ba in dai ba su Duka zaka Siyawa ba to shima wallahi ya zama dole na karbe shi ba zai hau shi ba sai Ranar da ka kawo guda biyu in Kuma ba haka ba wallahi shima sai dai ya xama haramiyar sa don ni bana son Rashin adalci Kai kuma abinda ka iya kenan.

Alh Sani ya dube ta yana Fadin

“Waye baren da kike magana? wai Al Mustafa? To tuna Mana Al Mustafa dan uwa na ne dole ne ya zamo gaba da su salim. kuma meye na Rashin adalci da kike neman yi min Rashin kunya? Ba karatu ne nace sai sunyi kokari ba zan siya musu keke? don Allah ke abin Bai burge ki ba ace wannan yaron ya sauke Al kur Ani? To kar ki kuma yi min wannan wulakancin a gaban yara ba kuma zan siya musu keken ba sai sunyi kokari irin na Al Mustafa.

“Kar Allah ya baka ikon siya musu keke Sani ni ai sai na siya musu tunda ban zama matsiyaciya ba .

“Ko kin siya musu shi  wallahi ba zasu hau su ba sai sun kai limit din da Al Mustafa ya kai na kokari in kuma kika ce Zaki saka hassada nee Ranki akan yaron nan  ki sani dashen Allah ya kamata ace kin gane hakan .

“Ai kuma ba zai yuwu ba wallahi ka rike kudin ka sai na siya musu  Keke kuma babu mai hana su hawan su wannan mulkin mallakar ya ishe ni haka a komai sai ka nunawa Yara banbanci ka fifita Al Mustafa akan su ? To wallahi ba zai yuwu ba na gaji ta ja yaran tana basu hakuri Akan su bari gobe zata siyo musu kekuna.

<< Azurfa Da Zinari 78Azurfa Da Zinari 80 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×